← Book details Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 89

Sashe 41

Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake mahaifiyarta ta ora ta a turbar zuwa wurin Bamaguje take ya yi mata binciken abin da za ta haifa wato 'ya mace ce, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ba ta damu ba take ganin tamkar dama ita ake jira ta zo cikin masarautar ta haifo Yarima mai jiran gado. Hankalin mahaifiyarta da ita kanta bai gama tashi ba sai lokacin da ta shafe sama da watanni ba tare atan wata ba, kamar ha in baki suna cikin fafutukar neman magani sai Fulani Asabe ta zo mata da maganar da ta nemi girgiza hanjin cikinsu. uri shugaba Zurufu ya yi wa Fargi da ke hannun mahaifinta sannan ya nuna wani farin kaskon arfe da ke tafarfasa da ruwan zafi, da hannu ya nuna masa kason sannan ya furta. "Ka ajiye ta a nan domin na tsaurara bincike a kanta." Babu musu mahaifinta ya ora ta a saman ruwan zafin ta ci gaba da mutsu-mutsu, sannan Shugaba Zurufu ya ebo wani jan gari mai ha e wa ansu gajerun asusuwa ya watsa mata. Wani haske ya gani ya gifta masa, sannu a hankali hasken ya dusashe sai wani zanen farin doki ya bayyana a saman goshinta. Da sauri Shugaba Shaddas ya saka hannu a saman goshin nata domin ya kwashen fararen taurarinta, bai yi tsammani ba ya ji wata irin haniniyar doki a saman kansa. Da sauri ya waiga bai ga komai ba don haka ya sauke ajiyar zuciya a kasalce. "Al'amarinta daban yake, na lura da ba on lamarin da ke tattare da ita. Akwai aukaka marara gushewa domin sanin kanku ne tsafi ko sihirin da ya shafi dawaki alheri ne. Don haka ina mai yi maka albishiri da kar ar wannan yarinya a matsayin waccan zan horar da horarwata ta musamman, na yi maka al wari matu ar ta samu horon daga gare ni za ta maye gurbina da duk wata gawurtar tsafina. Yanzu ina bu atar ka auke ta zuwa gaban abin bauta don samun albarka mafi girma daga gare shi." Zuciyar Mahaifin Fargi fes ya kar e ta ya fice da ita zuwa wurin abin bauta. Kafin wani lokaci tuni labarin karamcin da Shugaba Zurufu ta yi wa Fargi ya watsu, sai girma da mutumcin mahaifinta ya sake lullu e idanun al'ummar Rumzu. Suka ci gaba da yi masa fadanci kowa na son nuna kulawa a gare shi, a angare aya kuma Shugaba Zurufu ba aramin mamakin lamarin yarinyar ya yi ba, don haka ya ullo da wannan dabarar da rainon ta a hannunsa ko ba komai zai samu damar shiga halwar tsafinsa don ya kwashe tarin arzi in da ke auke a cikin rayuwarta. Zuciyar Mai gado ta gama karyewa cikin imauta da tashin hankali ta arasa wurin Fulani babba ta rungume ta tana sakin kuka cike da tausayi. A wannan lokacin Fulani babba ta gama galabaita numfashinta ya fara sar ewa cikin haki sama-sama ta furta. "Don Allah... ki kira mini... Takawa." Da sauri Mai gado ta mi e jiki na rawa ta fice da niyyar zuwa sashen Takawa, a babban tsakar gida ta ha u da Fulani Umaima saboda tashin hankali ko lura da ita ba ta yi ba. "Keee! Zo nan." Fulani Umaima ta kira ta, fuska auke da hawaye Maigado ta zube. "Ki mini aikin gafara ranki shi da e Fulani na cikin wani hali ta aika na kira mata Takawa cikin gaggawa." Sai da Fulani Umaima ta an waiga hagu da dama sannan ta furta. "Bayan ke waye ya san da wannan maganar?" "Daga ni sai Jakadiya, amma ita tuni ta fice ta mu wuri." Maigado ta yi maganar a gaggauce. "Yau Inna wuro ba ta jin da i don haka ki wuce ki gyara mini akina." A firgice Mai gado ta ago. "Ranki shi da e idan na dawo daga wurin Takawa kenan?" Harara Fulani Umaima ta wurga mata kamar idonta zai fa asa. "Maza ki wuce idan ba so kike na zartar miki da mummunan hukunci ba." Mai gado ba ta da za i don haka ta mi e ta wuce sashen Fulani Umaima tana zubar da walla. "Mutuwa zan yi don Allah ki kawo mini Abubakar na yi masa kallon arshe." Kalaman Fulani babba suka dawo cikin kwanyarta tamkar a lokacin take furta mata su. Jingina ta yi da bango tana sharce walla, sannan a gurguje ta arasa aikin tana fitowa ta samu Fulani Umaima a rumfa (Falo) har afa aya kan aya. "Idan kin kammala ina bu atar tausa afafuwana tsami suke yi." A wannan karon Mai gado amsawa ta yi a hankali don ta fahimci inda Fulani Umaima ta dosa. Sai bayan lokaci mai tsawo sannan Fulani Umaima ta sallami Mai gado, cikin zuciyarta tana yin dariyar eta don ta san ha arta ta kusa cim ma ruwa. Cikin sauri a an gurguje Mai gado take buga auren Takawa, sakamakon ta yi dace sashen na shi shiru babu Fadawa a ciki. Ta jima a tsaye har tana shirin juyawa ta ji Mai martaba ya bu e, da sauri ta