Sashe 57
Shu'umar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haka ba muna zaune za ki kunto mana masifar da za ta nemi ta gagare mu." Da kai Jawahir ta amsa sannan Mai gado ta sake ficewa daga akin. Sarki Abdul'aziz ya shafe sama da minti biyar a tsaye yana juya kalaman Dattijo Maharaz a cikin ransa, a angare aya kuma zuciyarsa na yun urin amincewa da abin da kunnuwansa suka ji. "Ta yaya zai zama jininka bayan ba ka ta a saninsa a cikin 'ya'yanka ba?" "An ya Dattijo Maharaz ba yaudararka yake son yi ba?" an mutum a ce anka ne kamar a mafarki, idan anka ne wace ce uwarsa? Kuma a yaushe aka haife shi?" Tarin tambayoyin da Sarki Abdul'azi ya dinga yi wa kansa kenan amma ya gagara samar wa kansa amsoshinsu. Da yar ya iya jan shanyayyun afafuwansa ya koma rumfa (Falo) ya zauna ya rafka uban tagumi. "Yaron nan makusancin Masarautar nan ne, anka ne, jininka ne kuma Magajinka ne." Kalaman Dattijo na baya suka dawo masa ra au a cikin kunnuwansa. Sallamar da Jakadiya da wasu 'yan matan bayi suka ne ya katse masa tunanin da yake yi, a sanyaye ya ago ya dube su hannuwansu auke da manyan tire sai a lokacin ya tuna da shirin tarbar Sarkin Bahdi wato Sarki Sulaiman bn Abdulwahab. "Barka da hutawa ranka shi da awisu mai yawan Ado. Allah ya ja zamanin Mai martaba, sukari ba ka yi farin banza ba bangon zuma kowa ya ra e ka sai ya lasa." Jakadiya ta yi maganar tana yi masa jinjina da hannu, sannan ta ci gaba da cewa. "Allah ya taimaki Mai martaba ya ara wa Sarki lafiya. Sarki Sulaimanu na asar Bahdi ya samu ikon arasowa." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'aziz ya sauke a sanyaye ya furta. "Jakadiya a sanar da Shamaki a ba wa Sarki Sulaimanu kulawa kafin mu araso, me aka zube a gabanmu haka Jakadiya?" Jakadiya da hankalinta ya tafi wani wurin sai a lokacin ta lura da kuskuren da ta tafka, abin motsa bakin da za ta saka Bayi su kai masaukin ba i sune ta sa suka ebo suka kawo sashen Takawa. "Allah ya taimake ka abin saukar i za mu kai sashen Ba i, shi ne muka biyo don mu sanar da kai isowar Sarki Sulaimanu." Jakadiya ta yi maganar cikin wayancewa. "A ba nu wuri Jakadiya." Sarki Abdul'aziz ya furta a ta aice. Da sauri suka mi e gaba aya suka fice. Jakadiya na kammala abin da yake gabanta cikin zumu i ta wuce sashen Yarima Muhsin don ta cim ma ku irinta a kansa. "A iya tsammanina Yarima ya fi arfin kowacce yarinya a ciki da wajen masarautar nan, kaicon wannan rana da na bu e ido na ga hawaye a idanun Yarima domin wata 'ya mace." A sanyaye Yarima Muhsin ya ago yana kallon Jakadiya ya sake sunkuyar da kai asa. "Ka share hawayenka Yariman masarauta, Sarkin gobe da yardar Allah. Ba Jawahir ba ko wacce 'ya kake muradi In shaa Allahu sai ka mallake ta Uban akina." "Jakadiya dama sunanta Jawahir?" Jakadiya ta yi murmunshin yin nasara. "Kar i wannan fura ce na dama maka ita mai sanyi ka sha ko zuciyarka ta yi sanyi Uban gidana. Sunanta Jawahir kuma sunan Mahaifiyarta Mai gado, yarinyar tamkar 'ya ce a wurina don haka kuwa