← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 95

Sashe 9

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda haka wannan azababben ciwon daya fitar dake daga hankalinki Fadeelah ba komai bane face alamun warkewarki.

Yanzu kin samu abu na farko, wato suna BINTU, tunda har kwakwalwarki tayi reacting akan sunan to yana cikin rayuwarki ta baya kenan, dole akwai wanda kika sani a baya mai suna Bintu.

Zan baki d'an littafi wanda daga yanzu duk sanda kika ji ko kika ga wani abu da ya sa kwakwalwarki ta d'auke shi, walau na farin ciki ko bak'in ciki komai k'ankartarsa kuwa zaki rubata shi a ciki, kuma zaki dinga yawo da ita ne koina ki rubuta dukkan abinda ya faru dake a take ba sai kin matsa wani wajen ba."
"Hakan na nufin zan dinga fuskantar irin wannan ciwon?"
"Ba wannan ciwon kad'ai ba Fadeela, creative reimagination yana zuwa a siga da yawa, a yanzu kinji murya a cikin kanki a gobe zaki iya haduwa da jiri, jibi zaki iya suma gabadaya ko kuma ki shiga furta wasu maganganun da hankali ba zai d'auka ba."
Fadeelah ta gyada kanta a hankali alamun ta fahimci hakan, sannan tace.

"Zaki yi min wata alfarma?"
"Ina jinki Fadeelah." Ta kara kokarinta wajen furta sunan.

"Karki bari su daddy su san ciwona ya kai haka please."
"Baki da matsala, babu wanda zai sani."
Dr.

Florence ta fad'a sannan ta kifta ido tana kallonta cikin wani abu mai kama da damuwa.

Haka kurum taji tausayinta har cikin ranta, a 'yan shekarunta kawai da basu fi k'irgen yatsu ba rayuwarta na shirin tarwatsewa.

Don Retrival stage mataki ne da in ba mai k'arfin hali da dauriya ba, a cikinsa d'an adam na iya haukacewa gabad'aya a rasa hankalinsa!

"Kin tabbata kinji sauk'i sosai?" Zahra ta tambaya tsaye daga gefen gadon tana danna wayar hannunta, kusan karo na biyar kenan tana mata wannan tambayar tun bayan shigowarsu cikin d'akin da aka canja mata daga ICU.

"Na warke Zahra, wai bakya gani tun dazu nake miki murmushi ne." Ta amsa mata tana washe fararen hakoranta.

"Gwara in tabbatar ne saboda zanyi posting a handle dina, bana so daga baya inzo ina cewa kin sake komawa rashin lafiyar."
"Toh dole ne komai sai kinyi posting?"
Ta d'ago ta kalle ta da idanunta rabi a bud'e tsabar jin kai, sannan hannunta a k'age gefen fuskarta.

"Hello, a 21st century muke fa ta yaya kike tunanin zan iya..."
"Zahra taho daga nan wajen ki barta ta huta."
Aunty Nina, d'aya daga cikin 'yanuwan Daddy na b'angaren Babansa da suma suke zaune a garin ta fad'a.

D'akin cike yake da duk wanda Mami Saffiya ta kira ta shaida musu cewa ana iya zuwa ganinta yanzu.

Daga can gefe idonta ya sake gano mata Iman, ta mak'ure a jikin Mami tana kallo ta, ta sake mata alamar tazo da hannunta amma ta matse kafad'unta.

Mami ta shaida mata cewa tun daga ranar da aka kawo ta asibiti kuka take yi tana ganin cewa labarin da ta bata ne ya tayar da ciwonta.

Pleeese!.

Bakinta ya fad'a ba tare da ta furta ba, Iman ta sake matse kafad'arta, ta san halinta sarai saboda haka tayi ta fad'a har saida taci galaba akanta ta taho.

"Kiyi hak'uri Aunty deelah..."
Ta fara tun kafin ta karaso.

"Sshhhh, waya gaya miki laifinki ne Iman? ki daina ganin hakan kinji, laifin kwakwalwata ce kawai da bata jin magana sosai, nasha gaya mata ta daina hargitsa ni amma bata fahimta."
"Amma ai ni na fad'a miki..."
"Iman." Ta sake katse ta.

