Sashe 66
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana zaune cikin falon Hajiyar Daddy, suna tsintar wake ita da Ladi, Hajiyar na daga kujera tana cin wani dambun zogale da ladi tayi tana ta santi, Anya ladi ba zamu cire mangwaron tsakar gidan nan a dasa zogale ba kuwa?
Kar fa rani yazo mu rasa inda zamu samu, Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya...
Mami Safiyya na tsaye daga cikin wani had'adden filin shak'atawa tana kiranta, Deelah sauke ta haka ku taho muci abinci, ta juya ta kalli Iman da take turawa a lilon, Aunty deelah sau d'aya dan Allah, Iman tayi magiya, bata saurareta ba ta d'ago ta cak daga kan lilon tana dariya tana k'okarin sauka suka nufi wajensu Mami Safiyya, Daddy, Faruk da Zahra da suka zagaye wasu tarin kwanuka akan dardumar dake wajen...
Tana tare da Al'ameen, a cikin wani kanti na siyar da litattafai, ya zagayo ta bayanta ya zuro mata wani littafi daya bud'a cikinsa, Akwai wannan sunan a wanda kike nema?
Ya tambayeta, ta girgiza kanta tace Judy ne sunan macen, sai ya rufe shi ya juya wata kantar neman wani, idanunta suka bishi da kallo, yana da kyau, mata nawa ne zasu so kasancewa dashi a wannan lokacin?
Sai kuma kunyar kanta ta kama ta, ta juya ta cigaba da bincika kantar dake gabanta...
Tana zaune a cikin d'akin karatun makarantarsu, suna lesson ita da Adam, da kaloli suke amfani a ranar saboda haka ta nutsu a cikin aikin daya bata tana tayi, ta d'ago da kanta taga ya tsura mata ido, Me ya faru?
Ta tambaye shi, baice komai ba kawai ya ya lumshe ido sannan ya d'ora yatsansa d'aya akan kumatunsa, ta d'ago da screen d'in wayarta ta kalli fuskarta, wata koriyar kala ce ta shafi a gefen kumatunta, sai ta juya da sauri ta zaro tissue a jakarta ta shiga gogewa...
Tana tare dasu Fateemah, Rahma da wasu tarin k'awayensu a cikin d'akin Aseeyah ranar da aka kaita, Rahma ta bud'e labulen tagar d'akin ta hango can wajen gate, To Asee da fatan kin shirya ga Ango nan tafe, Aseeyah ta d'ago da fuskarta tace, Ya k'araso mana, shiri na yaushe kuma?
Suka kyalkyale da dariya bakid'ayansu...
Tana zaune a gaban Daddy, yana yi mata nasihar dake shaida cewa ya bada aurenta ga Al'ameen, kuka take yi, na farin ciki da kuma bak'in cikin cewa rayuwarta zata d'ore ba tare da sanin Danginta ba...
Tana zaune ranar bikinta da Al'ameen, lokacin da Mc ke kiran su Zahra filin rawa, lokacin da Sadiya ta tunkud'o Mairo tsakiyar rumfar da take zaune...
Lokacin da rayuwarta juya, ta gangara sannan ta tankad'a gab'ar ramin da a yanzu take tunkararsa.
Ta lumshe idanunta a hankali sannan ta bud'e su tar!
Akan gefen zanin matar dake fuskantarta... in har duk wad'annan abubuwan sun faru da ita a rayuwarta ta baya, me ya rage zai tsorata ta kuma a yanzu?
Ta san cewa tabbas wannan wani sharrin ne daga su Kawu Danjuma tunda har bata ga Habiba tare dasu ba, amma tun lokacin da ta farka a asibiti ta yiwa kanta alkawarin dake zuciyarta ga dukkan wani k'alubale daga gare su, ta rantse zata fuskance su a matsayin wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya.
Ta rufe idanunta gaba daya sanda motar taja ta tsaya sannan rugugin bud'e gate d'in KURKUKUN daga can waje ya cika kunnuwansu.
Barka da zuwa Fadeelah.
Ta yiwa kanta gaisuwar da babu mai yi mata.
****
"Muna da dokoki anan..."
