← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 95

Sashe 31

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Barka da war haka Abbu."
Ya fad'a cikin tsantsar girmamawa lokacin da aka amsa wayar daga d'aya b'arin, yana shirin shan wani round-about ne a lokacin wanda zai kaishi hanyar chemist d'in da aka kwatanta masa.

Daga can cikin wayar muryar wani dattijo mai cike da kamala ta amsa.

"Barkanmu dai Al'ameen kana lafiya? ya aikin naku?"
"Alhmdlilah Abbu, aiki mun kusa gamawa, na kira jiya kafin jirginku ya taso amma ban same ka ba."
"Lokacin na cire layina na can ne, d'azu kuma naga kiranka amma shima a lokacin Maminku nata kiciniyar tarbata da girkinta mai dadi."
Murmurshi ya sub'uce a kumatunsa jin hakan, tun yana taro ya san mahaifinsa wani irin mutum ne mai saukin kai da yawa, hakan ne ya bawa
Aunty Miryamah damar rike kusan ragamar gidan bakid'aya, saboda kusan sai abinda tace yake yi, har kuwa zuwa yanzu.

Watakila kuma da yana da iyaye da 'yanuwa da wani abin yayi sauki, amma bashi da d'anuwa na jini ko guda d'aya, iyayensa sun mutu kuma sauran 'yanuwan duk na nesa ne dake rarrabe a garuruwa da dama, a da su kan ziyarce su lokaci-lokaci sai dai duk a cikin k'annensa ma shine mai iya tuna su sosai, don haihuwar Mami wata iri ce, bayan shi sai da ta shafe shekaru goma sha d'aya sannan ta haifi Fatima, daga nan Aysha da Haneefa suka biyo bayan shekaru bibbiyu, Saboda haka yafi su wayo a abubuwa da yawa.

Fatansa d'aya ne a yanzu, Mahaifinsa yayi amfani wannan damar ta ritaya daya samu wajen dawo da ragamar gidansa hannunsa, ya zama shine mai iko da komai ba sai abinda Maminsu tace ba..

"Yaushe kuke saka ran dawowa?"
Muryar cikin wayar ta katse tunaninsa.

"Babu rana amma dai kusan mun gama komai, So tahowar ba zata yi nisa ba."
"Allah ya taimaka kuma Allah ya kaimu, akwai zancen da zamu yi da kai in ka dawo."
"Insha Allah Abbu, nima zan taho da nawa."
Yaji alamun murmushinsa kafin yace.

"Ga Maminka nan ma ta shigo."
Al'ameen ne kuke magana? bani shi dama tun jiya bamu gaisa ba.

Tayi maganar tun daga nesa, a hankali yayi sallama da mahaifin nasa kafin ta karb'a.

"Al'ameen kana ne ina haka?"
Muryarta ta amsa daga cikin wayar.

Ya kalli kowanne gefe daga kan junction d'in da yake tsaye sannan yace.

"Na d'an fita ne, bana gida."
"Yayi, dama ban fiye son yawan zamanka a gidan ba, d'azu munyi waya da Hamida tace kace mata kun kusa tahowa ko?"
Ya cije gefen lebb'ensa kad'an, shi bai sani ba idan Hamida d'aukar maganarsa take daga baya ta kunnawa mata.

"Hakane Mami, jiya na sha'afa ne ban gaya miki ba."
"Ya kamata ai, mu muna nan muna ta shirye-shirye so nake daka dawo ayi bikin a gama kowa ya samu nutsuwa."
"Bikin wa?"
Ya tambaya yana zare ido sanda ya tsaya a daidai harabar wasu gine-ginen kantinan.

"Bikin ka da Hamida mana akwai wani ne? su zahra ma duk sun gama shirinsu, abinda ya rage kawai ka dawo kayi naka shirin sannan ka sanar da abokanka."
"Abbu ya san da zancen?" Kai tsaye bakinsa ya tambaya.

