← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 95

Sashe 63

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taron ya had'a harda wad'anda ba'a kira ba sai suka zo don jin abinda za'a tattauna, inda ba komai akayi ba sai rok'o da Kawu ibrahim d'in yayi tayi akan a taimaka a yafe mata laifin da tayi tunda har tayi hankalin dawowa cikinsu a yanzu, amma sai da aka kai ruwa rana sannan Kawu d'anjuma yasa baki a gajarce cewa shikenan taje sun yafe mata, bayan kuma ta gaya musu cewa tana da miji har da 'ya'ya biyu, sai komai ya nemi dawowa sabo...

Da yawansu suka saka baki kan cewar laifinta na raini ne da son zuciya, tunda har ta iya haihuwa biyu kafin ta neme su, su kace kar ta sake ko da wasa ta kawo 'ya'yan cikinsu balle kuma shi mijin data fifita akansu, ba irin kuka da magiyar da ba tayi musu ba cewa itama bada son ranta tayi hakan ba, amma haka aka tashi Kawu Ibrahim baici nasarar tara sun da yayi ba.

Daga nan ya kaita b'angarensa, inda matarsa Aunty Hassana ta karb'eta da mutunci, ta bata ruwa tayi wanka, sannan ta d'auko sababbin kaya a cikin nata ta bata ta sanya, ta fita daga cikin suturar data danganci Sadiq da dukiyarsa.

Bayan taci abinci kuma tasa aka samo mata magani saboda zazzab'in yayen Muhammad daya fara kamata, amma duk wannan abun da ake yi zuciyarta hanqoro kawai take na son ganin 'yaruwarta.

Yayin da duk wannan abinda ake yi kuma, Sadiq na daga can gefen layin cikin motarsa yana samun bayanin abinda ke faruwa daga wajensu Saminu, don da gaske Maryam take ta yanke alak'arsa da ita, bata k'ara nemansa ba kuma bata k'ara bari ya ganta ba, gashi ba ko waya a hannunta tunda daga asibiti ta taso, ga magungunanta ma suna zube a motarsa bata ko sake waiwayarsu ba.

A safiyar ranar ne k'annwn mahaifiyarsa biyu, su Umar suka zo kamar yadda tayi alkawarin turo su, kuma bayan bayaninsa mai cike da kwana-kwana ya lallab'a su suka koma ba tare da sunga 'yanuwan Mairo ba kamar yadda ya turo su da k'udirin hakan.

Kuma da yake har yanzu Nairar jikinsa na sawa ya fad'a aji sai suka yarda ya sama musu jirgin yawon da ya tashi k'arfe d'aya na rana
suka koma harda Zakkiya da Muhamnad.

A yanzu yana jiran kiran mahaifiyarsa ne da kuma duk wani hukunci da zai fito daga Maryam.

"Yallab'ai don girman Allah, wannan 'yaruwarta ce shekara da shekaru basu had'u ba, bama ni saina shiga ba ka taimaka ta ganta ko na minti goma ne."
Cewar Kawu Ibrahim, mutumin ya girgiza kai baya ko kallinsu.

"Naga gobe zaku shiga kotu, meya na saurin?

Ta ganta a can kawai."
Kafin Kawu Ibrahim ya sake cewa wani abun k'ofar ofishin ta bud'e, wani mai tsaro ya shigo.

"Ranka ya dad'e kira ne daga waje."
"Ahh haba dai!

To gani nan."
Ya rufe file d'in gabansa da sauri kawai sannan ya fita daga office d'in ya barsu."
"Kawu dan Allah mu zauna ya dawo, mu k'ara rokonsa ko zai yarda." Cewar Mairo bayan fitar tasa.

Sanin irin yadda ta damu ne yasa Kawu Ibrahim ya amsa mata suka cigaba da zaman jira a office d'in amma ya riga ya fahimci cewa bashi da niyya.

