← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai ba nan aka rubuta a jikin venue d'in ba da gaske?"
Wata 'yar kyakkyawar Matashiyar mata ta fad'a sanda take gyara hular kan yaron da take rik'e dashi a hannunta, kamar ita, yaron fari ne sosai sai dai har yaso ya zarta ta ma a kyau in akayi duba ga ya had'o da kammanin Mahaifinsa ne wanda ke zaune a gefensu yana shirin kunna had'addiyar motar da suke ciki.

"Sunan da address d'in duk iri d'aya,
amma sunce wai wannan sunan Amaryar Aseeyah ba Amina ba."
"Bibty mu koma gida kawai dan Allah,
kayi musu Allah ya sanya alkhairi in ka koma office, don ina jin ma Afra zazzabi ne ke shirin kamata."
Ta fad'a tana juyawa ta kalli wata 'yar yarinyar dake zaune a baya motar cikin shigar wasu pink kaya masu kyau, babu ko d'ankwali akanta sai yala-yalan gashinta da aka tufke cikin k'ananan kalba da ribbons.

"Hakan za'ayi kawai, nima na fara gajiya, don munsha yawo yau."
Mijin ya amince kai tsaye sannan ya shiga kokarin yin reverse a harabar wajen.

Sai dai me?

A daidai lokacin daya juya kan motar cikin saurin dake nuna lafiyar injinta, idanun matar nan suka sauka akan wata budurwa daga can nesansu, tana sanye cikin pink kaya na alamun ankon bikin sannan tana kokarin nufar wani saurayi dake jingine a gaban wata mota.

Da dare, da tazara tsakaninsu da kuma girma daya sauka akan fuskar budurwar, amma duk wad'annan ba komai bane, koda ragowar numfashi
guda d'aya ne ya rage mata a rayuwarta...

Ba zata tab'a kasa shaida kammannin k'anwarta jal a duniya ba.

BINTUN IKARA!

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
A lokaci guda komai ya haska tar!

Cikin idanun matar, a wannan duhun safiyar data tsallake shimfid'ar 'yar k'anwar tata ta nufi k'ofa, da sanda har ta zura kafarta waje ta juyo ta sake kallonta duk'unk'une cikin zanin rufarta kasancewar lokaci ne irin na sanyi a sannan, da kuma sanda ta ciro wani zoben hannunta da Bintun ke yawan k'alatarsa ta dawo ta ajiye mata a gefen fuskarta sannan tabi duhun safiyar da idanun jama'a suka yi k'aranci cikinsa, ta tafi ga abinda take jin gwara mutuwarta da ta rasa shi a rayuwarta.

Wannan wani abu ne da ta dad'e da mantashi, baya ma cikin lissafinta kwata-kwata, don tun bayan da hakan ta faru, bata tab'a waiwayarsa ba ko a cikin kanta, amma a yanzu da tunaninsa yazo mata, sai take jin kamar a jiya ne akayi komai.

"Menene?

Me ya faru?"
Mijin nata ya tambaya yana kokarin kallon inda ta juya, sai ta katse shi ta hanyar juyowa ta kalleshi da fararen idanunta k'al! wanda maik'on kwallar data fara taruwa a ciki tayi musu wani ado.

"Bibty wata na hango acan kamar..."
Maganarta ta katse, saboda a daidai wannan lokacin igiyar jikin wani mutum-mutumi da aka had'a da tarin layoyi ta sake daurewa tamau!

Sannan d'igon jini guda ya d'iga a jikin k'asar kabarin da aka binne shi.

Ta d'an tsaya cak!

Kamar wadda ake gogewa wani abu kafin kuma ta girgiza kanta a hankali sannan tace.

"Wata na gani kawai kamar na santa, mu tafi daga nan wajen dan Allah."
Ya gyada kansa sau d'aya sannan ya karasa juya kan motar suka nufi hanyar gate, Tarihi ya sake maimata kansa!

