← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 95

Sashe 74

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba irin tunanin da ban kawo akaina ba duk da irin bayanin da suka yi min, gani nake kamar k'arya suke wani abu ya faru da kai ne, wallahi har na fara hasko yadda zan caka musu wuk'ar dake jikina don su barni in fita in nemo ka...."
Sa'id ya shiga fad'a bayan sun rabu da jamil sun d'auki hanyarsu, Adam bai katse shi ba har sai da ya kai k'arshe, idonsa na kan titin birjin da suke bi sannan yace.

"Sa'id wacece Anna?"
"Anna?" Ya tambaya cike da mamakin me ya kawo sunanta kuma a wannan halin.

"Of course, ita."
"Wani abu ya gaya maka game da ita?

Cewa yayi ta san wani abu?"
Sa'id ya jero tambayoyin bi da bi, Adam ya cije lebb'ensa alamun baya son doguwar magana a lokacin, fahimtar hakan da Sa'id yayi yasa ya d'an kalli gefe hannunsa dunk'ule akan bakinsa kafin yace.

"Anna 'yar Babban gida ce itama, mahaifiyarsu d'aya da Babana, ta gamu da matsalar aljanu ne tun aurenta na farko, hakan yasa ta zama kamar bata da hankali sosai kowa yake gudunta, amma tana da nata hankalin don tana iya fahimtar wasu abubuwan."
"Wasu abubuwan kamar me?"
"Misali zata ci abinci kuma zata yi ibadar ta kamar kowa, kawai dai bata fiye tsabtace jikinta bane kuma tana saka shirme a maganganunta, amma bata da mantuwa, in har ta san abu, komai dad'ewarsa baya b'ace mata."
Adam ya gyad'a kansa yana jin kamar a lokacin ya tashi sama ya ganshi a Ikara kawai, kamar ya zuk'e duk tsawon tafiyar dake gabansu ya matseta cikin taku d'aya.

"Me ya faru?

Me Malam Salisun yace maka?" Sa'id ya yanke shawarar tambayar bayanin da baiyi masa ba.

"Zan fad'a maka."
Ya fad'a cikin harshen turanci sanda yabi motar gabansu yasha wata kwana...

Ya fad'i hakan ne kawai don ya rabu dashi, amma k'aidar bincikensa shi baya had'awa da kowa, baya gayawa kowa abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Har Sa'id ya bud'e baki zai sake magana wayarsa dake kan cinya ta shiga ruri, yayi saurin kallonta,
Ya Allah!

Ya akayi bai lura ba cewa sun shigo waje mai service ba, da sauri ya d'ago da ita cike da begen sautin kiran da yayi kewarsa tsawon kwanaki..

Bak'uwar namba ce da bai santa ba, ya d'an kalli Adam da idonsa ke kan titi kafin ya d'auka.

"Hello...

Eh Sa'id ne...

Eh muna tare dashi...

Okay tohm."
Sai ya mik'owa Adam d'in wayar.

"Da kai ake son magana."
Kamar bai ji shi ba don da alama yayi nisa cikin tunani, sai kuma ya mik'o hannu ya karb'a sannan ya kara ta a kunnensa.

Gaisuwa kawai Sa'id ya iya tsinta a cikin maganar da yayi kafin dogon bayanin da muryar ciki ke masa ya canza yanayin idanunsa zuwa wani abu da zai rantse ya kuma rantsewa bai tab'a gani tare da Adam ba, iya tsawon zamansa dashi.

Tashin hankali...

Tsantsar sa!
****
Basu sami airpot a Keffi ba, don haka dole suka k'arawa motarsu mai suka k'arasa cikin garin Abuja da kyar saboda yadda k'asan motar ya kwararrab'e da irin gurzar data sha cikin daji.

