Sashe 95
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Babu mutane sosai a k'ofar gidan amma duk da haka motar tasa na daga can gaba hanyar wata kwana da mutane basu fiye zama ba.
Sai da ta k'arasa sannan ta fahimci motar Sa'id ce bak'a wuluk mai d'auke da tinted glass a jikin tagogin, tayi kokarin bud'e k'ofar gaba amma taji ta a rufe gam saboda haka ta dawo ta bud'e baya.
Sanyin AC da kuma tsadadden k'amshin nan nasa suka fara yi mata maraba kafin siffarsa, da alama daga can guest inn d'in da suka sauka yake don yayi wanka ya canja manyan kayan daya yini dasu zuwa wani 3-quater wando sak irin socin sojoji da kuma bakar T-shirt mai laushi data kama jikinsa, Ya Allah!
Ita kam tun kayan rana ne a jikinta.
Kansa a jingine yake saman kujerar ya rufe idanunsa, kuma bai bud'e su ba har bayan shigowarta, a haka ya amsa sallamar da tayi.
A lokaci guda ta fahimci akwai abinda ke damunsa, ba dai gajiya bace don ta san wannan d'an taron kawai ba zai jijjiga shi ba.
"Daga wani waje kake ne?" Ta tambaya jin bashi da alamun magana.
Yayi murmushin jin muryarta kafin yace.
"Eh na koma masauki nayi wanka ne."
"Kaci abinci?"
Sai ya d'ago da kansa a lokacin ya kalle ta, amma bayan kyakkkwar fuskar ta har yanzu akwai wani jan haske da yake gani a gefen idonsa.
Irin hasken da tunda yake sau d'aya ya tab'a ganinsa a rayuwarsa, watanni biyu da suka wuce, lokacin da sab'anin farko ya shiga tsakaninsa da Fadeelah.
Ranar da yana duba hotunan wayarta ya tsinci wani hoton ta tare da Al'ameen, sun d'auka ne a cikin wani library cikin sigar selfie, dukkaninsu na dariya yayin da Fadeelah ke kallon camerar amma shi ya juya yana kallonta, yana kallonta...
Irin kallon da shima yake mata in yan tare da ita, a wannan ranar kwanan wayar nan ya kare don fasa ta yayi har batirinta.
Tun da yake a rayuwarsa bai taba tunanin Al'ameen d'in Fadeelah shine Al'ameen d'in da shima ya sani a America ba, duk da ba wani sabo suka yi ba amma zai iya cewa sun had'u kusan sau biyar ta hanya abokinsa Kamal daya taimaka masa a baya game da binciken asalinsa, a wancan lokacin zuciyarsa ta kwanta da Al'ameen ne kasancewarsa sabon lauya mai kokarin cimma burinsa, amma a yanzu hoton fuskarsa a k'one yake zuwa idanunsa a kullum.
Kuskuren da zuciyarsa tayi a wancan lokacin shine na kasa rik'e fushinsa har ya fasa wayarta kuma ya bari zargi ya shiga zuciyarsa na tunanin ko har yanzu Al'ameen bai gama barin zuciyarta ba, don a yadda hoton nan ya fassara masa komai, gani yake mu'amarlarsu tayi k'arfin da ba lallai har a lokacin nasa kokarin yayi nasarar cire shi a zuciyarta ba, ko don kyawun fuskarsa ma.
Don haka karo na farko aka samu sab'ani tsakaninsu har na tsawon kwanaki biyu, Fadeelah tayi fushin data daina yi masa murmushi balle dariya, bata fasa yin dukkan wata d'awainiya ta gidan ba amma komai yayi duhu a idanunsa, gidan ya zama babu haske balle nutsuwa, da kansa ya gano kuskurensa ya koma ya nemi yafiyarta.
Shin irin wannan kuskuren yake son sake aikatawa a yanzu?
Dukkanin wata kafa ta kwakwalwarsa ta shiga kokarin hana shi abinda yake shirin tambaya amma ya kasa danne zuciyarsa.
"Leelah waye Abdoul?"
Yana kallon yadda fuskarta ta canja a lokaci guda zuwa tunani, goshinta ta takure waje d'aya.
"Abdoul?
Waye shi?" Ta maido masa da tambayar.
Ya d'aga kafad'unsa kad'an.
"Mun had'u dashi ne a masallacin da la'asar bayan mun gaisa sai naji yana gayawa abokansa a bayana cewa da shine zai aure ki."
Ta d'an yi shiru kamar mai nazari, bayan wucewar wasu 'yan sakanni kuma ga mamakinsa kawai sai ta kyalkyale da dariya tana kallonsa.
