← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AYSHA SHAFI'EE
*33*
Bata san a wane irin yanayi motar ke tafiya ba don babu taga ko guda d'aya da zata nuna mata hakan, saboda haka ne ma bata san wace irin rayuwa ce ke gudana a waje ba, wannan wajen da a kodayaushe ke haskawa cikin mafarkinta.

Ta juya b'angaren hagu ta kalli sauran fasinjojin dake tare da ita, kamar yadda idanunta suka shaida mata ne tun farkon shigowarta..

Babu ko mai kamar Habiba a cikinsu balle ita kanta, ta gefenta wata Babbar mace ce mai d'aurarriyar fuska, akwai wasu mata biyu da fuskar su ke nuna tsoro da kuma tashin hankali kamar kusan duk sauran dake cikin motar.

Daga can jikin k'ofar motar idonta ya kai kan wata k'aramar yarinya bak'a mai manyan ido tana ta share hawayen dake zarya a fuskarta, a k'iyasinta baza tace yarinyar nan ta wuce shekaru sha uku ba amma ta san dole ne ta gota hakan tunda har mummunar k'addara ta jefo ta cikin wannan yanayin da take kan hanyar zuwa wajen da za'a tsareta kamar dabba.

Ko kad'an bata damu da sanin abinda ya kawo yarinyar ba balle sauran, saboda ta yarda kamar yadda k'addara ta jefo ta nan haka ma kowannensu zai iya tsintar kansa a ciki, damuwarta d'aya ce, wane irin kallo su suke mata?

Ta juyar da kanta gefe a hankali ta kalli fuskarta a jikin bak'in fentin motar, dishi-dishi inuwar fuskar me kawai ya fito don haka bata san wane irin yanayi ke jiki ba, wane irin yanayi ne ya sauka a jikinta tun daga lokacin da wani mutum ya shigo cikin d'an k'aramin cell d'inta a wata safiya.

"Kece Bintu Abubakar?"
"Eh." Ta amsa daga can k'asa inda take tsugunne.

"Bisa umarnin da aka yanke jiya a wannan koton za'a maida ke cikin kurkuku sai lokutan da za'a zauna shari'arki sannan za'a dinga kawo ki nan."
Maganar ta fito kamar a mafarki, ta kasa bada ma'ana a cikin kanta...

Wai za'a kaita kurkuku, ta yaya za'a kaita kurkuku?

Wata mace sanye da kayan masu tsaro da suka shigo tare ta nufo inda take ta mik'ar da ita, al'amarin yayi mata girma a cikn kanta, taji bangwayen cell d'in suna shirin had'ewa da ita.

"Ke kad'ai kin isa bama buk'atar tarkacenki."
Mutumin ya sake fad'a yana kallon ledar kayayyakinta dake ajiye a gefe, matar ta shiga k'ok'arin saka mata ankwa, tunaninta ya sake kwancewa, ta fahimci a sannan yake nufin za'a tafi da ita.

"Saboda me za'a kaini prison?

Me yasa baza'a barni anan har a k'arasa shari'ar ba?

Laifin me akace na sake yi?"
Ta jero tambayoyin tana kallonsa da dukkan wata ma'anar rud'ani.

"Hajiya laifin da ake zarginki dai shine, kuma ai ke kin ma dad'e anan akan wasu, k'aidar kotun nan zama in ya wuce biyu kurkuku ake tura mitum saboda bamu da waje da yawa, amma ke wajen zama biyar fa akayi akanki kina nan.."
Ya fad'a yana kallon cikin folder dake rik'e a hannunsa, zama biyar!

Zama biyar d'in da lauyansu Kawu danjuma ya gama fito da duk shaidunsa, Wannan kalmar kad'ai ita fahimtar da ita cewa da akwai ayar tambaya akan wannan hukuncin, in ba haka ba me yasa sai da Adam baya nan hakan zai faru?

"Lauya na ya sani?

Kun fad'awa 'yanuwana?"
Yayi wani guntun murmurshi.

