Sashe 86
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai mafi rincab'ewar al'amarin tana masa kallon tsana ne! tsana wadda ke tasowa tun daga k'asan zuciyarta, tsana wadda baya tunanin wani mahaluki ya tab'a yiwa waninsa akan abinda a lokacin bata san gaskiyarsa ba.
Abinda ya sani a yanzu shine da Fadeelah da Bintu abu d'aya ne, zuciya d'aya suke rabawa don haka in har bata sonsa
a matsayin Fadeelah, don ya koya mata karatu ko ya taimake ta, babu abinda zai canja a yanzun da ya same ta a BINTUN IKARA.
Matsala ta biyu kuma itace shi da ita basu tab'a had'a wani abu daya danganci hanyar aure ba, karatu ne kawai ya had'a su kuma ya raba tuntuni, don haka shi kansa bai san me yake ji game da ita ba bayan cewar yana kewar idanunta duk sanda yayi nisa dasu saboda sun zama kamar wani b'angare ne na zuciyarsa, amma a zahiri....
Idanunta nata ne.
Sa'id ya bud'e k'ofar bayan motar aka shiga saka wasu abubuwan da basu sami waje a booth ba, sai ya lumshe idonsa kad'an sannan ya k'ara sautin k'aratun da yake ji cikin bluetooth earpice d'insa, a yanzu abinda bai sani ba shine zuwa wane lokaci zai iya fahimtar da ita cewa rabuwar aurensu ba abu ne mai yiwuwa ba?
Zuwa wane lokaci zai iya gaya mata cewar alk'awarin da yayi mata k'arya ne? kafin kayan abincin nan su k'are ko kuma bayan an k'aro makamancinsu?
Idonsa ya kai kan d'an karamin mudubin gefen motar, a ciki ya hango Sa'id yana bawa wannan ma'aikacin kud'i kafin ya zagayo ya bud'e mazaunin direba ya shigo.
K'arar kunnuwar motar kuma yayi daidai da k'arar shigowar kira a wayarsa, sunan Mamanshi ya fito tar akan screen d'in, Julie Walker!
Baturiyar data amsa sunan mahaifiyarsa tsawon wasu shekaru a America, tun bayan da ya dawo Nigeria kuma bata manta dashi ba kamar yadda mijinta yayi, duk bayan wani lokaci zata kira shi a waya har ma ta taka matsayinta na uwa kan harkar lafiyarsa ko rashin cin abincinsa kamar sanda yana gabanta.
Shi yasa babu yadda ya iya dole ya gaya mata zancen auren nasa kuma ta dage akan sai ya had'a ta da Fadeelan sun gaisa a waya kafin lokacin da zata zo.
Ya cije lebb'ensa kad'an don abu ne a yanzu da ba zai yiwu ba.
Bai fad'a mata komai ba bayan cewar yayi auren kawai, don inda zai fad'a mata abinda ya farun ba lallai ta fahimta ba...
Ba lallai ta fahimci cewa a tsari na musulunci da kuma al'adar bahaushe iyaye nada damar aurawa 'ya'yansu wanda suke so ba tare da izininsu ba.
Ya bar wayar har ta gama rurinta sannan ya tura mata d'an k'aramin sak'on da ya san zata ji d'ad'insa ta kyale shi.
"Allah babu wanda zaice Ango ne kai muke ta yawo haka."
Sa'id ya fad'a sanda yake k'ok'arin tura text din, ya juyo ya kalle shi.
"Ango ba'a ganinsa?" Tambayar ta fito daga bakinsa kafin ma ya gane yayi ta.
"No, ana ganinsa mana amma ba'a ganinsa shi kad'ai haka sai tare da mutane."
Sai kawai ya juya ya kalli motar data tsaya a hold-up d'in gefensu sannan yayi murmushi a gefen kumatunsa yace.
"Tuna min ranar da kai ka tashi daga mutum."
Sa'id yayi dariya shima kafin ya sake magana.