Kusan minti biyar sai gashi ya dawo.

"Yawwa nace ku ai baku yi bayanin cewa 'yanuwa ne na kusa ba, ni tunanin da nake irin daga nesa kuke ne shi yasa, amma ba komai zaku iya shiga ku ganta yanzu, sai dai ku hanzarta don naga yamma tayi, kuje za'a fito muku da ita."
Ba Kawu Ibrahim ba, hatta Mairo dake cikin zumud'i sai da tabi mutumin nan da kallon mamakin yadda ya canja a lokaci d'aya.

Sai dai ita bata yi tunanin komai ba saboda hankalinta ya tafi gabad'aya ga son ganin Bintun, amma a tunanin kawu Ibrahim zato yayi Adam ne ya bada umarnin a barsu su ganta.

Sadiq na tsaye daga cikin office d'in wani Babban ma'aikaci a wajen ya sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da ya hange su sun nufi d'akin da ake ganawa da d'aurarrun.

Da ace akwai inda murna zata iya yin masauki a zuciyarta, da babu abinda zai hana Fadeelah jin hakan lokacin da aka shaida mata cewa ta sake samun mai zuwa ganinta har sau biyu a rana guda.

Watakila ba'afi awanni biyu da shan maganin da Adam ya kawo mata ba, amma har taji sauk'in yanayin jikinta da kuma taimakon kayan cimar ledar nan sannan ta d'add'aki ruwan ma kamar ba gobe, don ji tayi kamar ta shekara rabonta da ruwa mai tsafta irinsa.

K'afarta bi da bi take bin bayan mai tsaron nan Musa, har zuwa wajen da a yanzu shi kad'ai ne silar samun sassaucinta, tunda a nan ne kad'ai inda zata had'u da mutanen da basa ganinta da wannan laifin.

Kawu Ibrahim idonta ya fara gane mata, sannan kuma ta tsaya cak sakamakon fuskar Mairo data ci karo da ita a gefe, Mairo dai da ta gani a Abuja, Mairo 'yaruwarta tsaye tana kallon hanyar k'ofar data shigo ta ciki idanunta a zare kamar zasu zazzago daga mazauninsu su fadi k'asa.

A lokaci d'aya taji iskar da bata san wace iri bace ta zarce cikin makogwaronta sannan d'an mitsitsin sauk'in data samu game da kulawar Adam ya murmushe yabi iska, ta sake kallon Kawu Ibrahim sosai, sannan Mairon da bata jira komai ba ta fara kokarin tahowa gare ta da sauri, sai kawai ta juya da sauri itama ta fita daga wajen, ta koma hanyar da suka biyo.

Kawu Ibrahim ya sani, ta gaya masa cewa bata son ganin Mairo bata buk'atar sake ganinta a rayuwarta, amma shine ya kawo ta har nan...

Tiryan-tiryan tabi hanyar data haddace ta har cikin cell d'in da yake nata a yanzu, ba tare da wani mai tsaro ba ta shiga da kanta kuma ta janyo k'ofar ta had'e ta, yadda take ji a cikin ranta duhun wannan cell d'in ya fiye mata ganin Mairo da dukkan kasancewarta a duniya.

Ta san cewa tunaninta yafi karkata ga cewar ita Fadeelah ce a yanzu, amma tunda har tunaninta na farko a matsayin Bintu yana tare da ita, zata karbi kowanne hannu biyu ta bashi hakkinsa...

"...duk sanda Mairo ta dawo gareku kuce na yafe mata Malam, wallahi na yafe mata.

Muryar Innarta a ranar da zata mutu ta haska cikin kanta sanda ta nemi can k'arshen cell d'inta zauna, Inna Saratu ce taje ta tashe ta a safiyar ranar akan cewa tazo Inna Aminar na nemanta, kuma bayan tabi bayanta har zuwa d'akin da take ciki, ta tsinci k'arashen wannan zancen nata tana gayawa Baba dake zaune a gefe rik'e da hannunta.

