← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi maganar sannan ta mi e kamar ba za ta taka asa ba cikin kariraiya ta fice daga akin. Daga Takawa har Fulani Umaima da ido suka raka ta sai dai kowa da manufar kallon da yake yi mata. Fulani Umaima kallon mamakin kalaman yarinyar ta yi wa anda duk mai hankali idan ya saurara zai fahimci sannu a hankali take isar da sa onta. Shi kuma Takawa kallon shau i da birgewa yake bin Sailuba da shi, take zuciyarsa ta fara raya masa wani abu. Ganin har lokacin hankalinsa na kan ofa ya sa Fulani Umaima ta zungure shi tana fa in. "Ya dai ranka shi da e, me yake faruwa?" "Kin san fa su irin wa annan bayin sai ana bin su a sannu don gaskiya da sauran uruciya a tattare da su." Mai martaba ya yi maganar cikin wayancewa. Ba don Sailuba baiwa ba ce kuma ta san ko a mafarki ba sa'ar tsaran Takawa ba ce da tuni Fulani Umaima ta dasa wani zargi a kanta, amma a cikin zuciyarta take ayyana dole za ta gyara wa yarinyar zama don ta ga raini arara a wayar idonta. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya, tun Jakadiya na jan Sailuba a aikun ranaku zuwa sashen Takawa har ya zamana idan ita ka ai ta je sai ya sa an kira masa ita, haka kawai yarinyar taka birge shi musamma da da an kalamanta da kuma uruciyarta. Fulani Umaima ko ka an ba ta san wainar da ake toyawa ba, don haka tun tuni ta manta da shafinta ta ci gaba da harkokin gabanta. Sai dai ta lura da an ja baya da ta yi Mai martaba ya yi bai cika aikowa kiranta ta taya shi hira ba kamar yadda yake yi a baya. Jawahir ta yi wayo sosai don har ta fara tafiya da afafuwanta a lokacin shekararta aya har da rabi, tana da matu ar shiga rai da saurin sabo da mutane ta saba sosai da su Khadija don a yanzu wani lokacin har kwana take a wurinsu. Ta kama abinci sosai babu abincin da ba ta ci sai dai kuma wani abu da yake ciwa Mai gado tuwo a warya ba bai wuce duk yadda za a ka a a raya da ita ba, ba za ta ta a ci ko shan komai ba ranar juma'a. Kuma har kawo wannan lokacin ba a daima ganin gawar mushen saniya ba ranar Asubahin asabar. Da ta fara kuka kuma sai kunnuwanta su fara fesar da jini, lamarin da a kullin yake sake karya zuciyar Mai gado kenan. Akwai lokacin da wasu Bayi suka ta aukan mushen saniyar suka shiga cikin daji suka fe e ta suka ha a wuta suka gasa kowannensu yanka ai ya ci take cikkunansu suka fashe kayan cikinsu duk ya fito waje, dalilin da ya sa aka gano gawarwakinsu wani matashin Bawa ne ya ce ya ga lokacin da suka wuce cikin daji da mushen saniyar. Wannan al'amarin ba aramin aga hankulan Bayin da ke cikin masarautar ya yi ba, hakan ne ya sake saka su kowannensu ya shiga taitayinsu, tun daga ranar babu wanfa ya sake yin gigin aukan saniyar da niyyar ya gasa don ya kai namanta bakinsa. Watarana Sarki Abdul'aziz ya aika a kira Khadija a lokacin Jawahir na hannunta, duk yadda ta yi ta ajiye ta Jawahir ta i yadda, don haka ta ri e mata hannu suka fara takawa cikin birgewa duk wurin da suka bi sai an bi su da kallo. Suna shiga cikin turakar Mai martaba sai Jawahir ta cake a ta i shiga idanunta sauke a kan shurin da ke cikin uwar akin, da saka hannu tana nunawa ha e da yin gwarancin da ba kowa zai gane ba. Ganin haka ya sa Khadija ta ri o ta sai da yar Jawahir ta shiga duk a tsorace take kamar wani ne yake yi mata garga i. Sai da Khadija ta tsugunna cikin girmamawa ta gaishe da mahaifinta a zuciyarta tana mamakin kiran da ya yi mata. A hankali Jawahir ta tashi ta fara an tsalle-tsallenta a akin dalilin da ya sa ba su bi ta kanta ba. "Khadija mun aika a kira ki ne sakamakon Sarki Gumel Sarki Almustafa ya nema wa ansa Yarima Safwan aurenki kuma na ba shi ke duniya da lafiya." Ko ka an ta so a ce an ba ta za i wurin za ar mijin aure amma babu yadda ta iya musamman da ta tuna matsayin mahaifiyarsu a cikin masarautar. "Godiya nake da za inka ranka shi da e, Allah ja da kwana ya ji an mai Mai babban aki." Murmushi ya sakar mata yana cikin magana suka ji motsin Jawahir ta wuce can uwar akin Sarki Abdul'aziz, a bakin tsohuwar rijiyar ta tsaya ta fara bubbuga murfin rijiyar cikin gwarancin da take yi take fa in. "Afu e... afu e ni ce... danzo ciki, afu e ..." Da sauri Khadija ta auko ta tun kafin su fito Jawahir ta tsanyare da matsanancin kuka tana waiwayen rijiyar da