← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 95

Sashe 46

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Amarya Allah ya sanya alkhairi..."
Sai taji ya k'ara matsewa kamar zai iya tarwatsewa ne a lokaci d'aya, amma tsawon awa nawa kenan ana abu d'aya bai tarwatse d'in ba? sai nauyi kawai da zuciyarta ke k'ara yi.

Fatima ta sunkuyo da kanta lokacin da wasu k'awayen Mami data rako suka mik'e daga d'aukan hoton da akayi.

"Wai ban gane ba, baki gaiyaci ko k'awayenki d'aya bane?

Ni banga ko Salma da kuke yawo tare a makaranta ba."
"Salma bata nan." Ta bata amsa a hankali.

"Tana Kaduna gidan yayarta, kuma ana hutu wa zan gaiyata?"
Tayi tambayar ne muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka a kowanne lokaci, don bayan abinda take ji, idonta na kan wayarta dake matse cikin hannunta, kusan awanni biyu kenan tana jiran shigowar kiran Al'ameen, tunda daga lokacin da yace mata sun taho yaci ace sun dad'e da sauka tun d'azu amma bai kira ta ba,
Ya za'ayi ya kasa kiranta in har ya sauka d'in?

Me zai tsare shi?

Akwai abinda zai d'auke hankalinsa daga kanta ne a yanzu?

Duk hayaniyar taron da hargitsin jama'a bai sa wad'annan tambayoyin sun bar kanta ba, ba wai don ta damu dashi d'in bane a yanzu, sai don zuciyarta na gaya mata cewa rashin kiran nasa ba alkhairi bane.

"Shikenan ai." Cewar Fatima ganin yadda idanunta suka kad'a tana shirin kuka.

"Amma dai ki sani baki kyautawa kanki ba wallahi, shikenan ace duk wajen nan babu wani naki?"
Fatima ta fad'i kalmar NAKI ne da nufin k'awayenta, itama ta san hakan amma a lokacin sai kwakwalwarta ta fassara mata kalmar a baibai kuma ta karb'i hakan da hannu biyu.

Ta d'ago idonta ta kalli tarin jama'ar dake gabanta bayan wucewar Fatiman...

Ba karya bane duk taron wajen nan babu wani DANGINTA, kowa anan bare ne da bata had'a ko d'igon jini dashi ba, gashi auren da suka zo taya ta murnarsa ma na shirin d'auke ta ya maidata can wata nahiyar ta duniya inda zata yi nisa da su kansu wad'annan bare dangin data samu, watakila ita haka Allah ya kaddaro mata rayuwarta, watakila har ta mutu ba zata ga wani d'anuwanta na asali ba, watakila daga 'ya'yan da zata haifa a gaba ne zata fara kafa wani sabon DANGIN nata.

Ta fad'i hakan ne a rashin sanin cewa amsarta na dab! da k'arasowa inda take sannan komai na shirin canjawa kamar yadda ubangiji ya tsara.

A hankali ta sunkuyar da kanta kad'an ta share kwalla sanda Mc d'in wajen data kasance mace ke fad'in.

"Ku kwantar da hankalinku ai mun gama photo session, yanzu zan fito muku da amarya kusha rawarku ku more."
Sarai!

Fadeelah ta san Mc dasu Zahra take, don tun d'azu take hangosu suna faman zarya wajenta kan a saka musu wak'a suyi rawa, ita kuma tace komai nata a tsare yake lokacin rawa na nan tafe.

Sai dai me?

A daidai wannan lokacin da Mc bata kai ga bawa mai kid'a umarnin ya saka wak'a ba, da kuma ita da bata kai ga d'ago kanta daga share kwallar ba, abinda ya zama sanadin canjawar duniyarta ya faru, Fadeelah taji durk'usawar wata mace gabanta da wani irin k'arfi mai kama da an hankad'o ta.

Hakan yasa ba shiri ta d'ago da idanunta da bata kai ga goge kwallar jikinsu ba, abinda ta gani, yasa kwakwalwarta ta sara sannan zuciyarta ta shiga duka cikin kirjinta kamar zata dagargaje...