Muryar wata k'atuwar mata ta karad'e d'akin da aka tsayar dasu bayan shigarsu cikin kurkukun.
"...
Kuma dole ne kowaccenku ta kiyaye su walau dad'ewa zaku yi a wajen nan ko kuma akasin hakan, bayan dokoki akwai ayyuka da muke rabawa kala-kala kuma dole ne kowannenku yabi su don mu zamu gaya muku yadda zaku yi komai anan,
sanda zaku tashi, sanda zaku yi aiki, sanda zaku ci abinci sannan sanda zaku kwanta.
Ba'a tashin hankali a wajen nan, duk wadda tayi mana taurin kai zata fuskanci hukunci mai tsananin da zata gwammace kashe ta akayi a maimakonsa."
Yadda take magana idanunta a tsaitsaye da kuma sautin muryarta ya tsorata wasu da yawa daga cikin matan amma banda Fadeelah, ta riga ta saba had'uwa da mutane masu irin wannan siffar na baiyana tsana k'arara daga kowanne b'angare na rayuwarta.
Wasu matron biyu ne suka tafi dasu cikin wani gini daga nan, aka kaisu wajen da aka d'auki jinin kowaccensu don tantance lafiyarsu, bayan nan kuma dukkansu aka auna fitsarinsu don ganin inda akwai mai ciki.
Daga nan a mik'e hanyar wasu band'akuna a jere aka kaisu.
"Akwai sabulu a ciki kowacce ta wanke jikinta sannan karku maida kayan dake jikinku, akwai zannuwa a gefe daga ciki."
D'aya daga cikin matron d'in ta fad'a sanda mutum bakwai suka shiga cikin kowanne toilet d'aya.
Daga inda suke tsaye Fadeelah na hango k'afafun kowacce daga cikin matan kasancewar k'ofar bata kai har k'asa ba, hakan yasa ake iya ganin fasashshen simintin dake cikin kowanne band'aki, yayi ramuka wanda kowanne bak'in ruwa ya taru cikinsa.
Zuciyarta ta tashi a lokaci guda taji tana shirin yin amai, sannan wani abu ya shiga zarya a tafin k'afarta saboda tsananin kyankyami, anya zata iya zama anan kuwa?
Me yasa bata tambayi mutumin nan ko za'a iya samun number Adam ba?
"Ina da magana dan Allah..."
Muryar wata mata a bayan Fadeelah tayi magana.
"...inaga ni ba sai nayi wankan.."
Bata k'arasa ba d'aya daga cikin Matron d'in nan ta buga mata wani bak'in sanda dake hannunta a fuska, matar ta dafe gefen fuskarta yayin da jini ya fara fitowa daga hancinta.
Matron d'in ta lailayo wani zagi ta rafka mata sannan tace.
"Mu ke da iko daku yanzu ba ra'ayin kanku ba saboda haka kar ki kuskura ki sake magana idan ba'a tambayeki abu ba, gargad'i ne ga kuma dukkanku."
Tana rufe baki idonta ya kai kan Fadeelah, ta nuna ta da sandan hannunta tace.
"In kika kuskura kika yi mana amai anan sai naci uw*rki."
"Ku fito!
Lokaci yayi!" Daya Matron d'in ta kwalla wa na ciki kira.
Ba b'ata lokaci kowannensu ya fito rufe da wani yamusashshen zani, Fadeelah ta had'iye yawun cikin bakinta sannan tabi layin matan dake shiga band'akin.
Bayan kowannensu ya fito suka shiga wata k'ofa daga nan wajen inda k'aton d'aki ne mai cike da buhunhuna na kaya, wata k'atuwar mace ce a wajen kamar Matron d'in farko da suka fara gani, ta kintaci yanayin kowaccensu sannan ta shiga mik'o musu uniform na kurkukun mai kalar ruwan toka, kowacce kala biyu, sannan pant, da brassier, slippers, da kuma man shafawa roba d'aya.
Bayan sun shirya aka raba su gida biyu, anan Fadeelah ta fahimci a cikin su goma sha takwas, su biyar ne kawai ba'a yanke musu hukunci ba amma duk sauran da adadin watanni ko shekarun da zasu yi akansu.
