Sashe 30
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na d'auka kince taya ki zanyi, ai baki fara rubuta komai a jiki ba."
"Ai abinda nake nufi kenan, ka taya ni rubutawa ka rubuta min duka."
Bata ko jira amsarsa ba ta juya da sauri tayi hanyar kicin.
Ya d'an dafe kansa kad'an, daya sani bai amsa ba, don shi ya manta duk irin wad'annan abubuwan, ta yaya zai fara rubuta wani jawabi akan abokai yanzu?
In dai ba shari'a zai rattaba tsakaninsu ba.
Ya d'ago da idonsa ya kalli Zahra da take tsakiyar couch d'in falon tana kallon wani indian series yace.
"Ke 'yar Aljana me yasa baki rubuta mata ba kina zaune kina kallo."
Ta cuno bakinta kad'an don bata son irin sunayen da yake saka mata, sannan ta d'ago masa wasu zungura-zunguran takardu guda biyu.
"Guda uku na rubatawa yarinyar nan, amma d'ayan ma yaga shi tayi tace wai abinda na fad'a yayi iyayi da yawa ciki, dama Aunty Fadeelah ce ke rubuta mata, yau tunda bata da lafiya kowa ya shiga uku a gidan nan daga naka wajen su Farouk zata tafi, watakila ma har ta tsallaka mak'ota."
Yadda take maganar hausarta na fita fil-fil, ba wanda zai yarda tayi zaman k'asar turai kuma a shekara guda baya bata iya hausar sosai ba, yawan zama dasu Sameera da kuma sawa kanta kar ta banbanta dasu ya taimaka mata sosai.
"Al'ameen ka dawo?"
Muryar Mami ta katse kokarin tambayar me ya sami Fadeela da yake shirin yi.
Ya juyo ya kalle ta, cikin kayanta masu kyau tsaf take, sai dai da alamun damuwa kad'an a fuskarta.
"Eh na dawo Mami, na same ku lafiya?"
"Alhmdlilah, dama yanzu nake son kiran wani daga cikinku ya dawo ko kai ko Daddy."
"Lafiya dai? wani abu ya faru ne?"
Muryarsa mai taushi ta tambaya cike da damuwa saboda a yanayin muryarta kawai ya fahimci akwai wani abun.
"Fadeelah ce bata da lafiya tun safe, ko makaranta bata je ba, nayi-nayi da ita kuma muje asibiti amma tak'i yarda."
"Ya salam!" ya furta a hankali yana rik'e da hannun kujerar gefensa.
"Ya jikin nata yanzu?"
"Ba kamar da safe ba dai, amma har yanzu tana kwance."
Ya kalli k'ofar data fito daga cikinta, hanyar wani d'an k'aramin falo ne mai d'auke da kujeru uku a ciki, da alama Fadeelan tana ciki ne, don haka ba tare da yayi tunani sau biyu ba bakinsa ya furta.
"Bari in shiga in dubata."
Ya ture duk wani gargad'i da jar fitilar dake kad'awa akansa ya nufi cikin falon, ya san d'akin yana da d'an duhu kad'an amma fitilar a kunne take saboda haka a take ya hango ta akan kujera ta duk'unk'une cikin wani lallausan bargo kalar ruwan hoda, zuciyarsa ta narke gabad'aya sanda ya kalli fuskarta, idanunta a k'ank'ance suke alamun rashin bacci, da alama kuma bata yi tsammanin shigowar kowa ba, saboda tana ganinsa tayi motsi da sauri alamun gyara kwanciyarta.
"I'm sorry na tashe ki ne?"
Sai ta girgiza kanta a hankali tana k'ara gyara kwanciyar, ya k'araso ya zauna a hannun kujerar gefe.
"Mami tace baki da lafiya, ya jikin naki?"
Yaji alamun taja hanci kad'an kafin kai tsaye tace.
"Naji sauk'i."
"Kin sha magani?"
Idonsa na kanta saboda haka yaga lokacin da ta girgiza kanta a hankali.
"Saboda me?"
