← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 95

Sashe 17

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina za'a ajiye wannan?"
"Kitchen zamu kai, baki fad'a min me kuka dafa ba?"
Ya fad'a yana yin hanyar kichen d'in, sai tabi bayansa da kallo cike da mamakin yadda yake magana kamar dama can sun saba, tunaninta ya gaya mata shi ba mutum ne mai k'umbiya-k'umbiya ba.

A kitchen d'in ta same shi yana ta fito da kayan cikin ledojin, kallo d'aya tayi musu taga kusan duk wasu 'yan k'ananan abubuwa ne da suke buk'ata a gidan, ya akayi ya san babu su? ko dai Mami ce ta aike shi?

"Mami bata nan?" Ya tambaya yana kallonta, kallon yayi mata nauyi saboda haka ta k'arasa a hankali ta ajiye guda biyun na hannunta a gabansa.

"Sun tafi Saloon dasu Zahra."
"Ke kad'ai ce a gidan?"
Ta d'aga kai.

"Good, kice muna da isashshen lokakacin da zamu sha hira kenan, amma fara zubo min abincin tukunna, na gaya miki yunwa nake ji tun safe na bar gida."
"Zaka ci miyar water leaf?"
"Zan ci ko meye hannunki ya tab'a Fadeelan last year, ke dai zubo min."
Yaja kujerar jikin teburin tsakiya na kitchen d'in ya zauna.

Allah ya sani zuciyarta ta san cewa ya iya fad'ar sunanta kuma tana son hakan.

A plate mai fad'i ta zubo masa sannan ta had'o da lemo da ruwa, ya rufe idonsa yana girgiza kai bayan yayi yayi lomar farko.

"Ya salam! abincin nan yayi dad'i da yawa Mrs. chef hannunki mai albarka ne."
Tana zuba sauran abincin a warmers sanda ya fad'i haka, kamar tayi shiru ta karbi yabon, amma haka kawai ta samu bakinta da fad'in cewa ba ita tayi girkin ba Mami ce.

"Ai babu banbanci..." ya d'orar "...tunda kullum kina tare da ita kina ganin yadda take yi.

Kuma ni ke na gani ma kin k'arasa."
"Girki daban, K'arasawa daban."
Ya gyad'a kansa.

"Ashe kina magana sosai, yanzu toh ki zubo naki abincin kizo ki bani labarin kanki da yadda akayi ba wanda ya tab'a gaya min kin..."
Ihun ball d'in su Farouk ya sake katse maganarsa.

"A 'yan uwan Mami wane side kike?.." ya cigaba.

"... saboda a da ina yawan binsu hutu Nigeria na san wasu daga ciki."
Ta shiga rud'ani kad'an da wannan tambayar, don ta san ko tayi niyyar amsawa da k'arya babu amfani tunda duk daren dad'ewa zai zo ya san wani abu game da ita ne.

"Ni ba 'yar uwar Mami bace." Ta yanke shawarar bada amsar da bai furta kai tsaye ba."
Sai ya fasa kai cokalin da ya d'auko bakinsa, kallon da yake mata ya nuna tsantsar hanqoron jiran abinda zata ce na gaba, amma tayi shiru bata cigaba ba.

Har zaiyi magana ta juyo daga rufe warmers d'in ta kalle shi.

"Ni kaina ban san wacece ni ba, ban san komai a kaina ba, ance watak'ila nayi hatsari ne nayi losing 'Memory' d'ina, wanda hatsarin ma ban san sanda ya faru ba... na manta komai harda suna na, Hajiyan Daddy ta Nigeria ita ta saka min FADEELAH kafin rasuwarta."
Kalamanta suka tsaida duk wani sauran tunani a kwakwalwar Al'ameen saboda tsananin mamaki.

Memory loss ne ya same ta!

Ya maimata hakan a cikin kansa kamar sai ya fad'a tukunna sannan zuciyarsa zata yarda, ba'a karance ya san cutar ba kawai, akwai wani d'an ajinsu da suke shiri sosai a makaranta, mutum ne shi mai surutu da barkwanci, kwatsam! bayan wani hutu da akayi yayi hatsari yayi losing memory d'insa shima, ya manta komai ya manta kowa har iyayensa, haka ya dawo makaranta bai san kowa a cikinsu ba, tun basu yarda ba suna binsa da tsokanar daya saba musu har suka daina don kallo kawai yake binsu dashi.

