Sashe 68
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar yau, ita ke shaida cewa kwananta biyu a wajen, kwana biyu cikin wata sabuwar uk'uba ta rayuwa ba tare da zuwan 'yanuwanta ko Adam ba.
Ina ya tafi?
Yaush
e zai dawo duk tambayoyi ne da bata samu damar yi masa a lokacin ba saboda kiran wayarsa da akayi ya fita ba tare da sunyi sallama ba.
"Kowacce ta jawo tsinannen jikinta ta fito...!
Ba zan shigo d'aki tashin kowacce sh*g*ya ba."
Muryar Matron Gaje ta shiga karad'e dogon corridon yayin da wasu k'ananan ma'aikata ke ta faman bud'e kowanne cell da mukullan hannayensu, Matron Gaje wata figaggiyar mace ce mai kwala-kwalan idanu, amma an fi tsoronta fiye da duk wata Matron a kurkukun, hakan yasa yau da aikinta ya fad'o kan block d'in kowa ya mik'e a hanzarce aka shiga kafa dogon layin fita a cikin corridon, amma Fadeelah bata motsa ba, don kowacce gab'a ta jikinta amsawa take da azababbiyar gajiya.
Jiya aka raba su sababbi zuwa wajen ayyuka kala-kala na kurkukun, inda ta tsinci kanta a b'angaren masu daka da surfe, Buhunhunan masara da gero ne gasu nan a zube fal!
Da kuma turame da tab'are.
Babu wani b'ata lokaci taga duk matan da suka taho tare kowacce na d'aukan tab'arya suna kuma jan turamen zuwa inda wasu Matrons ke auna musu masarar, har rige-rigen d'aukan tab'arya mai kyau ake yi.
Babu yadda ta iya, haka ta lalubi wata tab'arya itama ta d'auka, bayan tsawon wani lokaci a rayuwarta, Fadeelah tayi daka, tayi ta dukan masarar da aka bata har sai da bayanta ya k'age amma babu d'aya a cikin Matrons d'in nan data d'aga mata k'afa, awa hud'u a jiyan nan sai da ta shafe su wajen dakan masarar tun tana fad'uwa tana tashi har sai da ta horu da gajiyar ta daina jin komai, ta gama dakan sannan ta zirce masarar ta fitar da dusar cikinta kamar yadda taga sauran sun yi, bayan nan kuma aka basu gero, suka surfa, suka wanke, sannan suka hau dakansa shima.
"Gwara ki tashi Binbi...
Matron Gaje shegiyar kanta ce, yanzu zata lalata miki rayuwa." Kenken ta fad'a tsaye a bakin gadonta.
Binbi, tsakanin jiya da yau sunan har ya fara binta, don 'yan d'akin sun d'auka kuma suna gayawa duk wanda ya tambaye su sunanta shi, Babu wanda ya k'ara jin maganarta tun ranar da aka kawota, sai dai ta san suna jin sheshshek'ar kukan dake kwace mata cikin dare idan ta tuno rayuwarta ta baya da kuma sanadin zuwanta wajen nan...Dangi!
Mutanen da bayan iyaye su ke da alhakin kare martabar duk wani mutum a duniyar nan amma ita suke tozarta tata martabar.
Wadda aka kawo su tare sunanta Shema'u, amma a jiya taji suna kiranta da Shisha don ita ta shiga cikinsu, ta karb'i dukkan nasihohi da kuma maganganun da suke gaya mata har ta saba suna hira, ita Allah ya taimaketa ta rabu da takurawarsu tun a safiyar jiya da Lalita ta saka doka a d'akin.
"Kar sh*g*yar da ta kuma takurawa Binbi a cikinku, musamman ke Kenken, idan kun kyaleta kwana nawa ne zata sauko ta neme mu?
Kun san dai halin sababbi irinsu, in kuma akwai wadda take son asirinta ya tonu kar ta fasa, idan aka kama yarinya kar 'yar kaza-kazar data sake ta kira suna na."
Bata tab'a magana da K'atuwar matar ba, amma a cikin zuciyarta ta gode mata da wannan gargad'in da tayi musu, duk da cewa kuwa bata fahimci komai a cikin zancen nata ba, ita dai ta san ta samu sauk'in yawan takura mata da suke yi, sai dai kawai yanzu suyi ta binta da ido.