da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne. Ni nan zan wuce maka gaba har gaban Takawa a game da aurenta matu ar hakan zai faranta maka." A fili Muhsin ya saki murmushin farinciki. Ya mi a hannu ya kar waryar hannun Jakadiya, ta zauna a gefe suna hira yana sha har ya shanye furar tass. "Ka shanye wayayen abin da za ka haifa Muhsin, ka gafarce ni ba da kai nake yi ba da mahaifiyarka nake yi don haka dalili ne ya sa aikina ya biyo ta kanka. Al awarin na auka ko zan tafi tsirara sai na cusa wa Umaima acin rai a zuciyarta, ka yafe ni Muhsin kai da ganin an cikinka sai dai a lahira idan ana haihuwa a can." Jakadiya ta wassafa wa annan kalaman a zuciyarsa har sai da murmushinta ya bayyana a fili, ta kar waryar wurinsa ta yi masa sallama ta fice zuciyarta fes. *SHU'UMAR MASARAUTA* *30* *Littafin ku i ne 500 idan kina bu ata za ki biya ta wannan Account in Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* A lokacin da soyayyar Fargi da Sulaiman ta yi arfi sai ya zama hatta wa ansu sirrikan na al aluman tsafi da sihiri Fargi ta fara koya masa, don ma Yarima Sulaiman ya kasance matsoracin gaske shi ya sa ba ya iya gudanar da wani aikin kai tsaye. Fargi ita ta yi tsayuwar tsayin daka ta yi wa Sulaiman aikin da zai gaji karagar mahaifinsa, sai dai tashin farko Mahaifinsa sai da ya aura masa aure da 'ya'yan abokansa biyu sannan aka yi bikin na in sarautarsa. A wannan ranar Fargi shiga daji ta yi cikin firgici da tashin hankalin da ba ta ta a tsammani ba, shi kansa Sulaiman bai ta a tsammanin haka daga wurin mahaifinsa don sai da ya ji a duniya dama bai ta a samun karagar mulkin ba a rayuwarsa. "Ban san me ya sa Takawa zai raunata zuciyata ba." Sabon Sarki Sulaiman ya furta a lokacin da ya ratsa cikin ungurmin dajin da Fargi ta ke e kanta a ciki. "Ya aka yi ka san ina wurin nan? Me ka zo za ka yi mini kai da kake da sabbin mata har biy..." Da sauri ya sa hannu a bakinta ya katse ta. "Ke ka ai ce matata! Da ke zuciyata ta saba kuma har abada da ke za ta rayu. Ban san so ba sai a kanki, ban ta anarsa ba sai da kika lasa mini zumarsa. Ke zuciyata ce, zuciyar da a duk bugun numfashi take jerenta hawa da saukar farashin aunarki a zuciyata. Fargiii!" Sulaiman ya furta da wani irin yanayi. A sanyaye ta ago ta dube shi nan take idanunta suka sake cikowa da wallah. "Ban ta a sanin haka soyayyarka ta yi tasiri a zuciyata ba Sulaiman, ina yi maka son da har abada ba na jin akwai hallitar da za ta yi maka kwatankwacinsa. Ina kishinka sai dai a yanzu ka yi mini nisa." Kuka ya an ci arfinta sai da ta yi mai isarta ta ci gaba. "Ka yi mini nisa Sulaiman, nisan da ba na hangen akwai ranar kusantowarsa. Kwatankwacin nisan da sararin samaniya ta yi asa. Yanzu shi kenan ka zama mallakacin wasu soyayyarka ta tashi a banza..." Kukan da ya kwace mata ne ya gayyato ha oranta suka datse harshenta, ta dur ushe a asa tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin zuciya. Da sauri Sulaiman ya ru o hannun Fargi ya fara janta har sun fara