Gabad'aya halayyarsa ta mutu tare da Memory d'insa, ya koma kamar wani soko da bashi da tunani sai abinda aka sa shi kawai, daga k'arshe dole iyayensa suka hak'ura da karatun nasa aka maida shi gida ya zauna, ya zama rayuwarsa ta dasa aya ne daga nan sai kuma ranar da Allah ya kawo masa waraka.

Saboda haka babban mamakinsa shine na yadda aka yi itama take da matsala irin tasa amma take wannan k'okarin da baya nuna gazawarta a komai cikin sabuwar rayuwar data fara, yaji zuciyarsa ta d'aure tamau da tausayinta, shi yasa ya fahimci Maminsa bata sonta kenan, don ya kwana da sanin cewa ita mace ce mai son 'yanuwanta masu kud'i kawai da kuma k'in duk wanda zai rab'eta in har bashi dashi, balle kuma ita da asali ma bata dashi.

Tunaninsa bai tab'a kawo masa abu makamancin haka akanta ba,
yayi zaton rayuwarta tana tafiya ne kamar ta kowa ba wai a birkice ba, saboda haka yaji kamar ansa muk'ulli ne an bud'e zuciyarsa, tausayinta da tarin wasu abubuwan fal suka cikata kafin a maida muk'ullin a rufe.

Ya fahimci ciwonta, ta shiga cikin rud'ani da tashin hankali a 'yar k'aramar rayuwarta, kuma tayi dauriyar da har ba'a ganin gazawarta.

Idanunta basa kallonsa a lokacin, suna kan yatsunta da take ta murza su kamar mai son fito da wani abun.

A hankali bakinsa ya furta...

"I'm sorry!"
Sai ta girgiza kanta da sauri.

"You don't need to be, bana son tausayawar mutane da yadda suke nuna ina cikin matsala, shi yasa ba kowa nake gayawa hakan ba, shi yasa kullum nake b'oye ciwo na inyi k'ok'arin rayuwa tare da kowa, tausayawar mutane ita take dakusar dani a koyaushe bayan na riga na saka zuciyata ta yarda cewar zan iya fuskantar komai har lokacin da zan warke.

So dan Allah kar ka nuna min tausayinka kaima."
Baiyi magana ba sai taji k'arar motsin kujerarsa, ya k'araso gabanta ya tsaya.. ba yadda ta iya haka ta d'ago da idanunta ta kalli nasa masu tsananin kyau a lokacin da take jiran amsarsa.

"Kin san irin wanda ake tausayi ? sune wad'anda zuciyarsu tayi rauni da yawa ko kuma ta mutu gabad'aya har basa iya tallafar kansu da komai, su ake tausayawa don ganin basu da wani sauran nasara a rayuwa, amma irinki alfahari akeyi dasu Fadeelah, ga duk wanda ya san mai k'arfin hali dana zuciya irinki tink'aho yake ya dinga bada misali a duk inda ya samu kansa.

Saboda haka in har akwai tausayinki a raina, ba wanda zaiyi galaba akanki bane, sai dai tausayin cewa tabbas kinsha wahala a baya, irin tausayin da zai bani k'arfin gwiwar ganin cewar nima na taimaka miki da wata hanyar da zata amfane ki.

Zuciyata ta samu interest akanki tun kwanaki uku a baya dana fara ganinki Fadeelah, so kina ganin zaki bani damar da zan fahimce ki mu zama abokai?"
A sabuwar rayuwarta ta san bata tab'a fuskantar bugun zuciya ba, amma tunaninta yana gaya mata cewa babu banbanci tsakanin bugun zuciyar da abinda take ji yanzu saboda tsananin rud'anin da kalamansa suka sa mata, a iya saninta kaf! bayan 'yan gidansu da kuma likitanta babu wanda ya tab'a yi mata magana da tsananin affection da kulawa irinsa, toh amma kasancewar babu da wata alak'a tsakaninsu da zata iya d'orarwa, sai taji kamar zata sulale ne k'asa ta narke.

