← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 95

Sashe 60

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In zancen
kud'inki ne banda canji."
Da wannan fadan, wannan fad'an dai da kowa ya santa dashi tayi maganar.

"Alqur'anin Allah bakuwa kika yi, lek'o ki ganta." Cewar Kubran.

Kamar ba zata leko ba sai kuma can ta d'age tattararren labulen ta zuro fuskarta, kallo d'aya ta yiwa fuskar Mairo ta mik'e ta fito.

"Ya rabbis samawati wal'ardi!

Kar dai Mairon Amina nake gani?

Mairo kece?

Daga ina?

Dama da gaske Sadiya take ta ganki?

Mairo kawai kallonta take yi da mamaki itama, itace dai Gwaggo lamin da ta sani amma tsufa ya kamata fatarta duk ta yamushe sannan jikinta ma ya tsomare.

"Gwaggo nice na dawo, ina Innata take da Inna saratu, na tambaye su sunce basu gane ba."
"Au da kuka had'u da Sadiyan bata shaida miki ba?

Ai Amina ta mutu babu dad'ewa da barinki gida, Saratu kuma tana can Kaduna tayi aure."
Mairo ta hadiye yawu mai zafi cikin makogwaronta, abinda Sadiya ta fad'a gaskiya ne kenan, mamarta ta mutu..

Innarta mai tsananin sonta wadda ta raini ta da dukkan kulawa, daidai da rana d'aya bsta taba bari kunya irin ta uwa da d'iyar fari ta shiga tsakaninsu bud'e zuciyarta take ta fad'a mata komai, don ta maida ita kamar k'awa ko kuna k'anwa da bata da ita.

Wani irin kuka da bata shirya masa ba ya faso daga bakinta sannan ta durk'ushe a wajen.

"Au, au...

Yanzu kika san ciwon Uwa Mairo? ai na zata dadi soyayyar saurayi tasha gaban komai a wajenki, kin san komai ai kika tsalkake kika bar baiwar Allah nan, wane irin bakin ciki ne bata k'unsa a dalilinki ba, wane irin zagi da habaici ne bata d'andana daga jama'ar gari dana babban gida ba?

Wanda hakan ya jawo mata ciwon zuciyar daya kaita kabari?

Sakayyar dake tsakaninku wannan sai ubangiji Mairo, amma Allah ya sani ki zalunci matar nan."
Mairo ta san halin Gwaggo lami sarai, ta san irin zuga da makircinta kuma ta san bata tab'a son mahaifiyarsu ba, amma ta yarda da duk kalaman da take fada a lokacin, don ta yarda duk wanda zai gaya mata sab'anin hakan ma ya rufe ta ne.

"Tana ina?

Nan ta shigo?"
Muryarsa Saminu ta karyo kwana,ya shigo tare dasu Isa a bayansa.

"Wallahi itace kuwa, sannu da zuwa
Mairo, ashe zaki gane hanya?"
Saminun ya fad'a yana kallonta.

"Zan zage ka Saminu, Mairon kake wa Sannu da zuwa?

Ko baka gane ta bane."
"Na gane ta mana Gwaggo, yanzu muka gama gaisawa ma ai da mijin nata.

Kinga Mairo ba nan ya kamata fa ki shigo ba, Babban gida zaki wajensu Kawu, nan duk 'yan haya ne ba wata tsiya ba, tashi muje mu raka ki."
Gwaggo lami kawai sakin baki tayi tana kallon yadda su Saminunke kokarin tashinta tsaye, zuciyarta ta d'arsa mata cewa tabbas Mairo ba'a wulakance tazo ba, daga yanayin fatar jikinta ma kawai zaka tsinci hutu a ciki.

Da kyar su Saminu suka raka ta Babban gida inda kafin isarta labari ya zaga gidan gabad'aya har wad'anda suka fara gyangyadawa ma sun mik'e.

