Sashe 15
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baku tab'a fad'a min tazo ba."
Ta jiyo muryarsa sanda yake komawa gaban motar.
Amsar da Aunty Miryaman ta bashi
cikin harshen turanci ta daki kunnuwanta ba shiri ta bud'e k'ofar falon ta shige.
"Uwarka ce Al'ameen, dole ai a gaya maka in tazo."
"Dan Allah Deelah kar ki saka damuwar Miryama a cikin kanki, kiji da tarin abubuwan da suke gabanki, na gaya miki insha Allah zata fahimce ki tunda sun dawo nan gabad'aya."
Mami ta fad'a sanda ta shigo gidan ta tarar tana wanke plates d'in da akayi amfani dasu.
"Takurawar da ake yiwa musulmai ne a can Vegas yafi yawa akan nan, har wasu mutane sun jefi Aysha a ido sai da aka mata surgery shine mijinta yace gwara su dawo nan garin tunda ko ba komai akwai 'yan uwanta a kusa, shi kuma yana can sai ya samu hutu zai dinga zuwa.
Jiya suka iso kuma unguwar da ya kama musu gida babu nisa daga nan, don haka gobe zamu je gidan gabad'aya zan taya ta siyayyar wasu kayayyakin."
"Wallahi Mami ba komai fa ni ba wai damuwa nake yi ba, na fahimci kawai jininmu ne bai had'u ba kuma zan dinga k'okari ina kaucewa hanyarta insha Allah, saboda haka gobe ma in zaki je ba lallai ne in biki ba."
"Ai ba zai yiwu ba kuma, kema kamar kowa ce a gidan nan don haka baza'a taba ware ki a komai ba, kuma itama ta haka ne zata saba dake.
Sannan ki k'ara hakuri akan abinda tace wa Al'ameen d'azu, na san kema baki sanshi ba, shine babban d'anta lokacin da kika zo yana England ne a makaranta."
Da murmushinta tace.
"Mami kuwa sai cewa kike inyi hak'uri kamar wani laifi aka min, wallahi na rantse miki ba komai ni banji wani abu ba."
"Toh Allah yasa, naso su Zahra ma sun bari sai gobe muje gabad'aya, yanzu dole sai sun saka shi ya dawo, wai ina Farouk yaje ne?
Al'ameen d'in yana ta tambayarsa."
"Stadium, Ball."
"Haka ne wato yau babu Tahfeez."
Har ta juya zata fita, Fadeelah ta juyo a hankali ta kira sunanta.
"Mami me ya faru da kantin daddy kwanakin baya?"
Sai ta tsaya cak daga bakin k'ofar cike da mamakin yadda akayi zancen da suke b'oyewa ya fito.
"Waya fad'a miki wani abu ya faru deelah? me kika gani?"
"Sau biyu ina jin yana amsa wayar dake ke da alak'a da zancen kantin ne, kuma na san ba haka aka saba ba."
Sai Mami ta lalubo ajiyar zuciya ta d'ora a kirjinta, da farko tayi zaton ko Fadeelan taji tattaunawarsu da Daddy ne a jiya.
"Babu komai ba abinda ya faru, watakila zancen sabon xubin d'in da zasu fara ne yasa yake yawan wayar."
Sanda ta fad'i hakan, Fadeelah na iya hango rashin tabbacin maganar a idonta, sai dai bata son matsawa akan abinda bata yi niyyar gaya mata ba, saboda haka tace.
"Gobe zanje wajen Dr.
Florence bayan makaranta."
"Kina da appointment ne?"
"Patients d'inta basa buk'atar appointment, kowa zai iya zuwa bayan ranar data maka fixing."
"Toh kar ki dad'e tunda zamu fita."
A baya duk ranar da tace zata je wajen Dr.
Gilbert Mami ko Daddy zasu tambaye ta akan me zata je, amma tunda ta koma wajen Dr.
Florence ta kula sun daina hakan, sun yarda cewa a yanzu ciwonta keb'antaccen abu ne da ba kowa ya kamata ta dinga zancen dashi ba.
