← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 95

Sashe 21

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In ma kalli wannan Maths d'in da muke yi ka san ba ta kowacce hanya muke binsa ba, akwai tsararriyar hanyar da dole sai ka bita sannan zaka yi daidai, ni ada ai wata hanyar nake bi daban inyi lissafina kuma ya tafi ba daidai ba, sai da na had'u da kai sannan kake d'ora ni kan hanyar da take daidai.

Kamar haka bauta ga Allah ma yake, akwai tsararriyar hanyar da ubangiji ya turo manzanninsa su nuna mana don mu bauta masa a daidai, ba sai ranar da zamu koma gare shi sannan muga cewar mun b'ace hanya ne kamar yadda nake yi a lissafina na da ba, sanda zan d'auko hanya daidai, sai daga baya in kauce in tafi wani shirmen daban.

Saboda haka yadda Mr.

Hawkins ya aiko ka don ka nuna min yadda ake lissafin nan daidai, kamar haka ne Allah yake aiko manzanninsa don su nuna mana hanyar bauta masa daidai, don idan muka ce zamu bi kowacce hanya zamu b'ata ne."
"Me yasa to kuke ganin musulunci ya zama shine hanyar daidai a cikin kowanne?"
"Saboda tarin dalilai da yawa, a cikin alqur'anin da muka gama ji yanzu da kuma sauran litattafan, har da Bible d'in da kuke..."
"Ni ba christian bane." ya katse ta tun kafin ta k'arasa, sai ta d'ago sosai ta kalle shi, idanunta cike da mamaki.

"Bani da addini." ya fad'a mata amsar da bata tambaya ba.

Sai ta gyad'a kanta a hankali kafin tace.

"Idan har baka da addini kuma kana da irin wannan tunanin akan musulunci, na yarda cewa kai ba kafiri bane gabad'aya, kana wani mataki ne da k'okorinka zai iya tsallako da kai hanyar gaskiya."
Da alama maganar ta bud'e wani b'angare na kwakwalwarsa kuma ta saka shi tunani, irin tunanin da baya son yi a gabanta, saboda da sauri ya kawar da kansa sannan ya bud'e jakarsa ya zaro wayarsa.

"Lokacin mu ya cika leelah, sai gobe kenan?"
Ta d'aga kanta a hankali sannan ta tattara kayanta ta cusa a jaka ta mik'e tsaye, shima ya mik'e.

"Sai gobe?" ya sake tambaya a hankali, itama ta sake d'aga kai kawai sannan ta nemi hanyar k'ofa.

Kafin ta isa gate d'in makarantar, motarsa ta tsaya a gefenta, ya sauke glass d'in sannan ya sunkuyo da kansa kad'an.

"Zan iya kai ki gida?"
Ta matse hannun jakar a jikinta sannan tace.

"Ka barshi kawai ina samun mota duk sanda na fita."
An dad'e da wuce lokacin da take gaya masa duk maganar data fito bakinta don ba amfanin yin hakan ga wanda ta fara gani kyautatawarsa a yanzu.

A hankali ya maida glass d'insa ya rufe sannan yaja motar ya wuce ta.

Amma daga wannan ranar sai ya zama kamar tayin yana d'aya daga cikin karatunsu ne, a kowacce rana baya sun fito zai tambaya in zai iya kaita gida ita kuma ta tankwab'e hakan.

Sannan a kowacce wucewar rana da fitowar wata, zuciyarta na k'ara bude wasu kofofin ne da take fahimtar halayensa masu kyau, hirar addini ma sai ta sami gurbi a lokacinsu, sau da yawa shi zai fara tambayarta wani abun da zata yi ta bashi iya amsar data sani tana kuma kawo masa banbanci musulunci da sauran addinan, har ta kai in ya koma gida zai duba wani abun a yanar gizo yazo ya nuna mata.