Wajen Kawu D'anjuma su Saminu suka shigar da ita inda kamar a wajen Gwaggo lami shima bata samu wata rarbar arziki daga gareta ba, yace shi bashi da ta cewa akanta tunda bashi ta yiwa laifi ba, iyayenta da yanzu basa duniyar sune alhakinsu ke kanta bashi ba, don haka ta tashi tabi mijinta su koma inda suka fito, duk sanda ta sake take so kuma tazo ta gaishe su, shi ba zai k'i amsa gaisuwarta ba.

Sannan kai tsaye ya shaida mata cewa bayan tafiyarta k'anwarta Bintu ta kashe mahaifiyarsu ta gudu, kuma yanzu da suka gano ta an maka ta a kotu har anyi zaman farko.

Hadiyar zuciya ne kawai ya rage Mairo bata yi ba jin cewa da gaske ne su Kawu saida suka kai Bintu kotu, ita tayi zaton su Kawu Yahya sun zo tafiya da ita ne kawai don tsoratarwa ba wai har abin ya kai kotu ba, saboda wallahi har cikin ranta ta yarda cewa Mairo ba zata iya kisa, bayan Aunty saratu duk duniya kaf!

Tafi kowa saninta, don ko Innarsu tana
d'aukanta ne a matsayin 'yar Aunty Saratu ba tata ba.

Ganin irin karb'ar data samu daga wajen Kawu D'anjuma, sai kowa ya shiga d'ari-d'arin tunkararta, don tun bayan da Adam yazo kowa ya sakar masa fuska suka fuskanci b'acin ran Kawu D'anjuma sosai, don janye tallafin da yakd bawa mutane da yawa dake rayusa a k'arshinsa yayi, don haka sun horu na mai sake iya tarbar Mairo hannu biyu.

Saminu da Isah ne kawai suka yita nan da nan da ita, har zuwa duk wajen wanda ya kamata ta gani a Babban gidan.

"A ina zaki kwana?"
Sadiq ya tambaya sanda ta foto daga Babban gidan wajen goma na dare.

Duk abinda akeyi suna rakab'e a mota shi da zakkiy da kuma Muhammad da har alokacin ke baccinsa, ba wanda ya neme su don haka shima baiyi kokarin kai kansu ciki ba, to yaje yace me?

Shine wanda ya gudu da 'yarsu ya kuma aureta ba tare da saninsu ba?

"A gidanmu." Ta bashi amsar a gajarce idonta baya kallonsa."
"Amma..."
"Sadiq dan Allah ka barni kawai."
"Sai ya gyad'a kansa sannan yace.

"Muhammad fa?"
Zai iya rantsewa sai a lokacin ta wulkita idonta cikin motar ta kalli Zakkiyar dake rik'e dashi sannan kai tsaye tace.

"Na yaye shi."
"What?

Maryam yaye?

Shekararsa d'aya fa?"
"Ban damu ba." Ta bashi amsa.

"A yanzu ban damu da duk abinda ya shafe ka ba Sadiq don na fahimci ka san komai, sanda muka shigo garin nan banyi maka kwatancen gidanmu ba, amma kai tsaye ka kai motarka har can, kenan kana sane da inda 'yanuwana suke duk tsawon lokacin nan, amma ka kyale ni, ka nesanta ni dasu tunda kai kana tare da naka."
Bai ce komai ba sai da ya had'iye yawu.

"Amma Muhammad D'anki ne Maryam, ki dubi girman Allah kar ki cutar da yaron da bai san komai ba." Muryarsa cike take da rok'o.

"Wallahi na yaye shi Sadiq, kuma bana fatan sake had'a kaina da duk wani abu daya dangace ka."
Bai iya cewa komai ba, itama bata sake cewa komai ba tayi gaba ta barshi anan, ya rasa mai zaiyi sai
kawai ya sunkuyo cikin motar yace da Zakkiya.

"Ko zaki bita?"
"Yaya wai ciki?

Kaga gidan kuwa? wallahi babu wajen da zamu zauna...

Sauro ma kad'ai damun Muhammad zaiyi."
Sai ya gyad'a kansa kamar k'aramin yaro sannan ya mik'e tsaye, daidai sanda su Saminu suka fito daga zauren na Babban gida.

