← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 95

Sashe 90

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dole ne ma ya ajiye komai a gefe ya gayawa Fadeelah gaskiyar manufar aurensu, don ba lallai ne nan gaba ya iya cigaba da yak'i da zuciyarsa akanta ba, ya gaji da kokarin da yake yi wajen b'oye mata yadda zuciyarsa ke ji game da ita don haka zai fad'a mata gaskiyar komai, amma kuma kafin nan sai ya tanadarwa kansa dauriya don in har bata fahimce shi ba, dole ne ya fuskanci juriya mafi tsanani a rayuwarsa na cigaba da zama tare da ita a haka har zuwa lokacin da zata karb'e shi a matsayin mijinta, don ba zai tilasta mata ba kuma ba zai tab'a rabuwa da ita ba.

Bayan yayi wanka tare da canja kayan jikinsa ne ya gabatar da sallar magriba sannan ya kira Sa'id game da maganar aikin da suke kokarin nemowa Awwal.

Daga nan ya fito ya nufi kitchen inda ya same ta kamar kodayaushe tana k'arasa ayyukanta.

Ya kai hannu ya kwankwansa kofar kitchen d'in kad'an tare da yi mata sallama.

"Wa'alaikum salam."
Sassanyar muryarta ta amsa masa sanda ta juyo kalle shi, tana nan dai cikin shigarta ta d'azu amma ta gyara d'aurin d'ankwalinta a yanzu, ta hana shi ganin gashinta.

"Me kika dafa mana?

Yunwa nake ji."
Tayi murmushi kad'an wanda yake nuna jin kunyarta, yanayin kunyarta dake burge shi a kullum, don abu ne da bai saba gani ba.

Fadeelah ta d'an had'iye wani abu a cikin bakinta, ta yarda yana daga cikin jerin dad'in duniya, ace mijinka ya fita waje
"Ban san me kake tunanin ci ba, amma dai
na dafa abinda nayi tunanin zaka so."
"Duk abinda kika dafa shi nafi so Fadeelah, ina son duk abinda hannunki ya tab'a."
Sanda ya fad'i haka ya lura wani abu ya gifta cikin idonta kuma a take murmushin fuskarta ya d'auke, me ya faru?

Ko dai ya fad'i wani abu ba daidai bane?

Ganin da gaske damuwa na k'okarin sauka a fuskarta, sai ya d'ebe zancen da cewa.

"Naga abincin amma zuwa nayi in tambaya ko za'a zo a taimaka a zuba min, don naji ance abinci yafi dad'i in wanda ya dafa ne ya zuba maka."
Sai tayi kokarin sake wani murmushin, hak'oranta masu kyau suka haska kafin ta gyad'a kai ta biyo bayansa zuwa dining d'in, yaja kujera d'aya ya zauna sannan ya ajiye wayarsa akan table d'in yayin da ta k'araso ta shiga bud'e kwanukan don zuba masa.

K'amshin fatan dankalin turawa na flask d'in farko yasa cikinsa ya d'aure, yunwar dake tare dashi tun safe ta taso.

"Dan Allah ki gaya min makarantar girki kala nawa kika yi?"
Ya tambaya muryarsa k'asa-k'asa lokacin data fara zuba masa kalolin abincin, ta kalle shi da gefen idonta, wani kallo da yaji yana shirin mantar dashi komai ya har kuwa da yunwar dake damunsa.

"Ni banyi catering school ba ko daya, a wajen Mami kawai nake koya."
"Koya?

A hakan? ai na tabbata kinfi wasu malaman da yawa iyawa, don haka watakila nan gaba zamu bud'e tamu makarantar mu ma."
Nan take yaga wannan damuwar ta sake baiyana akan fuskarta, ko dai yana fad'an wani abu ne da ba daidai ba? ko kuma tunani take babu 'Nan gaban' daya ambata ne a rayuwarsu?

Ta gama zuba masa abincin tare da lemon abarba mai rangwamen sanyi a cikin kofi sannan tayi niyyar komawa ta cigaba da aikinta amma ya tsaida ita.

