← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 95

Sashe 36

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi yasa har gobe take jinjinawa Mami Safiyya yadda ta iya barin wannan tarin dangin kaf! ta tafi k'asar da bata da kowa sai miji da 'ya'ya.

A hankali ta juya ta janyo jakarta daga bayan robobin ruwa da lemon dake ajiye kan table d'insu sannan ta zaro wayarta daga ciki.

Ba tare da ta kunna ba ta kalli fuskarta akan duhun screen d'in, itafa har yanzu bata yarda cewa fuskarta take ka
llo ba,
don an fente ta ne gabad'aya da abubuwa kala-kala a inda Fatima ta jata akayi musu kwalliya, irin dai wadda ke kan fuskar duk sauran 'yanmatan wajen da kuma su Zahra da take hangowa a gefe, sai dai su in ta kalle su sai taga kammaninsu suna nan, musamman ma dai Zahra da
tun da ta saba yin abarta.

Amma ita in ta kalli kanta sai taga kamar wata ce daban take kallo, don an k'ara fik'e komai na fuskar, an fito da ita d'al kamar wata 'yar tsanar da aka b'are a leda.

"Lalalala, gaskiya ya Fatima tayi kok'ari, yau kece kika yi kwalliya haka?

Aunty deelah kin ganki kuwa?

Kamar a sace!"
Ta tuno abinda Zahra ta fad'a sanda suka iso wajen, su kuma su Zahran sun fito zasu je taho da k'awayensu.

Ta kai hannu zata taba kan hancinta sai d'aya daga cikin k'awayen Rahma dake zagaye a teburinsu ta dakatar da ita.

"Kina tab'awa yanzu kwalliyar zata yi dabbare-dabbare, ki barshi kawai."
Tayi mata murmushi kawai ba tare da ta amsa ba, ta lura tunda suka zauna take son yi mata magana,
ita kuma bata iya sabon farad d'aya ba.

Beem!

A lokaci d'aya wayarta tayi haske alamun shigowar sak'o.

Na kira Mami ban same ta ba, kun isa wajen ne?

Al'ameen ne, kuma ta tabbata bai kira Mamin ba, kalmar 'Ku' tana nufin ita kenan, so yake yaji in ita tana wajen ne kafin ya k'araso.

Wannan shine sabon yaren da suka fara.

"Eh kowa yana nan.

Ka iso ne?"
Beem!

"Eh nazo, zaki fito ki nuna min inda Mami take?

Ba zan dad'e ba."
Tayi murmushi ita kad'ai.

"Kana ina?"
Beem!

Ina harabar wajen."
"Okay, gani nan."
Sati biyu da kwanaki, kokarin Fatima da kuma dabarunta ya juya waccan bahaguwar alak'ar data fara tsakaninta da Al'ameen a farkon zuwansa.

Hakan kuma ya dad'a tafiya ne da yawan zaman Al'ameen a gidan, don sun riga sun gama aikin daya kawo su har abokan aikin nasa sun koma, shine kawai Mami ta rik'e shi da cewar ya tsaya ayi bikin Aseeyah don yaga al'adar bikin Nigeria da bai tab'a gani ba, saboda haka ya k'ara sati biyu akan komawarsa.

Komai ya fara ne da shawarar Fatima ta farko,
taje ta gayawa Mami cewa magungunan da take sha bata jin dadinsu ko zasu gwada zuwa asibiti taga likita sosai, ta san sarai Mami shi zata ce ya kaita don hidimar bikin Aseeyah tayi mata yawa,
saboda haka da murnarta ta gaya masa, kuma bai ruguza komai ba yace ta shirya suje.

Ya kaita wani asibitin kud'i mai kyau ba tare da ya katbi ATM d'in Mami ba,
akayi mata shigen check up d'in da ta saba da irinsa a washington aka kuma bata tulin magunguna, daga nan aka basu appointment cewa bayan kwana hudu su dawo, sai ya zama kafin cikar kwanaki hud'un nan a kullum zasu gaisasannan ya tambaye ta yadda take jin maganin a jikinta, a rana ta uku kuma ya shaidawa Mami cewa abokan aikinsa zasu zo su gaishe da ita kafin su koma.

