← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 95

Sashe 62

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddy ma gobe zai taho, na san ba lallai ya samu zaman kotun ba."
"Allah ya kaimu lafiya, ni dai fatana kar shari'ar nan tayi tsawo da yawa, Allah ya baiyana komai cikin k'ank'anin lokaci."
Aunty Hadiza ta sake fad'a, dukkansu suka had'a baki wajen furta Ameen, amma na Fadeelah iya fatar baki kawai ya tsaya, babu sautin.

"Deelah ya cikin wajen yake?

Da sauk'in zama?" Mami ta tambaya.

A lokaci guda idonta ya hango mata duhun cikin cell d'inta da kuma azababben warin dake tashi daga toilet d'in da Allah kad'ai ya san adadin mutanen da suka amfana dashi, ga saurayen da kamar da gayya ake koro su, sai tayi murmushi a gefen lebb'enta tace.

"Mami ba wata matsala waje ne kawai na kwana, kuma ba'a had'ani da kowa ba ni kad'ai ce a ciki."
Daga murmushin kad'ai kowa zai fahimci cewa ba haka taso fad'a ba ita kanta, don haka Mami ta jawo hannunta ta janye hannun bak'ar jallabiyar da ba'a tab'a barinta ta canja ba.

Ilai kuwa tabo ne jazur na cizon sauro yarab- yarab dashi a jikin hannun nata kusan koina kuma.

"Deelah ki daina b'oye min abu dan Allah, in baki sani ba har fuskarki haka take."
"Wallahi Mami babu zafi, cizon ne kawai, kuma ni bana ma jin sauron."
"Waya baki shawarar sanya bak'in kayan ne ma Fadeelah, ai dole su k'ara takura ki." Cewar Aunty Hadiza.

Mami ta juya ta kalle ta tace.

"Yanzu ya zamu yi?

Gashi basa bari a shigo da komai."
K'ofar wajen ta bud'e kuma babu b'ata lokaci Adam ya sanyo kansa ciki.

Dukkaninsu suka juya suka kalle shi yayin da Fadeelah ta tsinci wani abu game da bugun zuciyarta ya canja, sai
kawai ta sunkuyar da kanta kan yatsunta ba tare da ta amsa sallamarsa da su Mami ke amsawa ba.

Ya k'araso ciki, sannan ya gaida su Mamin, mamaki ya kamata jin yadda muryarsa ta sauk'a kasa alamun tsugunnawa yayi, wai har yaushe yazo Nigeria ne ya iya al'adunsu?

Mami ta shiga tambayarsa game da aikin nasu yana bata amsa daki-daki, har sai da Aunty Hadiza ta dakatar da ita don ji tayi kamar tana son ya gaya mata k'arshen shari'ar da ba wanda ya sanshi ne.

"To Deelah bari mu tafi sai gobe insha Allah, ki kula da kanki kinji?"
Cewar Mamin lokacin da suka mik'e.

Sai tayo saurin jawo rigarta ta rufe hannunta ganin ya juyo da idonsa kanta shima.

A hankali ta had'iye wani dunk'ulen abu mai zafi cikin makogwaronta, duk wanda aka kai makarantar kwana alhali baya so, shi kad'ai ne zai fahimci abinda taji a lokacin, shi kadai ne zai ji makamancin abinda taji a lokacin da iyayensa suka juya suka tafi aka barshi a sabuwar duniyar da bai san koda mahaluki guda ba daga shi sai 'yan kayansa.

Kwata-kwata bata ji sallamar Aunty Hadiza ba ma har suka fita daga d'akin.

Kwalla ta taru a idanunta, amma tayi saurin dakatar da ita, tuna cewa Adam na tsaye a kanta.

Ya nazarci fuskarta daga inda yake tsaye, ta canja kwarai daga yadda tazo wajen amma kammaninta suna nan, musamman wad'annan idanun nata... bashi take kallo ba a lokacin ba amma ya gansu sanda take kallon su Mami, yanzu m kamar kullum ne, duk sanda ya kalle su sai yaji kamar mayen k'arfe ne a ciki dake jansa zuwa gare ta, saboda haka ya d'auke idonsa kan bakinta, d'an surut dashi kamar ta shafa masa wani abun...

