Sashe 80
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Toh tana jiran kokonta in kin gama."
Ashe wannan lokacin shine MAFARIN HARGITSIN RAYUWARTA! ashe sai da ya riga ya gama zuba gubar sannan yazo ya same ta, ashe daga ita har Habiba dake nata shirin sun fad'a tarkonsa ne cikin rashin sani...
Sai ta janye idonta hankali ta maida k'asa, wata kwalla mai d'umi ta taru a cikinsu, karo na farko taji kuka na shirin kwace mata a cikin kotun...
Ashe ba tsakaninta da Hajiya kawai Sule ya rusa a baya ba, rayuwarta gabad'aya ya ture daga tubali, ya barta tana reto a gefe, wani reto mai ciwo da wuya...
Idonta ya dinga hasko mata duk irin wuyar da ta sha tunda daga lokacin da tayi hatsarin nan ta farka kwakwalwarta a mace, kowanne k'alubale data fuskanta BAYAN TA MUTU.... duk akan wannan gaskiyar da bata fi tsakanin minti biyar a fad'e ta ba!
Sai ta kasa rik'e kukan da take dannewa a k'irjinta, kawai ta kifa kanta akan teburin gabanta sannan sautinsa ya shiga fita cikin siririyar muryarta da wani irin amo mai k'arfi, kuka ne irin wanda bata tab'a yi ba a wannan sabuwar rayuwar tata, kuka ne da Bintu kawai ta sanshi ba Fadeelah ba...
Kuka ne irin wanda Bintu kawai ta tab'a yinsa a wasu keb'abb'un lokuta...
Sanda aka nemi Mairo aka rasa...
Sanda Innarta ta rasu...
Sanda Babanta ya rasu...
Da sanda aka raba ta da Inna Saratu!
Kuka ne dake fitowa tun daga k'asan zuciyarta, tana iya jin yadda k'arfinsa ke jijjiga kowanne k'ashi na jikinta tamkar zasu b'alle su rabu da junansu, tana iya jin yadda jijiyoyin jikinta ke nannad'ewa kamar ana k'ulle su...
Sannan tana iya jin yadda bangwayen kotun ke amsawa da sautinsa tamkar zata iya zama silar tsagewarsu!
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
Zaune akan kujerarsa, Alk'ali yace.
"Bayan dukkan bayanai da kuma hujjoji da kotu taji daga kowanne b'angare, Kotu ta yanke hukunci cewa yarinyar da ake zargi bata da laifi, haka ma duk sauran wad'anda ake zargi daga baya sakamakon gano ainihin wanda ke bayan kisan Hajiya Balaraba, sannan kuma kotu ta yankewa Sule wanda aka samu da laifin kisan hukuncin d'aurin rai da rai tare da aiki mai tsanani a gidan yari.
Da wannan hukuncin kuma, kotu ta kawo k'arshen shari'ar da Iyalan Malam Idris Musa suka shigar watanni biyu da suka wuce."
Adam ya rufe file d'in gabansa a lokacin da wajen ya rud'e da hayaniya bayan tashin Alk'alin.
Ya mik'e tsaye shima jikinsa babu kwari, *It's over!* komai ya k'are...
Ubangiji ya amsa addu'arsa ya kawo k'arshen shari'ar nan a yau, Fadeelah zata cigaba da rayuwarta sannan zumuncin Babban gida kuma zai gyaru!
Kawu Ibrahim yace dashi.
"Ban san ta yaya zan gode maka ba Adamu, ban san me ma ya kamata ince ba."
"Nima ban cancanci godiya ba Baba, nayi abinda ya dace ne kawai." Ya fad'a a hankali kamar mai rad'a.
Sai yasa hannu ya rik'o kafad'unsa duka biyun yace.
"Ina alfahari da kai Adamu, ina alfahari da kai irin alfaharin da mahaifinka ya mutu yana burin samu, A yau ka shigo cikinmu ka tabbatar masa da mafarkinsa, kayi abinda ba wanda zai tab'a irinsa, ba a wajenmu kad'ai ba Adamu, wallahi duniya kaf zata shaida cewa kai tauraro ne daban a cikin taura..."
