← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda haka sai ya k'ara haskawa cikin kalar kayan, ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ebi wayoyinsa ya fita zuwa falo don samin abinda zai ci.

Allah ya sani yayi kewar girkin Mami da Fadeela kamar me!

"A'a ga Ango fa ya fara kyallinsa tun yanzu."
Muryar wata daga cikin 'yanuwan Mami ta fad'a a sanda ya sanyo k'afa daga corridor zuwa cikin falon.

Zuciyarsa ta sake ruftawa cikin raminta sanda ya d'aga ido ya kalle su,
'yanuwa Mamin tasa ne da yawa a falon sannan ga kaya ma birjik ana ta hayaniya...

Hayaniyar shirye-shiye...

Shirye-shiryen aurensa da Hamida...

Hamida dai 'yar kawar Mami...

Mami dake tsakiyar falon a zaune fuskarta cike da farin ciki...

Farin cikin ganin komai na tafiyar mata daidai ba tare da ta san me suka yi ba...

Abinda suka yi shi da mahaifinsa!

Na zuwa neman Auren Fadeelah har Nigeria da sanya ranar bikinsu kafin ma nata data dad'e tana tanadinsa!

Ga dai Adam a garin Abuja.

Ga Fadeelah a garin Abuja.

Sannan ga mutanen Ikara har biyu,
Sa'id da Sadiya mai aikatau a garin Abuja.

Sannan kuma ga shirye-shiryen biki shima a garin Abuja.

Can k'asar turawa kuma ga Al'ameen tsumu-tsumu cikin k'arya da ya rufewa Fadeelah da kuma mahaifiyarsa dake shirin yi masa aure!

Toh me kuke tunani zai zo a gaba?

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
*22*
BAYAN WATA GUDA
Rayuwa ta cigaba da gangarawa a kowanne b'angare na duniya,
abubuwa na faruwa wasu kuma na shud'ewa, mutuwa, haihuwa, arziki,
talauci, mulki, nasara, shirye-shirye,
cikin wad'annan abubuwan babu d'aya da lokaci ya tsaida su.

A cikin haka ne kuma shirye-shirye da lokacin da su Daddy suka tsayar na auren Fadeelah da Al'ameen ke gabatowa, saboda haka sai ya zama kusan dukkan hidima irinta bikin Aseeya ta dawo kan Aunty Hadiza da kuma Mami wadanda suka tsaya akan abun, banda su ma Fadeelah ta lura kowa nata 'yan shirye shiryensa,
babu irin su Zahra dake ta tanadin kaya set-set wanda zasu shiga su fita su kuma gwangwanje kamar yadda suke fad'i.

Sannan su Farouk da Usman ma na shirin had'a Cocktail su da abokanansu a cewarsu Aseeyah bata barsu sunyi komai da bikinta ba, ga Hajiya Amarya ma data ce zata karrama mai sunanta tayi yininta guda a gida, kowa dai nata 'yan shirye-shiryensa banda ita...

Ita d'in da take ginshik'i kuma Amaryar bikin.

A kullum ta tashi ta kalli hasken safiya, sai ta tambayi kanta wace irin rayuwa take yi ne?

Ita ko a labari bata tab'a jin mutum mai cakud'addiyar k'addara irin tata ba.

Misali game da ciwonta, a da bata tab'a barin kwakwalwarta ta yarda cewa ciwonta nakasa ne ba balle har ta nuna raunin da wasu zasu tausaya mata,
amma a yanzu hannu biyu tasa ta karb'i cewa kwakwalwarta ba daidai take da ta sauran mutane ba, ita d'in mai lalura ce da abinda ya raba ta da MAHAUKACI kad'an ne.

Saboda in ba rashin hankalin ba ta rasa abinda tunaninta ke janta akansa yanzu,
ita fa ta damu da Al'ameen d'in nan har ta bashi hanyar daya sake neman aurenta a karo na biyu, amma a yanzu duk sanda ta gama waya dashi, sai komai ya tsaya mata cak!

Ta kasa farin ciki, ta kasa sakewa kuma ta kasa karb'ar al'amarin hannu biyu duk da irin kulawar da yake nuna mata.

