← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 95

Sashe 71

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni shaida ce Maryam, daga ita har Babanki sai da suka yafe miki kafin su bar duniya!"
Mairo ta rufe idonta a hankali hawaye mai d'umi ya shiga gangarowa kumatunta har yana d'iga kan hijabin da Aunty Saratun ke sanye dashi, ji tayi kamar anja wani gingimemen dutse can gefe an sauke shi daga kanta.

Ganin Aunty Saratu a wannan lokacin ya zame mata kamar wani ruwan sama da ya sauko ya wanke rabin matsalolinta a lokacin.

A wannan ranar kuma daga ita har su Kawu Ibrahim suka ji cewar Adam ne yaje har gidan da take aure a can Kaduna, ya labarta mata duk abinda ake ciki na al'amarin Bintu ya kuma nemi alfarmar da tazo ta bada shaida a zaman da za'ayi na gaba.

Kawu Ibrahim ya jinjina kansa cike da mamakin yadda akayi Adam ya iya nemo gidanta har yaje, da gaske ne abinda ya fad'a kenan, Binciken ya tafi, amma to bayan ya bar Kadunan ina ya sake tafiya har tsawon wannan lokacin bai komo ba?
****
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
"Mami ki saurare ni dan Allah..."
Muryar Al'ameen ta fito ta cikin wayar dake kare a kunnen Mami Safiyya, ta girgiza kanta sannan ta amsa masa cikin yaren turancin da suke magana.

"Wallahi Al'ameen ba zai yiwu ba, Daddy ya d'auki zafi sosai akan maganar nan, yace abinda muka yi babban kuskure ne, sannan ni kaina na san nayi ba daidai ba...na biye maka akan abinda ko a musulunce bai dace ba, don haka kayi hak'uri kawai, Allah yayi iyakar mu'amalarka da Deelah kenan, shi yasa ma komai ya faru kafin akai ga d'aurin Auren.

Kayi wa mahaifiyarka biyayya shi yafi, don kamar yadda yanzu kake da ita kad'ai a duniya haka itama kai kad'ai take dashi, su Aysha mata ne, duk daren dad'ewa zasu yi aure su barta, amma kai zaka zama mai kula da ita har k'arshen rayuwarta, don haka babu wanda zai so ka bijere mata ko ka rab'u da wani abu da baza ta so ba.

Uwa tafi k'arfin komai, bayan biyayyar ka ga Allah tata biyayyar ce zata sa ka rabauta a duniya da kuma lahirar saboda haka dan Allah Al'ameen ka hak'ura da Fadeelah, wallahi don ka rasa ta babu abinda zai faru da kai ko ya ragu a rayuwarka.

Rahmar Allah yawa ne da ita, ba sai da Fadeelah kad'ai zaka samu farin ciki ba, na tabbata itama wannan zab'in ta Maminka alkhairi ce a wajenka, wuyar ta a zauna Al'ameen amma na san zaka fahimceta har ta zame maka matar rufin asiri, kai d'in mai kyakkyawar mu'amala ne ba wanda zai zauna da kai ya kasa fahimtarka...

Dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka saki ranka ayi auren nan, Fadeelah kuma ka cigaba da taya ta da addu'a an kusa kammala shari'ar kuma muna sa rai zata fito insha Allah."
Bi da bi, kowacce kalma ke shiga kunnen Al'ameen yana jin kamar maimaici ne akan irin maganganun da kowa ke gaya masa.
...

Don ka rasa ta babu abinda zai same ka.

Basu san cewa komai ya riga ya same shin ba, komai ya riga ya cakud'e masa, ya riga ya zama kamar d'an adam d'in da aka sassak'a da k'arfe, wanda abin juya shi ke hannun mutane da yawa, ya rasa duk wani emotion balle har yayi iko da kansa.