"Saboda naji sauk'i."
"Ta yaya kika sa.."
"Naji sauk'i Al'ameen ba sai ka tabbatar ba."
Ya Allah! ashe bata manta sunansa ba?
Ya ayyana hakan a ransa yana kallon fuskarta ta cikin hasken d'akin, ya san me take nufi sarai, don tayi maganar ne da muryar wannan Fadeelan daya sani a baya, mai k'arfin hali da dauriyar b'oye rauninta a gaban mutane.
Sai ya karkato daga kujerar da yake kai, ya k'ara fuskantar ta.
"In haka ne me yasa kike kwance tun safe?"
"Bacci ne bai gama saki na ba."
"Shi yasa idanunki suka canja?"
Sai ta lumshe idanun nata can k'asa har ya daina ganin kwayarsu sannan ta amsa.
"Har shi d'inma."
"Fadeelah rayuwa bata da adalci, ba komai d'an adam yake samun yadda yake so a cikinta ba, Allah yayi miki Rahmomin da mutane da yawa har da wanda suka fi ki a wani abin ke kwad'ayin samu, na fahimci uzirinki idan kin b'oye ciwonki a idanun jama'a, amma babu hujjar da zata sa ke da kanki ki dinga cutar kanki."
A hankali ta ware gashin idon nata ta kalle shi, Ashe har yanzu da guntuwar damuwar Al'ameen akanta? tayi zaton yayi cilli da komai na rayuwarta ne kamar yadda ya daina kulata.
Maganarsa kuma ta sata gajeren tunani, kusan abinda ya fad'a haka ne, duk da nakasarta tana da d'imbin rahamomin da yatsu baza su iya k'irga su ba, Allah ya sanyata cikin karamtacciyar zuri'ar da suka karb'eta cikinsu da hannu hiyu, suke kyautata mata kamar yadda zasu kyautatawa jininsu, ga damar karatu data samu, irin karatun da ta san bata yishi a rayuwarta ta baya ba, sannan ga tarin experience d'in da take dashi na rayuwa data samo a wani b'angare na duniya.
"Ki daina sawa zuciyarki ta yarda cewa baki da matsala kuma zaki iya daure duk abinda ya same ki ba tare da wani tallafi ba, in kina son ki cigaba a al'amuranki dole ne a karan kanki sai kin yarda cewa kina da rauni ta wani b'angaren, kin amincewa kanki da na kusa dake kun taimake rayuwarki, akwai mutane da yawa a duniyar nan da suke cikin hali wanda yafi naki, amma babu alamar da take nuna hakan saboda iya kokari suna taimakon kansu ta hanyar da zasu iya.
Kar ki sa dauriya a kodayaushe ta dinga rarake ki ba tare da kin ankara ba."
Wai ta manta ne cewar Al'ameen ya iya kwantar da damuwa? meye sanadin da yasa ta saba dashi a d'an k'ank'anin lokaci a baya? amma saboda kaifin akidarta sai ta girgiza kai tace.
"Watakila ka manta ne, amma na gaya maka cewa na dad'e da daina karb'ar tausayin mutane akaina, kuma ina ganin amfanin hanyar da nake bi sosai, don haka ka rik'e tausayinka, Nagode."
Sakan d'aya, biyu, uku, hud'u... yayi shiru kawai yana kallonta, gefen lebb'ensa a cije kamar mai sak'a wani abun cikin ransa, sai kuma ya mik'e zaune akan hannun kujerar sannan ya zaro wayarsa ya shiga dannawa.
Idanun Fadeela suka bi wayar da kallo sannan shi d'in kansa.
Me zai yi?
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
"Hello Ibrahim, ka bar office ne?...
Okay eh na bashi su, dama wannan Family doctor naku da kayi min maganarsa nake son in tambayeka zai iya zuwa gida?"
Shiru mai tsawo ya biyo baya, idonsa a tsaye kyam! alamun saurare kafin daga bisani ya gyad'a kai sannan yace.
"Nagode, zan turo maka da address d'in yanzu."