"Kin san k'addara ai koh? toh ko baki bani labarin nan ba, Allah ya kaddara haka zai faru kuma babu mai iya canjawa."
Ba ta ce komai ba tayi shiru kawai tana mutsutstsuka zanin gadon a cikin 'yan hannayenta.

"Kin san me? a lokacin da nake gudun nan cartoon d'inki kawai nake tunawa, na zata nima turbo zan shiga!"
Ta fad'i maganar cikin cartoon d'in da ta san tana so, 'Wreck it ralph' hakan kuwa yasa ba shiri ta kyalkyale da dariya.

Itama tayi murmushin tana kallonta, zuciyarta cike fal da fatan ina ma a yanzu rayuwarta zata koma baya irin shekarunta, alkalamin k'addararta ya zama a hannunta.

BAYAN SATI GUDA.

Ta koma makaranta d'auke da tarin jotters a jakarta wad'anda zata dinga recording duk wani single abu na farin ciki da kuma bak'in ciki daya sameta a kowanne yini, yadda a kowacce ranar k'arshen mako da take da appointment da Dr.

Florence zata kai mata dukkaninsu su tattauna wanda ya kamata.

Fatan Fadeelah guda d'aya ne a lokacin, kar ta sake jin irin wanban ciwon kan, ko kuma wani abu da yafi ciwon yaci galaba akanta.

"Good morning class, kwanan watan yau shi ya kama daidai da ranar da aka kafa makarantar nan wanda ina girmama hakan, saboda haka na hutar daku babu karatu ko Assignments daga yau har zuwa gobe, zaku iya yin hirar ku amma cikin hankali ba da k'arfi ba, kuma banda cin abinci ko fito da waya please!"
Malaminsu na English Mr.

Ryan ya fad'a lokacin da ya shigo cikin ajin.

Fadeelah ta kifa kanta a table d'inta, wannan class ne da bata yinsa tare dasu Melissa, ita kad'ai ce kuma sauran 'yan ajin duk ba wani sabawa tayi dasu ba don haka bata san dawa zata yi hira ba.

Sai kawai ta janyo textbook d'in English d'insu 'How to kill a mokingbird' ta fara karantawa yayin da ajin ya rud'e da surutu.

Lokacin da k'ararrawar gama period d'in ta kad'a, da sauri ta maida littafin cikin jakarta sannan ta riga kowa fita daga ajin.

Wayarta tayi k'ara a cikin aljihun doguwar rigarta lokacin da ta nufi lokarta don d'auko textbook d'in history da suke dashi, ta janyota ta kalli screen din, text ne daga Melissa.

Already @history, mun ajiye miki seat.

Ta maida ta cikin aljihunta, sanda ta k'arasa wajen lokar ta bud'e sannan ta rage litattafan jakarta a jiki, sai dai idonta ya kai kan wata 'yar siririyar paper data fad'o k'asa daga gefen lokar kamar dama an zura ta ne cikin dabara.

Ta sunkuya a hankali ta d'auko ta, wani tsararren rubutu ne a jiki kamar an buga shi sab'anin ink din biron da take gani.

Ya jikin naki?.

Aka rubuta daga tsakiyar paper cikin harshen turanci, sai daga can gefe kuma.

Mr.

Hawkin's yana nemanki.

Kanta ya d'an so ya d'aure, don wannan ba rubutun Mellisa bane ko Romilda, kuma ta san su kad'ai suka san da rashin lafiyarta a makarantar, sai ko principal da Daddy ya gaya masa a waya.

Kamar ta yar da paper amma rubutun jiki ya sake d'aukar hankalinta sai kawai ta zuge wani d'an k'aramin zip a jikin jakarta ta ninke ta a ciki.

Bayan ta d'auki littafin, tayi tunanin ta fara zuwa wajen Mr.

Hawkins kawai tunda su Romilda sun samar mata seat a kusa dasu kuma ta san ba zata makara ba.