Kamar komai na rayuwarsa, wannan karon ma mahaifiyarsa tayi jagoranci da hukuncinta, tun yana yaro bata tab'a barinsa yayi abu bisa ra'ayinsa ba, hatta kaya ko abinci bai isa ya zab'a ba sai wanda ta bashi, bayan ya girma kuma bai tab'a son zama lauya ba, burinsa ya karanci harkar Computer, ya iya sarrafata ya fitar da abubuwan zamani daga cikinta amma
tace tafi son ya karanci aikin lauya, abinda taso yi kenan a karatunta amma bata sami dama don haka shi yayi...

Zai iya rantsuwa bai tab'a sanin ranar da ta barshi ya zab'i wani abu da yake ra'ayinsa ba sai in har abu ya zama dole ne sai shi d'in zaiyi.

Sai a yanzu rana d'aya kawai daya riga ya kai wani minzali da ko a shari'ah zai iya zab'awa kansa abu, don ya bud'i baki ya fad'i ra'ayinsa sai ta sake cewa A'ah, kuma kowa ya amince cewa ya
cigaba da binta a haka?

Ya lumshe idanunsa a hankali, fad'ar Allah ne cewa babu wata halitta a doron k'asa da zata zama cikakka...

Tunda ya taso a rayuwarsa bai ga abinda Allah ya rage shi dashi ba sai wannan.

"Al'ameen kana jina?...

Yaushe ne bikin?"
Muryar Mami ta shiga kunnensa, sai ya k'arasa rufe idanunsa gabad'aya kafin ya amsa.

"Tace farkon wani watan mai kamawa."
"Toh Allah ya kaimu, su Zahra zasu zo insha Allah, in da hali ma zan had'a su da wasu cousins d'insu."
Ba wai fatan lokacin yazo yake ba amma jin ta d'ebe kanta yasa yayi saurin tambayar.

"Mami ke fa?"
Ta girgiza kai kamar yana ganinta.

"Da wuya Al'ameen, Miryaamah ta d'auki zafi a lamarin nan, ni kaina ba zan iya kai fuskata gabanta a yanzu ba, mu bari dai zuwa wani lokaci sai inzo in ziyarce ku insha Allah."
'KU' tana nufin shi da Hamida, Hamida a matsayin matarsa...

Abinda ya kasa haskowa a cikin kansa har yanzu, ya kasa rusa wannnan mafarkin daya gina a cikin kansa na irin rayuwar da zaiyi shi da Fadeelah.

A yanzu baya iya hango yaya rayuwarsa zata kasance a gaba, don ya san ba zai iya hak'urin rasa Fadeelah ba...

Ya rasa ta a farko kuma ya kasa hak'urin!
****
MIMBIR
I, 10:15 AM.

K'auyen Mimbiri, wani waje ne dake tsakanin babban birnin tarayya na Abuja da kuma garin Niger, k'auye ne k'arami da ko gwamnati bata san dashi ba saboda babu ko wutar lantarki balle ayi maganar ruwa, hanyar samun ruwansu ta jikin wani k'aton dutse ne dake bayan garin inda yake fitar da tsaftataccen ruwa mai sanyi wanda hakan ya sanyawa mutanen cikinsa d'orarriyar lafiya da kuma kuzari, gine-ginen cikin k'auyen na asalin k'asa ne da azara, k'asar ma ba irin wadda ake sarrafata zuwa bulo ba, don yanayin gidajen nasu babu fasali balle tsari.

Yarensu kuwa Hausa ce amma mai cakud'e da garhariyar yaruka kasancewarsu a tsakiyar garuruwa.

Kamar yadda k'auyen yake k'arami, haka mutanen cikinsa basu da yawa, banda gangarawar shekaru ma da suka zo da aurarraki da kuma hayayyafa, a da baifi a k'irge su zuwa 'yan dozinnai ba.

Hanyar zuwa cikinsa bata da kyau, don da kyar aka fitar da ita 'yar siririya ta tsakanin gonaki.

A shekarun baya ma babu hanyar, sai da aka yayyanka gonaki daga can hanyar babban titi sannan aka fitar da ita, 'yar k'arama mai cike da gargada wadda duk kyawun abun hawa sai yayi tangad'i akanta.