nisa ta an dakata tana tambayarsa. "Ina za ka kai ni?" "Zan kai ki a aura mana aure a yau in, domin ba zan iya rasa ki ba. Ba zan iya mallaka wa wa ansu kaina ba ke ba, ba zan iya sadaukar da komai nawa ba sai a kanki." Fargi ba ta amsa ba ta ci gaba da bin sa tamkar ra umi da akala. Sarki Abdul'aziz ya fito fes cikin asaitacciyar alkyabba sai baza amshi yake yi, sai dai ga duk wanda zai yi masa kallon urulla zai fahimci akwai wani abu da yake damunsa a asan ransa. An cika gaban Sarki Sulaiman da kayan ciye-ciye da kayan ma ulashe, da fara'a Sarki Abdul'aziz ya shiga akin saukar ba in suka shiga gaisawa cikin karamci da mutumta juna. Sarki Abdul'aziz ya girmi Sarki Sulaiman nesa ba kusa ba sai dai kasancewarsa mai sanin ya kamata da girmama na gaba, uwa-uba dattako da sanin mutumci an adam ya sa ta su ta zo aya shi da Sarki Abdul'aziz. Don haka a wannan karon Sarki Abdul'aziz yana zaune takarda ta iso daga asar Bahdi a kan Mai martaba Sarki Sulaiman zai kawo masa ziyara a kan muhimmiyar maganar da za ta kawo shi. "Allah ya taimaki Uba kuma shugaba a gare mu Sarkin Sarakuna Sarki Abdu'aziz." Wata irin izza ce ta sake kanainaye Sarki Abdul'aziz, ya saki murmushin gefen baki. "Da alama Sarki Sulaimanu da tsokana a kalamansa." Sarki Sulaiman ya saki murmushi sannan ya ci gaba da ce wa. "Kuma a ha anin gaskiya tsokana ba ta cancanci giftawa ta gaban mutanen da suke shirin zama surukai." Sarki Abdul'aziz ya girgiza kai yana dariya don Sarki Sulaimanu mutum ne mai barkwanci. "Ranka shi da e magana ta gaskiya neman iri ne ya kawo mu wurinku, idan babu damuwa ina son ha a aure da an wurinka Yarima Muhsin da 'yar wurina Raihan! Saboda ina kwa ayin wannan zumuncin namu ya sake arfi har cikin zuri'armu. Amma fa idan babu takura ranka shi da e, idan kuma akwai sai mu yi wa fatan kowa Allah ya ha a shi da rabonsa na alheri." Tun Sarki Sulaiman bai gama maganar ba Sarki Abdul'aziz ya saki murmushin farinciki. "Mun yi murna da wa annan kalaman naka Mai martaba, kuma mun amince da wannan maganar ko bayan ranmu wannan maganar ba za ta ta a sauyawa ba. Ba don kada na yi azar i ba, da sai na ce wannan auren a aura shi a ranar juma'a mai zuwa." Cikin farinciki Sarki Sulaiman ya amsa wa Sarki Abdul'aziz sannan suka ci gaba da tattaunawa a kan muhimman batutuwa dangane da yadda auren zai kasance. Daga arshe Sarki Sulaiman da Sarki Abdul'aziz suka tsayar da ranar aure makwanni hu u masu zuwa. Sarki Sulaimanu ya yi wa Sarki Abdul'aziz sallama da shi da Bafadawa da 'yan rakiyarsa suka koma Masarautarsu ta Bahdi cikin matsanancin farinciki. Inna wuro tun da yamma ta arato take saka ran ganin Kamalu amma babu shi babu alamarsa, tun tana tsammanin ko wani aikin ne ya ri e su har ta fara shiga damuwa. Ganin su Salisu abokan Kamalu sun dawo hakan ya sake firgita ta, musamman da ta tambaye shi Kamalu gaba aya suka shaida mata rabonsu da shi tun da safe. A imauce Inna wuro, Baffajo da sauran tsirarun Bayin suka shiga cikin Masarautar suna nemansa amma babu