← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kar ki damu in har addininki gaskiya ne wata rana zan shigo cikinsa, kuma watakila mu sake had'uwa in nuna miki hakan."
"Allah yasa hakan, ina fatan zuwa lokacin kuma ka koyo harda yadda ake fad'in sunana."
Ta fad'a tana tattara sauran papers d'in ta zura a tata jakar sannan ta mik'e, murmushinsa ya k'aru kafin ya sake cewa.

"Insha Allah."
Hakan ya sata murmushi itama sanda ta mik'e tsaye rungume da jakarta a k'irjinta, yadda kalmar ta fito a nannad'e cikin accent d'insa na turawa yasa ta murmushin.

"It's been nice knowing you, ina miki fatan alkhairi leelah Allah ya maida ku k'asarku lafiya."
Haka da wuri? har zasu yi sallama?

Zuciyarta ta tambaya amma kwakwalwarta tayi saurin ture hakan, to me kuma zasu tsaya suce, komai tsakaninta dashi a yau yazo k'arshe, karatun cikin wata guda ya zama sanadin bud'e abubuwa da yawa a wannan rayuwar tata, wanda muhimmai a ciki sune fargawa da lamarin Al'ameen tun kafin abubuwa su cakud'e mata da kuma yin hankalin cewa bai kamata ka d'orawa mutumin dake nesa da kai wanda baka fahimci halinsa ba tsana mai yawa, don daga baya zaka zo kana dana sanin hakan ne.

Tunaninta ya katse sanda ya mik'o mata zara-zaran yatsunsa na dama alamar su gaisa, sai ta janye nata ta b'oye shi a bayanta.

"Babu kyau gaisawa da maza a addini na."
"Ohh, I'm sorry."
Ya fad'a game da d'auke nasa hannun.

Lokacin da suka fita harabar parking d'in, ya juyo ya kalle ta sannan ya tambayi abinda yake tambaya kullum bayan gama karatun nasu.

"Zan iya kai ki gida?"
Ta girgiza kanta a hankali, ba zata k'are mu'amalarta dashi da abinda tun farko bata fara ba.

"Idan na fita..."
"... zan sami mota."
Ya k'arashe mata abinda take fad'a kullum, sai ta d'aga masa kai kawai da murmushi a fuskarta.

"Allah sada mu da alkhairinsa."
Wannan kalmar itace ta dasa aya guda a mu'amalarta da mutumin da take wa kallon muguwar tsana ada, a yanzu kuma take masa kallon wanda yayi mata taimakon da ba zata sake samun irinsa ba, zuciyarta ta bashi wani matsayin da har take ganin zata yi kewarsa a cikin ranta.

Adam ya lumshe idonsa kad'an yana hangen tafiyarta, yaso ya tambayeta k'asar da zasu koma amma sai yaga babu amfanin da hakan zaiyi masa, da kowanne taku da take yi, gani yake kamar tana warware wannan zaren da yake tunanin ya had'a k'addararta ne da tasa a waje d'aya.

A yanzu komai zai cigaba da tafiyar masa, ya kammala aikin da Mr.

Hawkins ya sanya shi, don haka dole ne shima ya cika alkawarinsa ta hanyar d'auko masa file d'in farko da Malamin phisics na makarantar ya fara cikewa sanda yazo kamar yadda suka yi yarjejeniya, tunda Mr.

Hawkins shine ke da iko akan d'akin da ake ajiye bayanan malamai.

Da bayanan cikin file d'in zaiyi amfani ya kammala abinda ya kaishi makarantar, dasu zaiyi amfani ya fito da dukkan wata shaida daya tattara da zata nuna cewar malamin physics na makarantar, David Peters
shine dai mutumin da ake zargi da kisan wata yarinya a garin Alaska shekara biyu da suka wuce!

A yanzu komai zai cigaba da tafiya kan tsarinsa kenan, zai koma bakin aikinsa sannan zai samu hutun da ya nema a baya wanda dashi ne zaiyi amfani ya gyara rayuwarsa, ya nemo asalinsa ya fita daga wannan rayuwar ta bogi da yake ciki.