"Alhaji ai bamu san ta fito ba, Kawu ne ya kira mu wallahi."
"Ta koma can gidan da muka fara zuwa tace anan zata kwana." Ya fad'a muryarsa a rikice.

"Wai can gidan namu?" Cewar Saminu da mamaki.

"Eh yanzu tayi kwana ta tafi."
"Ai na zata tare zaku wuce."
Sadiq bai amsa ba, sai ya zura hannu a aljihunsa kawai ya zaro kudin da shi kansa bai san adadinsu ba ya damk'awa Saminun.

"Mu zamu nemi wani wajen da safe zamu dawo, ga wannan ko zata buk'aci wani abun."
Saminu ya damk'e kud'in sannan ta gefen idonsa ya yiwa Isah alamar...

Me na gaya maka?

D'akinta tun na asali da babu komai a ciki sai tarin buhunhunan dusa na d'aya daga cikin mazan dake haya a gidan, nan Mairo ta shiga ta ture buhunhunan gefe tayi kwanciyarta, sannan ta bud'e wani shafin kukan sabo fil! kukan da aka kange ta daga yinsa tsawon shekaru, don Allah wadai take da kowacce rana da take iya tunawa bayan barinta Ikara, tana cikin mafi munin rayuwa amma har take iya farin ciki a wancan lokacin.

Ta yaya a yanzu zata iya rayuwa da sanin cewa bak'in cikinta ne ya kashe mahaifiyarta?

Ga mahaifinta ma har ya bar duniya bata san matsayinta a gurinsa ba, sannan yanzu ga k'anwarta can cikin kurkuku a garkame ana barazanar yanke mata hukuncin da zai guntule rayuwarta, Ya Allah!

Bata tab'a sanin cewa dangi suna da damar da zasu k'untata su kuma tarwatsa rayuwar d'ayansu ba sai a yanzu.

Da kyar ta yarda ta karb'i bargon da Saminu ya kawo mata wanda ya aro a wajen matar wani abokinsa da yayi sabon aure.

Zuciyarta cunkus!

Ta kwana da niyyar yiwa cikin garin Zariya tsinke, bata da kowa a duniya yanzu data fi kusanci dashi kamar k'anwarta Bintu,
a wannan daren.

A wannan daren Sadiq ya kasa runtsawa cikin tangamemen d'akin daya kama a wani guest inn, Zakkiya da Muhammad na kwance a d'akin dake gefen nasa yayin da shi yake ta juyi cikin tashin hankali, saboda tsabar rud'ewa ma ya kasa tashi ko sallah yayi yaji sauk'i, maganganun da suka zama tushen shigowar Mairo cikin rayuwarsa da fitarta a yanzu su ke ta mimatawa suna kuma haskawa a kansa.

Na rasa yadda zanyi Yusif, abubuwa sun taru akaina, mahaifiyata a kull
um neman in kawo mata take yi, dukkan d'awainiyar gidan ta dawo kaina ga kud'in makarantar yaran nan su Zakkiya don yanzu haka sunfi wata a gida, ga kud'in fanshon Baba da kyar ake samu, gashi ni kaina neman na bukatuna nake, don wallahi kaya yanzu zance maka basu fi kala biyar nake dasu ba kod'addu.

Kuma ita taki ganewa, gani take tunda nayi karatu na fita da first class ba inda zanje in rasa aiki, taki fahimtar cewa abin ba'a nan yake ba, wallahi Yusuf kullum nazo kwanciya sai nayi kukan rashin mahaifina, tunda sanda yana nan bukatuna ne kawai akaina.

Kuma yanzu bana ganin laifin yawan fad'an da suke yi da ita a da, don Mama mahaifiyata ce amma wallahi bata da uziri ko kad'an akan bukatun rayuwa, gani take kawai daka fita zaka samu ne ka kawo mata, bata damu da kome zai faru kafin a kawo matan ba.

Yusif d'in dake cikin idanunsa a wancan lokacin ya kyalkyale da dariya gami da bugun gefen kafad'unsa.

Shege Kwaro!
Chapter 60 · 0% Book details