Itama kuma sai ta godewa Allah da bata tambaya ba, don bata san ta yadda zata yi bayanin cewa zata je tambayar rainin hankalin Adam ne ba.
A wannan daren data zo kwanciya, tunanin hoton fuskar Al'ameen ya cika kanta, ba wai don bata tab'a ganin mai kyau irinsa ba, A'ah.. sai don bata taba ganin mai kyawu da tsarin halittar da yayi mata kwarjini irinsa ba.
Ta tabbata da Mahaifinsa yake kama wanda akace balarabe ne don babu abinda ya had'a siffar Aunty Miryaamah data fi kama da turawa da tasa.
Ta jawo wani d'an k'aramin throw pillow ta rungume lokacin da shirun d'akin da duhunsa ya shaida cewa Zahra ma ta ajiye wayarta tayi bacci.
Dole ne ma ta goge zancen kwarjini Al'ameen a ranta tunda dai ba abinda hakan zai k'are ta dashi kuma ta riga ta sani baza ta so koda tunaninta ya rab'i duk wani abu daya kasance daga hanyar Aunty Miryama ba, balle kuma jininta.
Ta jero addu'o'inta sannan ta rufe idanunta a hankali, amma sai hoton fuskar Al'ameen ya sake yiwa idanun nata rumfa!
Sai kawai ta d'ora filon a sama ta binne kanta cikinsa.
"Maganar Gaskiya ni bana tunanin mutumin nan niyyarsa ta koya miki karatu ce, in ba haka ba me yasa zaice wai kina da wata matsalar dake baki san da ita ba?"
Romilda ta fad'a sanda suke zaune a k'afar benen hanyar classes d'in dake hawa na uku a makarantar inda ba'a fiye wucewa sosai ba, suna k'arasa zana wani format na architecture da aka basu aikinsa.
"Sannan ta yaya ma za'a ce duk tsawon lokacin nan ba wanda ya tab'a fad'a miki hakan daga asibiti sai shi kawai, idan nice ke daga yanzu ba zai k'ara ganina ba."
Melissa ta fad'a kanta na kan zanenta, sai kuma ta d'ago ta tattara dogon gashinta ta tufke shi a baya, saboda yadda yake wa fuskar tata rumfa.
Fadeelah tayi ajiyar zuciya a hankali tana nata zanen, abinda suka fad'a haka ne tunaninta itama, amma babu zancen cewa kar ta koma wajensa, ta riga ta rufe wannan babin da kwarin gwiwar cewa zata iya, zata sadaukar da nata farin cikin don ganin bata b'atawa su Mami ba, saboda haka tace.
"Yau zanje Clinic idan har Dr.
Florence ta tabbatar min da bani da wata matsalar bayan ciwona, zanje muyi ta ta k'are dashi, in zai koya min fine! in kuma ba zai iya ba, na samu wata hanyar da Mr.
Hawkins zai canja min wani kenan.
Abinda Romilda ta fad'a yasa ta d'ago da kanta ta kalle ta.
"Bana tunanin zai tab'a bari hakan ta faru, sai idan har ba zai shafi dalilin da yasa ya shigo cikin rayuwarki ba."
A lokaci d'aya sai zuciyarta ta cilla kan wannan tunanin da itama ya d'arsu a ranta.
Wane dalili ne ya shigo dashi cikin rayuwarta?
"Barkanki da zuwa!
Kina da appointment ne yau?"
Receptionist d'in Clinic d'in ta tambaya a lokacin da Fadeelah ta tsaya gaban kantar ta.
Ba sau d'aya ba sau biyu ba, tasha tantamar shekarunta a cikin kanta, don wani lokacin sai tayi kama da babbar mace wani lokacin kuma yarinya, gashinta a kullum zube yake a gefen kafad'unta bak'i sid'ik yasha gyara yana kyalli, sannan idanunta kalar ruwan toka ne da duk sanda ta kalle su sai taji kamar tana son ta nemo wani abu daga cikinsu.
"Bani da appointment yau, nazo ganin Dr.
Florence ne."
