← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 89

Sashe 15

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take irjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga irjinta, da yar ta tattaro jarumtar ha a kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta an gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta arasa turakar Mai martaba amshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye ha inta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba. "Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani aci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya ha iyi ma aci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji sa on kana son ganina." "Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya fa a fuska a ha e kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. irjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina. "Don haka ba ma bu atar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma aya daga cikin akunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa aki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake bu ata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a asa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi da e, Allah ya sani Abubakar ba shi ka ai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin aunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan anci ne a ce jininka zai are rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ru ayya ne na yi maka al awari ko inuwarsa ba za ta ara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..." Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma ta a magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai t a canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tu acin rai. Tana shiga aki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na are ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata ma oshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a angare aya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta mi e ta nufi akin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share wallah sannan fito daga akin. Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi. "Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan acin da ba ki ta a gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa ka ai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole anwar na i ta zubar da makamanta, ta rungumi addarar da ta afka musu babu sallama. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tuna yadda suka kwashe da Takawa, a daren ranar da ta sake zuwa sashensa tana yi masa magiya a kan ya bar Abubakar ya ci gaba da zama a sashenta. Hawaye ya gangaro mata sakamakon ganin wata irin birgima da Abubakar ya fara yi a cikin jar asar da ke akin saboda akunan kowannensu babu da e a ciki. Wata asar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga akin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su fa ar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu. "Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin asa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin asa da murya. "Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ashin asa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arzi in da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na mi a su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya untata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta ta e baki a fakaice. "Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta an sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da wa annan shawarwarin na Jakadiya ba. "Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barba e na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin anonki." A an razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta ha e fuska. "Jakadiya muna bu atar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo. "Sakarai da ba ta gaji arzi i ba kya are a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta fa a cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje. Wacce ta shirya biyan ku in karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* ofa bu e take, za ta iya turowa ta wannan Acc in da ke asa domin free pages na gab da arewa. Wa anda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan bu e group bayan na kammala free pages. *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* *SHU'UMAR MASARAUTA*
Chapter 15 · 0% Book details