Fuska ce irin tata sak! wadda d'an banbancin jikinta dake nuna ba mudubi tale kallo ba d'an kadan ne.

Tayi niyyar k'ifta idonta ta sake budewa don tabbaci amma rud'ani ya hana ta motsawa, ta kasa gane komai har sanda matar ta kamo duk hannayenta biyu cikin tsananin mamaki makamancin nata tace.

"Bintu?

Bintu kin gane ni?

Mairo ce,
Mairo yayarki ta Ikara!"
Fadeelah taji me tace, amma ma'anar kalmomin basu nutse cikin kanta ba saboda rud'ewa,
kallonta kawai take da dara-daran idanunta dake nunawa tar! cewa bata cikin haiyacinta.

"Dan Allah kar kice kin manta ni Bintu, kin tuna Maironki dake miki kitso?

Kin tuna mai goya ki har makarantar Allo?

Mairo da take zuwa boarding ta dawo?

Kin tuna ni Bintu?

Mairo da kike cewa d'iyar Inna Amina ke d'iyar Aunty Saratu ce?"
Ta sake fad'a tana jijjiga hannayenta,
sai dai kafin tunaninta ya iya lalubo wani abin ya d'orar, wata muryar ta shigo cikin kanta.

Sanda ta d'aga idonta ta kalli matar dake tsaye akansu su duka biyun, sannan ne wannan abun na k'asan mak'ogwaronta ya fashe ya kuma tarwatse,
d'acinsa ya tab'o har kan zuciyarta data buga tamakar zata doko ta fasa k'irjin nata, wannan duk bai isa ba, sai da kanta ya sara kuma ya shiga juyawa a take sannan ko'ina a jikinta ya shiga rawa.

"An gaya muku ni Sadiya kanwar lasa ce da in kun gujewa kowa zaku guje min?

An gaya muku ban haifu a matsayin k'anwar mahaifinku ba?

Gaku nan yanzu a hannuna gabadaya,
ko kin manta ne ke BINTU?

Kin manta ranar da kika kashe Hajiya na d'au alkawarin kashe ki kema?

Da ace su kawu sun rabu dani da tun yaushe ban fanshi jinin mahaifiyata ba, amma aka barki kika tsallake kika gudu, kika taho wajen 'yaruwarki da tunanin kun tsira?

Har wannan garin mafaka ce?

Kun zata ba mai iya gano ku anan?

Nace ku gaya min kun zata mutanen Ikara kifayen rijiya ne da basu iya yawo kamar tsinanniyar uwarku 'yar gudun hijira ba?"
Muryar ihu take tana magana cikin haki wanda hakan ya jawo hankalin mutane da yawa ya dawo wajen.

Da kowacce kalma d'aya da take fad'a,
ba abinda Fadeelah ke iya fahimta saboda wani irin tarnik'in azaba da yake d'agowa daga cikin kanta.

Sai dai duk da haka b'arin kwakwalwarta guda da ya gama lalubensa a lokacin ya shaida mata cewa matar dake tsugunne a gabanta 'yaruwarta ce, kuma da gaske sunanta 'Mairo'.

Wadda ke tsaye kuma sunanta 'Aunty Sadiya' 'yaruwar mahaifinta na ASALI, kuma su d'in duka biyu DANGINTA ne!

Bayan hakan data fahimta, kwakwalwarta ta rasa duk sauran k'arfinta kamar yadda rud'ani ya tsaida numfashinta, a hankali tunaninta ya sulale cikin wani bak'in duhu dake jiranta.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
****
Ta fara sabuwar rayuwarta ne a tsaye, zagaye da w
ata irin busashiyar iska mai sanyi, sannan a cikin wani d'aki mai d'auke da gado d'aya.

Wajen da bata san ina ne ba ko kuma abinda ya kawo ta, ta zagaye cikinsa fiye da k'irgan mai tunani amma bata ga koda 'yar k'aramar k'ofar da zata iya baiyana mata abinda ke bayan katangar da ta raba tsakaninta da d'aya duniyar ba.