Su da ba'a yanke musu hukunci ba d'aki daban aka kaisu inda wani mutumi ya d'auki hoton passport d'insu ya lik'a a jikin forms d'insu da aka kawo daga can kotun.
_Shikenan!
Ta kafa tarihin da har abada ba zai goge a rayuwarta ba!_
A cikin su biyar d'innan Fadeelah taga harda wannan 'yar k'aramar yarinyar data gani a mota, ta daina kukan da take d'azu, da alama tayi ne har zuciyarta ta k'ek'ashe don idonta a tsaye yake kyam!
Tanabin fuk umarnin da aka bata
kamar inji.
A lokacin da aka gama komai aka sake had'e su da sauran, sai aka raba su gurin wasu matron shida, kowacce Matron aka bata mutum uku.
"Daga gobe za'a raba ku b'angare-b'angare na kalar ayyukan da zaku yi, yanzu za'a raba muku cell kuma nan zai zama wajen kwananku daga yau."
A sannan ne Fadeelah ta had'a ido da wannan yarinyar, sanda matron d'in da aka basu taja su zuwa wata hanya daban da inda su suke, Fadeelah bata san me yasa ba, amma ta hango wani zurfi a idon yarinyar makamancin nata, ta had'iye yawu a hankali sannan ta juya tabi tasu Matron d'in, bata sani ba ko zata sake ganinta.
Babu kowa a harabar wajen har suka shiga wani dogon gini mai d'auke da tambarin *'Block G'* wata irin hayaniya ta shiga kunnensu a lokacin da Matron d'in ta bud'e k'ofar wajen, Fadeelah ta juya kowanne b'angare na hall d'in ta kalli d'imbin fuskokin dake lek'owa daga kowanne cell, dukkaninsu mata ne sanye da uniform irin na jikinta da kuma sauran mata biyun da aka shigo dasu tare, bayan hayaniyar wani abu kamar tsami ko wari ya ziyarci hancinsu, Fadeelah taji cikinta ya juya aman d'azu na shirin dawo mata, anya bata yi kuskuren k'in kiran su Mami ba ko Kawu Sulaiman?
Ta yaya zata fara zama anan?
Taji kamar a cikin ruwa take tafiya lokacin da suke wuce tarin cells da maganganun matan dake lek'owa daga cikinsu, kwakwalwarta ta riga ta rufe a lokacin don haka bata iya fahimtar komai ba sai fito kawai dake fitowa daga kusan kowanne cell.
Matron d'in ta bud'e wani cell daga b'arin hagu.
"Shiga." Tace da Fadeelah da kuma d'aya daga matan.
Gabanta ya fad'i sanda matar ta shiga, ta d'an tsaya kad'an kafin tabi bayanta, garam!
K'ofar ta rufe, Matron d'in tayi gaba tare da d'ayar matar.
Kunnen Fadeelah ya amsa sautin k'arara rufewar k'ofar kamar wani abu dake gaya mata cewa sake fitarta zuwa duniyar waje abu ne mai wuya.
Fuskoki hud'u da suka juyo suka zuba musu ido yasa ta fahimci kowanne cell mutum shida ne, duk kuwa da cewar bashi da girma, wasu siraran gadajen k'arfe guda uku k'anana sai toilet na tsugunne daga can gefe inda aka kare rabinsa da katako, akwai kan famfo a samansa, amma babu alamun ruwa don warin daya gauraye iskar d'akin ta tabbata daga shi ne, Ya ilahi!
Watak'ila dai mafarki take yi!
Bai dace ta tsinci kanta a irin wannan wajrn ba.
"'Yanmata biyu a rana d'aya."
Muryar wata mace ta shaida mata cewa a tsakiyar zahiri take!
Babbar mace ce a jiki da kuma shekaru tana zaune daga kan gadonta tana kallo su, hak'oran cikin bakinta data washe sune kad'ai abu mai haskawa a fuskarta, a saman gadon kuma wata 'yar siririyar ce da fuskarta ke nuna alamun k'abila don ga bille nan rad'au
fuskarta.