Ya Allah!

Sai ya janye idonsa da sauri sannan yayi gyaran murya.

"In ga hannunki..." Muryarsa a hankali, mai zurfi, kuma a tsare ta fad'a.

Ba shiri Fadeelah ta d'ago da fararen idanunta ta kalle shi.

Yana tsaye daga baya kad'an ya zura dukkan hannayensa biyu cikin aljuhun wandonsa.

"Me kace?"
"Nace ki nuna min hannunki." Ya sake maimaitawa muryarsa fik'e da wani iko mai sanyi.

"Saboda me?" Ta sake tambaya don ta kasa gane me yake nufi da ta nuna masa hannunta.

Ya cije lebb'ensa kad'an kafin yace.

"Saboda na tambaya."
Sai ta dag'e siririyar girarta d'aya alamun tamabaya itama.

"Me ya kawo hannuna cikin wannan shari'ar?"
Maimakon ya amsa sai kawai taga ya fara tahowa inda take hannayensa duka biyun a aljihun wandonsa, sai da yazo gabanta sannan ya zaro su ya tsugunna daidai saitin gwiwoyinta, kuma bata yi wani tunanin me zai yi ba yasa duka hannayensa biyun ya janyo nata.

Abu biyu suka had'e cikin kwakwalwar Fadeelah a lokacin, farko wannan k'amshin nasa ya cika kowacce kwayar halitta ta hancinta da kuma cikin kwakwalwarta, his musky male scent.

Na biyu kuma sanyin tattausar fatar hannunsa daya sauka akan nata, taji tsigar hannun da ya zama d'an mitsisi akan nasa gabad'aya ta tashi.

A sannan kuma ta iya kallon fuskarsa sosai, wani irin fresh ne da fatar jikinta mai d'aukan hakali, gashi yayi shaving sajen sa tas!

Babu ko tuntub'en gashi, sannan gashin kansa...

Wannan gashin nasa a kwance cikin alamun danshi dake shaida cewa bai dad'e da fitowa daga wanka ba.

"Me yasa baki gaya musu baki da lafiya ba?"
Ya tambaya a hankali yana juya shi kowanne b'angare, hakan ya dad'a sa Fadeelah taji hannun ya zama kamar ba'a jikinta yake ba, saboda haka ta janye shi da sauri, ya d'an tsaya kamar baiji dad'in hakan ba sai ya mik'e a hankali ya tsaya akanta.

Bayan tabon, idonsa k'unshin hannunta kawai ya gane masa, k'unshin daya fara fita saura d'an zirin zanensa kawai waje-waje, bai san me yake tunani ba har sanda muryata ta bashi amsar da yake jira.

"Lafiyata k'alau, kuma idan ma bani da lafiyar banga abinda ya had'a ka da hakan ba." Ta d'ago da kanta tana kallonsa sanda ta fad'i hakan.

Ya ilahi.

Bata san ya yake jin kaifin wannan kallon nata ba, bai ce komai ba sai da ya lumshe nasa idanun tukunna.

"Idan baki da lafiya zai shafi aikina, don za'a k'arawa
shari'ar nan kwanaki ne muyi ta zama cikin abu d'aya."
Ta had'iye sauran wani burbushi abu a makogwaronta kafin ta iya bashi amsa.

"Ni lafiyata k'alau, wannan cizon sauro ne kawai."
Yana daga tsayen yace.

"Amma kina ciwon kai?"
Kamar ba zata amsa ba sai kuma tace.

"Eh."
"Kin ci abinci yau?"
A lokaci d'aya taji wani iri, don bata gane inda ya dosa ba, ita tayi zaton zuwa yayi mata wata tambaya ko ya gaya mata wani abu game da shari'ar da suke ciki, amma meye amfanin wad'annan tambayoyin?

Saboda su ya guntule mata d'an lokacin data samu tare dasu Mami?