"Seriously Wolfie?
Shine zaka cinye ni d'anya?"
Bai san lokacin da yayi murmushi ba shima jin sunan data kira shi, zai iya rantsewa ba'a kwana biyu a duniyar nan Fadeelah bata canja masa suna ba, suna nan da yawa...
Big guy, boobear, bunches, captain, cowboy, charmy, heartthrob, hoshi, habibi, Oppa, Ironman, Jaan, Ma cherie....
Ba zai iya lissafo su ba.
"Allah ya huci zuciyarka tough guy, ni wallahi yanzu in zaka shak'e ni ko kammaninsa ba zan iya ganewa ba, amma dai na tuna shi abokin yaya Salisu ne daya tab'a min magana sau d'aya, amma kafin ma a samu damar da zan bashi amsa k'addara ta d'auke ni zuwa hanyar da zan had'u da kai, so cool off kaci abincinka ka daina tunanin...."
Kafin ta k'arasa abinda zata fad'a, Adam ya jawo ta cikin jikinsa ya zagaye ta da dukan hannayensa, ya riga ya samu amsar sa kuma baya son shaid'an ya sake samun tasiri akansa, a hankali idanunsa ya sauka kan bakinta.
"I miss you." Ya fad'a muryarsa k'asa-k'asa.
Nan take jinin jikinta ya sake d'aukar d'umi yana neman tafasa don jikinta da zuciyarta sunyi kewarsa kamar babu gobe, kwanansu biyu kenan da zuwa Ikara ita da Mairo, tun ranar Alhamis suka taho shi
kuma sai jiya juma'a ya k'araso tare dasu Sa'id, kuma tun a jiyan waya kawai suka yi don shirye-shirye sun sha kan kowannensu, a yau kuma wayar ma bata samu ba sai hango shi kawai da ta dinga yi tare da mutane.
Ta d'ago da fuskarta kad'an yadda karan hancinsu ya had'u da juna sannan ta mik'a da hannayenta ta zagaye su a wuyansa.
"I miss you too."
D'aya hannunsa ya lalubi cikin k'asan rigarta yace.
"Babyna fa?"
"Shima yayi missing d'inka like crazy."
Sai yayi wani murmushi a hankali, sautin ya fito daga can k'asan mak'oshinsa.
Fadeelah ta nutse cikin d'umin jikinsa wanda ke had'e da k'amshin sabulu da turare sannan a hankali ta rufe idanunta sanda ya sunkuyo da fuskarsa kan tata, wata wuta kamar ta lantarki ta harba tsakanin fuskarsa zuwa tata, lebbensa masu taushi da d'umi suka d'aga ta zuwa cikin gajimare.
Zuciyarta ta manta da komai ta biye masa na wani lokaci kafin kuma ta tuna inda suke, da sauri ta janye jikinta sannan ta matsa gefe.
"A mota muke fa." Tayi k'okarin tuna masa.
Sai ya jefa kansa jikin kujerar motar sannan ya zura hannu cikin gashinsa yana sauke numfashi yace.
"I'm sorry Babe
im, na manta ne." Muryarsa ta fito a shagale kamar mai jin bacci ko wanda ya tashi.
Murmushi mai taushi ya sub'uce a fuskarta sannan ta juya ta d'ebo kayan takeaway d'innan, tace.
"Bismillah, time to eat."
"Yes Babe." Ya fad'a sanda ya juyo gabad'aya saitin ta ya tankwashe k'afafunsa akan kujerar motar sannan ya sake jawota jikinsa.
Ta d'ora abincin akan cinyarta sannan ta shiga bashi a baki, yana rik'e da d'aya hannunta sannan a hankali kuma wannan lallausar muryar tasa tana mata mitar yadda yayi kewar girkinta.
Idanun Fadeelah suka ciko da wata irin kwallar farin ciki da kuma godiya ga Allah, 'yan shekaru da basu fi cikin hannu ba a baya,
rayuwarta a hargitse take bata ma san wacece ita ba balle har tayi tunanin samun dad'in rayuwa haka, amma tun daga lokacin da ta fara sanin Adam a America, abubuwa suka fara bud'ewa d'aya bayan d'aya a rayuwarta.
A yau gata cikin jikinsa a matsayinsa na mijinta, gata d'auke da halittar dake shirin zama jininsu, gata a cikin garin da yake mahaifarta, cikin 'yanuwanta kuma cikin Babban gida a matsayin wani abu mai daraja.
