← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba zan iya tuna waye ya gaya min ba, sannan tunda aka fita da ita kowa ya gane cewa guba aka bata tunda kumfa nata fita ta bakinta."
Ga mamakinta sai ya gyad'a kansa kawai sannan yace.

"Mun gode Habiba."
Ya juya ga Alkali.

"Bani da wata sauran tambaya ya mai shari'ah."
Da haka ya koma ya zauna, Habiba ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi tana godewa wayonta, bata san cewa rami ta hak'awa kanta ba, don Adam ya riga ya gama abinda zaiyi ya d'aure ta da harshenta ba tare da ta sani ba, don yadda shaid'an ke shagaltar da bawa ga ayyukan zunubi ba tare daya farga ba haka Adam ke d'aure mai laifi da harshensa a kotu ba tare daya fahimta ba.

Shaida ta gaba da kutama ya kira Kawu Yahya ne, kamar sauran shima yazo ya gwamutsa k'arya da gaskiyarsa irin yadda suka shirya hakan tun a gida.

"Your witness.." Kutama ya fad'a sanda ya gama dashi amma sai Adam ya girgiza kansa alamun bashi da wata tambayar da zaiyi masa.

Ba sauran jama'ar kotun ba, hatta Fadeelah sai da ta d'ago ta kalle shi a lokacin, idanunta na haska tsantsar mamaki na rashin sanin inda ya dosa, ko kuma ma yana da tabbas cewa ya kama hanyar dosar wani wajen.

"Kotu ta d'age sauraren k'ara nan da ranar sha takwas ga wata, wato kwana uku masu zuwa, sannan kotu ta bada umarni a rik'e Habiba har zuwa sanda shariah zata daidaita."
Alk'ali Bashir Ali, ya shaida hakan sanda zaman kotun yazo k'arshe.

Da wani irin sauri Kutama ya mik'e.

"Ya mai girma mai shariah, Habiba bata da laifi...."
"Baka da hurumin k'alubalantar abinda kotu ta yanke Barrister, sannan kuma baka da hurumin k'alubalantar laifin wani!"
Da wannan hukuncin wani mai zak'in murya ya kawo k'arshen zaman ta hanyar d'aga muryarsa yace.

"Koooootuuuuu!"
"Me kake yi ne haka Adam?

Ka san cewa su Sadiya duk da suka tsaya a wajen nan k'arya suke fad'a, don me yasa su baka k'alubalance su ba?"
Kawu Ibrahim ya tambayi Adam a lokacin da ya same shi daga can bayan harabar wajen bayan yayi iya k'okarinsa wajen gujewa 'yan jarida da kuma tarin mutanen dake tururuwar jin ta bakinsa game da shari'ar.

A hankali ya sauke muryarsa k'asa sannan yace.

"Baba, na san duk abinda suka fad'a k'arya ne, amma da ace na tashi na k'alubalance su, da duk cikinsu babu wanda zai bar kotun nan a yau, Habiba ita kad'ai nake hari a lamarin nan, shi yasa ita kad'ai na k'ulle!"
Baku tambayi ina Mairo ba, Mairon Bintu, Mairon Sadiq!

Ya akayi har aka fara shari'ar nan babu labarinta?

Waye yarda cewa Adam ya kware a aikinsa???

Ina lawyers d'ina?

Ya kuga zaman mu na farko?

Sai mun had'u a zama na gaba!

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Mairo ta bud'e idanunta a karo na barkatai, don bata san iya adadin sau nawa tasha bud'e su tana komawa cikin mayen data kasance a cikinsa ba.

Cikin taimakon ubangiji wannan karon sai bata ji irin jirin dake sake maida ita duniyar data fito ba saboda haka ganinta ya tsaya akan wasu Nurses guda biyu dake tsaye a gaban gadon dake fuskantar nata, tun a baya kwakwalwarta
ta fahimci a asibiti take, amma bata yi tunanin cewa har a yanzun zata farka ta ganta a cikinsa ba, duk da cewa kuwa ta san abinda ya sameta ya cancanci hakan.

Bugawar zuciya, ba ciwo ne da rana d'aya za'a sallameta ta koma gida ba, amma tsawon kwanaki nawa kenan take nan?

