Sashe 12
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma ina fatan dukkanin mu mun k'aru daga bayanan da muka ji, Sannan akwai wani babban abu dana ke son in jawo hankalinmu akai, dole ne sai kowanenmu sai yayi taka tsan-tsan da kewayensa da kuma irin mutanen da zai dinga mu'amala dasu a yanzu.
Idan baku manta ba a shekarar data wuce ne cikin daren ashirin da bakwai na azumin Ramadan muka sami labarin kashe wata yarinya 'yar shekara 17 da daddare bayan ta fito daga McDonald's bayan gama cin abincin Iftaar d'inta zata koma masallacin k'ungiyarsu don yin sallar taraweeh, mutane da yawa sunyi kuka kuma sun jajanta akan tunanin wace irin America muke ciki da har za'a samu masu kashe yarinya k'arama irin haka don kawai tace ita musulma ce.
Saboda haka ya kamata mu iyaye musa ido sosai akan 'ya'yanmu, a lokacin yarintarmu da ake mana kallon bare, yafi sauki akan yanzu da 'ya'yanmu ke fuskantar zalinci da muzantawa k'iri-k'iri, don haka dole ne a kullum mu tashi da wannan tambayar a cikin kanmu...
Ta yaya zamu kare kanmu da kuma 'ya'yanmu daga irin wad'annan mutanen?"
Wani k'aton abu da Fadeelah bata san menene ba ya wuce ta cikin mak'ogwaronta, akasin tunanin kowa a wajen nan shine nata tunanin, kowa na gudun mutanen dake tozarta su, ita kuma a yanzu take shirin kai kanta ga d'aya daga cikinsu.
A take fuskar Adam ta haska a cikin idanunta, ko kuma yanayin fuskar, tunda bata tab'a bawa kanta damar k'are masa kallo ba balle har kammaninsa su zauna cikin kanta.
Wane tabbaci take dashi a yanzu cewa alak'ar dake shirin faruwa a tsakaninsu bata da aibu?
Abinda Melissa ta fad'a gaskiya ne, ya kamata ta binciki dalilin da yasa ya kawo kansa cikin rayuwarta, ba zai yiwu ace daga Mr.
Hawkins yayi masa magana ne zai amince ya b'ata lokacinsa akanta ba, ita d'in dake cikin jerin al'ummar da yake nuna tsanarsu a fili.
A lokacin da taron ya k'are suka koma cikin mota don tafiya gida, a lokacin ta d'auko jotarta ta rubuta.
Asabar, 11:30am
Bani da tabbacin abinda nake shirin yi.
Adam yasha had'uwa da mata kala-kala, dubunnai ma a tak'aice, manya da k'anana, masu burin cusa kansu cikin rayuwarsa ko don wani abun daban.
Kuma a duk cikin yawansu, baya tab'a maida hankalinsa kan rik'e sunayensu, sanin kamanninsu ko kuma tuna wasu 'yan k'ananan abubuwan daban, misali idanunsu.
Saboda kusan duka d'auke suke da sak'onni iri d'aya, hank'oro, fata, buri, naci, ko kuma jin kai.
Amma nata idanun suna da banbanci, banbanci daga na duk wata halitta da ya tab'a gani a duniyar nan.
Ya tuna ranar daya fara lura da hakan, wata safiyar laraba, tana tsaye daga jikin allon sanarwa tana karanta wani abu, wani abu da ya riga ya gama sanin menene, domin duk sanda zai hangota a wajen, zai kasance sanda suka gama manna fastocin ne.
Yaji zuciyarsa ta tsaya kamar yadda yake faruwa duk sanda ya ganta, yaji ba zai iya yin gaba ba tare da yaga yanayinta ba, yanayinta da baya tab'a canjawa a duk irin lokutan da yake ganinta tsaye a jikin lokarta.
Saboda haka ya juyo ya dawo wajen allon, ya samu kansa da tsayawa daidai bayanta sannan ya karanta abinda ya rubata da hannayensa cikin harshen turanci.
Zanga-Zangar da za'a gudanar don hana mata saka Hijaab!