Mami tace wai hakan ba wani abu bane, wai duk macen da za'ayi bikinta haka take ji, wai shi auren wani abu ne mai girma dake canja rayuwar d'iya mace.

Amma wallahi ita abinda take ji a ranta gani take yafi k'arfin taraddadin aure, ji take kamar mutuwarta ce ke shirin k'arasowa, kamar a kowanne motsawar lokaci zata iya bud'e ido taga mala'ikan d'aukan rai a gabanta ko kuma taji nauyin k'asar kabari akanta.

Bayan haka kuma ga wani azababben k'ulafacin son 'yanuwanta daya fara damunta, wad'annan dai 'yanuwan nata da bata iya tuna ko fuska d'aya a cikinsu, saboda da ace ana samun d'an adam d'in da yake zuwa babu dangi a duniya, da tuni ta dad'e da saka kanta cikin wannan layin.

Amma sanin cewa dole tana dasu d'in ne yake sawa in ta waiga taga Mami nata shirye-shiryen bikin, sai ta hango lokacin na Aseeyah da gabad'ayansu Mamin harda mahaifiyarta ake ta wannan hidimar, amma ita yanzu inda za'a d'auke harkar mutuntaka da kuma kyautatawa babu d'aya a cikinsu da zai mata wannan wahalar.

Da a cikin DANGINTA take fa?

Tare da iyayenta wad'anda suka haife ta, ta san ko babu kyautatawar ita hakk'i ce akansu da dole ne su sauke, suna ma tunawa da ita a yanzu?

Ko suna ma da rai tukunna?

Tunda kafin zamanta ya koma wajen Hajiyar Daddy a wancan lokacin anyi cigiya kamar wanda ya yar da kwabonsa na k'arshe a duniya amma babu wanda yazo yace shi d'anuwanta ne, hakan ne yasa a baya ta cire tunaninsu a ranta ta rungumi rayuwar su Daddy kawai, amma me yasa komai ke shirin dawowa sabo a yanzu?

Da irin wannan abun da take ji me ya raba kwakwalwarta da matakin hauka ?

"Kara ta sosai mana a wuyan na gani in ta zauna,
kin san ba mai saukowa bace."
Mami ta fad'a tana kallon Fadeelan dake zaune akan stool na gaban mudubi tana rik'e da d'aya daga cikin sark'okin da suka baje akan gadon d'akin, wata 'yar k'aramar riga ce a jikinta dake nuna bata dad'e daga tashi daga bacci ba amma su Mami har sunje siyayya sun dawo.

"Wai tsoron sarkar kike ji ne?" Fatima dake ta fito da wasu daga kwalayensu ta fad'a tana kallon fuskarta ta cikin mudubin.

"Naji kamar tana da nauyi ne." Muryarta ta amsa a hankali.

"To mik'o ta nan tunda kika ce nauyi Deelah na san ba sakawa zaki yi ba."
Ta juyo a hankali ta mik'a mata idonta na kallon sauran kwalayen sark'okin.

A satin daya wuce ne Al'ameen ya aikowa Mami da zunzurutun kud'in da bata san wane adadi na miloyoyi suka tsaya a kid'in Nigeria ba da cewar ayi mata siyayyar kaya (lefe kenan) da kuma wani sh'ani na bikin.

Bata san me yasa ba amma haka kurum jikinta yake bata cewa bikin nan ba daidai yake da kowanne ba, akwai wani abu tsakanin Al'ameen da Mami da suke b'oye mata, sai dai bata da hujja ko shaidar menene shi.

"A cikin atamfofin nan akwai wata mai lemon gree da milk ko?" Mami ta tambaya tana kallon Fatima.

"Anya kuwa kamar lemon green da brown ne sai wata mai lemon green kawai koh?"
"A'a gaskiya ni naga mai irin wannan kalar, yaya Hadiza ce fa ta d'auko ta ma ina tunawa."
"Toh bari in duba." Cewar Fatima ta mik'e ta tafi can d'akin Mamin inda kayan suke.

