← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 89

Sashe 52

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara ja baya, don haka ba ta kawo komai a kanta ba tun da a yadda ta lura hatta mahaifinsa ya fara sauya masa ba ita ka ai ba. Mahaifiyar Sarki Abdul'aziz ta rasu da watanni uku Sarki Usman, Fulani Rabi'atu da Fulani Asabe Allah ya yi musu rasuwa sakamakon hatsarin da ya afka musu a hanyar su ta zuwa gaisuwar mahaifin Fulani Rabi'atu da ke masarautar Nabaldu, wannan mutuwar ba aramin faranta ran Umaima da mahaifiyarta ta yi ba don a yadda ta fahimta Marigayi Sarki Usman yana matu ar son Fulani babba da 'ya'yanta. Kuma ta lura yana yawan yi wa Sarki Abdul'aziz kutse a cikin sha'anin mulki don haka bayan mutuwarsu ta ci gaba da cin karenta babu babbaka a cikin Masarautar Huddam. Jawahir har ta nufi sashensu na Bayi sai kuma ta yi turus tana tunanin abin yi don haka ta rasa yadda za ta ha u da Kamalu, dabara ce ta fa o mata da sauri ta saka aramar butar a cikin mayafinta ta aure ta tamau ta aure mayafin a ugunta ta yadda ko ka kalle ta ba lalle ka fahimci da wani abin a jikinta ba. Kai tsaye ta nufi sashen Inna wuro tana an kalle-kalle ko za ta gan shi amma ba ta ga Kamalu ba, don haka ta arasa akin Inna wuro ta same ta ta fito hannunta auke da kayan wankin Kamalu. "Inna sannu da gida! Kamalu ba ya nan ne?" Turus Inna wuro ta yi mamakinta ya bayyana a fili don ta san Jawahir da Kamalu ko ka an ba sa jituwa tamkar mage da era, ganin haka ya sa Jawahir ta an sosa kai a kunyace. "Yawwa dama Bala ne ya aiko ni na duba masa shi ko yana nan, shi ya sa na tambaye ki Inna." Inna wuro ta saki murnushi ta ce. "Yawwa ko da na ji, shiga ciki yana aki na ji dai ya ce fita zai yi." Inna wuro ta yi maganar tana wucewa, Jawahir sai da ta tabbatar da Inna wuro ta fita sannan ta kunto butar hannunta ta fa akin a lokacin Kamalu ya shirya cikin kayansa na Bayi da alama wani wurin za shi. Ba ta tanka masa ba don haka kai tsaye ta mi a masa, Kamalu na kai idanunsa kan butar ya ji wani irin yaaaammmmm kamar kiyashi na yi masa yawo a jiki. "Ta mece ce wannan?" "Idan ka kar a za ka san ko ta mece ce." Jawahir ta furta masa a ta aice tana bin sa da harara, ba don tana gudun mummunan hukuncin da matar nan ta mafarkinta ta ce za ta yi mata ba me zai kawo ta gaban Kamalu. Sai da ya saki guntun tsaki kamar ba zai kar a ba sannan ya saka hannun hagu ya kar a a yatsine. Jawahir tana mi a masa ta juya ta fice, take jikinsa ya auki karkarwa gumi ya shiga keto masa. Kansa ya ji ya yi masa nauyi dum kamar an ora masa dutse, don haka ya tsugunna ya sanya hannuwa biyu ya toshe kunnuwansa. Tamkar wanda ake hajijijiya da shi haka ya ga akin yana juya masa, ya jima a cikin wannan yanayin sannan ya ji tamkar ana fisgarsa don haka ya fice daga cikin akin har lokacin hannunsa auke da butar. "Ka yi gaggawar zuwa ka ora ta a saman gidan tururuwar da ke kallon shurin uwar akin Sarki Abdul'aziz." Kamalu ya ji an furta masa a cikin kunnuwansa. Cike da warin gwiwa ya damke butar, kai tsaye ya wuce sashen Sarki Abdul'aziz. Shugaba Zurufu ya jima a halwar tsafinsa yana bincike game da Sulaiman da Fargi, yayin da ya ci karo da wani aton haske mamaye da duka tauraronsu. Duk yadda ya so gano ainihin mene ne sai ya gagara fahimtar komai, sai dai jikinsa yana ba shi akwai wani sabon al'amari da zai faru a nan gaba wanda yake ji ba zai zame masa alheri ba. "Fargi babu ke babu yi wa yaron nan aiki wannan umarni ne nake ba ki ba shawara ba, don haka kada ki ulla wata ala a da shi." Shugaba Zurufu ya furta wa Fargi a lokacin da ya kirata. "Saboda me Shugaba? Ina ganin aikinsa ba aiki ne mai wahala ba." Tun da Fargi ta zo duniya wannan ce maganar ja'in'ja ta farko da ta ta a shiga tsakaninsu, don haka Shugaba Zurufu ya sake kafe ta da idanu yana yana nazartarta. Ganin haka ta sa Fargi ta nemi yafiya a wurinsa sannan ta nuna masa ba za ta sake shiga sabgar Sulaiman ba, amma a asan zuciyarta ba ta jin za ta iya yanke ala arta da shi sakamakon ba on yanayin da ya ratsa zuciyarta. Tun daga wannan ranar sai ya zamana Fargi ta yi takatsantsan wurin gudanar da mu'amala a tsakaninta da Sulaiman, tun suna mu'amala a matsayin zumunci har ala arsu ta fara riki ewa zuwa soyayya. Kuma duk wannan soyayyar suna gudanar da ita ne a masarautarsu Sulaiman a sirrance ba tare da wani ya sani ba, a duk lokacin da ta so ziyartarsa kai tsaye take riki