Jin alamun mutum a bayanta yasa ta juyo da sauri, yana tsaye dab! da ita ne don haka fuskokinsu suka yi kusa sosai, idanunsu suka had'u na wasu sakanni kafin ta matsa baya da sauri.
Sai dai shi ya kasa motsin ya kuma kasa d'auke idonsa daga kanta, rana ta farko kenan a rayuwarsa da ya fara tsayawa kusa da ita haka, ya kasa daina kallon kyakkyawar fuskarta dake nad'e cikin mayafin dake nuna shaidar addininta, sannan kamar kullum idanunta na manne da siraran glass d'in da ya k'ara fito da ilhamarta, idanunta kyawawa masu maik'o da kyalli, suna haskawa kamar an kunna wuta ta k'asansu.
Sai dai mafi rincab'ewar al'amarin tana masa kallon tsana ne! tsana wadda ke tasowa tun daga k'asan zuciyarta, tsana wadda baya tunanin wani mahaluki ya tab'a yiwa waninsa, sannan tsana irin wadda bai san dalilin wanzuwarta ba, don ko a cikin...
Wani dunk'ulallen naushi ya ziyarce shi a tsakiyar bayansa, bai tab'a wajen ba balle ya juya sai ya d'ora tissuen hannunsa kawai akan hancinsa dake zubar jini.
"Meye haka kuma Alex, na zata kun gama wasan?"
Muryar Matar dake amsa sunan mahaifiyarsa ta fad'a lokacin da take k'arasowa hannunta d'auke da towel da kuma robar ruwan d'umi.
Kowacce ranar Asabar, rana ce da suke wasan dambe (Boxing) shi da mahaifinsa kuma yawanci shi yake yin nasara, amma yau rana d'aya da Mahaifin nasa 'Alex Steve' ya cinye shi sai murna yake yana k'ara kawo masa wani naushin akai-akai yana fad'in cewa kar ya damu kansa da zafin, zai rayu.
"Nasha fad'a muku bana son wasan nan ko kad'an don banga amfaninsa ba, ta yaya ma za'a kira wannan da sunan wasa?
Kalli fa irin raunin dake jikinka, meye amfanin hakan yanzu?"
Ta fad'a tana danna masa tawul d'in a gefen idonsa, Adam ya lumshe idonsa a hankali yana sauraren mitar tata, sannan kuma yana jin yadda jikinsa ke amsawa da ciwo, kamar gab'ob'insa sun kumbura ne saboda tsabar duka da naushin daya sha kota'ina.
Wanda abu d'aya ne ya jawo masa hakan, tunanin wad'annan idanun da bai tab'a ganin abu makamancinsu ba.
"Ka tabbata ba abinda ya sameka?" Ta tambaya tana zuro kanta gefen fuskarsa.
Yana jin yadda dogon gashinta ya sauka a jikinsa sai ya mik'e tsaye kawai ya girgiza kansa.
"Ba abinda ya same ni, ina jin na gaji ne kawai."
Kusan hakan ne kuma, ciwon jikinsa bai dame shi ba, gajiya ce kawai a tare dashi, gajiyar da yake so yaje ya kwanta yayi barci ko ya samu ma kwakwalwarsa ta wanke tunanin da ya tashi dashi a yau.
Tunanin idon wata yarinya.
"Ina ganin zanje in d'an kwanta."
Ya fada sanda ya k'ara share jinin hancinsa.
"Amma baka ci abinci ba fa, ta yaya zaka kwanta cikinka ba komai?"
"Bana jin yunwa.."
"Ban yarda ba, dole ne kaci wani abun, ba zai yiwu weekends ma ace baza kaci wani abun kirkin ba..."
"Mum..!" Ya kira ta da sunan da ya san dole ne ta saurare shi, sai ta juyo daga k'ok'arin tafiya hanyar kitchen d'in da take ta kalle shi, hannunta rik'e da towel d'in nan.
"Bana jin yunwa, zan ci idan na tashi okay?"
Ba zata iya yi masa musu a yanayin da yake yanzu ba, baza ta taba iyawa ba... saboda haka ta d'aga kanta kawai tana kallonsa da idanunta masu cike da ramin da take so ya cike su, wani abu kuma da ta san ba zai taba faruwa ba.