Da shawarar Fatima, ta hutar da Mami a ranar ta shiga kitchen ta had'a musu abinci mai dadi, harda kalar na turawa da ta iyo a can.

Kuma ba'yan gidan kad'ai ba, ita da kanta kanta tana juya al'amarinta a kwakwalwarta, wai Al'ameen d'in da k'iri-kiri ta yiwa kanta katanga dashi a baya shi zuciyarta kuma ke janta yanzu akansa, tana gaya mata cewa komai ba zai zama matsala ba tsakaninsu.

Sai dai wannan abun shine kusan
jigon daya fara dawo da hankalin Al'ameen kanta, don a washegari da taje yiwa Mami sallama zata tafi makaranta da kansa yace bari ya d'auko muk'ullin motar ya kaita.

"So shekara d'aya?

Me kika cimma a rayuwarki so far?"
Ya tambaya sanda go-slow ya tsaresu akan hanya.

Tayi shiru kafin ta d'aga kafad'unta kad'an, idonta na kan motar dake gabansu tace.

"Abubuwa da dama kamar... na shiga university, ciwona yayi sauk'i, na saba da dangin su Mami sannan na iya hausa sosai."
Yayi guntun murmush a gefen lebb'ensa kafin yace.

"Nice! kin samu abubuwa da yawa, na
miki murna."
Ta gyad'a kanta,
"Nagode."
"You're welcome."
Shiru ya biyo baya, kafin ya bud'e kofar motar ya fita, yayi d'age kad'an don hango adadin motocin dake gabansu kafin yaja tsaki ya dawo.

Kamar kar tayi magana sai kuma ta kalle shi tace.

"Sai hak'uri Nigerian mu kenan."
Ya sake wani guntun murmushin da kyallinsa ya haska cikin idanunsa ya kuma sa ta jin wani iri,
Ya Allah! ba wannan ne karon farko data kalle shi ba, amma tun bayan zuwansa,
wannan ne karon farko da ta kalli cikin idonsa kusa da kusa haka, wai meke damunta ne?

"Waya gaya miki bana son Nigeria,
zan iya dawowa nan ma baki d'aya, ina son duk k'asar da kokarin ka zai yi determining waye kai."
Sai ta kawar da kanta gefe.

"Baka san Nigeria ba, Mami tace a anan matsayinka da kuma matsayin wanda ka sani shine kawaia zai fanshi duk kokarin ka."
"Wannan kusan koina ne Fadeelah..."
Sai zuciyarta tayi tsalle ta dira gefe d'aya jin yadda harshensa ya nad'o harafan sunan nata.

"...

Kawai dai na wani wajen yafi na wani yawa ne."
Bata k'ara cewa komai ba ta cigaba da kallon rayuwar mutanen waje dake faruwa a bayan windon motar, so take ta tambaye shi bayan gemunsa daya k'ara kyau me kuma ya faru dashi a shekara guda, amma harshenta yayi nauyi ya cika bakinta.

Tun daga wannan ranar sai hira ta fara shiga tsakaninsu, hira mai ma'ana ba irin wadda suke yi a shekarar baya ba, babu wasu kalamai masu taushi, sai magana kawai mai muhimmanci data danganci ra'ayin kowannensu da kuma abubuwan da suke burin cimma.

Ranar daya fara samun numberta kuma Mami ce ta kira shi cewar ya taimaka ya d'auko ta daga makaranta, su dukkaninsu basa nan don shirin bikin Aseeyah ya kankamaa lokacin.

Dole ya karbi numberta ya kira ya shaida mata cewa zai zo d'aukanta,
kuma bayan ya d'auko tan maimakon ya kaita gidan Hajiya Amarya kamar yadda Mami tace, sai da suka tsaya a wani k'aton library tukunna, ya nuna mata wani abu da suka yi musu akansa game da rebe-raben k'asashen duniya.