Tsoro ya cika zuciyarta fal, taji kamar zuciyar zata faso daga k'irjinta ne ta gudu zuwa wata mab'oyar daban! rawar da jikinta keyi yasa k'afafunta suka zame a hankali ta kai har dandaryar k'asa._
Ina ne wajen? me ya kawota? ko su waye suka kawo ta? meye dalilin kawo tan, sannan wace ce ce ita?

Daga ina tazo?

Sai dai maimakon amsar d'aya da daga cikin hakan ta baiyana gareta sai ya zamo kamar an k'ara duhun bak'in hayakin daya lullub'e kwakwalwarta ne a lokacin, wanda ta kasa gane dalilin wanzuwarsa, tunda tunaninta yana aiki ba tare da tangard'a ba wajen k'ok'arin sanin ita d'in wace da kuma wajen da take ciki.

Sannan tana iya jin ilimin sanin abubuwa a cikin tunanin nata, hotuna da sunayen abubuwa da yawa, sanin halittar d'an adam da kuma yadda rayuwarsa ke tafiya.

Tana iya tuna yadda rana ke fitowa ta kwalle a sararin sama, tana iya tuna titi cike da d'imbin mutane kala-kala, tana iya tuna cin abinci, tana iya tuna yadda da dare wata kan haskaka doron duniya, tana iya tuna d'awaininyar uwa akan 'ya'yanta, tana iya tuna dariya da bak'in ciki sannan tana iya tuna komai na yadda d'an adam ke tafiyar da rayuwarshi, komai kuma yana nufin harda 'yan k'ananan abubuwa na mu'amala.

Amma duk da haka bata iya tuna wacece ita, ko daga ina tazo ko su waye iyayenta, Bata ma san meye sunanta ba.

Hotunan fuskokin mutane da yawa suka cika tunaninta amma babu ilimin saninsu, ko yaya tayi yunkurin yin hakan sai fuskokin su maye gurbi da tarin hargitsin wasu kaloli marasa ma'ana.

Ta kasa tuna koda mutum d'aya da ta sani ko wani abu data tab'a furtawa a rayuwarta.

Tsaya, rayuwarta? tana ma da ita ne a yanzun?

D'akin ya cigaba da zama a k'amewarsa yayin da mintoci suka yi tsawo suka juye awanni, a lokacin tayi duk dabarar fita daga d'akin har sai da tunaninta ya fara kad'ewa kamar yadda iska ke d'iban busasshen garin da aka shanya tana tarwatsi dashi.

Bayan wani zamanin guda, fatanta ya karb'u...

Muryoyi suka cika kunnuwanta yayin da takunsu ke k'arasowa gare ta, Ta mik'e da gabadaya ragowar k'arfinta yayin da jikinta ya shiga rawa, tsoro ya sake matse zuciyarta.

Ba zata iya tantance ainihin abinda suke fad'a ba duk da ta fahimci wasu abubuwan don da sauri suke maganar yayin da takunsu ke k'arasowa.

Idanunta suka ware cike da rarraunan zumud'i sanda k'arar bud'ewar boyayyiyar kofar wajen ya karad'e koina.

Ta k'ank'ance idanunta a hankali lokacin da wani haske mai yawa ya dallare idanunta, da farko ba abinda take iya gani sai hasken kawai, amma bayan 'yan sakanni... idon nata ya d'auko mata hoton siffofin dake tsaye a bayan hasken, siffofin dake mallakar muryoyin nan.

Ganinta ya koma tar! kamar lokacin da na'urar d'aukar hoto ta saita hankalinta akan wani abun!

A firgice ta farka daga nannauyan baccin da ta kasance cikinsa tsawon lokaci, don bata san dad'ewarta a hakan ba, amma dai ta san tasha yunkurin bud'e idanun nata bata iyawa.

Farin rufin d'aki tas ya shigo cikin ganinta mai hazo, ta kifta idanunta fiye da kirgen da zata iya kafin ta samu su saitu daidaita tar, a hankali kuma ta juya kanta b'angare d'aya na d'akin inda taci karo da wani gadon k'arfe mai d'auke da farar katifa irin wanda take kai.

Daga gadon babu komai sai wata k'ofa da take hangowa a rufe, akwai sanyi a iska wanda ke nuna cewa koma daga ina ne akwai A.C a d'akin.
Chapter 46 · 0% Book details