A lokacin k'afafunta rik'ewa suka yi ta kasa karasawa cikin d'akin, bata kai yanzu wayo ba amma tun a sannan tayi zaton cewa irin bak'in ciki da wahalar da Mairo ta jaza musu ba wanda zai iya ko d'aga ido ya kalleta duk ranar da ta waiwaye su balle har ayi zancen 'yafiya'.

Taso a yanzu zata iya haskawa Mairo wannan lokacin da Innarsu ke kan gab'ar mutuwa amma tana fad'in cewa ta yafe mata duk da cewa kuwa itace silar ciwon nata, taso zata iya nuno mata taga irin soyayyar da ta gujewa ta tafi neman wadda bata k'unshi komai ba sai sha'awar duniya, taso zata iya nuna mata irin bak'in ciki da kuma azabar da dukkaninsa suka jure a dalilin son zuciyarta...

Taso zata iya nuna mata yadda ta rasa uwa, Baba ya rasa mata, inna Saratu ta rasa 'yaruwa duk a gaban idonsu saboda ita kad'ai kawai.

Ta rufe idonta a hankali sanda ta jingina da bangon, ta dad'e da d'aukarwa ranta alkawarin cewa ba zata tab'a yafewa Mairo ba koda kuwa duniya zata nad'e da ita a cikin k'asa.

Jinginen ba dadi saboda haka ta lalubi
dandaryar simintin nan ta d'ora fuskarta
sanda tunaninta ya dawo mata lokacin da Baba ke biya kalmar shahada cikin kunnen Innar da kowacce gab'a ta jikinta ke girgizawa mintuna kad'an bayan shigarta d'akin.

A lokacin hawayen dake fita daga idanunta sun k'afe, tana rik'e da hannunta mai d'umi da ita Innar da kanta ta miko mata ta kama, Baba ya cigaba da furta kalmomin shahadar cikin kunnenta kafin ta iya karb'a da wata irin murya mai k'arfi data cika d'akin.

"Lailah ha ilallah, muhmad rasu..."
Shiru ne ya biyo baya bata k'arasa ba, sannan a lokaci d'aya kuma hannun da ke cikin nata yayi sanyi kalau, idanunta suka bi sama da kallo sannan numfashinta ya yanke, ya yanke tare da duk wani ragowar tunaninta a lokacin.

Tana iya tuna yadda shirun d'akin ya fallasa k'arfin kukan Inna Saratu yayin da Baba yayi k'ame kawai rike da hannun gawar kamar yadda itama take.

A duniyar nan kaf!

Gwaggo lami da ta shigo d'akin daga baya, itace ta fara furta rasuwar Inna Amina.
****
Gwaggo lami ita ta fara zuwa a matsayin shaidar Kutama ranar da akayi zama na biyu, tazo ta fad'i duk wasu k'arairayin da babu ko d'igon gaskiya a ciki, amma ta rantse ta kuma kalli Alkali ta tabbatar da gaskiyar ta fad'a.

Fadeelah ta san Adam bai so yi mata
tambayoyi ba amma irin maganganun data fad'a yasa shi ya mik'e, amma da yake ita d'in tsohuwar makira ce ta bashi dukkan amsoshin da suka tafi daidai da k'aryar data fad'a.

Bayan ita Kutama ya kira 'yan sandan da suka je neman Bintu har garin Kano a lokacin da akace motarsu tayi hatsari, ya kira
likitocin da suka tabbatar da irin gubar da aka sanya a kokon, ya kira wad'anda suka tantance shaidar hannun Bintu da ya fito a jug d'in data kai mata kokon, hatta mai markaden geron da akayi sai da ya kira kuma Alkali ya gamsu bayanansa da yawa ta yadda a cikin wata guda kawai ko makaho zai shaida inda shari'ar ta dosa.
Chapter 63 · 0% Book details