Idonta ya juya kan agogon d'akin, k'arfe hud'u da 'yan mituna ya nuna, matsalar shine bata san wace k'arfe hud'un ba ta dare ce ko kuma ta rana?

Amma a take kwakwalwarta ta shaida mata cewa idan har k'arfe hud'un dare ne wad'annan Nurses d'in da take gani a tsaye ba lallai ne a same su ba.

Saboda haka ta yunk'ura ta mik'e zaune, tana jin kowacce gab'a ta jikinta tayi mutuk'ar nauyi wanda hakan ke nuna cewa lallai ne ta dad'e a kwance.

"Sister Hawwa, 185 ta farka."
Muryar d'aya daga cikin Nurses ta fad'a sanda ta juyo tana kallon gadon nata dake d'auke da wannan number.

A lokaci d'aya suka yo kanta gabad'aya, wadda aka kira da Hawwa ta d'ora bayan hannunta a k'asan wuyanta sannan tace.

"Sannu ya jikin naki?"
"Da alamun sauki, tunda a file dinta babu high blood sugar."
D'ayar ta fad'a, Mairo kallonsu kawai take yi ba tare da ta fahimci me suke cewa ba, don hankalinta yana kan wayar dake hannun wadda aka kira da Hawwa d'in, kamar kuwa ta karanci zuciyarta sai ta ajiye kayan hannunta har da wayar a gefenta ta juya ta shiga tab'a wani monitor dake gefen gadon nata.

Mairo bata jira komai ba tasa hannunta ta d'auki wayar ta danna ta, hasken daya kawo a screen ya nuna mata lokaci da kuma kwanan wata na ranar.

Laraba, sha biyar ga wata.

Kwakwalwarta ta shaida mata hakan a daburce, abin ya d'aure mata kai, taji kamar a cikin mafarki take, don gani tayi kamar jiya ne ta fad'i a band'aki Sadiq ya d'auko ta ya kawo ta asibitin nan cikin mawuyacin hali numfashinta na kakkatsewa...

Bayan hakan abinda zata iya tunawa kawai shine an shigar da ita CCU (coronary care unit.) Likitoci da yawa suka taru akanta daga nan akayi mata wata allura da ta janye ta daga cikin tunaninta.

Amma duk da haka yaya za'ace har anyi kwana uku da hakan?

"Kawo wannan mu gani, hannunki akwai allura." D'ayar Nurse d'in ta fada tana kokarin karb'ar wayar hannun nata.

Sai dai ga mamakinta tana karb'ar wayar Mairo tasa d'aya hannunta ta cisge allurar drip d'in dake shiga jikinta, sannan tasa d'ayan kuma ta cisge wayoyin monitor da aka manna a hannunta.

"Ya salam..

Meye haka?

Ina zaki?" Ta tambaya da tsananin mamaki ganinta diro daga kan gadon.

Bata ko saurare ta ba, idonta ya shiga bin d'akin da kallo, hijabi ko mayafinta take nema amma sai ta tuna ai daga cikin toilet d'in nan da ta shiga alwala haka Sadiq ya d'auko ta ba mayafi.

"Mijina yana nan?" Ta tambaya tana kallonsu su duka biyun.

"Yana nan, yazo harda sauran 'yanuwanki ma, yanzu ki koma ki zauna zamu kira miki su."
Sai tasa duka hannayenta biyu ta kwance d'ankwalinta ta maida shi yanayin yafe.

"Ina zaki je?

Kinga ki dawo ki zau..."
D'aya daga cikinsu tayi kokarin rik'eta amma ta fincike hannunta da karfi ta nufi k'ofa.

Ta san sun biyo ta amna hakan bai dame ta ba ta kama hanyar fita waje da iya saurin da zata iya, don sunfi shekara biyar da yin rijista da asibitin, ta riga ta san kowanne lungu da sak'o na cikinsa.

"Sister Rabi'a dan Allah taimaka ki tsaida ita." Muryar Nurse d'aya ta fad'a daga bayanta, amma kafin Nurse d'in dake gabanta ta fahimci me suke nufi ta wuce ta da sauri ta nufi hanyar matattakala ta sauka k'asa.