zube a asa tana haki. "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai, Fulani babba na son ganawa da kai..." Tun ba ta rufe ba ki ba ya katse ta a tsawace. "Ba ma son shashanci a matsa daga gabanmu a ba mu wuri idan ba haka ba za mu ata muku rai. A ce mata ta yi ha uri zuwa dare za mu araso aki mu ji abin da yake damunta." Daga haka ya rufe ofar ba tare da ya sake jin ta bakinta ba. Hannuwa biyu ya sa ya dafe kansa yana jin damuwa na mamaye shi. "Shin abin da na ji daga wurinsu Inna wuro ne ya tsaye mini a rai ko mene ne?" Kamalu ya tambayi zuciyarsa. "Ba tun yau na so sanar da kai oyayyun sirrikan da ba ka san da su ba, na jima da fara yi maka hannunka mai sanda amma na lura har yanzu ba ka ankare da ni ba. Kada ka ji aci don sun sanar da kai gaskiyar abin da suka sani, su ba iyayenka ba ne kamar yadda suka sanar da kai. Sai dai ya zama dole a jinjina musu sakamakon namijin arin da suka aiwatar game da rayuwarka..." "Ya aka yi kasan wa annan kalaman, alhalin daga ni sai su muka tattauna su? Me ya sa a kullin kake neman dulmiya ni cikin kogin tunani? A yanzu haka zuciyata ta yi nisan kiwo wurin zabarin mafitar da za ta dasashen acin da ke cikin zuciyata. Na jima ina ora ayar tambaya akanka amma wani tsagin na zuciyata na garga ina a kan abin da nake zargi." Kamalu ya yi m aganar cikin damuwa. Dattijo Maharaz ya dawo gaban Kamalu yana murmushi, "Na so a ce ka jima da fa awa kogin tunani akaina, sai dai yanzun ma ba a makara ba, duk zargin da za ka yi ina son ka yi shi a kan zato na alkairi." Shiru Kamalu ya yi bai tanka masa ba yana nazartar kalamansa. "Ka biyo ni zan wuce da kai ta wani sirrintaccan zaure matu ar ka amince mini a yau zan sanar da kai ainihin wane ne ni da ala ata da wannan Masarautar." Kamalu kamar ba zai bi shi ba sai zuciyarsa ta ingiza shi suka fara tafiya kai tsaye suka nufi babban sashen Sarki Abdul'aziz ta angaren sashen da yake makwaftaka da su Ciroma da Galadima. Cikin matsananciyar damuwa Maigado ta koma sashen Fulani babba a lokacin Abubakar yana kwance yana yin gwarancinsa, kallonsa ta yi zuciya a karye ta fa akin Fulani babba. Daga can gefenta ta tsugunna ta ora hannunta a saman na Fulani babba, "Allah ya taimake ki na je Takawa ba ya nan." Ta samu kanta da sauya kalaman sa anin abin da Mai martaba ya gaya mata. Hawaye ta gani na gangarowa daga idanun Fulani babba, Mai gado ta sunkuyar da kai asa hawaye na zuba. Wani tunani ta yi da sauri ta arasa ta samu Baiwa Zainaba suka shiga akin Abubakar suka fito da shi hannuwansa auke da mari, akin Fulani suka shiga da shi Mai gado ta zaunar da shi a gefen gadon da take kwance. Da wayar idon Fulani babba suka lura da irin kallon da take bin Abubakar da shi hawayen idanunta na sake aruwa. Hannu ya kai saman fuskarta yana jijjigawa yana dariya, take Mai gado da Zainaba suka fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sororo ya yi ya fara kallonsu bayan wani lokaci ya sake kai hannu kan hannun mahaifiyarsa yana ago ta alamar ta tashi. Motsa baki ta fara yi Mai gado ta matsa gabanta da sauri ta kara kunnenta a wurin bakin Fulani babba. "Ga Abubakar nan...don Allah ki kula mini... ki kula mini da shi... Duniya da Lahira... na mallaka miki shi... Mai gado mutuwa zan yi, irjina ciwo yake ki danne mini shi." Cikin kuka Mai gado ta sa hannuwa biyu ta danne irjin Fulani babba. "La'ilaha'ilallahi... Muhammandur... Rasulillah..." Fulani Babba ta furta cikin sar ewar murya idanunta a kan Abubakar numfashinta ya fara yin sama daga arshe ya auke. "Ranki shi da e! Ranki shi da e!" Mai gado ta furta a firgice tana jijjiga Fulani babba, a sanyaye Baiwa Zainaba ta arasa ta rufe wa Fulani babba idanu ha e da jan zani ta rufe mata fuska. Da ar ta zauna a gefen gado kamar ha in baki ita da Mai gado suka rushe da wani irin sabon matsanancin kuka. "Mai gado duk ranar da na ga Abubakar ya warke sai na 'yanta ba yi goma, kuma sai na raba dukiyata biyu na bayar da ita sadaka." "Mai gado kin san rannan mafarki na yi wai Abubakar da Yaya Halima sun warke, kin ga dai a cikin mafarki ne amma wallahi kar ki ji farincikin da na ji." "Da Allah ya sa Abubakar lafiyayye wallahi babu abin da zai hana ban ha a shi aure da Jawahir ba, saboda jin Jawahir nake tamkar 'yar cikina." "Tsakanin ke da Abubakar ban san wanda ya shiga tsakanina da 'yata Jawahir ba, ta shafe kwanaki ban ganta ba an ya Mai gado ba a matsa wa Jawahir da aiki kuwa?" "Wani abu ne yake damuna Mai gado, na san dai
Chapter 41 · 0% Book details