Komai zai tafi masa daidai da yardar ubangijinsa.

Komai!

Ya k'ara jaddadawa kansa sanda ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga.

Sai dai abu d'aya ne bai tabbatar dashi a cikin komai d'in ba... yaushe kwakwalwarsa zata goge hoton idanun Fadeelah daga cikin kansa? tunda a tunaninsa shi da ita sunyi hannun riga a yanzu, k'addarar data had'a ta raba su.

Sai dai abinda bai sani ba shine...
... wata k'addarar bata ma fara ba!
_Me ya faru tsakanin Al'ameen da Fadeelah a wannan ranar da yaje makarantarsu?_
_Wace k'addarar ce ke shirin jan akalar labarin bayan shekara guda?_
_Wai ina mutanen Ikara ne?

'yan uwan Bintun mu me hatsari?_
_Ina Maryam 'yar uwar Bintu? ko kuma ince Mairo?_
_Kuna tunanin akwai dalilin shigowar wad'annan lauyoyin biyu cikin rayuwar Fadeelah?_
*Waye ya hango cewa yanzu zamu fara warware zaren labarin?*
*BAYAN NA MUTU!*
AYSHA SHAFI'EE
*12*
*BAYAN SHEKARA GUDA*
*ABUJA, NIGERIA.*
Asiya ta ware atamfar dake hannunta daga tsaye a gaban mudubi, kalar peach ce, k'asanta kuma yana da ado irin na leshi.

"Kai! gaskiya atamfar nan tana had'u wallahi, Zainab ta iya fito da anko...

Rahma kalle ta fa a bud'e."
Cewar Fatima wadda fitowarta kenan daga band'aki bayan ta d'auro alwala.

Rahma dake kan gado tana danna waya ta juyo da kanta.

"Kai-kai, ke anya ba zan siya ba kuwa?"
"Wallahi mu siya.." Fatiman ta amsa 15k sai mu canja kala kawai tunda ba bikin zamu je ba."
Asiya ta kalli Rahma tace.

"Amma kuwa da anyi mara zuciya, a kwace muku saurayin sannan kiyi ankon bikinsa."
Rahma ta tab'e bakinta.

"Ke wallahi Nanah ita ba damuwa tayi ba, don yanzu ma tana da wanda suka tattaka shi a hannu,
kar kiyi mamaki ma ya gaiyace ta kuma taje."
Fatima ta k'araso daga k'ofar toilet d'in ta d'auki dardumar sallah sannan tace.

"Haba ko bata son shi fa da ciwo abin sai taji ba dad'i ko yaya ne, zata daure ne a gaban ku kawai."
"Baki gama sanin duniyancin Nanah bane wallahi, dama shi ya nace mata amma tun farko ya san tafi k'arfinsa."
Asiya ta juyo fuskarta da alamun mamaki kafin tace.

"Deelah kin san Nanah k'awar Rahma?"
Tayi tambayar tana kallon can gefe k'asan window inda FADEELAH ke zaune ta baje tarin littattafai a gabanta, da alama karatu tayi ta gama don a yanzu hannunta dake rik'e da pencil d'in da ta gama zana graph akai zane yake yi, irin zanen da mutum kanyi a lokacin da yayi nisa cikin tunani.

Kiran sunanta da Asiyan tayi ne ya katse dogon tunaninta, da d'an sauri ta d'ago da fuskarta wadda cikin shekara d'aya ga wanda ya santa a baya, yanzu zai hango alamun girma a idanunta da kuma kyawunta da ya sake fitowa, kamar an k'ara fik'e wasu abubuwan ne na fuskar tata.

"Me kika ce?"
Ta tambaya a hankali tana kallonta ta cikin siririn medicated glass d'in idonta.

"Kin san wata Nanah k'awar Rahma?"
"Eh, kamar na tab'a ganinta sau d'aya."
"To kinga ankon bikin saurayinta ne wannan, wai shine Rahma take tunanin yi."
Kafin Fadeelah tayi magana Rahma ta mik'e zaune tace.