"To bama wannan ba, da gaske ya kamata ace ka fad'a a office sun baka hutu, bai kamata ace duk wannan zirga-zirgar da kasha kuma jibi ka fita aiki ba."
Hutu ba maslaha bane a wajensa yanzu, don yafi so ya bawa Fadeelah isashshen lokacin da zata samu nutsuwa hankalinta ya kwanta tukunna kafin ya nemi fahimta daga gare ta, ya yarda in har suka bawa juna iska abubuwa suka d'an huce komai zai fi tafiya daidai.
Saboda haka sai ya bagarar da zancen da wata tambayar.
"Da gaske ne wai kun kwashe duk wasu kayana a gida?
Yau dana tashi fa kayan da zan saka kawai na gani a wardrobe."
"Wallahi Awwal ne, ina jin hatta chager wayarja tun jiya ya maida su gidan, haka suka dinga layi shida 'yanuwanta masu kai mata kaya.
Shi yasa da sassafe ya tafi Ikaran, kuma na san kayansa gabad'aya na can zai d'ebo."
Suka yi dariya a tare, don tun sanda suka dawo daga Ikara Awwal murnarsa d'aya ce ta zai samu d'akin Adam in ya tafi, kuma bai wani jira umarni ba ana gama cinikin gidan da aka siya ya fara d'iban kayansa yana kaiwa can, shi mutum ne mai yin komai b'aro-b'aro kawai.
Sun isa gidan a lokacin da babu ko mota d'aya a waje balle su saka ran samun mutane a ciki, maigadi ya bud'e musu suka yi parking a ciki sannan suka d'ebi wasu daga cikin kayan motar ciki, masu nauyi kuma suka barsu a mota zuwa safe.
Ba Sa'id kad'ai ba, hatta Adam sai da ya tsaya kalli tsarin kayan da aka jera a gidan wanda suka k'ara fito da kyan fasalinsa, daga falo, dining area har zuwa kitchen komai cikin kala biyar yake, grey, ash, white, silver da kuma zirin bak'i a wasu wajajen, bai tab'a tunanin cewa mata suna da fasahar da zasu tashi abu mai kyau irin haka ba.
Ya d'an jingina da kujerar falon yana kallon adon wasu k'ananan flowers da aka jera a saman Tv, fatansa d'aya ne a lokacin, ubagiji ya bashi damar da zai iya jan hankalin Fadeelah ta zauna dashi, don rabuwarsu ba mutanen babban gida kad'ai zata shafa ba har da nata iyayen da suka baje kokarinsu wajen gani sun kyautata gidan aurenta haka.
Idonsa ya kai zuwa hanyar shiga d'akunan kwana dake gefe, ya san dole ne Fadeelah tana d'aya daga ciki a yanzu haka, clutching the lip of her veil as his wife, his bride!
Ya lumshe idonsa a hankali, zai so ganinta kwarai amma ya san ba shawara bace yaje wajenta a lokacin..
Don ba lallai ne taso ganin fuskarsa ba a yanzun da saboda shi ta rabu da komai na rayuwarta ta baya.
Said ya fito daga hanyar kitchen a lokacin bayan ya ajiye wasu kayan, sai kawai ya juyo ya mik'a masa ledar kayan cimar daya siyo yace.
"Ka kai mata wannan tana ciki."
Daga haka bai jira amsarsa ba ya wuce shi ya nufi hanyar wajen dining, inda anan corridon shiga d'akinsa yake.
*NB*
_*Bani da mallaki akan wakokin dake cikin chapter nan.*_
*BAYAN NA MUTU!*
AYSHA SHAFI'EE
BAYAN SATI BIYU.
Hasken rana ya shigo ta tsakanin wata siririyar hanya a jikin labulen d'akin, a k'aida kamata yayi ta zuge labulen d'umin ranar ya shigo ko ya rage azababben sanyin da tiles d'in k'asa ya d'auka, amma kuma bata son hasken ko kad'an saboda ciwon idonta dake shirin dawowa a dalilin rabuwarta da glass na tsawon lokaci.