a zuwa siffar tantabara sai ta sauka a wurin sha atawarsa. Shi kuma Sulaiman yana ganinta yake shaidata don haka suka gina soyayyarsu mai arfi ba tare da mutum aya daga cikin zuri'arta sun fahimci haka ba. A duk lokacin da ta tuna babban zunubi ne wani daga cikin zuri'arsu ya ulla soyayya da wani jinsin da ba nasu ba, sai hankalinta ya kai matu olokuwar tashi fargabarta bai wuce kaca su kashe ta ita da Sulaiman ba su soke gawarsu a jikin bishiyar abar bauta. Duk da a kan idanunta Jakadiya ta aiwatar da abin da Boka Shaddas ya saka ta amma har lokacin babu walwala a tattare da ita. Duk yadda Jakadiya ta kai ga son lallashinta da ban baki tuni Sailuba ta yi nisan kiwon da ba ta jin kira. "Inna yau ita ce rana ta farko da na yi da-na-sanin aurena da Takawa, don Allah yanzu Inna wacce irin riba muka samu? Tun d aka yi auren nan babu kwanciyar hankali daga wannan sai wannan, tura da kai ni bango gaskiya zan je na nemi takardar saki a wurin Takawa idan ya so na samu Umaima ta karya duk wani kaidi da ta ulla mini kin ga na yarda wallon mangwaro dole zan huta da uda..." "Dakata mini sakarya mara sanin kishin kai." Jakadiya ta katse Sailuba a hassale. "Kina son ki zubar mini da ima a wurin Umaima ne? Wallahi idan kika aikata wannan anyen rashin hankalin sai na tsine miki albarka, domin da ki watsa mini asa a gaban Umaima gara ki watsa mini a idon duniya." Jin haka ya sa Sailuba ta sake fashewa da matsanancin kuka. Tashin hankalin Fulani Umaima ya sake ninkuwa sakamakon jin motsi a uwar akinta, da sauri ta le a ciki amma babu kowa don haka ta koma ta zauna ta rafka uban tagumi. Babban abin da yake sake ci mata tuwo a warya bai wuce yadda a kullin kusancinta da Takawa yake sake nisanta ba, ta lura tun bayan rasuwar Fulani babba ba ya ta tata da kullin maganarsa tana kan Abubakar. A angare aya kuma ga yama, da hantarar da yake yawan yi mata, ta lura hatta Sailuba da take oyi tana zubar da ruwa mai wari ba ta fuskantar tsangwamar da take fuskanta a wurinsa, sai dai ita ma Sailuban ba wani shirin arzi i suke yi ba don ta ji labarin ko zuwa sashen Takawa ta daina yi. Ita kanta ganin cin kashin ya yi yawa ya sa ta janye jikinta gefe har lokacin da za ta shawo kan matsalar gaba aya. "Me ya sa matsalolina suke rikitowa rayuwata a daidai ga ar da na ci burin cin duniyata da tsinke tsire, a lokacin baya babban tunanin Fulani babba ce matsalata amma me ya sa bayan na kawar da ita sai matsaloli suke sake kunno mini kai?" "Saboda kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Kuma duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba ta shi ko umi ba za ta yi ba, ai tarin masifa da bala'in yanzu kila fara gani Umaima." Jakadiya ta katse Fulani Umaima rai a "Wa ya kasa da ke ballantana ki auka, don Allah Jakadiya ki je ki ji da matsalar gabanki. Kada ki yi la'akari da halin da nake ciki don kowa ya biya allonsa wankewa yake." Fulani Umaima ta arasa maganar tana shigewa uwar aki, don yadda zuciyarta take a dagule ba ta jin za ta iya biye wa Jakadiya. Jakadiya ta ja guntun tsaki sannan ta fice daga akin. Tunanin Fulani Umaima kacokan ya tafi a kan yadda za ta kawo wa Bamaguje yarinyar da ya bata umarni, lokaci aya ta saki shu'umin murmushi da wata shawara ta fa o mata. Da sauri ta fita ta sa aka kira mata Uwar Bayi ta bata umarnin a tattara mata 'Bayi yara da manya domin a fa arta za ta 'yanta yaran Bayi goma iyayensu biyar. Nan take babu jimawa Uwar Bayi ta tafi sashensu na Bayi ta sanar da sa on Fulani Umaima, cike da murna Bayin suka fara tururuwa suna taruwa a babban filin harabar masarautar suna jiran fitowar Fulani Umaima kowa a zuciyarsa yana fatan Allah ya sa yana daga cikin masu rabon da za a 'yanta. aya bayan aya haka Fulani Umaima ta sa aka diga wucewa da Bayi ko za ta yi tozali da ita amma ko mai kama da ita ba ta gani ba, don haka cikin yanke auna ta za i wa anda suke da rabo a gurguje ta nufi sashenta don a wannan karon ta yanke shawarar zuwa wurin Bamaguje don ta gaji da jegon jakar da take yi babu dare babu rana ba tare da biyan bu ata ba. Tun bayan da Jawahir ta kai wa Kamalu butar hannunta ta wuce sashensu na Bayi haka kawai take jin tamkar ta sauke wani babban nauyin da yake kanta, a lokacin da ta koma Mai gado ba ta nan don haka ta an sha ragowar kokon da ta rage sannan ta koma ta kwanta tana tunanin rayuwa. Duk yadda ta ji Bayin sashensu na tururwar
Chapter 52 · 0% Book details