Zuwa wannan lokacin Sa'id ya fahimci me ake ciki don kiran waya ne barkatai ke ta shigowa wayarsa bi da bi na neman Adam, kasancewar shi wayarsa basu ma san inda take ba cikin tarkacen motar, kuma dukkanin kiran suna dangantuwa ne da labari d'aya, cewa bayan tafiyarsu kotu ta tura Fadeelah kurkuku wanda hakan ya faru da sa hannun lauya mai shigar da k'ara Kutama.

Sai dai abinda bai fahimta ba shine irin rud'anin dake haskawa cikin idon Adam, haushin abinda Kutaman yayi ne ko kuma me?

Shi fa ya kasa gane wace irin alak'a ce tsakanin Adam da wannan case d'in, ko kuma yace Bintun ita kanta, don ba zai yiwu ace duk wannan wahalar da kashe kud'in da yake yi saboda Kawu Sulaiman bane kawai, har yaushe ya sanshi da zai ta sadaukar da kud'i da lokacinsa saboda shi haka?

Yafi danganta cewa akwai wani abu tsakanin Adam d'in da Bintu.

Tunda ance ta zauna a America tare da marik'anta, zai iya yiwuwa ya santa ne tun a can, sai dai kuma kansa ya sake k'ullewa da tunanin in har su san juna me yasa daga shi har ita ba wanda yayi maganar hakan.

Ya juya ya hangi fuskar Adam d'in dake tsaye tare da wani dillalin sayar da motoci, inda suka tsaya zasu saida motar tasu bayan isarsu cikin garin Abujan, a yanzu ya fahimci cewar jinin mahaifinsa na hausawa ne kawai ke yawo a jikinsa, amma dabi'unsa kaf irin na al'adar turawan daya tashi a cikinsu ce, baya tab'a fad'in abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Bayan da kyar an samu wani makaniki ya sayi motar, suka tsaya anan gidansu na Abuja suka kintsa jikinsu kafin lokacin tashin da jirgin da Adam yayi musu booking, Sa'id yaso su huta zuwa washegari amma yaga babu niyyar hakan don haka ya rik'e ra'ayinsa.

K'arfe hud'u da 'yan mintuna jirgi ya d'aga dasu daga filin tashinsa na Nnamdi Azikiwe International Airport zuwa filin saukar jirage na garin Zaria.

Sa'id ya riga ya yiwa Awwal waya kafin su taso don haka tun kafin saukarsu yana tsaye a harabar wajen rik'e da muk'ullin motar da suka bar masa anan gidansu na Zariyan.
****
"....

Bayan tafiyarka da kwana biyu muka sami labari wai an d'auke ta daga nan cikin kotun zuwa wata kurkuku ta mata dake can hanyar barin gari, wallahi babu irin kokarin da ba muyi ba amma ma'aikatan kurkukun sun k'i saurararmu, sunce sai dai mu koma can kotun da aka kawo ta, daga nan ne za'a iya wani abu, kuma a can mun rasa wa zai saurare mu..."
Banda wad'annan kalaman na Kawu Ibrahim babu abinda ke maimaitawa a cikin kan Adam.

Ya rufe idanunsa tsam!

Ya k'ara jingina da kujerar cikin jirgin, ya kasa yarda wai Fadeelah na kurkuku a lokacin, ya kasa yarda cewa tafiyarsa ta jawo mata fad'awa mummunan halin da yafi wanda ya barta a ciki, yaya zuciyarsa ke ji ma sanda tana tsare a kotun balle yanzu kuma an gwamutsa ta cikin wata k'azamar rayuwa... kurkukun da ya sani a k'asashen da suka cigaba ma yaya suke balle kuma ta nan Nigeria?

Sannan ya kasa barin tunaninsa ya hasko yadda ta koma yanzu, musamman wad'annan idanun nata, sun d'ashe saboda wahalar rayuwar da bata saba ba?

Sunyi zurfi?

Sunyi fari?

Ko kuwa dogwayen gashin jikinsu sun zube saboda rashin abinci mai inganci?

Ya rantse a cikin kansa ya kuma rantsewa in d'aya daga cikin wannan ya tabbata sai Kutama ya biya koda kuwa bayan shari'ar ne...