Sanda yazo mik'awa mai gadin wajen pass d'in hannunsa ne ya kalleta ta gefen ido, ta sunkuyar da kanta kad'an sannan da zaren hular kan d'ansu Muhammad ta d'auke 'yar k'aramar kwallar data fara taruwa a idonta.

Bai san me ta gani ba amma a take yaji zuciyarsa ta matse cikin k'irjinsa, wata irin matsewa mai rad'ad'i, irin yadda yake ji a duk lokacin daya tuno abinda yayi da kuma sanadin kasancewarta matarsa.

Wani gefe a cikin tunaninsa ya shiga shaida masa abinda ya shafe tsawon lokaci yana nusar dashi, cewa lokaci yayi da zai daina bautar da ita ta hanyar dole!

Watak'ila a yanzu zata zauna dashi ko don albarkacin 'ya'yansu.

"Nayi zaton ka shigo ciki."
Fadeelah ta fad'a sanda takunta ya k'arasar da ita gabansa.

Sai da Al'ameen ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa jin siririyar muryarta sannan ya mike tsaye daga jiginar da yake.

Tsawonsa akanta ya baiyana tazarar incinan dake tsakaninsu sosai duk da cewa ya lura takalmin k'afarta na da d'an tudu.

"Naji ance kamar biki biyu ne a wajen, shi yasa ban san ina zan shiga ba."
"A'a..." Ta girgiza kanta.

"Fatima tace bikin wata Aminah ne suka yi mistake suka saka date din yau alhali sai gobe ne nasu, shi yasa mutane ke ta zuwa suna tambaya."
"Okay, na gane."
"Baku taho tare dasu Ya Abdullahi ba?"
"A'a, su suna ciki ai ina jin, ni kai tsaye daga gida nake."
Sai ta gyad'a kanta a hankali, kwakwalwarta na gaya mata duk mutanen ita kad'ai ce ta san hanyar shigar dashi kenan, a sannan shi kuma ya tsaida idonsa akan fuskarta da kuma surarta mai shagaltar dashi na 'yan wasu sakanni kafin yace.

"Kinyi kyau 'yanmatan Mami."
Sai ta kautar da kanta gefe kadan cikin jin kunya, wanda hakan ba komai ya haifar ba sai kara tsima shi da tayi sakamakon wata mota data shawo kwana ta haske fitilarta dal akan fuskarta.

"Kaima kayi kyau, Mr.

Balaraben Bature kuma Bahaushe a yau."
Ta fad'i hakan ne, tana kallon kayan jikinsa, wani yadi ne mai d'an banzan kyau da yasha fitted d'inki mara aiki irin wanda samari ke yayi a yanzu, kuma tun zuwansa k'asar, yauce rana ta farko daya fara sanya dogayen kaya, don telan Ya Abdullahi da suka fara shiri dashi a 'yar tazarar dake tsakanin gama aikinsa da yanzu ne ya bawa kwangilar yin kayan don kar ya fita daban a taron bikin.

Yasa hannu ya shafa lallausar sumar k'eyarsa sannan yace.

"Yana iya?

Tunda hausawan sun rik'e ni ai dole ne in ajiye komai a gefe in shiga cikinsu."
"Kar ka damu, bikin dai daga yau sai gobe, Mami ta kusa sakinka."
Amma ke fa?

Zaki taba sakin zuciyata ne Fadeelah?

"Mu shiga ciki?"
Ta tambaya jin baice komai ba, sai ya gyad'a kansa kawai tare da nuna mata hanyar.

Da kowanne taku da yake bin bayanta, ji yake kamar ya fisgo hannunta ya tsaida ita, ya gaya mata dukkanin abinda zuciyarsa ke ji game da ita, cewa komai ya dawo sabo...

Yana sonta kamar zaiyi hauka!

Amma ina! irin wannan kasassab'ar ita yayi a farko, ya gaya mata yana sonta ba tare da wani tsari ko shiri ba, ba tare da ya shagaltar da zuciyarta ta manta da duk wani k'alubalen da zai iya faruwa tsakaninsu ba.

Mace kamar kwai ce...