"Ki zauna ki taya ni ci mana."
Ta girgiza kanta." Naci nawa tun d'azu."
Shima ya girgiza nasa kan.

"Wannan ba tsari bane gaskiya, daga yanzu ko zaki ci abinci ki dinga ci kad'an yadda idan na dawo zamu ci tare, inaga kamar hakan zai fi ko?"
Hukunci ya yanke, kuma ya tambayi shawararta duk a lokaci d'aya, sai kawai ta gyad'a kanta sannan taja kujerar ta zauna, ta d'auki plate d'aya ta zubawa kanta jollof d'in wata macaroni mai siffar shinkafa 'yar kad'an sannan ta tsiyaya lemo, amma ba k'amshin abincin take ji ba, k'amshin turarensa kawai hancinta ke d'auko mata wanda ya had'u ya cakud'e dana sabulun da yayi wanka.

"Ba zaki ci naman ba?"
Ya tambaya yana miko mata flask d'in da ta zuba mm asa farfesun kifi, sai ta girgiza kanta.

"Idan naci abincin da yawa zai cika min ciki."
Ta fad'a a hankali, ya lura har a lokacin yanayinta bai dawo daidai ba saboda haka yayi tunanin bin wata hanyar daban.

"Kin san lokacin da ina America akwai wani a office d'in mu sunanshi James, yana da k'iba sosai da k'aton timbi kuma mutane suna yawan tsokanarshi akan hakan, kawai watarana sai yazo ya sanar cewa yayi joining wani gym na six months zai rage k'iba don haka ya koma vegetarian ya daina cin duk wani kalar nama."
Ta d'ago tana kallonsa da wani guntun murmushi a a gefen lebbenta, don duk sanda yake magana tana mamakin hirarsa, a fuska irin mutanen nan ne da zaka yanke musu hukuncin miskilanci cikin rashin sani,
don sai kana kusa dasu zaka yi mamakin yadda zasu dinga zaro magana soi-soi kamar ba daga bakinsu take fitowa ba.

Yana kokarin cin naman ya cigaba da cewa.

"Ba'a dad'e ba sai ranar Thanksgiving tazo, aka had'a babban party kuma aka yanka talo-talo masu yawa, kowa ya san James baya cin nama don haka ba'ayi serving d'insa ba, ashe shi kuma yana ta kwad'ayin naman ba wanda ya gane, sai can da aka kusa tashi Mark ya zagaya zai shiga band'aki unexpectedly yana bud'e k'ofar na farko kawai ya ganshi zaune kan toilet d'in ya d'ebo sauran nama da k'ashin da aka ci yana ta
kokawar ci..."
Fadeelah ta tuntsire da dariya tana rufe fuskarta, don a yadda yake bada labarin haka shima yake kokawa da nasa naman, ita bata hango wani James ba shi kawai take gani.

Adam ya kalle ta sannan ya kalli hannunsa dake rik'e da fork yana kokarin gutsirar nasa naman, ya lura da abinda ta fahimta don haka cikin turanci yayi sauri yace.

"Da gaske nake miki fa, haka Mark ya kama James d'in ba wai santi nake yi ba."
Ina, Fadeelah kawai dariyarta take yi, da ya sake kallon hannun nasa bai san lokacin da shima ya fara dariya ba, don a baiyane yake cewa santin yake yi kuma babu da abinda zai iya kare kansa dashi.

Ya sake kallonta, yana sauraren yadda sautin dariyar tata ke fita a hankali kamar ta 'yar yarinya, me yasa ne take rufe fuskarta?

Yana son yaga yadda idanunta zasu haska da kyallin dariyar.