"Yaushe ma ya dawo garin, zamu yi maganar dai dashi."
"Mami dan girman Allah ki ajiye komai sai na dawo tukunna, ai ba lokaci ne zai k'ure ba."
"Ai na san haka zaka ce dama, shi yasa tun farko ban fad'a maka ba sai da muka kusan gama komai tukunna, har yaushe zan zauna jiranka Al'ameen? tsawon shekara guda fa kenan dana had'aka da yarinyar nan, kuma ka san ta gama karatunta da komai, zama zamu yi tayi rana jiran k'ailularka?"
Ya tamke bakinsa cike da hasala.

"Shikenan to Mami, zan kira ki anjima akwai abinda zanyi yanzu."
Bai ko jira amsarta ba ya katse wayar, fatansa d'aya tunda Mahaifinsa na kusa yaji duk abinda ta fada, ya fara d'aukan mataki kafin ya yanke nasa hukuncin.

A cikin k'asan ransa ya ayyana cewa watakila lokaci yayi da zata daina juya su gabad'aya.

Bayan ya koma gida, Mami yaso ya dank'awa maganin hannu da hannu don ta tabbatar da cewar ta sha, amma sai tsautsayi ya had'a shi da Fadeelan a tsakiyar kitchen
d'in da ya biyo ta cikinsa.

Tana sanye da wata doguwar riga da ta d'an kama jikinta kad'an wanda hakan ya fito da irin ramar data zabge ta a kwana biyun da ta takura kanta take tunanin ciwonta ne ya tashi ba wani abun daban ba.

Bai san me take yi ba amma ta juya baya yafe da d'ankwalin kayan akanta, yayi gyaran murya had'e da sallama sai dai bata juyo ba ta amsa, saboda haka ya k'araso ya ajiye farar ledar magungunan a daidai gefen hannayenta.

Ta juyo a hankali ta kalli ledar sannan shi d'in da idanunta dake sanye da medicated glass, A cikin 'yan sakanni kawai abu guda d'aya tak! ya faru, ta samu amsar abinda take nema a cikin kanta tun bayan zuwan Al'ameen Nigeria, ta fahimci cewa a wannan shekara d'ayan da take ganin ta cire zancensa a zuciyarta, ba abinda ya ragu sai ma kewarsa da ta dad'a yi, wadda a baya take ture ta da tarin abubuwa, amma a yanzu ganinsa ya sabunta komai.

Shi yasa take jin ba dad'i yadda baya kulata a farko take kuma damuwa da son sanin abubuwansa.

"Watakila likitan ya gaya miki zazzab'i ne kawai ke damunki, in zaki taimaki kanki ga magani nan kisha."
Abinda ya fad'a kenan kawai kafin ya juya ya nufi hanyar k'ofa, a yadda yayi maganar baiyi tsammanin amsarta ba shi yasa ya juya ya tafi, zuciyarta ta gaya mata cewa in har bata ce komai ba kuwa to ba k'aramin rashin kyautatawa bace, saboda haka ta saki cokalin tean da take had'awa ta juya da sauri tabi bayansa.

"D'an tsaya..."
Har ya sanya rabin jikinsa a waje sanda ta fad'i haka, sai ya juyo a hankali ya kalleta, hasken fitilar kitchen d'in ya haska mata wannan kyakyawar fuskar tasa mai cike da kwarjini, sai taji k'afafunta sunyi rauni kamar taliyar data dafu da yawa.

"Nagode."
Kalmar ta fito kai tsaye ba tare da wani shakku ba, yayi shiru kamar hakan ya bashi mamaki kafin ya gyad'a kansa a hankali sannan yace.

"Sai da safe."
Ta koma ta jingina da durowar dake bayanta sanda ya bar kitchen d'in, bayan fitarsa tare da likitan d'azu ba irin tunanin da bai faru a cikin kanta ba, ta fassara maganganun daya gaya mata ta hanyoyi da dama akanta, ta gane cewa da gaske ne abinda ya fad'a ta dad'e tana cutar da kanta ta hanyoyi da dama bayan ma rashin lafiyarta.