"Koto ce ke da hakki akanki yanzu Hajiya ba wai 'yanuwanki ba, don haka in sun zo zasu sani, sannan lauyanki dole a gaya masa mana in ya dawo, don ina zai dinga samunki in ba can ba."
Matar ta gama saka mata ankwar sannan ta cafki saman hannunta alamun ta fara tafiya, sai ta juya ta sake kallonsa.

"Dan Allah malam ka ara min wayarka inyi kira minti d'aya dan Allah."
Guntun murmushinsa ya karu a sannan.

"Hajiya da alama kin manta matsayinki anan ne, waya gaya miki
kina damar 'yancin kira?

Sannan ko za'a barki ai sai da sharad'ai, ba wai in baki waya kamar a titi ba."
Ta sake girgiza kai ta a kallonsa.

"Dan Allah minti d'aya kawai zan kira 'yanuwana."
Ya girgiza kansa shima.

"Na gaya miki za'a sanar da 'yanuwanki..."
Ya kalli matar dake rik'e da ita.

"Hadiza, ja ta muje."
Kafin ta sake wata magana matar taja hannunta zuwa wajen cell d'in, ta wata doguwar hanyar daban da inda ake bi da ita ganin bak'i suka bi, don haka idonta ya gane mata tarin cells a jere kowanne cunkushe da mutane hud'u ko sama da haka, akwai na mata daban da kuma na maza, ashe da mutane da yawa a wajen bata sani ba?

Wani irin kokari Kawu sulaiman yayi har aka bata wannan cell d'in ita kad'ai ba tare da kowa ba? ihu da maganganu suka yi ta fitowa daga kowanne cell da suke wucewa.

"Yallab'ai an sallame ta ne?..."
"Oga mu kuma fa?

Ya za'ayi ne?"
"Baby, prison za'a kaiki, zan zo in fitar dake..."
Rikicewarta bata bari ta fahimci dukkan abinda suke cewa ba.

Wannan bak'ar motar rufaffiya na jira a harabar kotun sanda suka fita, ta juya ta sake kallon mutumin.

"Dan Allah yallab'ai ka taimaka min in kira 'yanuwana dan Allah."
Bata san wane irin tunani ne ya canja ra'ayinsa ba, don tsayawa kawai yayi ya d'an kalleta na wani lokaci sannan yace.

"Okay, amma minti d'ayan kawai da kika ce, Hadiza juyo da ita."
Ya fad'i hakan ne don kar sauran securites d'in dake can jikin motar su hango su, ya zaro wata 'yar k'aramar waya daga aljihunsa ya mik'o mata.

Sai dai tana karb'ar wayar, wani tunanin ya dirar mata...

Wa zata kira?

Daddy zata kira ta gaya masa har Mami taji hankalinta ya k'ara tashi ko kuma Kawu Ibrahim zata k'ara rikitawa ta gaya masa komai ya cigaba da cakud'ewa?

Me zai yi a yanzun da Adam baya nan?

Wa zai zo ma ya tunkara?

Adam kad'ai shine wanda ya kamata ta kira, shi kad'ai ne zai iya wani abin a yanzu amma baya nan kuma bata da numbersa kamar yadda ta tabbatar wannan karamin ma'aikacin ma bashi da ita, in har za'a samu sai a wajen manya irinsu Kutama ko wanda shari'ar tata ta shafe su, ta juya a hankali ta kalli motar dake tsaye ana shigar da wasu matan ciki, sannan mutumin dake tsaye a gabanta yana jiran wayarsa...

Babu wannan lokacin, sai ta girgiza kanta kawai sannan ta mik'a masa wayar.

"Na fasa, na gode."
Tafiyar cikin motar mik'ak'iya ce da bata da niyyar k'arewa, ga zafin injin bodin da suke zaune ga kuma warin man fetur wanda ya had'e dana jikin matan dake gefenta, amma Fadeelah bata damu da hakan ba, ta riga ta d'auke tunaninta dama kwakwalwarta baki d'aya daga cikin motar, ta tafi can wani lokaci baya, wasu zamaninnika da suka shud'e....

Tana zaune Inna saratu na yi mata kitso a tsakar gidansu, bata kai shekaru goma ba a lokacin, yayin da innarta ke ta zarya tsakanin kicin da inda suke alamun girki take yi, Mairo ta shigo rik'e da alqur'ani, ta tashi ta tafi da gudu ta rungumeta, kin siyo min yaya?