Har ta kai hira tsakaninsu ta zama ba wani abu sabo ba, har ta kai shashashar zuciyarta ta fara rage yawan duhun tsanarsa a cikin zuciyar tata, har ta kai su Melissa ma sun sauko daga tunanin da suke akansa... sannan har ta kai zuciyarta na tuna shi bayan sun rabu har tayi hirarsa a wani waje, hirar yadda ta tsane shi kamar annoba a baya da yadda kirkinsa yazo ya canja tunaninta, sannan hirar data zama sanadin bud'e wani sabon shafi a rayuwarta!

"Wai me yasa kike yawan zancen Adam d'in nan ne Fadeelah?"
Al'ameen ya tambaya ta cikin wayar da suke yi a wani dare.

Earpiece ne a kunnenta saboda haka ta danne giyar motar da take driving a cikin game d'in da take yi sannan tace.

"Na gaya maka yana da kirki sosai, ban tab'a tunanin haka halinsa yake a baya ba, sannan baka ga tarin topics d'in dana iya ba saboda shi, kuma yana da son musulunci don ya rage abubuwa da yawa da yake yi a makaranta, yanzu kuma jikina yana bani kamar ta hanya ta zai iya musulunta."
"Ta hanyarki?" ya tambaya a hankali kamar iya abinda yaji kenan kawai.

"Kince kun kusa gama lesson d'in, me zai hada ku kuma bayan nan?"
"Babu." Ta amsa kai tsaye.

"... amma a makarantar yake ai, duk da ma Mami na ta shirye-shiryen komawarmu Nigeria..."
"Please..." ya katse ta a hankali.

"...Fadeela bana son zancen nan duka biyun."
Ta koma ta kwanta akan gadon da take zaune.

"Saboda me? na san baka son zancen tafiya Nigeria, amma meye da zancen Adam?"
"Ban sani ba..." ya sake fad'a cikin speaker a hankali.

"Ban sani ba ko kishinsa nake yi."
Cak! tunanin cikin kanta ya tsaya a lokaci d'aya.

"Ban san me yake faruwa dani ba but I think I'm falling in love with you, kullum ina gayawa zuciyata cewa ni dake kawai abokai ne amma abin ya kasa yiwuwa Fadeelah, ban taba jin yadda nake ji akanki game da kowa ba, shi yasa bana jin zan iya cigaba da pretending ban fad'a miki abinda yake zuciyata ba...

Da gaske nake ina sonki!"
A daidai wannan lokacin motar cikin game d'in ta daki wani gini, ta tarwatse sannan ta kama da wuta.

Kamar yadda ake zarewa mutum laka ya zama bashi da wani katab'us, haka Fadeelah ke jin jikinta a safiyar data wayi gari bayan Al'ameen ya bud'e mata dukkanin sirin zuciyarsa game da ita.

Ta rasa kuzarinta da walwala dama komai, tunani ya hargitse fal a cikin kanta harda kuwa irin tunanin da take yi duk sanda ciwonta ke kokarin tashi, irin tunanin dake son tuna mata wani sabon abu a rayuwarta ta baya.

Hakan yasa ta rubuta a jotarta cewa makamancin hakan ya tab'a faruwa da ita a rayuwarta ta baya kenan, Wani ya tab'a cewa yana son ita d'in da bata san ko wacece a baya ba.

Tun bayan sallar asuba har kusan azahar tana kwance a d'aki bata fito ba, ba irin tambayar da Mami bata yi mata ba akan me ya same ta amma ta kasa lalubo wani dalili ko ma k'arya guda d'aya ta fad'a mata, harshenta yayi nauyi, bakinta ya k'ulle gani take data bud'e zata fad'o dukkan kalaman da Al'ameen ya gaya mata jiya ne ta fallasawa Mami.

Ganin bata da niyyar magana yasa Mamin tace da kowa ya kyaleta watakila hutu take buk'ata kamar yadda ta lura a yanzu duk sanda ciwonta ya tashi in ta huta yana yin sauki ne.