Bai k'arasa ba Adam ya rungume shi kawai, don shi kansa a wannan lokacin ji yake tsakaninsa da magana akwai tazara mai nisa.
Alh.
Ahmad, marik'in Fadeelah yace dashi.
"Kayi aiki mai kyau Adam, kayi namijin k'okarin da ba kowa ne zai iya shi ba, mun gode kwarai da gaske kuma na tabbata wannan case d'in zai jawo maka muhimmiyar d'aukaka a Nigeria, you did a brilliant job!"
Sauran mutanen Babban gida suka yanyame shi da murnar Allah ya sanya alkhairi da kuma jinjina ga k'ok'arinsa.
Sa'id ya mik'o masa hannu suka gaisa sannan yace.
"Ba sai ka gaya min komai ba, na riga naga dukkan abinda na dad'e ina jiran amsarsu daga wajenka yau.
Kayi k'ok'ari sosai yaya, Allah ya k'ara k'arfin basira."
Bayan mazan, mata ma birjik suka yi ta taruwa a gabansa da irin tasu murnar, ba 'yan Babban gidan kad'ai ba, har da mutanen waje na Ikaran da kuma jama'ar gari wad'anda suka zo kallo, sai dai duk a cikinsu wadda yafi rik'ewa itace marik'iyar Fadeelah, matar Alh.
Ahmad.
Da hawaye a kowanne idonta ta kamo hannunsa d'aya da duka nata biyun, ta dinga jero masa wasu tarin addu'o'i da bai tab'a samun irinsu ba a rayuwarsa, don addu'o'i ne irin na uwa kuma bahaushiya wadda bai tab'a samu ba.
Har yaje kwanciya a wannan ranar bayan tarin hayaniya da kuma cike-cike na rufe case d'in kafin a baza shi ga Media, abu biyu ne basu gushe daga ransa ba, farko addu'o'in matar da yaji kowa na kira da Mami Saffiya, sannan kuma kamar koyaushe a rayuwarsa...
Idanun Fadeelah, sanda ta tafi ta rungume yayarta da yaji ana kira da Mairo bayan awanni hud'u da gama shari'ar kafin a kammala komai kotun ta sallameta, Mairon ce farkon wadda ta fara zuwa ta rungume sanda ta fito wajen tarin jama'ar dake jiranta, yana iya tuna yadda dukkan jikinsu ke jijjigawa da wani irin kuka da yafi k'arfin a kira shi da na murna, kuka ne da su kad'ai kawai suka san abinda suke fitarwa daga cikinsa.
Fitarwa.
Kalmar ta d'auki hankalinsa, ya lumshe idonsa kad'an sannan ya k'ara lumewa cikin filon dake k'asan kansa, fatansa a lokacin shine Fadeelah ta gama fitar da dukkan wani bak'in ciki yau cikin kukan da ta sha, kukan da ya hana shi samun magana ma da ita, don ba zai so ace ta cigaba da wahalar da kanta da irin wannan kukan ba...
Ta cigaba da wahalar da idanunta!
Ya rufe idanunsa a hankali tare da hoton nata a cikinsu sanda azababbiyar gajiyar dake nukurkusar sa taci galaba akan kowanne b'angare na jikinsa.
Sai a lokacin ya fahimci abinda Sa'id yaji lokacin da suka dawo daga Mimbiri, don sai a sannan ya shiga biyan bashin kowacce gwagwarmaya da yayi tun sanda ya karb'i shari'ar Fadeelah.
Burinsa a wannan lokacin bai wuce ace ya samu kamar kwanaki uku ba abinda yake sai bacci ba.
Sai dai me?
Washegari ya tashi da abubuwa guda biyu, farko wani irin matsanancin zazzab'i mai zafi daya rufe shi, na biyu kuma labarin rasuwar SADIYA daga Babban gida!