Ya nufi hanyar d'akinsa a hankali, d'akin da ya shafe shekaru a cikinsa yana gina rayuwar da ba tasa bace, rayuwar da kuma baza ta tab'a zama tasa ba.
Ya saka muk'ulli ya k'ulle kofar sannan ya kife akan gadonsa, fatan iyayensa a yanzu wani abu ne da yake wa kallon fitar rak'umi ta ramin allura, don ba zai tab'a kasancewa ba, lokaci ya riga ya tafi da abinda ya shud'e kuma babu wanda ya isa ya dawo dashi baya!
A yanzu ba abinda yake fata da buri, irin tsarinsa ya tafi daidai, komai ya tafi babu tangard'a, kuma da alamun nasara tunda a yanzu zai fara taka mataki na farko a hanyar samun mafitarsa.
Oh God!
Idanunta suka haska cikin kansa, Me yasa ne k'addara ta had'a hanyarsa da tata? wane tabbaci yake dashi a yanzu cewa alak'ar dake shirin faruwa a tsakaninsu baza ta kawo masa matsala ba?
Da daddare a wannan ranar, bayan dukkan harkokinsa basu goge hoton idanunta daga cikin kansa ba, wani b'ari na zuciyarsa ya tabbatar masa cewa bashi da tabbacin abinda yake shirin yi.
RANAR MONDAY.
Fadeelah ta kalli kanta a mudubi, ta gyara zaman nad'in d'in hijaab d'inta sannan ta furtawa kanta cewa zata iya!
*BAYAN NA MUTU!*
AYSHA SHAFI'EE
*06*
A karo na goma sha ya d'aga kansa ya kalli k'ofar, babu alamun an tab'a ta ma balle yasa ran shigowar wani, ko kuma ita d'in da ya ke zaman jira fiye da mintuna goma sha biyar a yanzu.
Ya sake kallon agogonsa, ya rantse a cikin ransa cewa minti biyar in ta k'aru akai zaiyi tafiyarsa ne, ba zai b'ata awa gudar daya sadaukar cikin lokacinsa a banza ba.
Baza ta so kasancewarta tare dashi ba ya sani, don haka ba zaiyi mamaki ba in har bata zo, sai dai in bata zo ba zata b'ata masa tsarinsa ne, zata k'ara masa nisan hanyar da zai kai ga manufarsa alhalin yana ganin ya biyo gajeriyar hanya.
Ya janyo jakarsa dake gefe ya bud'a aljihun gaba, ya san ba zai rasa wani abin ci ba, don ka'ida ne kullum mamansa sai ta saka kayan cima kala-kala cikin jakar, a nata tunanin wannan sabuwar kulawar zata sa ya manta komai, zata sa ya manta k'aryar da suka raine shi a ciki.
Ya zaro ledar wani biscuit mai chocolate, ya bud'e ya fara ci a hankali yana lumshe idonsa, a shekarun baya rayuwarsa bai-bai take, kamar wanda ya saka riga gaba a baya ne yake ta harkokinsa, sai a yanzu daya ankara ya shiga fafutukar juya ta.
Ya jingina sosai da kujerar da yake kai sannan ya sake kai biscuit d'in bakinsa a karo na biyu ya tauna, zuciyarsa na gaya masa cewa zai cimma manufarsa, zai tsallake duk abubuwan dake gabansa kuma zai kai ga manufarsa da yardar ubangijinsa!
Abinda bashi da tabbacinsa guda biyu ne, gwagwarmayar da zai gamu da ita, da kuma lokacin da komai zai k'are, sannan ga matsalar ciwonsa ma, bai sani ba ko hakan zai shigo cikin hanyarsa, amma alkawari yayi wa kansa cewa ba zai k'ara dosar hanyar asibiti ba, yana da nasa hanyoyin da zai saita kansa.
A daidai wannan lokacin k'ofar ta bud'e, Idanunsa ma suka bud'e a lokaci d'aya, ita d'in da yake jira ce ta shigo, sanye cikin doguwar riga da nad'in da ya rufe gashinta, ta rataya jakarta sannan ta rik'o wannan folder a hannunta.