Benen na kallon waiting area don haka tsaf idanunta suka gane mata wanda take nema, Sadiq na tsaye jikin ginin receiptionist d'in wajen yana magana da ita, hannunsa na hagu d'auke da Muhammad.

Bata jira komai ba ta nufi wajen nasa sanda Nurses d'in dake biye da ita su kai ga cimmata, zaune a waiting area, mahaifiyar Sadiq ce da k'annesa mata biyu da kuma wasu daga cikin danginsu duk mata, sai 'yarta Afra dake ta 'yan wasanninta.

Kusan awarsu d'aya kenan a wajen saboda tun bayan zuwansu ranar da aka kwantar da ita, aka ce ba wanda zai iya ganinta sai zuwa yau daya kama kwanaki uku.

Mairo duk bata lura dasu ba, don idanu dama hankalinta na kan Sadiq da ya juya bayansa don haka bai ga tahowarta ba, sai Recieptionist d'ince mai suna Amina ta zare idonta cike da mamaki tana kallonta.

"Ai gata nan ma ta fito, har an sallame ta ne?"
A lokaci d'aya ya juyo da tsantar mamaki daidai sanda ta k'araso itama ta shige jikinsa saboda saurin da ta taho dashi.

"Maryam yaushe kika farka?"
"Sadiq mu tafi gida."
Dukkkansu suka yi maganar a tare, kuma lokaci guda.

Hakan yasa ya sake saurin tararta.

"Me kika ce?"
"Ikara zaka kaini." Ta fad'a tana kallonsa da idanunta wanda suka kad'a suka yi jawur alamun tana cikin ciwo har a lokacin.

Sadiq yaji duk wani tashin hankalin duniya ya dira cikin kansa a lokaci d'aya sannan mamaki ya k'ulle bakinsa.

"Yallab'ai yi hakuri wallahi fitowa tayi..."
D'aya daga cikin wasu Nurses guda uku da suka iso ta fad'a lokacin da suke kokarin rik'e hannunta, amma ga mamakinsa Mairo bata ko juya ba ta fizge hannunta da wani irin k'arfi da bai tab'a sanin tana dashi ba, a lokacin kuma Muhammad ya kwallara kuka mai d'agawa na alamun gane mahaifiyarsa da yayi, ya shiga mik'o 'yan hannayensa gare ta, amma Mairo bata ko kalle shi ba, idanunta a tsaye ta sake cewa.

"Sadiq gida zaka kai ni." Muryarta na d'auke da wani irin kaushi mai cike da ciwo.

"Subhanallahi, Sadiq me yake faruwa haka?"
Yayar mamansa ta fad'a sanda dukkaninsu suka taso daga waiting area d'in, k'anwarsa Zakkiya ta k'araso da sauri ta karbi Muhd d'in dake ta kuka a hannunsa ta shiga jijjiga shi, amma zillewa kawai yake yana mik'a hannu wajen uwar da yayi kewarta tsawon kwanaki, uwar da bata ma san yanayi ba, don bata kallon kowa a wajen, idonta na kan Sadiq kawai da ta shige cikin jikinsa kuma ta rik'o da kwalar rigarsa har sama, rik'o irin na alamun rok'o.

"Har ta farka?

An sallame ta ne?"
Da yawansu suka had'a baki wajen tambaya.

"Wallahi Hajiya ba'a sallame ta ba, farkawa kawai tayi ta fito, kuma tak'i bari a maida ita."
Nurse d'in nan ta fada.

"Sister Nafisa, jeki d'auko Diazepam
(allurar saka bacci.)"
Nurse Hawwa ta bawa d'ayar umarni.

"Sadiq gida nake son zuwa.." Mairo ta k'ara maimatawa tana jijjga shi, da alamu bata ko fahimtar abinda ke faruwa a bayanta.

"Bari inje in gayawa Dr.

Haruna, ina ganin ba zamu iya rik'e ta ba.."
"Bibty gida zani...."
"Me ya same ta haka me ya faru?" Wata likita da tazo wucewa ta tambaya.

"Kana jina?
Chapter 57 · 0% Book details