Kamar Al'amarinta dashi, ta sani cewa hadisi ne guda daga manzon Allah cewa zuciya tana son wanda yake kyautata mata, amma ita take ta kokarin karyata hakan akanta, Al'ameen mai tausayinta ne da kuma kyautata mata tun farkon had'uwarsu, shi yasa zuciyarta ta yarda dashi a iya d'an wannan lokacin har ta saba dashi amma tazo ta karyata kanta a gabansa da dimbin mutane cewa bata sonsa kuma ba zata tab'a sonsa ba, ta cutar da kanta tsawon wannan lokacin, watakila ma shi yafi ta cutuwar.

A hankali ta juya ta koma wajen ledar magungunan nan, ta kai hannunta ta bud'e ciki, sanyi ne da ita kalau na rab'ar A.c motarsa da bai gama hucewa ba, sai taji sanyin ya shiga har jikinta kamar yana gaya mata wani abu da ta kasa fahimta, kuma bata kai ga fahimtar ba k'ofar kitchen d'in ta hanyar falo ta bud'e, muryar Zahra ta kwararo ciki.

"Aunty deelah kizo inji Daddy."
A hanyarta ta zuwa falo ta ayyana a ranta cewa lokaci yayi da ya kamata ta canja, ta samu wanda zata dinga raba damuwarta dashi.
****
BAYAN KWANA BIYU.

"Fadeelah son Al'ameen kike."
Zuciyarta ta fad'i ta rugurguje jin haka, da sauri ta d'ago da idonta ta kalli Fatiman dake zaune a gabanta, A duniyarta kaf! banda Mami, Fatima kawai zuciyarta ta zab'a don gayawa sirrinta.

Shi yasa a yau da suka zo gidan daga kasuwa bayan sayayyar kayan bikin Aseeyah, zuciyarta tata ta kasa hakuri sai da ta jata can k'uryar d'akin Mami ta
shaida mata komai da yake faruwa tsakaninta da Al'ameen tun farko.

"Kin riga kin sani kema kawai dai kin k'i barin kanki ki fahimta ne saboda tsoron da kika sa na mahaifiyarsa, ki lura sosai ki gani a wancan lokacin da kika saba dashi sanda kuna America, kin manta ne kwata-kwata da zancen mahaifiyar tasa kin ture ta a cikin kanki, amma daga lokacin da ya fad'a miki yana sonki kika dawo da komai kika datse alak'arku."
Ta girgiza kanta sannan ta k'aryata abinda ta gama lissafawa a ranta.

"Wannan hasashenki ne kawai Fatima, amma ni bana tunanin ina son Al'ameen, kawai dai ina ganin kyautatawarsa ne game dasu Mami da kuma yadda yake damuwa da al'amarina."
"Ai ba tunani kike ba Fadeelah, d'an balaraben nan ya dad'e da tafiya da zuciyarki, ki bud'e idonki sosai ki gani me yasa kike yawan tunaninsa?"
Ya salam! yawan tunani shine so?

To in haka ne Adam fa? ta tambayi kanta, a kwanakin baya ma ai tafi damuwa da tunanin Adam, zuwan Al'ameen ne kawai ya rage shi, kamar ta gaya mata zancen Adam d'in sai kuma ta fasa, zata rikita tane kamar yadda tata kwakwalwar itama take a rikice yanzu.

Fatima dake kallonta ta d'auki shirunta a matsayin nazari.

"Kin yarda kina sonshi Fadeelah?"
Sai ta d'ago daga mutsikka 'yan yatsunta ta kalle ta.

"Ko na yarda babu amfanin hakan ai, na fad'a miki na riga na gaya masa cewa bana sonsa kuma ba zan tab'a sonsa ba sannan a cikin mutane fa?"
Fatima tayi murmushi ta kamo hannunta d'aya sannan tace.

"Kuma sai aka gaya miki shi ya yarda? yaya ma kike tunanin zai yarda?
Chapter 31 · 0% Book details