Sashe 17
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ba zan barka haka ba Umaru dole za mu aiwatar maka da naka tukwici mai tsoka." Umaru ya saki murmushin ya e yana godiya, sannan Mai gari ya sallame shi. Kamar zai tashi sama haka ya arasa gidan yana alla-alla ya auko Jawahir ya kai musu ko ya yarda wallon magwaro ya huta da uda. Masarautar Huddam A ranar da aka kai Abubakar akin da ke angaren gidan ajiya da gyaran hali ko runtse Fulani babba ba ta runtse ba, ba inciki da acin rai ya mamaye zuciyarta. Sai gabannin asuba sannan ta samu hawaye ya zubo mata, zuciyarta cunkushe da acin rai. Wani abu da ya so aure mata kai ganin ta wayi gari lafiya amas babu fitsari a shimfi arta, ba ta ankara da haka ba sai da aka kira sallar asuba da za ta yi wanka kamar yadda ta saba duk asuba sai ta wanke fitsarin jikinta. Amma wannan ranar da ta kwana idonta biyu sai ta ga babu komai a jiki, mamaki cike da zuciyarta ta yi alwala bayan ta gabatar da sallah a gurguje ta nufi sashen da Abubakar yake kwance auke da kayan sawar da za ta sake masa kamar yadda ta saba tsaftace shi. "Waye nan?" Aka furta mata cike da tsawa a lokacin da ta arasa jikin babban auren ofar. Ba in ciki ya kama ta jin antaccan bawa na buga mata tsawa, da ace a sashen ta yake babu wanda ya... "Ina magana waye nan?" Kamalan Dogarin suka katse mata tunani. Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Fulani ce na zo wurin Abubakar." Cikin girmamawa Dogarawan suka zube. "A gafarce mu uwar gijiyarmu, muna neman afuwar sa on da zai fito daga bakunanmu." Zuciyar Fulani ta fara azalzala kamar za ta hudo irjinta, fargabarta aya kada su ce mata wani abu game da Abubakar. "Allah ya taimake ki, ki yafe mu amma Takawa ya ja kunne da kada a sake bu ofar nan har sai hantsi ya aga wurin arfe tara." Da sauri ta dube su. "Yaushe ya bada wannan umarnin?" "Ranki shi da e jiya da dare." Sai da ta ha iyi yawu mai aci sannan ta mi a musu kayan hannunta da akushin abincin da ta taho da shi. "A gyara Abubakar da shi a tabbatar da an yi masa wanka, wannan abincinsa ne." Jim suka yi sannan aya daga cikinsu ya furta. "Allah ya taimake ki koda mun kar i kayan nan sai lokacin da Takawa ya zartar za mu bu ofar, amma a gafarce ni ranki shi da e." Wani irin kukan takaici ne ya taso mata, gudun kada ta bar abin fa a ya sa ta juya da sauri ba tare da ta amsa musu ba. Fulani babba na zuwa sashenta ta fashe da matsanancin kuka, tana tsaka da kuka ta ji Khadija mai kimanin shekara goma sha shida ta dafa kafa arta. "Ummi me ya sa kullin cikin kuka kike? Ummi kin san idanun masarautar yana ko ina a lungu da sa o don Allah kada ki bari a samu a bin fa e, komai ya yi tsanani maganinsa Allah kamar yadda na ji kina fa a. Wuya ba ta kisa na san a kan Sadiq kike wannan kukan don Allah ki kwantar da hankalinki na tabbata babu abin da zai faru da shi." Khadija yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, idan tana magana kamar babbar mace, a hankali ta goge wa mahaifiyarta hawaye ta ci gaba da tausarta har damuwar da take ciki ta yaye. Haka ta ha urtar da zuciyarta har lokacin da ya dace, sannan ta auki kayan da kanta ita da Khadija suka nufi wurin Abubakar. Tun tasowar Abubakar ko da wasa Fulani ba ta ta a yun urin ba wa wata baiwa hidimarsa ba, haka ta sawa ranta har zuwar arshen rayuwarta za ta ci gaba da kulawa da shi ba tare da ta sare ba. A lokacin da suka arasa akin duk da kasancar safiya ce udaje ne suka fara yi musu maraba, a kwance suka same shi kamar yadda Fulani ta bar shi da dare sai dai ya fitsari da kasaye duka kayan jikinsa. udajen da ke kai-kawo a kansa yake aga kai yana cafko duk wanda ya zo hannunsa ya kai bakinsa ya cinye. A fakaice Khadija ta share hawayenta, sannan suka gyara masa jikinsa. Khadija ta kira Baiwa Salamatu ta dam a mata kayan Abubakar don a wanke su, sannu a hankali Fulani babba take ba shi abinci wani ya kar a wani ya zubar bayan sun gama suka tashi suka rufo shi suka fito daga sashen zuciyoyinsu babu da Tsaye take hannunta auke da wata irin shar en tsafaffiyar takobin da Boka Bamaguje ya bata don kare kanta da shi, ta hango urar an matashin yaron ya tunkaro ta da bai fi sa'an Muhsin in ta a shekaru ba, duk yadda ta so hana shi shiga cikin ofar Masarautar Huddan sai abu ya gagara. Ganin haka ya sa ta zaburo da sauri kafin ta aiwatar da abin da yake ranta ya sa hannuwansa biyu ya mauje ta, ta fa asa warwasa. agowar da za ta yi ta hangi Baiwa Maimuna a bayansa tana sakar mata murmushin mugunta, sai wata inuwa da ta gagara tantance wace ce ita. "Ban yafe miki abin da kika yi mini ba kuma sai na auki fansa a kanki." Rufe bakin Baiwa Maimuna ta sa hannu ta fara jan Fulani Umaina a asa kanta sai kurjewa yake jini na zuba, ko da ta hango Bamaguje yana tsaye a gefe yana kallonsu cikin magiya da tashin hankali ta fara ro onsa. "Da kai ka ai na dogara Bamaguje ka taimaka mini za su kashe ni." Wata irin mahaukaciyar dariya ta ga ya bushe da ita, ya juya mata baya ya fara tafiya yana fa in. "Na riga na gaya miki kin yi sake wannan yaron ba kamar an uwansa yake ba." Firgigit Fulani Umaima ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin wa annan miyagun mafarkai nata. Kusan kullin sai ta yi mafarkin wannan yaron yana barazana da rayuwarta. "Waye wannan da yake arin kutsowa cikin rayuwata har yake neman dagula lissafina?" Ta tambayi kanta ba tare da ta san amsar tambayarta ba. irjinta ya buga a lokacin da ta tuna jaririn da baiwa Maimuna ta fitar da shi yana nan a doron asa, " arya ne ba shi ba ne! Ba zai ta a razanar da ni ba." Fulani Umaima ta furta tana kai wa da kawowa. *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* *SHU'UMAR MASARAUTA*