Baiwa Maimuna take ciki. Sarki Abdul'aziz ya sallami Khadija sannan suka fice har bayan wani lokaci ba ta daina kuka ba. "Kin tabbata a kan idanuwanki ya ci wannan tufar da na dam a miki?" "Me za a fasa Inna? Wallahi ita ya fara ci ma." Sailuba ta fa a cike da farinciki. "Haba na gaji da gafara sa ban ga aho ba, har yau so muke ya furta maganar aure amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, don haka na koma jiya na sake kar o miki na sha yanzu magani yanzu. Boka Shaddas ya ce mu bada zuwa nan da kwana biyu." Jakadiya ta arasa maganar tana washe baki. Sailuba ta rungume ta, "Inna ina mai shaida miki matu ar na auri Takawa, zan murzan kambun da har abada Umaima ba za ta murza shi ba, sai na shayar da ita ruwan mamaki daga arshe na nuna mata bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Bayan Kwana Biyar A allah kusan watanni uku kenan da ta lura kullin ala arta da Sarki Abdul'aziz ara baya take, ta sha mamaki matu a duk da ya san cikin da take auke da shi wanda a alla ya tafi watanni biyar, nesa ba kusa ba ya fi ba ta kulawa a lokacin da take auke da cikin Ru ayya amma sai ta yi masa uzuri sakamakon 'yan tafiye-tafiye da yake yawan yi a lokacin. Babban tashin hankalinta bai wuce ganin yadda Boka Shaddas a mafarkinta da har kullin yake yata mata dariyar eta ba. A yau ma da ta ji Sarki Abdul'aziz ya neme ta a turakarsa cike da zumu i ta shirya sai dai tana shiga ta yi turus sakamakon ganin Fulani Babba a gefe ta yi kyau abin ta babu laifi, sai dai zuciyarta cike da fargabar kada fitsarin da ke yoyo daga jikinta ya zubo Mai martaba ya kore ta ko ya yi mata wula anci a gaban Fulani Umaima ba . A wula ance ta dube ta sannan ta zauna can kusa da Takawa tana aga hanci tana basarwa. "To da farko dai, Assalamu alaikum. Mun tara ku ne domin mu sanar da ku wasu muhimman abubuwan akhairi guda biyu. Na farko mun gama yanke magana mu da Sarkin Gumel mun tsayar da ranar aurin auren Khadija da Yarima Safwan ranar juma'a mai zuwa, mun ta aita abin ne sakamakon ana yin auren zai tafi asar Mai duguri harkokin kasuwancinsa, don haka ba ma bu atar ata lokaci. Fulani Babba ta yi shiru a tunaninta Fulani Umaima za ta amsa ta yi mata kara tun da zancan auren Khadija ake yi, shi ya sa ta yi shiru ta yi wa Fulani Umaima kara ba ta amsa ba. "Abu na gaba kuma da zan sanar da ku har ila yau a dai wannan juma'ar ne ni ma zan aura aure da Baiwa Sailuba wacce tuni na 'yantata ta zama 'yar cikin gida, ina fatan za ku ba ni ha in kai domin zama cikin kwanciyar hankali da lumana." Na ce ko akwai mai zuwa mu je dannar irjin Umaima SHU'UMAR MASARAUTA *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* A razane Fulani Umaima ta mi e tsaye jikinta na karkarwa har ta manta da cikin da ke jikinta, baki na rawa ta nuna Takawa don tuni idanunta suka rufe har manta matsayinsa a gare ta. "Me kake fa a? Ka na nufin Sailuba baiwar gidan nan? Sailuba antacciyar baiwar da ba ta isa a 'yantata ba? Wallahi ba ka isa ba, ba zai ta a faruwa ba, kai da arin aure har abada." Cikin zuciyarta Fulani babba ta saki murmushin mugunta don ko ka an auren Takawa bai a ta da asa ba, tun da ta san da ita da babu a gidan duk aya ne ba ta saura fada a wurin Takawa. "Fulani ya kamata a san a gaban wanda ake magana, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan aci, zan zartar miki da mummunan hukuncin da ba ki ta a tsammani ba. Na 'yanta Sailuba domin ita ce za ina wacce zuciyata take da mura in shimfi a rayuwar aure a tare da ita." Sarki Abdul'aziz ya furta cike da tsare gida. Kamar butum-butumi haka Fulani Umaima ta zuba masa idanu don gani ta yi ya koma mata kalarsa ta ainihi, a an tsorace ta dube shi tana maimaita kalamansa a fili cike da mamaki. "Ina taya Mai martaba murna da fatan alheri a kan tagwayen labaran da ya sanar da mu masu auke da farinciki, ba tun yau ba na san kai jajirtaccan gwarzon mazaje ne. Allah ya baka ikon kwatanta adalci domin kai in mai adalci ne, kuma na tabbata za ta ci gaba da adalci kamar yadda kake yi a kodayaushe. Shigowar Sailuba cikin zuri'arka babban alkairi ne da ke tattare da faranta rai Zakina, na san ko mata ari a tara maka ba za ka ta a za ni kunya ba." Fulani Babba ta yi maganar cikin sanyin murya da karyewar zuciya tana
Chapter 31 · 0% Book details