← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 95

Sashe 58

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ka kaini gida..."
"STEMI patient ce kawai ta farka ta fito." Nurse Hawwa ta bata amsa.

"Bibty dan Allah..."
Kwakwalwar Sadiq ta hargitse a lokaci d'aya don ya rasa me zai d'auka ya fara aika mata, magiyar Maryam, kukan Mahammad, hayaniyar Nurse d'in, ko kuma tambayoyin dake ta fitowa daga bakin 'yanuwansa...

Yaji ya zama tamkar wani mutum-mutumi ba abinda yake iya fahimta sai yadda hannayen Mairo ke jijjiga kwalar rigarsa da dukkan k'arfin da zata iya.

Bai farga da komai ba, sai sanda wannan Nurses d'in ta dawo d'auke da allurar da aka aiketa, bai san amfaninta ba amma ya tabbata idan ta shiga jikin Mairo zata sa ta k'ara fita daga haiyacinta ne, saboda haka yayi saurin had'eta da cikin jikinsa bakid'aya sannan ya juyar da ita gefe.

Sai hayaniyar ta ragu kowa a wajen ya tsaya kallonsa da mamaki.

"Alhaji, matarka fa bata gama warkewa ba, ba sallamarta akayi ba."
Mai rik'e da allurar ta gaza jinkirin b'oye mamakinta.

"Ba sai kun sallame mu ba Nurse, a barta haka, sauran da kuka yi ma ya isa."
"Ai ba zancen isa bane Yallab'ai, wannan patient dinmu ce a yanzu, kuma ba zai yiwu a bari ka fita da ita ba tare da sallama ba."
"Zamu tafi yanzu?" Muryar Mairo data sake magana, ta nunawa kowa a wajen cewa bata cikin hankalinta, don duk da shorun da akayi baisa ta juyo ta kalli kowa ba.

"Sadiq wai me yake
faru ne?

Me ya same ku
duka biyun?"
A yanzu mahaifiyarsa ce ta fad'i hakan, ganin har yanzu sun gaza fahimtar abinda ke faruwa.

"Mama gida zan take son zuwa."
Kusan a rikici yake don haka baiyi shawara da tunaninsa ba ya fad'i abinda ya rufe su a cikinsa tsawon shekaru.

"Wane gidan, naga duk gamu mun taho."
Ya girgiza kansa yana k'ara kallonta.

"Gida can wajen 'yanuwanta nake nufi."
"Yan'uwa?

Yaushe Maryam d'in ta samu 'yanuwa bamu da labari?"
"Pleaseee Bibty..."
"Ba'a dad'e ba, kuma dalilin ciwon nata kenan, shi yasa ta rikice take son tafiya."
"Don darajar ma'aikin Allah Sadiq..." Muryarta rawa take a yanzu, somi-somin kuka hakan ya d'arsa tausayinta a zuciyar duk wanda ke tsaye banda Nurses d'in nan, banda Nurses d'in nan dake hango query da zasu iua amsa in har basu maoda ita gadonta ba.

Daga inda take tsaye, mahaifiyarsa ta tsaya ta kalle ta, a shekarun zamanta kaf da Maryam ba zata iya tuna rana d'aya da ta b'ata mata rai da gangan ba, ita d'in mai tsananin biyayya ce ga mijinta da kuma su, har wasu a danginta na cewa tunda bata da 'yanuwa su ta same su ai dole ne ta rik'e su, saboda haka yadda take tsaye a yanzu ba tare da ta kalli d'aya daga cikinsu ba, kuma ta shige jikin Sadiq d'in da a gaban idonta ko hannunta bata bari ya tab'a, ya tabbatar mata cewar bata cikin haiyacin da zata fahimci komai sab'anin abinda take so.

"Abubakar ka tabbata ba matsala?"
A rayuwarsa kaf!

Sadiq ya san sau biyu ne ta taba kiransa da Abubakar, a ranar da ta kira shi a waya yana makaranta ta shaida masa zancen rasuwar mahaifinsa, sai kuma ranar da yaje mata da maganar auren Mairon, saboda haka ya tabbatar da ta fahimci halin da Mairon ke ciki, ta fahimci cewa idan aka maida ita cikin asibitin nan tabbas su dukkansu sun zalunceta.