Abu d'aya ne ya ceceta daga jiran amsarta da yake wadda bata santa ba, sautin k'ararrawar doorbell daya karad'e kaftanin falon.

"Mun dad'e ko Deelah?" Mami ta fad'a sanda suke shigowa cikin falon bayan ta bud'e musu k'ofa.

"Gaskiya baku dad'e sosai ba."
"Aah tunda Al'ameen sarkin surutu yazo ai ba zaki ga dad'ewarmu ba dama."
Cewar Mamin tana kallon Al'ameen daya fito daga kitchen d'in bayan ya biyo bayanta, ya rarumi Iman ya d'aga
ta can sama a hannunsa, ta shiga callara ihun murna tana k'ank'ame shi.

"Baby girl, muga kwak'idon gashin naki da aka gyara, yayi kyau?"
Zahra ta turo baki jin haka kafin tayi hanyar d'aki bata ko kalle shi ba.

"Allah ya kawo ranar da zaki fahimci tsakonarki nake yi."
Mami tayi dariya kawai tana k'ok'arin
fito da wasu 'yan kayayyaki da suka siyo, Sai yanzu Fadeelah ta fahimci ashe basa shiri shi yasa bata tab'a jin zancen Al'ameen a bakin Zahra ba, duk kuwa da had'uwarsa na irin mazan da take bi a social media.

Yana k'ara cilla Iman a hannunsa ya nufi d'akin Farouk inda sautin k'arar TV ya ragu jin dawowar Mami.

"Mami wasu kayan kuka siyo?"
Fadeelah ta tambaya tana kallon ledar gabanta guda biyu.

"Kaya dai na siyo, amma kinga an kawo wasu ne yau?"
"Al'ameen ya shigo da wasu d'azu suna kitchen, nayi zaton ma ke kika aike shi."
Rana ta farko da bakinta ya fara furta sunan 'Amintacce!'
Murmushin dake fuskar Mami ya k'aru kafin tace.

"Allah ya kawo mu kenan ya dawo, in dai Al'ameen ne Deelah yanzu kika fara ganin wannan d'awainiyar tasa."
A take Fadeelah taji zuciyarta ta nutse can wani k'arshe mai nisa, tana son mutum mai kyautatawa a rayuwarta.

Har ya tafi a ranar, basu k'ara magana ba don sai da Magriba ya baro d'akin su Farouk suka je masallaci gabad'aya, bayan sun dawo kuma hira sosai ta kama tsakaninsa da Mami don ta fahimci suna shiri sosai, haka kurum ta samu kanta da yawan kallon fuskarsa mai fara'a lokacin da suke hirar da Mami har sai da Iman dake gefenta ta lura.

A wannan daren lokacin da tazo kwanciya, sai wayarta tayi k'arar alamun shigowar sak'o, ta d'auko ta a hankali daga bedside drawer ta kalla.

Bak'uwar number ce a jere mai kyau, sai dai sak'on jiki ne yasa zuciyarta ta matse ta kuma kwance a take.

Hey memory loss girl!

Good night!

Murmushi mai fad'i ya sauka akan d'an k'aramin lebbenta, har ya tale zuwa tsawon da bata tab'a tunanin ya tab'a kaiwa ba.

Allah ya sani a wannan ranar kaf! ta manta cewar Al'ameen jinin Aunty Miryaamah ne.

"Bari in duba in gani, idan baya nan sai mu tafi."
Fadeelah ta fad'a bayan sun gama classes d'insu na ranar suna shirin tafiya gida, Romilda taja tsaki kafin tace.

"Dole ne sai kin duba? kawai ki taho mu tafi, meye amfanin zuwanki kullum yana b'ata miki lokaci?"
"Ina ga yafi da ace banje ba gabad'aya, zan miki text in zan tsaya d'in."
Lokacin da ta murd'a k'ofar Library d'in ta shiga, yana zaune daga wani sabon tebur, dogo mai fad'i, akansa tarin wasu ledoji ne kamar na siyayya.
Chapter 17 · 0% Book details