Sashe 48
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace musu ita mai laifi ce a cikin DANGINSU, shi yasa ko da suka zo ba wanda yabi ta kanta, tun kallon farko da suka yi mata a harabar asibitin ita da mijinta, basu k'ara bi ta kanta ba, ta bi su a ranar duk inda suka sa k'afa sannan ta rok'e su kamar mahaukaciya amma wallahi cikinsu ba wanda ya kula ta, ya rasa a duniya wane irin mutane ne DANGIN Fadeelah don haka suka tsallake ta a harabar asibitin nan suka tafi.
A take kwakwalwarsa ta gaya masa cewa yayar Fadeelah ita zata zama tsaninsu wajen ceto ta, ta san rayuwarta ta baya ta san komai, zata basu cikakken bayanin abubuwan dasu basu sani ba!
A D A M
Ya dace da mafarkin 'yanmata, ya dace da irin mazan dake nik'e zuciyar mata su fad'a cikin tarkonsu a d'an kalilan lokaci, sannan ya dace da irin mazan da wata macen zata kusan bauta musu don samun hankalinsu zuwa gare ta kawai.
Yana zaune cikin d'akin daya mayar office d'insa a gida, ya kurb'i tean dake tiriri cikin kofin hannunsa a hankali, idonsa na manne kan screen d'in labtop d'in dake gabansa, wasik'ar da matar da ya girma yana mata kallon mahaifiyarsa yake karantawa, kamar koyaushe rok'o take kan ya bata adireshinsa anan Nigeria zata zo ta ziyarce shi, ya san k'ulafuci irin na uwa akan d'anta, ya san irin yadda ta sawa kanta damuwarsa sannan ya san cewa ita a wajenta har yanzu tana masa kallon D'a ne, amma zuwanta wajensa yayi wuri yanzu, so yake ya manta da komai na waccan rayuwar ya saba da sabon kewayensa da kuma mutanen cikinsa tukunna, don haka zuwanta zai iya dawo masa da komai baya ne, zata canja masa tsarinsa.
K'ofar d'akin ta bud'e a lokaci d'aya, Sa'id ne ya shigo rik'e da waya a hannunsa.
"Yaya wayarka a kashe take?"
Ya tambaye shi cikin harshen hausa, don tun farkon zamansu baya tab'a bari yayi masa turanci, shi yasa yanzu sosai ya iya yaren, 'yan kalmomin da bai sani ba kad'an ne.
Ya cije gefen lebb'ensa na k'asa a hankali, don a lokacin ba zai ce ga inda wayar tasa take ba, wannan satin akayi zaman k'arshe na wani case d'in siyasa da yayi mutuk'ar wahal dashi, saboda da kyar ya samu b'angaren da yake wakilta suka yi nasara, shi yasa wular da ita bakid'aya, ba zaice ga inda take ba.
Cikin kasalalliyar muryarsa ya kalle shi yace.
"Sa'id ai na manta ma ina da waya ni."
Sai ya k'araso cikin d'akin yana fad'in.
"Shi yasa ake ta nemanmu ba'a samu ba, ashe su Kawu yahya sun zo garin nan har kwana biyu bamu sani ba."
"Kai ina wayar taka?" Ya tambaye shi yana k'ifta idonsa a hankali.
"Na canja layi tun last week, kuma na manta ban kira su ba sai yanzu dana kira Mama (yana nufin mahaifiyarsa)
take gaya min, yanzu munyi magana da Kawu Ibrahim yace in baka wayar."
Haka kurum sai yaji gabansa ya fad'i amma ya ture hakan ta hanyar gyad'a kansa a hankali.
"Kira shi." Ya fad'a kamar da kyar maganar ta fito.
"Baba muna lafiya?"
Ya gaishe shi cikin gurb'atacciyar hausar sa da ba kowa ke ganewa ba.
Ya zab'i ya kira shi Baba don ya yarda cewa shi kad'ai ne a duniya mafi kusanci da mahaifinsa.
"Lafiya k'alau Adam, ya ibadun naka?"