"Wallahi babu matsala Mama, so take yi kawai ta gansu.."
"Alhaji mu fa ya kamata mu tabbatar muku da hakan ba ku da kanku ba, don haka ku bada ita a maida ta."
Bai ko saurari Nurse d'in ba ya cigaba da kallon Mahaifiyarsa wadda ke k'ara tambayarsa sunan garin 'yanuwan nata.

"Kaje ka kaita Sadiq, amma ku tafi tare da Zakkiyya ta rik'e Muhammad, don ba'a san abinda zai faru ba...

Insha Allah zuwa gobe zan turo su Umar su ga me ake ciki."
Wannan izinin na mahaifiyarsa, shi ya haddasa tafiyar da d'ayansu bai shirya mata a yau ba.

Don Nurses d'in nan babu yadda suka iya suna gani likitan dake duba ta ya sallame ta da tulin magunguna, saboda yana zuwa shima
yaga halin da ake ciki yace ai dole ne ayi mata abinda take so don in ba haka ba zuciyarta zata iya sake bugawa kwatankwacin na da.

A duk abinda ake yi Mairo na rik'e da Sadiq wanda ke ta bata hak'uri da cewa zasu tafi yanzu, don duk tarin jama'ar dake kansu kaf!

Shi kad'ai take gane abinda yake cewa.

Kafin a kammala komai d'aya k'anwarsa ta koma gida ta d'ebo musu 'yan kayayyakin sakawa da zasu buk'ata, kuma har a lokacin Mairo bata karbi Muhammad dake ta ihunsa ba har ya gaji yayi baccinsa a bayan Zakkiya, kowa a wajen nan ya tausaya mata don sun shaida cewa da gaske ne bata cikin haiyacinta, in ba haka ba meye zai shafe tausayin dake tsakanin uwa ga d'anta?

A waje biyu kawai suka tsaya kafin su hau kan titin express way, inda Sadiq ya tsaya ya siya musu tulin abinci sai kuma gidan mai da ya cika tankin motarsa taf.

Tunda suka d'auki hanya kuwa, idanun Mairo na kafe akan titi, bata sake cewa komai ba, kuma ko sau d'aya bata juya ta waiwayi su Muhammad dake zaune a baya ba, Shi kansa Sadiq baice da ita komai ba, don abinda ke faruwa a cikin kansa ma ya ishe shi.

Ya riga ya yarda cewa tabbas lokacin rabuwarsa da Mairo ne yazo...

Ya kama hanya zai kaita inda baza ta taba dawowa gare shi ba, don ya san babu abinda zai hana ragowar asirin nan kwancewa in har tayi ido biyu da mahaifarta!

Akwai wani zane a hannunta irin na 'yan indiya, anyi shi da kalolin bak'i da kuma ja, duk da ba zai iya tuna yaushe a rayuwarsa ya tab'a kallon film d'in india ba, ammma yasha ganin hotunansu kuma hannunsu da irin wannan zanen na flower daya fito d'al akan farar fatarta.

Ya rufe idonsa ya sake yin baya cikin lallausar kujerar falon da yake zaune, a daren jiya baccinsa kad'an ne, don rabin daren ya shafe shi ne wajen rubuce-rubuce na fitar da yadda zaman kotun na farko ya kasance da kuma yadda zai shiryawa na biyu, sannan da yadda tsarin tasa hanyar zai cigaba da tafiya.

Bayan ya gama kuma da yaji baya jin bacci sai ya tashi kawai yayi ta sallolin nafilarsa yana rok'on Allah daya bashi sa'a a shari'ar na, sannan kamar kullum yana neman yafiyarsa kan yadda ya shafe rabin shekarun rayuwarsa yana bauta ga wani abun daban.

Sai gashi a yanzu d'an baccin da yake nema kuma ya gagara, kwakwalwarsa tak'i hutun, bayan idanun Fadeelah yanzu ta bud'e wani sabon shafi kuma na tunanin hannayenta da zanen da aka yi musu.