"Ki shirya, likita zai zo ya duba ki."
Ya fad'a sanda yake danna wata number a wayarsa da niyyar kira.
Fadeelah ta tsuke bakinta kad'an tana kallonsa, ba don yayi amfani da kalmar mace ba, baza tace da ita yake ba saboda yadda yayi maganar hankalinsa baya kanta.
Haka kurum sai taji wani fata na cewar dama wannan ne farkon saninta dashi, dama k'addara bata had'a su a baya ba, da watakila hakan ya gyara alak'arsu yanzu.
"Babu likitan da zan gani Al'ameen, nagode da tausayawar ka."
Ta fad'a kanta tsaye tana kallon fuskarsa, sai ya juyo shima ya kalle ta, karo na farko data tsinewa idonta kenan, don ta tabbata fatanta ya nuna tar! cikin idon.
"Watakila kin manta ne, amma na gaya miki tun farko cewa bana tausayinki, taimakon da kika kasa yiwa kanki zanyi yanzu... don Mami kawai."
Yana fad'in hakan ya mik'e ya fita, tabi fad'in kafad'unsa da kallo da tafiyarsa mai cike da aji...
Don Mami kawai! ta furta a hankali.
Ya riga ya saba b'oye damuwarsa, ya saba yin harkokinsa kamar ba komai, alhali damuwar na rarake ruhinsa ne ta ciki a hankali, sannan ya koyi yadda ake hak'uri da abu ma, alhali abun nan mai mutuqar muhimmanci ne.
So yake kamar yadda shekara guda ta horar da zuciyarsa, a yanzu ma ya cire ta a ransa, ya k'arasa abinda ya kawo shi sannan ya tafi, tafiya mai nisan da zata k'ara datse duk wata hanya ma da zata had'o kalmar 'ita' a rayuwarsa, ya samu yin harkoki kala-kala, aikinsa ya bunk'asa, yayi abubuwa, yaci nasararsu, sannan ya samu cigaba a rayuwarsa...
...amma gani yake kamar komai ba zai yiwu ba, kamar bashi da kuzarin da zai cim musu, duk akan yawan ganin Fadeelah yanzu da yake yi, shi yasa tun farko bai bawa kansa tabbacin in zai iya cigaba da bin umarnin mahaifyarsa akanta ba.
"Zazzabi ne kawai da matsanancin ciwon kai ke damunta, amma ba wani abu bane, tasha wad'annan magungunan na kwana uku, idan baiyi sauki ba sai kuje asibiti ayi mata wani check up d'in."
Likitan da Ibrahim (abokin aikin daya hadu dashi anan) ya turo ya fada yana miko masa takardar da yayi rubutu akai bayan fitowarsu daga cikin gidan.
"Okay, amma babu wani abu game da ciwonta dana gaya maka?"
"Gaskiya ni a dubawata ban gani ba, duk da cewa iya b'angarena kawai na bata maganin, amma dai in tasha magungunan ba'a sami yadda ake so ba, sai dai a nemi wani likitan da yake kwararre a b'angaren kwakwalwa."
"To shikenan Doctor, Nagode sosai!"
Ya fad'a da murmushi sanda ya karbi takardar maganin.
Ya raka shi har mota yana k'ara yi masa godiya kafin ya kalli takardar daya bashi, wajen magaunguna hudu ne a jiki, watakila Mami zata sha daga da ita kafin ta yarda tasha, watakila kuma idan ta fahimci cewa ba ciwon nata bane zazzabi ne kawai ya sameta ita da kanta ta yarda ta karb'a.
Maimakon ya koma cikin gidan sai ya d'auki mota kawai ya juya ya fita, ya soke duk wasu abubuwan da zaiyi a lokacin ya fita neman maganin Fadeelah, a ciki harda cin abincinsa da tun jiya bai sa komai a cikinsa ba bayan ruwa, da kuma Hamida dake jiran wayarsa, rashin lafiyar Fadeelah tabi ta ruguza komai banda abu d'aya, abu d'aya da ba zai iya tsallake shi ba!