Gaisuwarsu kenan a kullum sai ya tambaye shi game da addininsa, don yafi kowa tuna cewa shi bak'o ne a addinin kuma yafi kowa damuwa da ya san abubuwan cikinsa.
"An gaya maka su Yahya suna garin koh?"
Kawu Ibrahim d'in ya tambaye shi bayan sun gama gaisawa.
"Eh, yanzu nake ji a wajen Sa'id."
"Ai ana ta kiran naku ba'a same ku ba, yanzu dai sunce zasu turo muku da inda suke sai kuje ku same su, wani tsohon case ne na gida ya taso, har Kawu Danjuma ma yace bai sani ba ko kana da aiki da ba sai an d'auki lauyan gwamnati ba."
Ya cusa yatsunsa biyu cikin sumar kansa ta baya sannan yace.
"A'ah, Baba bani da wani aiki dana karb'a yanzu."
"To maganar bata waya bace ba, idan kaje wajensu Yahyan zasu fara yi maka bayanin komai, in kaga zaka karbi shari'ar, sai a sanar da kotun da al'amarin yake hannunta anan."
"To Baba, zamu je wajen nasu yanzu insha Allah."
Ya amsa a hankali kafin suyi sallama.
A cikin ransa ya k'udirce cewa dole ne ma ya karbi wannan case d'in, dole ne yayi abinda zai faranta ran DANGINSA ko ya k'ara samun yardarsu, ba tare da tunanin komai a ransa ba ya kudirce cewa zai karb'i case kuma Allah zai taimake shi yayi nasara kamar sauran duka cases d'insa da baya tab'a faduwarsu a baya.
Kuna tunanin Adam zai karb'i case d'in bayan yaji komai?
Ya kuma ga BINTUN da har yau baya iya bacci sai da idanunta a cikin nasa?
Kuna tunanin Al'ameen zai samu license har ya karbi case d'in Fadeelah?
Ya kuma kara da Adam d'in dake mutuk'ar burge shi a matsayin takara?
Fadeelah zata ga Adam a matsayin d'anuwanta?
Me yasa danginta suka kasa yafewa shari'arta tsawon wannan lokacin?
Ina Habiba?
Taji labarin ganin Bintu?
Wane tunani Mairo ke yi game da mijinta?
Shin zata had'a hannu da Al'ameen su karbi case d'in Bintu?
Wace k'addara ce ke shirin sake faruwa tsakanin Fadeelah, Al'ameen da kuma Adam?
Akwai tambayoyi da dama da zamu cigaba da kwance su.
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
I K A R A.
Salisu ya shigo cikin d'akin da sallama sannan ya nemi waje ya zauna jiran fitowar Kawu D'anjuma daga k'uryar d'akinsa.
Safiyar ranar lahadi ce saboda haka kamar koyaushe ya kan jinkirta fitowa don samun hutawa.
Ba'a fi k'arfin minti goma ba kuwa,
labulen d'akin nasa ya d'age sannan ya fito.
"Salisu kaine?
Har ka dawo kenan?" Ya tambaya sanda ya lalubi wajen zamansa ya hard'e, kafin Salisun ya amsa, sai da ya sunkuyar da kai ya gaishe shi cikin girmamawa sannan ya mik'a masa envelope d'in dake hannunsa.
"Gashi Kawu, ranar goma sha biyar ga wata suka tsayar, nan da kwanaki goma sha d'aya kenan."
"Yawwa to, sannunka da kokari."
Ya fad'a bayan ya karb'i takardar, ya juya ya d'auko glass d'insa dake tare da 'yan tarkacen su Robb a gefen kujerar da yake kai ya sanya a idonsa, layi bayan layi sai da ya karanta takardar da ta fito daga Babbar koton birnin Zariya kan shari'ar da suka shigar ta zargin 'yar d'anuwansu Bintu da kashe mahaifiyarsu ta hanyar sanya mata guba a abin sha da kuma guduwar da tayi bayan hakan, a wancan lokacin sun shigar da k'arar ne musamman saboda tunanin hukuma zata taimaka musu wajen gano inda take cikin sauk'i, amma a yanzu sun maida k'arar ne da fushin cewa da gaske Bintu ta gudu daga gare su ne don wannan laifin har ta bud'e sabuwar rayuwar da take ganin baza su gano ta ba.
