← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na san kina cikin damuwa Bintu, watakila ma zan iya kwatanta halin da zuciyarki take ciki, amma kar ki manta kowacce k'addara tana tafiya ne bisa tsarin ubangiji mu bamu isa mu yiwa kanmu komai ba, don haka kiyi kokarin kwantar da hankalinki ki fahimci sabuwar rayuwur da zaki fara yadda zaki samu farin ciki a cikinta, amma ki sani watarana b'acin rai zai iya giftawa a tsakaninku, kuma dole ne ki daure..."
Kuka take sosai a sanda Mairo ke wannan bayanin, don ta fahimci kamar wani b'ari ne na rayuwar aurenta ta d'auko take biya mata shi.

Duk yadda taso a kyale ta a lokacin, babu yadda ta iya sai da ta saurari nasihar duk mutanen d'akin da Fatima ta kawo ta bayan ita dasu Rahma sun gama shirya ta cikin wata yellow laffaya mai laushi.

Bayan nan Mairo taja hannunta har cikin motar dake jira a waje, a lokacin hawayenta ya tsaya kukan zuci kawai take yi.

Wata tsohuwa mai zak'in murya daga cikin 'yan aikin gidan Hajiya amarya tana ta wak'a a bakin motocin, sai dai saboda hayaniya tsakiyar wak'ar kawai
Fadeelah ta iya tsinta.
...Aure martaba, darajoji mai tarin yawa...

Aure!

Wanda ke raba 'ya da Umma idan ka cire mana mutuwa.

Aure!

Ta rayu gidan mijinta su zama abokan shawara.

Aure!

Rayuwar aure da dad'i nima rana na zuwa..
..

Yadda duk na dad'e haka in nai auren sai kuga nai haske.!

Hannayenta suka shiga rawar
sanyi bayan ta shiga motar, ba saboda sanyin Acn dake ciki bane, sai don a lokacin wani irin abu ya dirar mata na cewar da gaske ne ta zama matar aure kuma matar Adam, za'a tafi da ita can duniyar da daga shi sai ita sai kuma alkawarin da yayi!

Tafiyar mai tsayi ce, don ta dad'e tana sak'a abubuwa a cikin zuciyarta kafin a k'araso gidan da kowa ke kira da nata, kuma kamar dai amaryar gaske bata ga komai na cikinsa ba har aka sadata da d'akin da shima aka kira da nata, ta san dai kafin a k'arasa k'afarta tayi ta bi takan wasu tausasan carpet da taji kamar a kyaleta iya nan kawai ta nutse cikin taushinsu ta k'arasa kukan dake matse a k'irjinta.

Watakila an d'auki kusan awa guda koma fiye, kafin hayaniyar mutanen da suka rakota ta ragu a fara tafiya mota bayan mota.

Su Fatima ne na k'arshen tafiya tare dasu Aunty Hassana da kuma Mairo Kuma kafin su tafin Fatima ta kasa d'aure duk wani gargad'in Mami na cewar ta kyaleta, ta jawo kunnenta ta rad'a mata.

"kin san ni malamar kice kuma na san baki manta darasinmu na baya ba lokacin zuwan Al'ameen, don haka wannan karatun shi zaki d'auko ki fad'ad'a shi a yanzu, ki ajiye duk wata kunya a gefe Deelah ki tsaya da k'afarki ki zama matar gida, mijinki bature ne bai san komai na al'adarmu ba don haka ki rik'e shi da soyayya da shagwaba irin na matan arewa har sai ya manta inda ya fito...

Kiyi kwaliya, kiyi girki, ki masa hira, akwai abubuwa da yawa kuma zan dinga kiranki a waya ina kara jaddada miki su, in kika yi haka ba ke kad'ai ba, ko ni zan samu nutsuwar cewa aurenki mutu-ka-raba zai zama."
Duk yadda taso ga daurewa sai da Fatiman ta saka ta murmushi a lokacin wanda ya fito tare da ajiyar zuciya ta sheshek'ar kuka.