..Muhammad ba zaka kyaleta ba?
In nazo wajen nan zan zaneka fa?
Fadeelah ta d'an rufe idonta kad'an saboda yadda Mairo ke ihu ta cikin wayar da suke yi tana rabon fad'a tsakanin 'ya'yanta, ta cusa yatsanta cikin barbajajjen gashinta daya baje akan pillow, tashinta kenan a lokacin don wayar Mairon ce ta farkar da ita, ta d'aga kai ta kalli agogon d'akin k'arfe goma na safe amma har su sun tashi suna bidirinsu, ta murza idanunta da tana k'okarin saita ganinta har a lokacin Mairo na sulhu ta cikin wayar.
"Ya salam ya Allah!
Ace yaro baya ko magana amma sai tsabar rashin ji...
Ita kuma tayi ta masa kuka?" Ta fad'a bayan wani lokaci.
Fadeelah tayi murmushi sannan tace.
"Dan Allah yaushe zaki kawo min ita?
Kinga kema sai ki huta."
"Ai ba don next week zasu koma makaranta ba tattaro miki ita zanyi wallahi, amma dai zan tambayi babanta may be tazo miki wani
weekend d'in."
Ta mik'e zaune sannan tace.
"Har naji kamar inzo d'auke ta wallahi."
"Kar ki damu zata zo, kinji kuwa an yankewa Habiba k'afa d'aya?"
Maganar ta daki tunaninta, tace.
"Yaushe?"
"Shekaranjiya Aunty Hassanah take gaya min, wai tun daga cinya don ciwon yaci k'arfinta."
Bata san me zata ce ba don haka tayi shiru kawai, zuwa can kuma ta daure tace.
"Allah ya bata lafiya."
Watakila Mairo ta fahimci halin da zuciyarya ke kokarin fad'awa ne don sai tayi saurin canja zancen da cewa.
"Kin tambaye shi kuwa zuw asibitin?"
Sai ta kifa kanta akan tafin hannunta gashinta ya sunkuyo a barbaje, sannan ta girgiza shi kamar Mairon zata gani.
Yau asabar ya kama sati biyu kenan da fara sabuwar rayuwarta ta aure, kuma a cikin wad'annan kwanakin, ta samu wani nutsatstsen hutu da kwanciyar hankalin da har hakan yasa zuciyarta ta fara wankuwa game da abubuwan da suka faru da ita.
Watakila don ta d'an rabu da hayaniya ne kwana biyu saboda tun sanda aka kawo ta babu wanda ya sake zuwar mata, hatta su Aunty Saratu a waya suka yi sallama, kuma ba sai wani ya gaya mata ba ta san su suka tsara hakan don ko kowa ra'ayin kansa ne k'in zuwan da taga su Zahra da suka dawo a cikin satin saboda k'arewar hutun makaranta, amma su d'in ma har yanzu sai a waya kawai take ta fama da kaud'insu.
Wayar da Mamin ta bawa Sa'id ya kawo mata sabuwa a kwalinta, kuma a ranar da suka yi waya ta gaya mata cewa akwai kud'i a account d'inta na banki... tun wannan kud'in data tura mata lokacin bikinta da Al'ameen, a yanzu da aurenta ya koma kan Adam, an samu gudunmawa sosai daga Babban gida da kuma su Aunty Saratu don haka bai fi rabin kud'in aka tab'a ba.
Shi yasa yanzu da idonta ya dame ta da ciwo take son taje asibiti a duba ta kuma ta sake glasess, tana son siyo kayan zane ma sannan tana son taje inda zata siyo wasu 'yan k'anan abubuwa da take buk'ata, amma duk hakan ba zai yiwu ba sai da izinin mijinta.
Haka Mairo tace kuma itama ta san baza ta iya fitar ba sai da izininsa.
"Bintu kina jina kuwa?" Muryar Mairo daga cikin wayar ta dawo da ita daga wannan dogon tunanin.
Sai tayi saurin d'ago da kanta sannan ta amsa.