"Kinga..." Ya fad'i hakan sanda ya nemi wata kujera a gefe ya zauna."
"Ina tambayarki duk wannan abun ne saboda yanzu aka fara shari'ar, kuma kowa ya ganki zai san cewar kin canja mutuk'a daga yadda kika zo wajen nan tun ba'ayi zama na biyu ba, ni lauyan ki ne dole ne in damu ..."
Kamar wani ya katse shi ya tsaya bai k'arasa ba, saida ya saita kalamansa dake shirin zamewa sannan ya cigaba.

"Wannan cizon da sauro ya miki ko baki yi zazzab'i yanzu ba zaki iya gobe ko jibi, ba zan iya kawo likita nan ba amma zan iya samo miki magani ko hanyar da zaki ji saukin abubuwa, na gaya miki in kika fara rashin lafiya zai shafi dukkaninmu."
Ba wai ta yarda da zancen bane yasa tayi niyyar bashi amsa, kawai ta k'agara ya tafi ne don bata son abinda take ji a yau game dashi, maganganunsa wani a hankali kamar sai sunyi tracing kan fatar ta ne kafin su shiga kwakwalwarta, sannan ga inda ya rik'e hannunta har yanzu tana ji kamar k'ankara aka d'ora a wajen....

Saboda hakan ta bud'e baki ta gaya masa duk wasu abubuwan da take fama dasu a wajen, abubuwan da bata taba gayawa waninsa ba, sai hirar tasu ta zama kamar ta tsakanin likita da mara lafiyarsa kwata-kwata bai sako mata zancen da ya shafi shari'ar ba itama bata tambayi komai har kuwa ya tafi, don zuciyarta na cike da d'acin yadda har yanzu baya nuna wata alama ta ya san hallitarta a America.

Ba'afi awa d'aya da tafiyarsa ba, Musa mai tsaronta ya kawo mata wata madaidaiciyar leda mai d'auke da tarkacen magaunguna da kuma da kuma kayan ci ma irin na leda, sannan harda wani lotion da in mutum ya shafa sauro baya iya hawa jikinsa, bayansu sai manyan robobi na ruwa.

Allah kad'ai ya san irin hanyar da yabi kafin a bar kayan nan ya iso gareta, don su Mami ba irin kokarin da basu yi ba amma aka hana su shigo mata da ko ruwa.

Akwai 'yar jotter a cikin ledar daya rubuta mata yadda zata sha magungunan, idonta ya tsirawa rubutun ido...

Ta kara yarda cewa tabbas wannan Adam d'in data sani a America ne don ga rubutunsa nan kamar yadda ta haddace sh a lokacin tutorial d'insu, mamaki ya sake d'aure tunaninta game dashi, ta kasa gane dalilin da yasa yake b'oye mata kansa, kamar yadda ta kasa gane yadda akayi yazo Nigeria har cikin 'yanuwanta.

"Haba Hajiya, nan fa ba gidan dubiya bane, d'azu wasu suka zo suka matsa sai da suka ganta yanzu kuma kinzo?

Ba fa a ma barin ziyara da yawa a kotun nan amma ku tun yaushe muke d'aga muku k'afa?

Daga wannan yazo sai wani yazo, ko an gaya muku ku kad'ai ne masu 'yar uwa a koton ne?"
Wani mutumi dake zaune a teburinsa ya fad'a cikin masifa sanda Mairo da Kawu Ibrahim ke tsaye a gabansa suna rok'on abinda Mairo ke ganin a yanzu rayuwarta ta ta'allak'a akai.

Ashe har wasu sun rigata ganin Mairo a yau?

Saboda su kuma ake shirin hana ta ganinsu yanzu...

A cikin zuciyarta ta tsinewa lokacin data b'ata a wajen su Kawu D'anjuma da bai amfane ta da komai a yau ba, Kawu Ibrahim daya samu labarin zuwanta ne da kuma abinda ya faru a jiyan ya had'a taro na gaggawa bisa alfarmar daya nema a wajen Kawu D'anjuma.
Chapter 62 · 0% Book details