"Shigo." Muryarsa ta bata umarni sanda ta kwankwasa k'ofar office d'in nasa.

"Na samo miki wani labari mai dadi ne..

"
Ya fad'a a lokacin data k'arasa gaban desk d'in nasa rik'e da hannun jakarta.

"Game da performance d'inki ne, na samo wanda zai dinga miki lesson a makarantar nan tunda kince baza ki iya samun malamin lesson ba.

Shine best sudent da muke dashi a maths gabad'aya makarantar nan don haka in kin maida hankalinki kin saurare shi zaki yi passing sosai ki tsallake sirad'in maimaita ajin da kike kai."
Wani irin dad'i da farin ciki ya mamaye zuciyarta a lokaci d'aya, taji cewar insha Allah kamar ta tsallake masifar Maths ne don ba abinda zai hana ta sauraren wanda zai koya mata ita kadai sab'anin na aji mai gabadaya.

Hannunta ya damk'o jotter ta a cikin jaka da shirin rubuta hakan kafin ta hau yiwa Mr.

Hawkins godiya.

"Zaku dinga zaman awa d'aya ne kullum bayan an tashi daga makaranta, So sai ki gayawa iyayenki."
"Ba matsala, Nagoode sosai da sosai."
Bai saurareta ba ya d'auko wata paper daga cikin ma'adanin littattafanshi ya mik'o mata.

"Ga number shi nan a jiki na rubuta, ki kira shi kuga yaushe zaku fara, amma zan baki shawara, gwara ku fara da wuri don lokacin jarabawa ya k'arato."
Kamar yadda ruwa ke d'aukewa daga famfo in an kashe shi, kamar yadda tashin hankali ke samun Bawa a lokaci d'aya sannan kamar yadda mutuwa ke janye ruhi cikin kiftawar ido haka Fadeelah taji an zuk'e farin cikinta lokacin da idonta yayi arba da sunan dake jikin takardar.

Adam Steve.

Daga can cikin jakarta hannunta ya saki jotter nan data rik'o a hankali.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
"An kori Zainab daga aiki."
Zainab, k'awar Mami
ce da suka had'u tun a makaranta, kuma har a yanzu da shekaru ke gangarawa kowannensu cikin iyalai da nasarori, babu abinda ya shafi abotarsu.

Fadeelah ta juyo daga tsane plates d'in data gama wankewa a gaban sink ta kalleta, suna gyaran kitchen ne a lokacin bayan gama cin abincin dare.

"Ya salam!

Mami yaushe?

Me ya faru?"
"Zancen hijaab dai, in ba haka ba me zaisa deelah, abin k'aruwa yake kullum."
A farkon canjin shugaba da kuma tsare-tsaren sabuwar siyasa, sabuwar gwamnatin ta bawa european court of justice's decision goyon bayan cewa ma'aikata nada damar cire duk wani nau'i na shigar musulunci a wajajen ayyukansu.

A farkon hakan Fadeelah bata tab'a tunanin cewa abun zaiyi yawa ba sai bayan an kori Mami kuma an cigaba da korar duk ire-irenta da suka ki yarda su cire Hijaabin d'in nasu kafin zuwa aikinsu.

"Naso kinga yadda last CEO d'in da nayi interview a wajensa yake saurarata, ya rufe idonsa yana d'aga kansa irin yadda mutane suke yi idan ba amsar da suke so kake basu ba d'in nan.

Daga k'arshe kuma, tambayar dana san ita ta kore ni shine lokacin da yace.

You or your parents must
ve immigrated from somewhere, right?
(ke ko iyayenki kun zo daga wani waje ne koh?)
Ban damu da fad'awa kowa asalina ba saboda ina alfahari dashi, kai tsaye na gaya mishi ni 'yar Nigeria ce, kuma daga nan bai k'ara cewa komai ba, kawai wani kallo yayi min dana fassara da cewa.

Lady, ba zan taba d'aukan ki ba.

Ta d'anyi shiru sannan ta cigaba.
Chapter 9 · 0% Book details