A lokacin ne kuma Fadeelah taga dama ce gareta da zata fad'awa Mamin abinda ke cin ranta.

"Mami."
Ta kira sunan da dukkan dauriyar da take da ita a lokacin.

"Al'ameen har yanzu bai fadi inda zan zauna ba, kunyi maganar dashi ne?"
Zata iya rantsewa wani abu ya gifta cikin idon Mamin kafin ta girgiza kanta tace.

"Bamu yi ba deelah, amma me yasa zaki damu kanki tunda dai ai in an d'aura auren ba zai barki anan ba."
"Mami karatuna nake tunani,
so nake in san matsayarsa tun tanzu kafin a koma hutun."
"Fadeelah karatu ba matsala bane, duk inda ya d'auke ki ya kaiki a duniya zaki cigaba da yinsa, nasha gaya miki Al'ameen bashi da matsala ko kad'an, wallahi duk abinda kike so shi zai yi."
"To Mami Aunty Miryaamah fa?

Ni fa har yanzu banji kuna zancenta ba, banji ana cewa suma suna nasu shirin ba, sannan shima banda lokacin da yace min ta amince da zancen auren baya tab'a son in d'auko masa zancenta, dan Allah Mami in da wani abin ki fad'a min."
Ka san abinda mutum yake ji a lokacin da yake son nusar da k'aramin yaron da mahaifiyarsa ta mutu cewa ba zata tab'a dawowa ba?

Sak haka Mami taji sanda Fadeeelah ta fad'i hakan, ta yaya zata gaya mata cewa Aunty Miryamah bata san da zancen auren nan ba kwata-kwata?

Ta yaya zata gaya mata cewa Al'ammen ya roke ta ne kamar hauka kan ta taya shi boye wannan sirrin don ya sami Fadeelah a rayuwarsa?

Ta yaya zata gaya mata cewa suna hasashen Aunty Miryaman zata saduda ne in taga an kai k'arshen komai?

"Mami, Mami, Umma ce ke kiranki."
Rahma ta katse komai sanda ta shigo cikin d'akin rike da wayar Mami da mahaifiyarta Aunty Hadiza ke kira,
bata jira konai ba kuwa ta kara mata a kunne.

"Yaya wayar na can falo ne wallahi..." Cewar Mami cikin wayar.

"Mrs.

Skeleton ya akayi ne?" Rahma ta fada sanda ta juyo ta kalle ta.

Wani murmushi ya subuce a kumatun Fadeelah,
tace.

"Nice kwarangwal d'in?"
"To ba gashi nan ba..." Ta amsa tana zama a gefen gadon.

"Duk kin bi kin fita haiyacinki tun yanzu."
Ko waye a takalmina zai fita haiyacinsa Rahma.

Ta amsa hakan a cikin tanta ba tare da ta furta ba.

"Kinga deelah..." Cewar Rahman tana kamo hannunta.

"Ki kwantar da hankalinki fa, Aseeyah tace min ba wani abu wallahi mijin ma watarana in kika tashi ji zaki yi haushinsa kike ji, sannan ko ni da zan auri miskilin yaya Saifudeen ban d'aga hankalina kamar ke da kullum Al'ameen d'in nan ke tare dake yana nuna miki kulawa ba."
A daidai sanda Rahman ta fadi haka,
wayarta ta zabi lokacin ta shiga ruri na alamar shigowar kira,
idonta ya kai kan sunan.

Al'ameen ne.

Ta juya ta kalli Rahma dake kallonta sannan Mami dake magana tana ta had'a sarkokin nan, da Fatima ta shigo a lokacin tana nuna wa Mami atamfar data d'auko, sai ta dawo da idonta kan wayar.

A wannan lokacin ta yarda cewa ba zancen karatunta ba, ba zancen wajen zama ba, ko zancen Aunty Miryaamah mahaifiyarsa bai isa ya canja k'addararta da Al'ameen ba, sai dai wani abin kuma daban, wani abu da zai shallake tunaninta!

RANAR D'AYA GA FARKON WATA.
Chapter 42 · 0% Book details