Tayi mata wannan murmushin da kowacce sakatare ke mannawa a fuskarta sannan ta juya kan computer, ta danna harafan da suka had'a sunanta.
"Kin goge appointment d'inki na ranar Asabar baki zo ba, haka ne?"
Haka ne.
Bata zo satin daya wuce ba, wannan satin data yanke shawarar zuwa wajen Adam a Alhamis d'insa, a juma'a kuma ta had'u dashi ya bata sunayen topics d'in, saboda haka Dr.
Florence bata da masaniyar alak'ar ta dashi kenan ko kuma dukkan abinda ta rubuta game dashi a cikin jotar ta, Ta ayyana a ranta cewa bayanin da zata yi mata zaiyi tsawo kenan.
"Kiyi hak'uri amma rashin zuwanki yasa kinyi missing sak'on Dr Florence, ta tafi wani aikin garin Alaska ranar Monday kuma sai nan da sati uku zata dawo, saboda haka yanzu file d'inki yana hannun Dr.
Martins in kina so zaki iya ganinsa yanzu don yana ciki."
Sai tayi shiru kawai tana kallonta, kwakwalwarta na k'irga adadin sati uku a cikin kanta, don ba sai tayi tunani ba ko ta laluba, zata jira ta ne har zuwa sanda zata dawo kamar yadda ta tab'a yi lokacin da Dr.
Gibert yaje New York tsawon wata guda.
Don ta tsani cewar duk sanda likitanta yayi tafiya sai taje ta maimata abubuwa da dama a wajen wani sabon, sannan in ya dawo kuma ta sake maimata abinda aka d'ora ga wanda ya dawo.
Matsalarta ma a yanzu Dr.Martins ba zai fuskance ta ba, ta san shi sarai wani dattijon likita ne mara fara'a, sab'anin Dr.
Florence mace mai sanyi hali da juriyar sauraro.
"Ba sai kinyi min booking appointment ba, zan dawo wani lokacin."
Ta fad'i hakan tare da wani d'an guntun murmushin dake tsayawa iya fatar baki.
Lokacin da ta nufi k'ofar fita daga clinic d'in, zuciyarta ta gaya mata cewa a yanzu k'addarar mu'amalarta da Adam a hannunta take!
A daidai bakin k'ofar, wata tsohuwar Baturiya ta bud'e ta shigo hannunta rik'e da sandar dogarawarta, a lokaci d'aya Fadeelah taji kanta ya sara sanda ta kalli sandan, kamar kwakwalwarta na son tuna mata wani abu data sani a baya game da irin sandar, kanta ya fara
juyawa a take sannan idonta ya fara yin duhu daga hasken ranar dake dallare a ko'ina.
Ta shiga k'ok'arin rik'e bangon gefe lokacin da abubuwa da yawa suka shiga faruwa a cikin kanta, abubuwan da suka fi yi mata kama da tarin muryoyi na jama'a kala-kala wanda ta kasa fahimtar me suke fad'a da wani irin sauti da take jinsa kamar reza na yanka cikin kanta.
"Lafiya?
Me ya faru?
Wata murya daga gefenta ta tambaya.
"Me ya same ta? ku rik'e ta."
Wata muryar a zahiri ta sake fad'a da turanci, hakan ya tuna mata cewar a cikin clinic d'in nan take inda a yanzu za'a iya kwantar da ita a kira su Mami cewar bata da lafiya bayan alk'awarin da tayi wa kanta cewar zata fuskanci dukkan matsalolinta a yadda rayuwa ta kawo mata, kuma ba zata sake yarda ciwonta yayi galaba a kanta ba.
Sai ta saki bangon ta mik'e tsaye sosai ta kalli mutanen dake shirin taruwa a kanta ta cikin dishi-dishin idanunta tace musu lafiyarta k'alau babu komai.
Hankalinta yayi nisa da tunaninta lokacin da ta bud'e k'ofar ta fita, banbancin tafiyarta da gudu kad'an ne, don tana iya jin yadda k'afafunta ke dukan k'asa da k'arfi kamar mai shirin had'a wani sauti na kid'a.