Babu wanda kuma ya jira isowar Adam suka had'a kansu suka tafi, suka barta daga ita sai halinta.

Kuma wani abin mamaki sai ta nemi kukan da take ta tanadinsa ta rasa, saboda haka ta rungume k'afafunta ta zauna shiru kawai tana kallon d'akin da kayan cikinsa, a lokacin zuciyarta fayau take bata tunanin komai sai nazarin d'akin, komai na cikinsa kalar milk and orange ne, kuma ba wai kalar ce ta k'ayatar da ita ba, a'ah.. yadda kalolin suka kwanta cikin juna ne, yadda suke had'ewa a idon mai kallo musamman a jikin labule da kuma d'an k'aramin carpet d'in dake gefen gado da kuma k'asan stool d'in mudubi, duka furnitures d'in farare ne tas sai aka musu ratsin dogwayen layi na kalar orange d'in.

A baiyane yake cewa su Mami sunyi k'ok'ari sosai wajen gwangwajeta da kaya masu kyan gaske a gidan da ba lallai zamanta ya d'ore ba.

Agogon d'akin a tsaye yake kuma bata da waya, don haka sai ta kintaci duhun da ya shigo ta cikin labule kawai ta k'addara magriba tayi don bata tunanin akwai masallaci a kusa da zata ji kiran sallah..

Ta d'auro alwala a band'aki ta fito ta bud'e wardrobe, akwatunan kayanta a tsaitsaye suke don haka ta jawo wanda taga Mairo ta saka mata dogwayen riguna da kuma hijabai ta bud'e shi, bayan ta d'auko hijabin kuma ta shiga kiciniyar maida akwatin, ta san zamanta ba mai d'orewa bane amma dole ne ta jera kayanta don d'auko su a akwati wahala zai zame mata.

Bayan ta idar da sallar, ta dad'e zaune akan carpet d'in tana jero addu'ointa, da kowacce addu'a fata take ubangiji ya zab'a mata abinda yake mafi alkhairi a rayuwar da zata fara kuma bata san tsawon wane lokaci hakan ya d'auka ba kafin ta jiyo motsi daga can hanyar da take tunanin ta falo ce.

KOMAI NISAN DARE dole ne gari zai waye, ta riga ta sani dama dole ne ta fuskanci irin wannan lokacin tunda har an riga an d'aura mata aure, dole ne ta fuskanci wannan lokacin da kowa zai matsa gefe a rayuwarta ya barta daga ita sai Adam d'in kad'ai!

Al'ameen.

Ta tuna rayuwarta dashi da irin mu'amalar da suka shimfida har kuwa bayan tsawon lokacin da ta yakice shi daga rayuwarta, bai yi fushi da ita ba ya sake dawowa ya karb'i soyayyarta kuma yayi duk wata fafutukar da rayuwarsu tare zata d'ore.

Da ace gidansa aka kawo ta yanzu...

"Assalamu alaikum."
****
A D A M
Ya rufe idonsa a hankali game da cusa yatsunsa na hagu cikin sumar kansa, bai san me yake damunsa ba, ya gaya mata aurensu ba mai d'orewa bane don ya kwantar da hankalinta, don yayi nasarar goge wannan firgicin da ya hango a cikin idanunta sanda take zaune a gabansa, amma kuma wannan alk'awarin da yayi, ba abu ne da yake hango tabbatuwarsa ba.

An takura ta ya sani, don abinda su Kawu Ibrahim suka yi wani abu ne da bai tab'a tsammani ba, ya san cewa ya tashi ne a cikin turawa inda duk wani d'an adam ke da 'yancin kansa da zarar ya kai shekaru sha takawas, amma baya tunanin ko a al'adar hausawa koyaushe ne ake samun iyayen da zasu d'aura aure ba tare da sani ko tuntub'ar d'aya daga cikin ma'auratan ba.
....ina nemawa d'ana ADAM izinin auren 'yarka FADEELAH!!