"Wai sai cewa kuke saurayinta, mutumin da har ya gama bilinbituwarsa akanta bata taba bari yaje gidansu ba."
Fatima ta karb'e da saurinta.

"Amma dai ai saurayinta ne, tunda taci kudinsa kamar ba gobe, kuma ko ke nan kinci kud'insa ba ita ba."
"To wannan ne zai nuna tana sonsa, kawai dai yazo ya bata rabonta da Allah yayi zai fito daga hannunsa ne."
"Kin san Allah.." cewar Asiya.

"... zan iya rantse miki Nanah ta so shi don watarana na had'u da ita a Stream (Asibiti) tace min shi akayi wa aiki taje duba shi, kuma kin san Nanah in bata son mutum ko mutuwa yayi sai taga dama zata ce Allah ya jikanshi."
"Kai k'arshen zance kawai bari in nemo muku ita kuji daga bakinta.."
Rahma ta fad'a tana danna wayarta, yayin da Fatima ta cigaba da zancen tana fad'awa Asiya, Fadeelah daga gefe kawai murmushi take tana kallonsu, bai kai minti d'aya ba Rahma ta nuno musu screen d'in wayarta data hau kan video call na whatapp, hoton fuskar Nanah wadda da alama daga bacci ta tashi ya nuna tar! akai.

"'Yar iska bacci ma take yi." cewar Asiya.

Ta cikin speaker wayar muryata ta fito.

"Yo me yafi raina Asee."
Fatima ta taho da sallaya a hannunta tace.

"Nanah bikin Umar za'ayi next two weeks."
Ta d'an had'e fuska kad'an.

"Wanne?"
Rahma ta zuro kanta.

"Dalla Umar fa sky."
"Ohh shege ya turo min katin last week nace Allah ya sanya alkhairi, kun san amaryar ne?"
"K'awar Asiya ce." Fatima ta amsa.

"Haba! kice zaku sha biki kenan, a watse a barta da gaiyar tsiya."
Asiya tace.

"Wannan dai kishi ne Nanah, don kin san mun yi miki kwace."
Ta cikin wayar ta d'an zare idonta alamun mamaki sannan taja tsaki.

"Wannan kwarangwal d'in zan wa kishi, to Allah na tuba in ana zancen maza ma wannan ai supplementary list zai zo, ko ita k'awar taki ba don kud'insa ba ba abinda zai sa ta kai kanta wannan wahalar."
Suka kyalkyale da dariya kafin Asiya ta sake fad'in.

"In dai har da gaske bakya kishi ga ankon bikin nan kiyi."
Ta d'ago mata atamfar daga kan cinyarta.

"Tayi kyau kuwa ba laifi, sannan kar ki damu kanki shine ma zai yi min... anjiman nan zan kira shi ince ya kawo min anko, ke nan gidan ma zance yazo wallahi dani dake zamu je mu karbo a wajensa."
"Yawwa Nanah!" cewar Rahma.

"Kice ke da k'awayenki ne ya kawo hud'u har da Fadeelah."
"Biyar ma zance besty, baza'a rasa wani mai son ba, ko a k'arawa Asee ta had'a biyu, in tana ganin kishin wannan abin zanyi."
Suka sake kyalkyalewa da dariya, sanda Fadeelah ta maida idonta kan zanen da hannunta ke yi.

Sak! idanunta suka gano mata wad'annan lumsassun idanun irin na Adam akan paper ta, abinda take zanawa dama kenan? wane irin tunani ta tafi haka?

Sai ta lalubo cleaner da sauri ta gurje shi daga kan paper, amma duk da haka shatinsa bai tafi ba saboda yadda ta danna fensirin ya shiga ciki.

Ya Allah! wai yaushe tunanin Adam zai barta ta runtsa ne? shekara guda fa? me ya sami kwakwalwarta ne.

Sai ta mik'e ta wuce su Asiya dake cigaba da zancensu ta nufi corridor d'in da zai kaita k'asa da niyyar zuwa kitchen ta d'auko ruwa.
Chapter 24 · 0% Book details