"Kin manta kuma baki tambaye ni zancen matar ba?"
Sakewarta yasa ya tuno mata da labarin daya bata jiya, akan case d'in wani mutumi ya kawo musu k'arar matarsa, cewa tayi yunk'urin sace takardun filayensa, shi kuma ya lura da hakan kafin ta d'auka saboda haka ya canja takardun dana bogi ba tare da ta sani ba don a yanzu haka ita har ta nemi dillali an saka filayen a kasuwa, shine yazo ya kawo case d'in maaikatarsu a matsayin wani ne ya gane don a tsorata ta kawai.

Ta d'ago ta kalle shi da zumud'i a fuskarta tace.

"Tazo?

Me ya faru?"
Ya k'arasa tauna abincin bakinsa sannan yace.

"Abinda mijinta ya fad'a ne ya faru, ta tsorata sosai don mun ce mata ne za'a kai case d'in kotu, tayi ta rok'o tana rantsuwar cewa ba zata sake ba zata mayar masa da takardunsa."
Yana kallon yadda kafad'unta suka yi k'asa a hankali kafin tace.

"Sai naji mijin nata bai kyauta ba kuma."
"Saboda me?" Ya tambaya "Sata fa tayi niyyar yi masa."
"Na sani, amma ina ganin bata haka ya kamata ya hukunta ta ba, tunda ya san tana da tsoro sosai bai kamata ya kawo ta har wajen hukuma ba."
Ya d'auki kofin lemonsa ya kurb'a a hankali yana kallonta.

"So what's your own view?" (yaya kike ganin ya dace ayi?)
Ta d'an cije lebb'enta kad'an.

"Kamata yayi ya zauna su magance matsalar iya su kawai, a tunani na matarsa sirrinsa ce bai kamata ya tozarta ta a wajen wasu ba in har yana sonta, laifi tayi masa amma tunda har ya gane, sai ya zaunar da ita ya nuna mata kuskurenta sai in bata ji bane sannan ya d'auki wani matakin daban amma shima ba wanda zai had'a da hukuma ba.

Watak'ila ma yana da hali ne amma baya d'aukan d'awainiyarta, ko kuma tun farko basu sami fahimtar juna ba bai san komai nata ba balle har ya san matsalolinta."
Adam bai san me fuskarsa take nunawa ba a wannan lokacin, ya san dai kawai idan wani zai hango shi daga nesa zai ce yana zaune ne rik'e da kofi a hannunsa yana kallonta da idanunsa dake cike da d'imbin abubuwan da ba zai iya furtawa ba.

Amma a cikin kansa tunani yake lallai tana da zurfin tunani, ,and he likes smart women._ sannan kuma in har ta san wannan to watakila ba lallai ne ya samu matsala wajen gaya mata abinda ke zuciyarsa ba, waya sani ma idan yayi sa'a ta fahimce shi, amma kuma mai tace?

Cewa tayi
'in har yana sonta.." Ya manta ne cewa shi bata son sa?

Wajen k'arfe tara na dare bayan ya dawo daga masallacin isha'i, ya same ta tsaye akan d'aya daga kujerar dining tana kokarin d'auko wani abu a shelf d'in dake sama, sai d'age take yi don hannunta ya kasa kaiwa.

"Me kike yi?" Ya tambaya yana jingina da bangon gefe, hannayensa sunk'e cikin aljihu.

"Wad'annan containers d'in nake son in d'auko in ga ko zan iya zuba abu a ciki."
Sai ya gyad'a kansa a hankali ya cigaba da kallonta, tana ta kokarin mik'a hannu amma ko kusa baya yi, in ta mik'a da yawa kuma sai kujerar tayi kamar zata tuntsira.

Abin yaso ya bashi dariya, sai dai ganin da gaske ta kasa yasa ya matso ya hawo kujerar don ya taya ta, sai dai me?

A lokaci guda wannan k'amshin nata ya buso shi don ya tsaya ne kusa da ita sosai saboda yanayin kujerar, zuciyarsa ta matse a daidai lokacin da ta shiga k'ok'arin sauka k'asa amma sai kujerar ta tafi kamar zata hantsila dasu don haka bai san sanda ya saka hannunsa na hagu ya rik'o k'ugunta ba.
Chapter 90 · 0% Book details