← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 95

Sashe 84

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A k'aidar yadda aka tsayar, babu wani biki da za'ayi duba da halin da ta fito daga ciki da kuma rasuwar Sadiya da ba'ayi ko arba'in ba, don haka a yau d'in asabar kawai kaita za'ayi, Sai dai ance wai gidan biki baya b'uya don duk da ba wani taro ake ba amma gidan na Mami a cike yake da mutanen da ba wanda ya san yaushe aka gaiyato su, don hatta wasu daga cikin 'yan Babban gida sun zo duk kuwa da tazarar dake tsakanin Abuja da Zariyan.

Aunty Saratu tazo daga Kaduna sati guda daya wuce kuma tun daga lokacin suke ta zirga-zirgar yi mata kafi a gidan da Adam ya bayar tare da Mami da kuma su Aunty Hadiza.

K'ofar d'akin ta bud'e, Mairo ta shigo biye da ita 'ya'an Aunty Hassana ne su biyu, tayi kyau sosai cikin wasu kaya kalar Maroon. suka shiga jidon wasu manyan ledoji dake cike da kayan kitchen zuwa waje.

"Akwai wata motar da zata tafi yanzu ne?"
Asiya ta tambayeta.

"A'a, pick-up ce zata d'auki wannan, bake su Rahma suke jira mota ba?"
"Ai sunyi tafiyarsu, yanzu ta lek'o tace baza su jira ni ba."
Mairo tayi murmushi tace.

"Kawai fad'a miki tayi, amma su usman d'in ma Mami
ta aike su gidan Hajiya Amarya yanzu, sai sunje sun dawo sannan zaku tafi."
Fadeelah tayi murmushi sanda Asiya tayi kwafa tana fad'in.

"Zata san ni zata yiwa burga kuwa."
Mairo ta juyo ta kalle ta tace.

"Au kun kusa gamawa ma, bari na d'auko miki kayanki sai ki shirya kawai, gasu Jamila can sun zo suna tambayarki."
"Su waye su Jamila?"
"Jamilan kika manta?

Matar Yaya Salisu fa(wansu, d'an wajen gwaggo lami.) Ita da kishiyarta ne da kuma matan 'ya'yan gwaggo Ramatu, yanzu suka sauka."
Sai ta gyad'a kanta kawai don har yanzu Mairo ta fita gane mutane, don ta fita wayo a lokacin da duk suka bar gida, sannan ga matsalar ciwon kwakwalwar da tayi ma, har yanzu ba kowa take ganewa ba.

"Momy zanci abinci." Afra ta fad'a kafin ta sami damar cewa wani abun.

"Okay zauna nan, yanzu zan kawo miki."
Cewar mairon da murmushi akan fuskarta sanda d'auki wata leda tabi bayan 'ya'yan Aunty Hassanan.

Sai dai duk da murmushin nata, Fadeelah na iya hango wani abu kamar alhini a can k'asan idanun nata.
halin yanzu labarinsu kusan d'aya ne, ciwonsu iri d'aya ne kuma suna shiga cikinsa ne daki-daki, zata iya rantsewa tana iya jin abinda Mairon ke ji a zuciyarta don itama a wannan lokacin irinsa take ji....

Daga yau rayuwarsu zata cigaba ne tare da mazan da suka zama kamar k'alubale a gare su.

A waccan ranar da aka d'aura aurenta ne Sadiq yazo tare da k'annen mahaifinsa maza kuma anyi zama mai tsaho tsakaninsu dasu Kawu Ibrahim harma da Mairon kanta, bata san me aka tattauna ba don a lokacin bata cikin nutsuwa amma dai an kawo k'arshen komai da cewar Mairon zata koma d'akinta, don haka Kawu Ibrahim ya bata damar zab'ar ranar komawar tata wanda ya kama a yau Asabar d'in da itama zata bar su Mami.

Banbancinsu kawai shine tunda suka dawo Sadiq ke zarya zuwa gidan yana neman shawo kan Mairo, yayin da ita kuma tun bayan dawowar tasu, sau d'aya tasa idonta a cikin na Adam, ranar da yazo ya tarwatsa duk wani ragowar kuzarin data fara samu a zuciyarta...