Sai ta juya a hankali ta hango ginin k'ofar Babban gidan, kantangarsa mai tsayi na nan a tsaye kyam kamar wani gingimeman dutse, a lokaci d'aya idanunta ya dawo mata da wani zamani daban, sanda ta bud'e k'ofar wannan gidan ta fito, sanye da cukurkudadden hijabinta cikin duhun dare!
Sai kawai ta rufe idanunta a hankali kwallar dake cikinsu ta gangaro kan kumatunta.
Rayuwa.
Mece ce ita?
Tasha tambayar kanta hakan!
ALHAMDLILLAH.
KARSHE.
BAYAN NA MUTU.
AYSHA SHAFI'EE
SHARHI
Bayan na mutu labari ne da jigonsa ya k'unshi muhimmancin dangi a rayuwar
d'an Adam.
Dangi wasu mutane ne da Allah ya halitta a rayuwar kowanne mutum, dangi sune ginshik'i kuma k'ashin bayan dake tafi da rayuwar duk wani mai rai.
Dangi sune mutanen da suka san ka tun lokacin da baka san kanka ba har zuwa mutuwarka, Dangi sune masu taimakonka, sune mutanen dake tare da kai a lokacin nasara da kuma fad'uwarka, sune mutanen dake k'aunarka a yadda kake ba tare da wani dalili ba, sune wad'anda ke d'orar da kai akan halayyar da zata maida kai cikakken mutum.
Dangi sune mutanen dake iya fahimtar damuwarka ko baka furta ba.
Mutane da yawa zasu danganta rabi na wad'annan ma'anonin da wani zamani daya wuce ba wanda muke ciki ba, A yanzu mafi yawancin mutane zasu gaya maka ma'anar Dangi ne a matsayin K'ALUBALE kawai!
Idan muka dubi rayuwar BINTU, ita kanta zata iya bamu wannan fassarar...
Amma rayuwar ADAM ta nuna mana akasin hakan, ta nuna mana cewa duk wani jin dad'in rayuwa da matsayin da mutum zai samu a duniyar nan zasu koma gefe d'aya ne su taru in har baya cikin DANGINSA, DANGI wani b'ari ne na jikin mutum ne da in har babu shi, dole ne girma da darajarsa ta ragu.
Ina fatan Allah ya bamu damar rik'e zumunci a tsakanin DANGINMU ta yadda duk tsanani da k'alubalen hakan ba zai kawo rabuwar kai ba kamar yadda ya faru da al'ummar BABBAN GIDA.
Akwai mutane da yawa a duniyar nan irin ADAM da basu da masaniyar DANGINSU, wasu suna iya samun su wani kuma har ya koma ga Allah babu wanda zai iya nunawa a matsayin nasa, Ina fatan Allah ya sanya hak'uri da juriyar hakan a zukatansu ya kuma mayar musu da hakan a matsayi rahma a ranar gobe k'iyama.
Bayan Adam, rayuwar FADEELAH ma wani karatu ne mai zaman kansa, rayuwar hak'uri da juriya da kuma fuskantar k'alubale kala-kala, wanda duk daga k'arshe ke juyewa zuwa tarin alkhairi.
Ina fata Allah ya bamu irin hak'uri da juriyarta, ya kuma saka mana da fiye da alkhairin data samu, don babu wata nasara data wuce samun jin dad'in duniya da kuma na lahira.
Nagode da tarin hak'urinku da kuma lokacinku da kuka yi amfani dashi wajen karanta labarin nan.
Ina fata kuma ku amfana da wani abu daga cikinsa.
MA'ANAR SUNAN LABARIN BAYAN NA MUTU.
Labarin ya fara ne ta cikin tunanin wata yarinya Bintu, wadda ke bamu labarin rayuwarta tare da kakarta bayan rasuwar iyayenta, bayan ta gudu daga gida ne tayi hatsari daga nan sai labarin ya cigaba ta b'angaren mai bayarwa ana nuna labarin Fadeelah.
A wannan hatsarin, kwakwalwar Bintu ta mutu, tunaninta ya shafe bata san wacece ita ba balle har ta cigaba da bamu labari, don haka duk wani abu daya faru bayan nan, Bintu na gaya mana cewa ne....
BAYAN NA MUTU...!
Signed.
Aysha Shafi'ee.
08067794315.
Times New Roman
Times New Roman
SimSun
Symbol
Symbol
Arial
Arial
SimSun
SimHei
Courier New
Courier New
Wingdings
Wingdings
Z&!),.:;?]}
Normal.wpt
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
itel S33
TECNO LD7
WPS Office
5e1dddbff1ed4e8aa0417faea907cd95