Ya san cewa abun yayi masa kyau ne, amma kuma abu nawa ne yayi masa kyau kuma yake saurin manta shi, me yasa sai komai nata ne zai tsaya a kansa?

Motsin shigowa cikin falon yasa ya bud'e idonsa, Sadiq ne d'auke da ledoji na abincin da yaje siyo musu, yayi zaton ma Awwal ne ya fito, wanda tunda ya biyo Sa'id daga wajen kotun jiya yak'i komawa ya samu d'aki yayi kwanciyarsa.

Yaga alama kamar Sa'id d'in ya damu don da alama Awwal bashi niyyar komawa Ikara kwata-kwata, amma shi bai damu ba don ya san yana da faragar da in mutum talatin daga Babban gida zasu dawo k'ark'ashinsa a yanzu zai iya d'aukar nauyinsu.

Ya dad'e da yarda cewa DANGI kowanne iri ne kuwa sune ginshik'in kowanne mutum a duniya.

Sa'id ya shigo ya gaishe shi sannan ya ajiye ledojin akan center table na falon.

"Yaya ina son anjima inje Ikara."
Yaji shi amma sai ya d'anyi shiru yana wani tunanin kafin ya amsa.

"Shi yasa nace maka kamata yayi mu sayi wata motar kawai, guda d'aya tayi kad'an a wannan zirga-zirgar."
A jirgi dukkaninsu suka zo, sai suka biya wani direba ya taho musu da motarsa.

"Yaya in dai ba kyauta zaka yi da ita in mun tashi tafiya ba, ni gani nake yi asarar kud'i ne kawai."
"Kyautar nayi niyyar yi da ita ai, naga Baba yana yawan zuwa cikin Zaria, kaga sai kawai Jamil (d'an kawu Ibrahim d'in) ya dinga kawo shi duk sanda zai zo tunda
ya iya driving."
Sa'id ya gyad'a kansa.

"Hakan yayi, zaiji dadi kuma Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen." Fatar bakinsa ta furta ba tare da sautin ya fito ba.

Har Sa'id ya mik'e zai shuga ciki ya tsaida shi a ta hanyar kiran sunansa.

"Sai'd ya sunan abun da naga mata suna zanawa a hannunsu?"
Mamaki ya d'an kama shi.

"Yaya wai k'unshi?"
"Sunansa kenan?"
"Eh k'unshi ko lalle suke ce masa."
"Saboda me suke yi?"
"Saboda kwalliyarsu kawai, amma yawanci sai za'a yi bikin aure suka fi yinsa, musamman ita amaryar kusan dole ne ma tayi k'unshi."
...ranar da aka fara bikina ne, komai ya tarwatse, Sadiya ta gan ni sannan Mairo ma tazo nemana, ni kuma ganinsu ya tayar min da ciwo na, ban sake fahimtar komai ba daga hakan sai bayan na farka Mami tace min Al'ameen ya dakatar da d'aurin auren namu saboda halin da nake ciki.

Iya wadannan kalaman nata a lokacin da take bashi labarinta suka gutsiro suka haska cikin kansa, Ya Allah!

Ya akayi ya manta da hakan, ya akayi ya manta daga ita har Kawu Ibrahim dasu Mami marik'anta sun shaida masa cewa a ranar da aka fara bikinta wannan hargitsin ya fara?

Shine har zai zauna a cikin kansa yana yaba kwalliyar da ta yiwa wani?

Ganin Adam bashi da niyyar sake magana yasa Said ya juya ciki yana tunani me ya had'a k'unshi kuma da zancen wannan shari'ar.

Kusan minti talatin kafin ya iya goge tunanin k'unshin Fadeelah daga kansa, ya mik'e ya bud'a abincin
da Sa'id ya ajiye, sai dai lomar farko tunaninsa ya sake hasko masa ita, wane irin abinci take samu a wajen?

Zata ma iya cin abinda suka bata tukunna?
Chapter 58 · 0% Book details