Wanda kuma zuwa wajen la'asar d'in ta fara jin d'an dama-dama, sai dai ba'aje koina ba Iman ta shigo ta b'arar da hakan sannan ta d'auki duniyarta ta juya gaba a baya.

"Aunty deelah, kinga trophies d'ina?

Mami tace yanzu su Haneefa zasu zo zan nuna mata ne?"
"Wace Haneefan?" Bakinta ya furta a hankali amma cike da rud'ani, kamar akwai wata Haneefan da suka sani ne bayan k'anwar Al'ameen a garin.

"Haneefan Aunty Miryaamah, yanzu zasu zo gabad'ayansu."
Kalmar 'gabad'ayansu' ta ruguzo da wani k'aton gini a zuciyarta.

Tun daga ranar da suka je gidansu ita da Mami ana kwana d'aya da dawowarsu bata k'ara taka k'afarta a gidan ba, duk sanda Mami ko
su Zahra zasu je zata nemi wani uzirin da zai sa ta zauna a gida, kuma yawancin lokacin zuwan Aunty Miryamah gidan tana makaranta ne, saboda haka tsawon wata guda bata sanya matar a idonta ba... wani babban dalilin daya k'ara gina alak'arta da Al'ameen, don in suna tare zuciyarta bata taba tuna mata cewa ya dangance ta.

Sai a yau da yazo da wani sabon labarin daya canja rayuwarta shine zai tattaro uwar tasa su zo? idonta ya kai kan wayarta dake gefe, ta tabbata ya kira ta yafi k'irgen mai tunani Saboda tun jiyan bata kunna ta ba, don haka babu makawa ta san ma shi zai kawo su ba driver ba.

Mintuna goma bayan haka, hayaniya daga falo ta tabbatar mata cewa sun iso, gabanta yayi wata mummunar fad'uwa sanda taji Aunty Miryamah na fadin.

Al'ameen baka rufe k'ofar motar ba."
Ta kad'e har ganyenta, in har wannan matar ta san yadda ta saba da d'anta a cikin watan daya wuce, balle kuma ta san maganganun daya fad'a mata jiya? ta tabbata babu abinda zai hana ta kashe ta har lahira.

Sai ta lalubo wata shud'iyar hular sanyi mai k'atuwar toluwa ta auduga ta d'ora akanta, hakan bai hana bargajajjen gashinta fitowa ta kowanne gefe ba, ta bud'e window d'akin daya tafi ta bayan gidan ta tsallaka ta fita, anan taga tarin
kayan wankin da Mami ke shanyawa kasancewar dryer su ta lalace, sai ta sunkuya kawai ta d'ebo wasu ta shiga shanyawa don tana buk'atar wani abu da zai d'auke zuciyarta daga hayaniyar falon da take jiyowa.

"Fadeelah..."
Muryarsa ta amsa a cikin kanta sanda take kokarin shanya wata rigar Mami, wannan muryar tasa mai taushi da kullum ke saka ta farin ciki da nishadi, amma a yanzu sai wad'annan abubuwan suka juye zuwa hargitsi da rud'ani, taji k'afafunta sun k'ame a wajen ta kasa juyowa ta fuskance shi.

A hankali take jin k'arar nasa takun har ya zagayo ya tsaya a gabanta, amma sai rigar data shanya ta zama wani hijabi tsakanin fuskokinsu.

Bata iya wani motsi ba har yasa hannunsa d'aya ya zuge rigar ta koma gefe.

Ya salam! yayi kyau cikin wasu hadaddun kaya k'irar pakistan, kalar bak'i wadda ta k'ara fito da hasken fata da kuma kyansa, yayin da ita take sanye cikin bulamar rigar baccinta kalar yellow da kuma shud'iyar hular sanyi, ga gashinta duk a barbaje ya hargitse cikin rashin gyara, duk da ya d'an had'e rai amma fuskarsa na haskawa da wani annuri yayin da tata ke a kumbure saboda rashin wanka da kuma kwanciyar data dinga yi tun safe.
Chapter 21 · 0% Book details