Babban abin taraddadi a k'auyen Mimbiri shine zuwan Bak'o, abu ne sabo da ba kasafai yake faruwa ba, saboda in har ka hangi wani akan hanyar shigowa k'auyen, to d'aya daga cikin 'yan d'aid'aikun 'yan uwansu ne da suke fita birni yin sayayyar kayan masarufi, ko kuma a wasu lokuta 'yan wani k'auye dake can nesa dasu su shigo cin kasuwarsu, amma shima ba koyaushe ba, duk ranar kasuwa kusan su kad'ai ke cin kasuwarsu saboda k'arancin mutanen kewayen da suka ma san da zamansu.

Sa'id ya juyar da kansa gefe yana mai k'ara sautin wak'ar da yake ji cikin earpiece d'insa, idonsa ya kai kan cajin dake kan wayar, bai ko kai kwata ba, gashi man dake cikin motar tasu ya kusa k'arewa, na cikin boot ma ragowarsa bashi da yawa.

Tun da gari ya waye fatansa shine su sami mutumin nan a yau su koma cikin gari, tsawon kwanaki hud'u kenan rabonsa da sevice d'in waya, ba don yana caji a motar ba ma da wayar ta dad'e da mutuwa.

Allah ya sani bai tab'a ganin k'untataccen waje irin k'auyen na Mimbiri ba, tun daga 'yar banzar wahalar da suka sha a daji
yaji ya tsani garin, don sunfi k'arfin awanni biyu cikin daji suna karo da dutsuna da kuma busassun shukoki kafin su iso cikinsa, har sai da ya fara tunanin matashin da suka d'auko daga can wani k'auye k'arya yake musu bai san garin ba.

Tun a wancan lokacin kuma ya yarda cewa da gaske ne idan Adam yasa kansa yin abu, to ba k'aramin dalili za'a samu ba da zai canja ra'ayinsa, kwata-kwata bai d'auka da gaske zasu taho har wannan k'auyen neman tsohon da ya bashi labarin ya gani a wajen Habiba ana i-gobe rasuwar Hajiya ba.

Tausayin ganin yadda yake ta fafutuka akan shari'ar ne da kuma ita Bintun da yake hangen za'a datsewa rayuwa yasa ya fad'a masa cewa yaga shigar tsohon wajenta amma ba wai don yana tunanin hakan zaiyi amfani ba, ga mamakinsa kawai sai Adam d'in ya nuna zak'uwarsa wajen k'arin yi masa tambayoyi.

Ya gaya masa iya abinda ya sani cewa ya san tsohon ne kawai ta hanyar wani abokinsa dake siyan magungunan gargajiya a hannunsa...ga k'arin mamakinsa, sai cewa yayi wai ya had'a kayansa zasu yi tafiya.

Washegari suka nufi Ikara, yayi sallama dasu Kawu Ibrahim akan zaije bincike ne kuma shi zai raka shi, daga nan suka tafi wajen abokin nasa daya bashi labari, acan yake gaya musu cewa tsohon ya dad'e da barin ikara kuma asalinsa d'an wani kauye ne wai shi Mimbiri a can gaba da birnin tarayya.

Kaduna suka fara tsayawa, inda mamaki ya sake cinye shi ganin yana ta bin wani adireshi a cikin wayarsa har kofar gidan tsohuwar matar mahaifin Bintu, Saratu.

A hanya hira kala-kala ba wadda basu yi ba harda ta shari'ar da ake ciki, amma bai fad'a masa inda zasu ba ko yadda akayi ya samo gidan Saratun.

Bayan sun baro Kaduna, hanyar Abuja a mik'e suka d'auka bayan sun cika motarsu taf! da kuma wasu manyan jarkuna a boot d'in motar da man fetur, a cikin Abujan suka tsaya wani bakery suka siyo tarin kayan cimar fulawa mara saurin lalacewa da fruits da katan-katan na ruwa da lemo kamar masu barin garin.
Chapter 71 · 0% Book details