Sai da ya gama karantawa tsaf!
Sannan ya
juyo ya kalli Salisun da a lokacin shi nasa tunanin na takaici ne kan yadda manya irin su Kawu D'anjuma ke shirin aikata abin kunya a zuri'arsu, ta yaya zasu yi shari'a da 'yar d'anuwansu? ya san laifin kisa musamman na mahaifiya yafi k'arfin komai da kuma tunaninsa, amma wannan abinda ya dad'e me yasa baza su manta shi ba musamman akan yarinya k'arama irin Bintu?
Matsalar ma shine irinsa masu wannan tunanin a Babban gida kad'an ne, don kusan kowa yana goyon bayan yin shari'ar ne duba da yadda matsayin Bintun yake a wajensu tun farko.
"In ka fita ka kira min kawunka Ibrahim." Muryarsa ta katse gajeran tunanin da yake yi.
Sai ya sunkuyar da kansa kad'an sannan ya amsa da.
"Insha Allah Kawu, na barka lafiya."
Lokacin da Kawu Ibrahim ya shigo cikin falon, fuskarsa bata nuna yanayin kammaninsa na kullum.
Damuwa ce fal a ransa game da abinda yake shirin faruwa yana ji kuma yana gani.
"Wallahi bani da shakka akanka Ibrahim, na san koda na mutu zaka kare min iyalina ba zaka tab'a bari su tozarta ba."
Wad'annan kalman na d'anuwansa marigayi su ke ta yawo akansa tun daga lokacin da Sadiya ta dawo da shelar ganin Bintu kuma Kawu D'anjuma ya bada umarnin tuntub'ar kotun da case d'in ke hannunsu tsawon wannan lokacin, sannan kuma aka tura yayyensa biyu da 'yansanda hud'u daga kotun don su taho da ita.
"Wallahil azeem Kawu, na san darajar
rai kuma na san laifin kisa, ba zan tab'a iya cutar da hajiya ba kome take min kuwa, ina sonta a matsayin kakata da kuma mutum mafi kusanci da nake dashi na b'angaren Baba, na san hukuncin kashe mutum wallahi Kawu ba zan tab'a iya kashe ta ba, wannan tunanin ma bai tab'a zuwa kaina ba...."
Kalaman da Bintu ta gaya masa a daren da zata gudu suka amsa a cikin kansa, zuciyarsa na gaya masa cewa da gaske ne Bintu ba zata iya kisan nan ba, amma daga ranar da yayi k'okarin furta hakan yaga b'acin ran Kawu D'anjuma, ya tabbatarwa kansa cewa bashi da iko a al'amarin.
"An tsayar da ranar shiga kotun, nan da kwanaki goma sha d'aya, ina son ka sanar da Habiba da kuma duk wanda zai iya zama shaida cewa su zama cikin shiri, don na tabbata su Yahya ma zasu taho da yarinyar kafin nan."
Ya jinjina kansa a hankali yana kallon takardar sanda Kawu D'anjuma ke masa wannan bayanin, kwanaki goma sha d'aya rak suka rage k'addara ta yanke wannan yardar da d'anuwansa marigayi ya bashi ita.
"Kunyi magana da Adamun?"
Sanda Kawu D'anjuma yayi masa wannan tambayar, a sannan kwakwalwarsa ta haska masa cewa idan ba zai iya juya su Kawu D'anjuma ba, to tabbas zai iya juya Adam d'in da suke saka ran samun taimakonsa!
"Wai me zai tashi hankalinki ne?"
Salame, aminiya ga Habiba ta tambaya sanda suke zaune tsakar katafaren d'akinta da yasha gyara ya kuma banbanta dana kowacce mace a Babban gida.
Habiba ta ja tsaki k'asan numfashinta sannan tace.