Kamaal ya tab'a gaya masa a wani lokaci.
... iya kokarinka wajen lallab'a kwan nan da kula dashi, shi zai sa har ka kai ga cinsa.

Amma da zarar kace zaka rik'e shine ta duk yadda kaga dama, to a lokaci guda zai fad'i har dandaryar k'asa ya fashe.

Sanda suka k'arasa cikin hall d'in kusan kowa na cin abinci anata aikin bawa ciki ba babba ba yaro, don haka wata cool music ke tashi a wajen babu hayaniya sosai.

Ance wai idan mutum na cikin damuwa a lokacin yake fahimtar me ake fad'a wak'a musamman idan wak'ar ta shafi shigen halin da kake ciki ne, don dalla-dalla Al'ameen ke jin kowacce kalma da wak'ar dake tashi take fadi a lokacin.

I wish I could go back to the very first day I saw you
Should've made my move when you looked in my eyes
'Cause by now I know that you'd feel the way that I do
And I'd whisper these words as you'd lie here by my side
I love you! please say
You love me too, these three words...

They could change our lives forever...

Duk tarin d'imbin jama'ar hall din nan suka zuk'e a idanunsa, Fadeela dake take tafiya a gabansa kawai yake gani da kuma wak'ar da yake jin kamar daga bakinsa take fitowa, da kyar ya sawa k'afarsa birki bai had'e da ita ba sanda ta tsaya daga tsakiyar hanyar tana waige-waige.

"Anan wajen fa na barta dasu Aunty iyami, ina kuma suka tafi?"
To whisper in your ear
Words that are old as time
Words only you would hear
If only you were mine...

Baitin wak'ar yayi daidai da yadda ya tsaya dab da ita kamar zai rad'a mata wani abun, a lokacin itama ta juyo ta kalle shi bakinta a bud'e kamar zata yi masa magana, sai kuma ta maida shi ta rufe sakamakon wani irin maganid'isun abu data hango daga kyawawan idanunsa.

Hasken flasher ne ya katse ya kuma janyo su daga tunanin da kowannensu ke shirin fad'awa a lokacin.

"Yawwa Hajiya, ku d'an juyo nan haka kuma muga, d'ari biyu ne kowanne kati ba tsada."
Wani mai hoto daya saita camerar sa akansu ya fad'a yana k'ara durk'usawa.

Ita ta fara janye idonta ta juyo ta kalli mai hoton sannan ta girgiza kanta da sauri tace.

"Yi hakuri Malam ba hoto zamu yi ba."
"Ayya hajiya wallahi baki ga yadda d'ayan yayi kyau ba, ko biyu ne mana ku tsaya a d'an kara yi, ku ajiye na tarihi."
Ta sake girgiza kanta.

"Ka goge shi kawai mun gode..." Ta juyo ta kalli Al'ameen d'in dake tsaye baice komai ba tace.

"Ga wajensu Ya Abdullahi can, ko zaka je kafin in nemo Mamin."
Bata jira amsarsa ba ta juya zata tafi, sai dai me?

Caraf ya riko hannunta guda d'aya, ya zagaye yatsunta cikin nasa yayi musu rumfa, gabanta ya fad'i sannan zuciyarta ta buga a lokacin d'aya kafin ta juyo ta kalle shi, idanunta na nuna tsananin mamaki.

"Ki tsaya ayi mana hoton ko guda d'aya ne."
Jin haka yasa mai hoton dashe baki sannan ya sake d'aukar saiti don kyallara musu.

"Please."
Ya fad'a da muryarsa a hankali yana kallonta, ya had'a ta da Allah, ba yadda ta iya, bama zata k'i iyawar ba.

Sai ta gyad'a kanta sau d'aya sannan ta juya kawai ta kalli mai camerar da ya gama shirinsa yana jiran nasu, ta gefen idonta taga sanda shima ya juyo ya kalli mai hoton da guntun murmushi a fuskarsa.

"Masha Allahu, wallahi Alhaji kunyi kyau, ko amarya da angon nan sai haka."
Murmushin nasa bai goge ba yace.
Chapter 37 · 0% Book details