Yana tunanin wad'annan kalaman sun jijjiga shi fiye da zazzab'in da ya fito daga cikinsa, don har aka d'aura auren bayan sallar la'asar a wannan ranar yana ganin komai ne tamkar a mafarki, abu da bai tab'a hange ba balle har ya hango
faruwarsa, don daga lokacin da aka kammala shari'ar nan yayi zaton zaren daya sake had'a kaddararsa data Fadeelah ya kwance, sai gashi Kawu Ibrahim yasa hannu ya d'aure shi yadda kwancewarsa kuma zata yi wuya.

Ya hard'e hannayensa sannan ya gyara zama, a lokacin yana zaune ne a cikin mota yayin da wani ma'akacin kantin da suka yi siyayya keta loda tulin kayayyakin abinci dana amfanin da suka siyo a booth d'in motar, Sa'id na tsaye daga gefensa yana nuna masa yadda zai sa kayan.

Siyayya ce irin wadda Sa'id d'in ya saba zuwa yayi musu a gidan da suke, sai dai yau da banbanci, ba gidansu zasu kai ba, gidansa da Fadeelah zasu nufa.

Yau Asabar aka yanke cewar zata tare a gidan da aka kaita, bai san abubuwa da yawa na al'adarsu ba don saida Said ya tuna masa cewar dole ne ya samu gida don ba gidan da suke za'a kawo ta ba, kuma cikin sa'a a unguwar da suke inda yayi kusa da wurin aikinsa, sai suka sami wani gida flat mai kyau, k'aton compound d'in da gidan yake dashi ne yasa ya canja shawara akan karb'arsa haya ya siye shi kawai gabad'aya, siyan da ya girgiza tattalin arzik'insa don masu shi basu yi niyyar sayarwa ba da suka ga ya dage sai suka saka masa kud'i masu yawa.

Gidan nasa ne a yanzu, kuma a yau an kai Fadeelah ciki da sunan matarsa, matar da yayi wa alkawarin cewa zai rabu da ita bayan wani lokaci, wani lokaci da ba zai tab'a zuwa ba don babu ta yadda zai iya kallon Kawu Ibrahim ko wani daga cikin 'yan babban a duniyar nan duk ranar daya rabu da Fadeelah, ya yarda da dukkan nasihohin da kowa yayi tayi masa a wannan larabar, nasihohin da ko sau nawa aka juya su cikin mabanbantan kalmomi, ma'anarsu d'aya ce dai!

Cewa aurensa da Fadeelah wani babban ginshik'i ne da zai gyara zumuncin DANGINSU.

To ta yaya kuwa shi zai zama sanadin b'ata wannan zumuncin?

Bayan haka kuma akwai wajen wani malami da yake zuwa d'aukar karatu bayan sallar isha'i a unguwarsu, tunda Sa'id ya shaida masa cewa yayi aure, yake ta murna da sake d'orar dashi kan hanya mai tafarki da zai bi da gidansa, yana kuma k'ara gaya masa muhimmancin aure da darajojinsa a musulunci da kuma illar rabuwarsa.

To ta yaya kuwa zai so ya fara karya k'aida a matsayinsa na sabon musulmi?

Matsalar kawai guda biyu ce, Farko, ba sai wani ya tuna masa ba, Fadeelah tana da wanda take so a baya har ana shirin bikinsu wannan al'amarin ya faru, saboda haka ko da matsalar da aka samu daga wancan ne, ya san baici ace zuwa yanzu ta manta dashi ba balle har
ta fara tunanin bud'e wata sabuwar rayuwar dashi d'in data tsana a baya.

Ya kai hannunsa bayan wuyansa ya shiga murza fatar wajen a hankali, har yau yana iya tuna yadda fuskarta take a lokacin daya fara ganinta, nad'e cikin mayafin dake nuna shaidar addininta, sannan kamar kullum idanunta na manne da siraran glass d'in da ya k'ara fito da ilhamarta, idanunta kyawawa masu maik'o da kyalli, suna haskawa kamar an kunna wuta ta k'asansu.
Chapter 85 · 0% Book details