Zazu, wannan mai kama da k'abilar ta juyo sanda ta kai bakin fita daga cell d'in.
"Kenken ki kyaleta, idan Gaje taci uw*rta zata gane ne."
"Ki sauko kafin ta k'araso, ba zaki so abinda zata yi miki ba." Muryar Kenken ta k'ara fad'a sanda ta isa bakin k'ofar.
"Kowa ya fito, bani da lokacin b'atawa akan kowacce 'yar isk*."
Muryar Gaje ta biyo baya, ba yadda ta iya haka ta share kwallar dake shirin fito mata ta sallalb'o ta diro daga gadon, tabi dogon layin da ya fita har waje don daga yanayin yadda take jin muryar Gaje, ta san da gaske zata iya azabtar da ita.
"Kece Bintu Abubakar?"
Wata Matron ta same ta a layin sanda suka fita waje.
Ta tab'e baki tana kallonta bayan ta amsa.
"Ba laifi dole su rikice akanki, amma abin ne yayi yawa kamar wani tashin duniya?"
Fadeelah bata fahimci me take nufi ba saboda haka ta cigaba da kallonta kawai.
"'Yanuwanki ne suke neman rikita kurkukun nan saboda an k'ulle musu 'yar gwal, mun gaya musu akwai ranakun da ake ziyara amma sunki fahimta sai da suka san yadda suka biyo ta hanyar shugaban wajen...."
Shikenan!
Wahalarta ta k'are, Su Kawu Ibrahim sunzo taimakonta, ta san ko bata bar wajen nan a yau ba zasu saka a canja mata cell.
"Ki biyoni." Matar ta fad'a sannan ta cigaba da cewa.
"Akwai damar da ake bayarwa anan mutum ya amsa kira sau d'aya a wata, kin ci sa'a an bani izinin ku gaisa, kuma minti biyar kawai ba dad'i ba k'ari."
Zuciyarta ta d'an karye jin cewa a waya ne zata yi magana dasu, taso a zahiri zata gansu IDO DA IDO, don Allah ya sani 'yan kwanaki kawai rabonta dasu amma tayi kewarsu kamar watanni biyu.
"Ki gaya musu..." Cewar Matron d'in tana sauke murya k'asa-k'asa sanda suka shiga wani d'an siririn d'aki mai d'auke da kan waya d'aya."
"...Idan suka biyo ta hanya ta, a sauk'ak'e zasu dinga ganinki
bama ta waya ba kuma babu wani tashin hankali."
Fadeelah ta gyad'a mata kai sau d'aya sannan cikin zumud'i ta d'auki wayar ta kara a kunnenta.
"Assalamu Alaikum."
"Wa'alaikum salam Fadeelah."
Muryar Daddy ta amsa harda d'an saurinsa, sai ta rufe idonta a hankali sannan ba shiri kwalla ta ziraro kan kumatunta, muryarsa kad'ai kamar komawarta gida taji a cikin zuciyarta.
"Barka da rana Daddy."
"Barkanmu dai Fadeelah, ashe abinda ya faru kenan kiyi hakuri kinji?
Muna nan muna ta fafutukar a fito dake, kuma insha Allah muna sa ran zasu saurare mu."
"Tohm..." Muryarta na rawa ta amsa.
"Na san da wuya, amma kiyi kokarin kwantar da hankalinki kinji?
Komai zai zo k'arshe, bama samun wayar Adam ne amma da zarar ya dawo zaki fito insha Allah."
"Insha Allah Daddy." Ta asake amsawa tana gyad'a kai, hawayenta na d'iga a k'asa.
"Ga kawunki, tare muke dashi."
"Toh.."
"Bintu..." Muryar Kawu Ibrahim ta fito a gajarce.
"Na'am Kawu..."
Sai da ta amsa sannan ta fahimci lokacin kiran ne ya k'are shi yasa muryar tasa ta katse, damarta ce ta yanke ba tare da ta ko shaida musu hanyar samun wata damar ba ta hanyar Matron d'in, _Wannan wace irin minti biyar ce?_
Ta juyo a hankali ta kalli Matron d'in, taji duk abinda ya faru don haka bakinta a tab'e tace.