Kin siyo?

Ta tambaya tana tsalle a gabanta, Mairo tace ba'a samu ba Bintu mai siyarwar bata zo ba...

Mairo!

Inna saratu ta kira sunanta daga can inda take zaune, sai tayi murmushi sannan ta zaro wasu kayan
wasa na k'asa daga cikin hijabinta...

Tana tsaye a cikin ofishin Principal d'in makarantarsu na primary, Yarinyar tana da mutuk'ar k'okari Alhaji, Principal d'in ke fad'awa Babanta dake zaune a kujerar gabansa, Shi yasa muka ce ba sai tayi aji na biyar ba daga na hud'un ma zata iya yin jarabawar shiga sakandire, Babanta ya juyo ya kalle ta fuskarsa d'auke da murmushi na alfahari...

Suna tafe ita da Mairo akan wata hanya da babu mutane sosai, Tsaya anan ina zuwa, Mairo ta fad'a sannan tayi gaba, tabi inda ta nufa da kallo, wani saurayi ne tsaye sanye da fararen kaya, hasken yammacin ya haska manyan kyau na fuskarsa, da isar Mairo gabansa ya mik'o hannayensa duka biyun ya kamo nata, sai ta juya bayanta da sauri ga barin kallonsu...

Tana lek'e ta tagar d'akin Mairo, Mairo na zaune a gefen katifarta tana rusar kuka yayin da jamila k'awarta ke rarrashinta a gefe, Na san yaya Aliyu yana da kirki kuma yana da halaye masu kyau amma wallahi Jamila bana sonsa a matsayin mijina Sadiq kad'ai nake so, Jamila ta kalle ta sannan tace, Baki tsane shi ba kenan?, Mairo ta girgiza kanta, Ban tsane shi ba, matsayin da ake k'ok'arin bashi a rayuwata kawai na tsana...

Tana kwance a wani d'aki mai cike da mutane, hawaye na bin fuskarta yana jik'a filon da take kwance, hannunta na hagu d'aure da allurar k'arin ruwa, daga can gefe Inna saratu ce zaune a tsakiyar 'yanuwanta tana ta hawaye wasu na rarrashinta, wasu daga cikin mutanen d'akin suma kuka suke yi, wasu na jan carbi yayin da wasu ke karatun alqur'ani, wata tsohuwa ta shigo ta tsugunna a gaban Inna Saratu muryarta na rawa tace, sai hak'uri Saratu ki d'auki dangana irin ta mai sunanki uwargida a gun khalilullahi...

Abubakar ya tafi (Babanta), yabi Amina (Innarta) muma duk nan jiranta muke....

Har Sule ne zai saka ki aiki ki kasa yi masa sauri?

Hajiya Babba ke fad'a yayin da take tsugunne a gabanta, Ki zauna lak'aki magariba ta tarad dake saboda baki so yi ba?

To kuwa yau baki da abinci dare, yadda kika kwana jiya haka yau ma zaki kwana in yaso yunwar ta kashe ki...

Tana tsugunne gaban Hajiya Babba sanda jikinta ke girgizawa bakinta na fitar da wannan farar kumfar, sannan idanunta a zare tana kallonta, kallo irin na zargi da mamaki...

Tana kwance a dandaryar kwaltar titi, wani azababben ciwo na amsawa a cikin kanta, jini na zuba ta hancinta, daga can gabanta wata k'aramar yarinya ce kwance cikin jini, rigarta ta yayyage sannan naman cinyarta na wani gefe ya zaftare, ta tuno sanda maman yarinyar ke biya mata addu'a a farkon tashin motarsu, _subhaanal-lathee sakhkhara lanaa haathaa.._ Wasu mutane suka zo suka durk'usa gaban yarinyar, d'aya daga cikinsu ya tambaya, Tana da rai?

Yanzu muka kai mahaifiyarta waccan motar ta rasu!

Idanunta suka rufe a hankali ta koma cikin nata ciwon...
Chapter 65 · 0% Book details