Sanda ya sauke ta a harabar gidam Hajiya Amarya, Fatima ta d'ago mata hannu daga barandar saman benen alamun fara samun nasararsu fiye da koyaushe.

"Bafa wani abu Faty, har yanzu gaisawa muke sai kuma 'yar hira kawai."
Fatiman tayi dariya a lokacin sannan ta sauke muryarta k'asa don kar su Mami dake gefe suji tace.

"Zauna nan, ke kin san tunaninsa ne?

Duk sanda kuke tare kin san me yake ji?"
Me yake ji?

Fadeelah tayi tambayar a cikin kanta, don itafa har a lokacin in banda kyawun Al'ameen da kirkinsa da take gani bata san me take ji game dashi ba.

Amma shi kuma fa?

Me yake ji game ita?

Ji yake zuciyarsa na bugawa da wani irin salo duk sanda yake tare da ita sannan ji yake kamar ita kad'ai ce abinda ke sashi annashuwa a rayuwarsa, sabon da suka yi a yanzu babu abinda yake haifar masa sai k'ara tunatar dashi cewa zuciyarsa ta k'aunace ta a baya kuma bayan wata yarinya daya tab'a kulawa a makaranta, ita kad'ai ce wadda ya taba ji cewa yana son kasancewa da ita har k'arshen rayuwarsa.

Baya gajiya ko kad'an da sauraren hirarta sannan baya taba fasa d'okin wayewar gari a kullum don ya ganta, murmushi kad'ai in tayi sai yaji zuciyarsa ta k'ara dulmiya cikin tunaninta.

Ya san cewa ya rufe wannan babin a da, amma yanzu da kowacce dakika in suna tare, k'ara burge shi take, tana k'ara shiga cikin zuciyarsa sannan kuma tana raba tunaninsa gida-gida.

Kuma a cikin kowanne rabe-raben,
abu d'aya ya sani shine har yanzu yana k'aunar Fadeelah kuma ba abinda zai canja hakan, sai dai zai cigaba da mafarkin zaune ne muddin cewa bai motsa ba, bai sake gwada sa'arsa a karo na biyu ba, sannan bai d'ago da kwantaccen hargitsin daya san zai faru daga b'angaren Maminsa ba.

Ya nisa a hankali ya fitar da iska ta siraran k'ofofin hancinsa, yana tsaye ne a gaban motarsa daga harabar wajen bikin, a gabansa mutane ne ke ta wucewa suna shiga ciki, har kuwa da jerin 'yanmata kala-kala kowacce cikin kwalliya, sai dai a idanunsa shi duk mata a irin wannan shekarun na 'yammatanci d'aya yake ganinsu, ba turawan da yake cikinsu ba, ba kuma wad'annan jinsin hausa-fulanin da yake gani a yanzu ba, kowaccensu kallo d'aya kawai yake musu,
na Mace kawai!

Amma Fadeelah, tun daga ranar daya fara ganinta a cikin kitchen d'in nan,
yaga kamar ansa wata filtila ne ta samanta an haska ta, hasken da ya shiga har cikin idanu da zuciyarsa ya haska su, yasa ya yarda cewa ita d'in daban ce da kowa, tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu kuwa.

Shi yasa yake ganin lokaci yayi da zai fuskanci k'addarar dake biye dashi tsawon wannan lokacin.

A sanda Fadeelan ta ratso daga cikin wajen ta nufo wajen adana motocin da yake, zuciyarsa ta matse fiye da koyaushe ganin yadda kwalliyar fuskarta ta sake fito da tsantsareren kyawunta da bai taba gani ba, kamar yadda bai taba ganinta cikin kwalliyar ba.

Kwarai lokaci yayi da zai sake gwada sa'arsa kan Fadeelah a karo na biyu, karon da yake jin cewa ba zancen Hamida ba, a yanzu ko Maminsa bata isa tasa ya guntule farin cikinsa ba.

Abu d'aya kawai shine bai san cewa in a yanzu zata karb'e shi ba, ko kuma tarihi zai sake maimata kansa!
Chapter 36 · 0% Book details