Don ji yake kamar idanun nata a manne da zuciyarsa suke saboda tun daga ranar da k'addara ta had'a shi da ita, basu tab'a barinsa ba, tare dasu ya shiga duk wata gwagwarmaya ta rayuwarsa ya fito.

Fatansu Kawu Ibrahim da wannan mutumin marik'inta shine yanzu a dawowarsa yasa a fito da ita daga kurkukun a maida ta cikin kotun, amma shi ba wannan ne shirinsa ba, ya riga ya yiwa kansa alk'awari cewa daga jibi da zai kama ranar da za'a sake zaman shari'ar, k'afafun Fadeelah baza su sake takawa su koma wani k'azamin waje ba, zai k'are shari'ar a ranar ya kuma dank'a mata 'yancinta a tafin hannunta, 'yancin da zai wanke ta a idon duniya kuma 'yancin da zata zaga koina a cikin Ikara da kuma shi kansa Babban gidan ba tare da wani mai zarginta ba...

Abinda ya rage masa kawai yanzu shine Allah ya tabbatar da wannan alkawarin daya d'auka.

A hanyarsu ta shiga cikin gari bayan sun sauka daga jirgin, ya kira Jabir, wannan k'aramin lauyan da kotu ta bashi a matsayin mataimaki, shi ya gaya musu sunan kurkukun da Fadeelah take da kuma kwatancenta, yana iya ganin mamaki k'arara a fuskar Sa'id lokacin da ya cewa Awwal ba gida zasu nufa ba sai yaje yaga Fadeelah tukunna.

Har saida Sa'id d'in ya tambaya, Ba sai gobe ba? ya girgiza kansa kawai, ta yaya zai iya wani bacci bai je ya ganta ba?

Ta yaya zai iya runtsawa baije yaga wad'annan idanun ba...

Awwal cike da d'okin tuk'i kuwa yayi ta bin kwatancen map d'in da Jabir ya turo masa ta wayar Sa'id, don shi in za'a d'ora masa bindiga a lokacin ba zaice ga inda tasa take ba sai dai a shigar da harsashin kawai.

Zuciyarsa tayi girma kamar gingimemen gate d'in da suka tarar a k'ofar kurkukun, aka bud'e musu suka shiga bayan ya nuna I.D Card d'insa.

Bayan sunyi parking kuma wani daga cikin masu gadi ya shigar dasu har wajen receiptionist inda suka tarar da wata d'irkekiyar mace zaune akan desk d'in wajen fuskarta babu ko d'igo na alamun rahma.

Zuciyar Adam ta sake matsewa da tunanin har kwana nawa Fadeelah tayi tana rayuwa da irin wad'annan mutanen.

Matar ta d'auki wani kan wayar intercom bayan ya gama yi mata bayanin WAYE SHI da kuma abinda ke tafe dashi.

"Receiptioninst area.

Akai Bintu Abubakar waiting room, lauyanta yazo ganinta."
Tana fad'in haka ta ajiye kan wayar sannan ta mik'a masa I.d Card d'insa da ta duba, daga nan ta umarci wata Matron a gefenta da ta kaishi shi kad'ai can waiting room d'in, su Sa'id kuma su jira shi anan.

Lauyanta.

Adam ya maimaita kalmar a zuciyarsa sanda matron d'in ta jashi zuwa wata k'ofar, yaya Fadeelah zata ji in akace mata lauyanta ne yazo ganinta?

"Lauyanki ne yazo ganinki."
Wata Matron ta fad'a tsaye akan Fadeelah, a lokacin k'arfe shida da 'yan mintuna ne na yamma, tana zaune a harabar masallaci an idar da sallar magriba, tafin hannunta da yayi sab'a da kuma alamun kanta take bi tana d'ayewa a hankali yayin da Kenken wacce sai bayan an idar da sallar tazo ke zaune a gefenta tana bata labarin da ba ganewa take ba.
Chapter 74 · 0% Book details