Shi kad'ai yazo a ranar, banda Sa'id da ya zama kamar k'anin Mami a yanzu saboda komai da ya shafi Adam d'in shi ake nema akai.

A lokacin data same shi a falon Daddy inda aka sauke shi, 'Yan k'ananan fitilun ceiling na tsakiya ne kawai a kunne don haka a lokacin d'akin yayi duhu har ana iya ganin hasken wayar da yake dannawa akan fuskarsa...

Ta fitar da numfashi a hankali lokacin da ta zauna a gabansa kuma hancinta ya zuk'o mata wannan k'amshin da ta dad'e da yiwa tambari da NASA.

A speaker ya amsa wata gajeriyar wayar Sa'id kafin su gaisa don haka ta sami damar kallonsa sosai, Ba ranar ta fara ganinsa cikin dogwayen kaya ba, amma ranar ta fara ganinsa cikin dogwayen kayan masu kalar sky blue, ya sanya hula sannan har a lokacin gashinsa a taje yake, yak'i ya barbaza shi irin na Adam d'in da ta sani a America...

Waye ne yace lokaci baya gudu?

Waye kuma ke tantama da faruwar al'amarin Allah cikin d'an lokaci?

Kamar 'yan kwanakin baya ne fa kad'an take gabansa yana koya mata karatu a matsayin wani bare, yau sai gashi a wasu matakai masu girma har guda biyu, na d'an uwa da kuma mijinta!

Sai dai ba wad'annan abubuwan ne masu amfani ba, abinda ya fara gaya mata a lokacin shi yafi komai muhimmanci a wajenta, sunanta ya kira, ainihin sunan daya fara saninta dashi.

"Fadeelah."
Bata san lokacin da ta d'ago ta ware idonta a kansa ba da tsananin mamaki, sai dai meye abin mamakin, ita fa ta nemi hakan a wajensa tun
ranar da zasu rabu don tsaf da maganar da suka yi a can baya ta dawo cikin kanta.

"... ina fatan zuwa lokacin da zamu sake had'uwa ka ka koyi harda yadda ake fad'in sunana."
Amma mai yasa bai fad'a ba tuntuni sai yanzu?

Da muryarsa mai taushi ya bata amsar da tambayarta.

"I'm sorry Fadeelah, kiyi hakuri tsawon lokacin da muka had'u ban nuna cewa na sanki ba, nayi hakan ne saboda yanayin aikina, case d'inki babba ne da bai kamata na bari wani abu yayi distracting d'ina ba, ko su Kawu Ibrahim ban sanar dasu komai ba, sai bayan da aka k'are shari'ar tukunna na fad'a musu."
Iya wad'annan kalaman kawai da zai iya fad'arsu cikin layi uku su suka dad'e suna sata tunanin kwana da kwanaki, taji kamar ta tambaye shi wane irin yanayin aiki ne da zai hana shi fad'a mata hakan kawai amma sai ta cakud'a yatsunta cikin juna wajen kokarin saita kanta kafin tace.

"Me yasa zaka bani hak'uri akan abinda ba laifi ba, nima na fahimci kana da uziri shi yasa ban ce komai ba, beside wannan ma ya wuce, kamata yayi mu fuskanci abinda ke gaba yanzu."
Saura kad'an ta mari kanta, me yasa zata fad'i hakan, ai sai yayi tunanin ko tana da wata manufa ne akan auren nasu.

Ta cije lebb'enta sannan ta shak'i iskar dake d'auke da k'amshinsa ko zata samu sassauci.

Ya nisa kad'an sannan yace.

"Nima abinda ya kawo ni kenan."
Sai ta gyad'a kanta jin ta samu tallafi, Abinda ya kawo shi kenan ba ita kad'aice take wannan tunani ba, amma tsaya?

Me ye abinda ya kawo shin?

Ya cigaba da cewa.