Sadiya ta rasu ne a dalilin hatsarin mota data samu a hanyarta ta komawa Abuja tsakanin garin Zariya da Kaduna, cikin matsanancin gudun da mai motarsu keyi yaci karo da wani mai irin nasa gudun ya bangaje shi, abin da ya haddasa motar ta shiga wul-wuli kenan akan titi tana wullar da mutanen dake cikinta, Sadiya ta booth ta fito kanta ya bugu da kwaltar titi ya tsage ta mutu a take, kuma har aka kawo ta gida bayan su Kawu Yahya da aka kira ta wayarta sunje sun d'auko gawarta, akayi mata wanka da sutura, jini bai bar zuba daga kan nata ba, haka akayi mata sallah aka kaita kabarinta.
Ba wai alhinin rashin Sadiya ne ya girgiza 'yan Babban gida ba, a'a yanayin mutuwarta ne da basu kad'ai ba hatta jama'a da yawa daga cikin Ikaran basu tab'a gani ba, don da farko ma da aka kawo ta rasa mai yi mata wanka aka yi, saboda yadda kowa ya tsorata da ganin gawarta kai a rabe, sai daga baya aka samu su Kawu Ibrahim da Kawu Nazifi da kuma limamin unguwarsu suka yi mata wankan sannan aka sallace ta.
Don haka babu laifi a jajantawa Sadiya kuma anyi zaman makoki na gaske, don ko Fadeelah wadda tun bayan sallamarta take b'angaren Kawu Ibrahim tare da Mairo, ta ture komai ta jawo wannan dangantakar ta cewa ko ba komai Sadiya k'anwar mahaifinta ce, Dangin ta ce ta hanyar da baza a rasa irin jininta a nata jikin ba, saboda haka ta bud'e zuciyarta tayi mata addu'a da fatan Allah yayi mata rahma.
A yau ake sadakar uku don haka gidan ya cika fiye da koyaushe, kusan kowanne b'angare da mutane ana karb'ar gaisuwa, suma suna zaune a falon Aunty Hassanah tare da wasu daga cikin danginta.
Ta juya kanta gefe kad'an inda Aunty saratu da Mami Saffiya ke zaune waje d'aya, duniyarta guda biyu had'e a waje d'aya!
Mami ta koma Abuja tun washegarin ranar da aka sallameta daga kotu, amma yau ta sake biyo jirgi ita da Faruk suka zo addu'ar ukun wadda daga ita za'a share makoki...
A tsakaninta da Aunty Saratu bata san soyayyar wa zata fifita sama da ta d'aya ba.
Aunty saratu ta sota tsakani da Allah kuma ta kula da ita tun a lokacin da mahaifiyarta take raye, sannan bayan ta rasa jigon iyaye duka biyun, ta kula da ita har bayan sanda aka raba su, sanda take zaune a gaban Hajiya, wani lokaci da ya zama a duniya kaf! itace kad'ai wadda zata gani taji dad'i....
Ga Mami Safiyya kuma, wadda ta tsince ta rana tsaka ta hanyar dangin karere, amma tun daga wannan lokacin bata tab'a banbanta ta da 'yayan cikinta ba, tana yi mata soyayya ne irin wadda Allah yake halattawa uwa ga d'anta.
Kuma cikin wani ikon na Allah sai su biyun suka had'a kansu tun sanda suka had'u a zama na k'arshe a kotu, to mai hali iri d'aya ne ya had'u da d'anuwansa.
Ta lumshe idanunta a hankali sanda muryar Mami wadda ke waya ta shiga kunnenta.
"To ai ban gane bane Abdullahi, wai fingerprint d'in Samiran ne yak'i hawa?"
Bata san sanda ta dakatar da duk wani tunani ba ta tsaida hankalinta akanta.
"To me yasa tun jiyan baka d'auke ta daga islamiyya ba kuje a sake yi mata?"
Ta sake tambaya tana k'okarin nemo wani abu cikin jakar gabanta, jin haka sai Fadeelah ta juyar kanta d'aya b'agaren d'akin, ta sauke ganinta akan mutanen dake zaune sannan zuciyarta ta shiga bugawa da sauri.
Tsawon wani lokaci Mami ta dad'e da daina yi mata zancen Al'ameen, amma shekaranjiya bayan sun dawo gida, sanda ta samu kad'aicewa da Kawu Ibrahim ya gaya mata cewa su Daddy sun zo masa da zancen an fasa aurenta da Al'ameen saboda mahaifiyarsa ta zab'a masa wata a can zai aura.