"Kar ki wani damu, ai ba'ayi miki hukunci ba tukunna, duk sanda kika fita zaman shari'a kya gaya musu, in kuma sun damu da yawa da kansu ma sa nemo ni."
Fadeelah bata fatan bayan fitarta ta k'ara dawowa wajen nan, amma ta san hakan wani mafarki ne a iska don haka ta kalli gefen rigar Matron d'in inda aka rubuta sunanta ta karanta, saboda amfanin goben da bata san a yaya zata zo mata ba.
... bama samun wayar Adam ne..
Kalaman Daddy suka dawo cikin kanta sanda ta zira k'afarta waje, basa samun wayar Adam?
Toh ina ya tafi haka?
Suma basu sani ba kenan?
Don da Daddy zai fad'a mata yace bai dawo daga waje kaza ba, amma basa samun wayarsa yana nufin suma nemansa suke kenan?
Bata san lokacin da ta sulale ta tsugunnan a wajen ba, Ina Adam zai je da har zai k'i fad'awa ko Kawu Ibrahim kuma kuma a kasa samun wayarsa?
Wane irin bincike zai tafi alhali anan take tsananin buk'atarsa?
Kwallar d'azu ta shiga k'ok'arin tunkud'owa daga idonta amma muryar Matron d'in nan ta katse ta daga baya.
"Tashi in maida ke, bana son duk wata masifar da zata had'a ni da Gaje."
Yinin ranar ya shud'e cikin matsananciyar wahala da azaba kamar na jiya, suka gama dukkan buk'atun waje, aka maido su...
Fadeelah ta dawo cikin cell d'insu Kenken, ta kwanta akan katifar Binbin, aka kad'a k'ararrawar shirin kwanciya, Tara daidai haske ya d'auke daga kaftanin rukunan d'akunan kurkukun, a hankali kuma hiraraki da maganganu suka yi ta kad'ewa har tasirin duhu ya rinjayi dukkan wani mai rai, nauyin bacci ya kanainaye idanuwa amma banda nata.
Idanunta a tsaye suke kyam sunyi jawur saboda tsananin azabar da take ji a jikinta da kuma cikin zuciyarta...
Cikin zuciyarta da dukkan tunaninta ke taruwa yana kuma d'ebewa wajen son hasaso tambayoyin dake lilo tare da k'addarar rayuwarta.
Ina Adam Ya tafi?
Me yasa yak'i gayawa kowa wajen da zashi?
Wane irin bincike yaje yi?
Wane irin waje ya shiga da waya zata kasa k'arasawa?
Ko dai wani abu ya faru dashi ne?
Bata tab'a tunanin zata samu amsoshinta da wuri ba sai a washegari wajen k'arfe biyar na yamma lokacin koyon sana'o'i, tana rab'e daga can k'arshen k'aton hall d'in da mutane suka rabu kashi-kashi wajen koyon karatun yak'i da jahilci da kuma sana'o'i, bata shiga cikin kowacce k'ungiya ba don haka ta rab'e daga nan tana kallonsu, zuciyarta na k'okarin tunkud'o mata rayuwarta ta baya amma tana turewa..
A yanzu ta yarda cewa akwai wasu k'ofofi a cikin kanta da ya kamata ta k'ulle su zuwa wani lokaci.
Kenken ta d'ago mata hannu daga can k'ungiyar masu koyon takalmi, ta juyar da kanta gefe, a duk cikinsu itace tak'i daina bibiyarta, bata san cewa zuciyarta ta k'ara kyamar mu'amala dasu ba tun daga gargad'in Lalita akanta.
"Wacece Bintu Abubakar?"
A lokaci guda wata murya ta karad'e hall d'in daga cikin lasifika daga can farkon inda wasu Matrons d'in suke gadinsu.
"Bintu Abubakar..." Kiran ya cigaba da karad'e wajen, Fadeelah ta shiga juya kanta koina don ganin wata ta taso amma ba wanda ya mik'e, Ta yaya za'ace duk tarin matan nan ita kad'ai ce mai irin sunan nan?
Me tayi da za'a neme ta?