"Na san daga ke har ni komai yazo mana ne babu zato, kuma a yanzu muna cikin wani hali da babu abinda zamu iya yi akai, amma ba zan takura ki ba kamar yadda aka takura ki yanzu, zuwa lokacin da komai zai daidaita I promise to set you free...

Zan barki ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kike so insha Allah."
Cewa yayi zai barta bayan wani lokaci, yana nufin auren ba dad'ewa zaiyi ba tunda ba aure ne dasu duk biyun ke da ra'ayi ba, idan an d'aura bada yardarsu ba su zasu iya kwance shi da kansu!

Nasa ra'ayin kenan, irin tunanin da yake yi kenan a lokacin da ita take zagaye da mutanen dake hango mata d'orewar rayuwa tare dashi.

Su Kawu Ibrahim, sun yanke shawarar had'a ta dashi ne don suna ganin cewa auren ne kawai zai iya wanke zuciyarta daga irin uk'ubar data fuskanta kuma shi yafi kowa dacewa da ita sannan hakan zai gyara zumuncinsu, amma sai a lokacin kwakwalwarta ta fahimci tunaninta
da nasa shigen d'aya ne banbancin kawai shine a yayin da ita take ganin kamar anyi kyauta da ita, shi kuma gani yake kamar an bashi ita ne a matsayin ladan wahalar da yasha... kuma baya buk'atar hakan!

Tun daga wannan ranar kuma bata sake ganinsa ba amma sun rabu ne lafiya kalau don bata nuna masa komai ba ta bari suka rabu akan hakan.

To me zata ce masa bayan ita kanta bata san me take ji game da auren ba da kuma shi kansa, ta san dai ba wai bata sonsa bane balle kuma ace ta tsane shi, don in har ta fad'i hakan ma za'a iya bata wani muk'ami a k'ungiyar makaryata.

Don zuciyarta ta damu dashi tun daga lokacin daya fara koya mata karatu har bayan shekara guda da dawowarsu Nigeria tunaninsa bai tab'a barin ranta ba, zuwan Al'amin ne kawai ya d'an d'auke hankalinta daga kansa a baya, sai kuma gashi ya sake shigowa rayuwarta da wani babban taimako...

To ta yaya kuwa zata tsane shi?

Matsalar kawai shine bata tab'a hasko wa kanta rayuwar aure dashi ba kuma tana ganin an bashi ita ne ta sigar da ba lallai yaga darajarta ba.

KARFE BIYAR DA RABI NA YAMMA.

"Kar kiyi kuka Deelah, wannan itace martabar duk wata 'ya mace, don haka kema martabarki ce kamata yayi daga mu har ke mu godewa Allah daya nuna mana wannan ranar don tsari na ubangiji babu yadda d'an adam zai yi ya canja shi, Allah ya sani daga yau zanyi bacci mai dad'i sanin cewa kina gidan aurenki lafiya, don haka ina rok'anki ki yafe min in har a zamanmu.."
"Mami dan Allah..."
Muryar Fadeelah na rawar kuka tayi saurin katse k'arashen maganar Mamin ta hanyar rungumeta, har kalmar laifi ta isa ta rab'i alak'arsu balle har ta kai ga neman gafararta?

Allah ya sani in da za'a tsallake duk wannan nasihohin kowa yayi mata fatan alkhairi a kaita kawai da yafi, watak'ila in komai yazo k'arshe taje can d'in, ta duk'unk'une a waje d'aya ta fitar da nauyin kukan dake k'irjinta zata ji sauki...

Aunty Saratu ta rungumeta itama sannan ta shiga fad'in abinda kowacce mace ta haddace shi.

"Aljannarki tana hannunsa Bintu don haka biyayyarki gare shi ita zata kwato miki wannan matsayin, kiji tsoron Allah ki bishi sau da k'afa, kar ki tab'a tsallake maganarsa Bintu sai in har ta kaucewa addini ne, sannan kar ki tab'a barin rashin gaskiya ya shigo cikin zamanku..."
Mairo ta kama hannayenta duka biyu tace.
Chapter 84 · 0% Book details