← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 89

Sashe 65

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne." Dattijo Maharaz ya furta wa Jawahir. *SHU'UMAR MASARAUTA* *34* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* Tun da suka fara tafiya tsakanin Fargi da Sulaiman babu wanda ya tanka wa aya daga ciki, kallo aya idan ka yi wa Fargi za ka fahimci matsanancin tsoron da take ciki. Har sun kusa fita titi ta waigo a hankali ta furta. "Haka kawai nake jin zuciyata tana bugawa, bugawar da ke alamta mini wata ila wani al'amari ya faru a cikin zuri'ata." "Saboda me kike tunanin haka bayan kin inke duk wata arakar da Shugaba zai iya gano halin da muke ciki?" Sulaiman ya furta yana an dakatar da dokin da suke kai. "Na fi kowa sanin waye Shugaba Zurufu! Na san bibiya da hatsabibancinsa, jikina yana ba ni zai iya banka a labulen sirrina ko ba yanzu ba, kar fa ka manta ni ce mace ta farko da na auri an wata zuri'ar da ba tawa ba, shi ya sa..." Sarki Sulaiman ya katse ta. "Ni kuma ina ji a jikina babu wani abu da zai faru da mu In shaa Allah." "Me ya sa kake da warin gwiwa idan ka ambaci abin bautarku?" Ta wurga masa tambay. "Saboda na gasgata Shi a matsayin Ubangijin sammai da assai." Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da furta komai ba, sannan ya ka a linzamin dokinsa suku fara tafiya. Da fara tafiyarsu babu jimawa sai Fargi ta riki e zuwa surar Tantabara ta ane saman kafa arsa har suka arasa cikin Masarautarsu. Shigar Sarki Sulaiman tare da tantabarar da ke kafa arsa ya sa kallo gaba aya ya koma kansa, duk da ya san Fargi ba za ta ba shi kunya ba amma sai da irjinsa ya buga yana tsoron kada a gane abin da yake tare da shi. "Jarumin Sarakai daga ina ka samu kyautar wannan kyakkyawar tantabarar da ke kan kafa arka? Ta yi matu ar birge ni ka san ni da son tsuntsaye." Mahaifiyar Sarki Sulaiman ta furta a lokacin da ya shiga sashenta ya gaishe ta. Cikinsa ne ya karta don lokaci aya ya ji kansa ya kulle, "Amm... dama.. wani abokina ne ya... mini kyautarta azu." Jinjina kai ta yi sannan ta an ha e fuska babu alamar wasa. "Sulaiman!" Ya ago a sanyaye don ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta i, ya san maganarta ba za ta wuce a kan matansa ba ne. "Yau kwana hu u da aurin aurenka amma babu wani bayanin farinciki da Jakadiya ta sanar a masarautar nan, kasan dai gaba aya idanun masarauta yana kanka ko?" Sai da ya an waiga ya dubi Fargi da ke cikin siffar tantabar, ya an sunkuyar da kai asa yana jin babu da i sannan ya ce. "Allah ya taimake ki kin san tun kafin auren nan ba ni da lafiya, yanzu haka afafuwana ne suka ri e mini shi ne na an zaga bayan gari. Amma In shaa Allahu za a yi abin da ya dace." Amsa masa ta yi sannan ya yi mata sallama ya fice. Kai tsaye turakarsa ya arasa, tun bai arasa shiga ba ya kira Jakadiya ya garga e ta akan baya bu atar ganawa da kowa har zuwa wayewar gari. Inna wuro na kai idanunta kan Kamalu da sauri ta arasa wurinsa ta ri o shi idanunta na zubar da walla, kamar aramin yaro haka ta fara tatta a fuskarsa tana duba jikinsa cikin kuka ta furta. "Kamaluna ina ka shiga? Babu dai abin da yake damunka ko yake yi maka ciwo?" Kamalu ya sake lafewa a jikin Inna wuro tamkar wani zai wace shi, ya aga kai yana kallon Baffajo ya ce. "Inna don Allah ki daina kukan nan kowa yana kallonki." Maganar Kamalu ta so ba wa Dattijo Maharaz dariya, jin yadda Kamalu yake maganar a shagwa "Baffajo bismillah zauna." Sarki Abdul'aziz ya fa Jakadiya na ganin kamar hankulan mutane ba ya kanta ta juya har za ta fita Bamaguje ya katse ta. "Maharaz ka dakatar da Jakadiya za ta ba da shedata." Kallon da Sarki Abdul'aziz ya wurga mata ne ya sa jikinta ya yi sanyi gabanta ya ci gaba da fa uwa, ta koma tsumu ta zauna. Tun da Jawahir ta le o cikin akin Yarima Muhsin ya kasa zaune ya kasa tsaye, wani irin bugu zuciyarsa take yi tamkar za ta yi tsalle ta fa o daga irjinsa. Idanunta a saman fuskar Kamalu ta sake jingina a jikin ofar akin, haka kawai ta tsinci kanta da shiga farincikin da ita kanta ba ta san dalili ba, duk da Kamalu ya kasance abokin fa anta. Kamalu da har lokacin yake gefen Inna wuro ya ago ya wurga mata harara ganin haka ya sa Jawahir ta fara juya idanu tana yi masa fari ha e da murgu a baki. "Jawahir!" Dattijo Maharaz ya furta da arfi, silar haka ya sa ta ago da sauri; karaf idanunsu suka ha u da juna. uri ta yi tana kallon wayar idonsa wani irin yanayi ya fara ratsa ta, irjinta ya shiga bugu da sauri fat fat fat. Tana shirin juyawa ya dakatar da ita. "Ki arasa ki aiwatar da aikinki." Tun bai rufe bakinsa ba Jawahir ta fa a cikin akin, tafiyar da afafuwanta suke yi take son dakatarwa amma tamkar wacce ake fusga haka ta ji ana yin gaba da ita. Tamakar kazar da aka ji a da ruwan zafi haka Jakadiya ta arasa gefe ta zauna jiki a salu e, a madadin aljanin da ke auke da surar Basiru ya koma angaren da Fulani Umaima take sai ya zauna a gefen Jakadiya, suna ha a ido da Dattijo Maharaz ya yi saurin sunkuyar da kai asa. "Buguzu! Me kake yi a wurin nan?" Dattijo Maharaz ya tambaye shi. Buguzu ya sunkuyar da kai asa sannan ya furta. "An dakatar da matata ya za a yi na tafi." Take cikin Jakadiya ya uru ruwa, fargabarta ta ninku gumi ya ci gaba da keto mata. "Wace ce matar taka?" Dattijo Maharaz ya tambaye shi da sauri don a tsammaninsa Jawahir yake nufi. Buguzu ya ago ya nuna Jakadiya ya ci gaba da cewa. "Ga amaryar tawa nan, na ga kun dakatar da ita a hakan ma aga muku afa na yi don akwai babban uzurina da zan aiwatar a daren nan." A razane Jakadiya ta ja baya cikin tashin hankali, har tana fa awa kan Sailuba ba ta sani ba. "Wallahi ni ba matarka ba ce, ba za ta ta a sa uwa ba bindiga a ruwa." "Basiru kana cikin hankalinka kuwa? Jakadiya ce a gabanka idan muka ji makamamciyar wannan maganar ranka zai yi mummunan aci." Sarki Abdul'aziz ya tsawatarwa Buguzu a tsammaninsa Basiru ne. "Wannan fa ba Basiru ba ne Sarki Abdul'aziz! Wannan an autan aljani ne riki a ya yi kamar yadda ni ma na riki e zuwa wannan surar." Inna wuro da Baffajo a tsarace suka dube shi, lokaci aya suka yi fir ai-fir ai da jin kalamansa. an autan aljan fa kace Dattijo Maharaz? Basiru fa nake nufi da yake gefen Jakadiya." Mamaki ya sake bayyana a fuskar Sarki Abdul'aziz bayan ya je wa Dattijo Maharaz tambaya. "Ni ma shi nake nufi Sarki Abdul'aziz, amma mu je zuwa mahaukaci ya hau kura za ka tabbatar da zancena." Jawahir na shiga cikin akin ta ji wani irin dum! Tamkar an buga mata guduma a kanta, hannuwa biyu ta sa ta toshe kunnuwanta sai da ta daina jin ku ar ta cire hannunta. Wata irin ara da araji ta fara ji a wurin rijiyar, a angare aya kuma wani sauti ta ji yana ambatar sunanta sa wata irin murya. A hankali ta arasa bakin rijiyar, ta aga rigarta take tambarin cikinta ya sake fitowa ra au ya yi jajir, haskensa ya mamaye saman rijiyar tamkar an dasa wan fitila. Hannunta ta kai saman cikinta duk da tana jin umin zafin da ke fita daga cikin tambarin bai sa ta sauke hannunta ba, wata irin ara ta sake jin an wallah ta sake kai idonta kan rijiyar da wani ba in haya i ya fara fitowa. Sauke hannunta ta yi ta sa iya arfinta ta bu e rijiyar nan take wani irin auri da ba in haya i ya mamaye akin. Tamkar yadda gajimare yake ara haka ilahirin mutanen da ke cikin akin suka fara jin wani irin rugugi, tamkar aradu za ta fa o musu a tsakar ka. Jawahir ta sauke rigarta sannan ta fito daga akin zuwa rumfa wurin da su Fulani Umaima suke zaune. A wannan karon Fulani Umaima jikinta ya ji e sharkaf da gumi, ga wani irin karkarwa da jikinta yake yi saboda matsanancin tsoron ganin yanayin da za ta yi tozali da Baiwa Maimuna. "Wace ce ita Dattijo Maharaz? Me ta aiwatar a akinmu wanda ya sababba wannan rugugin da ba in al'amura? Shin ko ita ma tana daga cikin zuri'arka ne?" Sarki Abdul'aziz ya yi tambayar a an ru e, don lamarin abin da yake faruwa ya daina ba shi mamaki tsoro yake ba shi. "Ko ka an ba ta daga cikin zuri'armu Sarki Abdul'aziz, bil'adam ce tamkar kai. Hasali ma wannan yarinyar a shekarin baya mun ta a tattaunawa a kanta, idan har ba ka manta hirar da muka yi a kan zuri'ar Rumzu da ake shayarwa da Manyan shanu duk ranar juma'a ba." Sarki Abdul'aziz ya mayar da kallonsa wurin Jawahir da ke tsaye a gefe yam, daga bayanta suka fara jin wani irin taku was kwas kwas tamkar ana taku da takalmi mai tsini. Sautin ba aramin jam hankulan mutanen wurin ya yi ba don haka suka mayar da kallonsu, ita kuwa Jawahir ko motsi ba ta yi ba idanunta sauke a kan Fulani Umaima. Tafe take idanunta a wale, duk taku aya idan ta yi sai wata irin ba ura da yana ta fa o daga jikinta. Kayan jikinta duk sun yi ba i ga wani irin gashi buzu-buzu da ya lullu e ilahirin jikinta. Kallo aya idan ka yi mata ba za ka ta a tsammanin hallitar bil'adam ba ce sakamakom yadda surar jikinta ta sauya, ganin
Chapter 65 · 0% Book details