Sashe 59
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko zata iya ci ya san tashin hankalin da take nad'e cikinsa ba zai barta taci na kirki ba, dole ne ma ta fara ramewa akan sanda ya fara ganinta, sai rufe nasa kawai ya mik'e ya shiga ciki.
Wasa-wasa, tunaninsa ya dinga k'aruwa, duk wani abu daya zo yi sai ya kwatanta shi da halin da Fadeelah ke ciki a lokacin, saboda haka ya rasa sukuni ko kad'an, aikin nasa ma ya kasa k'arasawa, yana jin hirarsu Awwal da Sa'id amma ya kasa cewa komai, daga k'arshe wani yanki na zuciyarsa ya kasa daurewa, ya gaya masa cewar bazai rasa shari'ar nan ba don kawai yaje yaga Fadeelah sau d'aya, shi lauyanta ne yana da damar da ko tsakar dare ya tashi zai iya zuwa yace a fito masa da ita ya ganta.
Saboda haka bai bari wani tunanin ya danne wannan ba, ya tashi ya shirya ya d'auki muk'ullin mota ya fita.
Motarsa ce amma ta zama kamar ta Sa'id saboda ko a can Abuja yafi shi amfani da ita, shi yasa bai san abubuwa da yawa a cikinta ba, a yanzu ma yana kunna ta ya hau titi, wak'ar dake cikin Cd da Sa'id d'in ya sanya ta fara playing.
I can be your hero baby..
I can kiss away all the pain..
I will stand by you forever..
You can take my breath away.
Sai ya maida kansa ya jingina da saman kujerar, saboda yadda sautin wak'ar ya karad'e motar a volume d'in da Sa'id ya barshi.
Am I in too deep?
Have I lost my mind?
Well I don't care...
You're here tonight!
Adam ya lumshe idanunsa yana kallon titin, ji yake kamar kowanne baiti dashi ake yi!
****
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
"Kai inda zaka san duk duniya ba inda munafunci yake tasiri kamar Babban gida, ace wai baturen nan yazo amma kowa haba-haba yake dashi, kai ba zaka ci kowa yana wajen ba sanda aka kafa dandalin Allah ya tsine masa."
Isah d'an gidan Kawu Bashir ya fad'a sanda suke zaune a dakalin dake gaban wani k'aton gida na k'asa bayan maghriba tare da wasu 'yanuwansa da abokansa.
Saminu d'an gidan ne ke sayar da rake a wajen saboda haka sai ya zame musu kamar dandali, harda ba siya yazo yi ba sai ya zauna a shiga hira.
"Kud'iii...!
Ake gaya maka yaro, kaima kayi kud'i ka gani wallahi har babanka durk'usa maka zai yi, har ka mutu kuwa in kana dasu baza ka taba jin mai zaginka ba." Cewar wani abokinsa.
"To yanzu ma meye ba'ayi ba, shi baban nawa da yazo kaga wani sussunkuyar masa da kai da yake yi, ance fa har zancen shari'ar sai da suka yi dashi."
"Ai shi yasa kullum nake cewa Sa'idu ya haye wallahi, don ance fa yanzu ma aiki yake nema masa a can Abujan." Cewar Saminu yana kankare rakensa.
"Yanzu ai kwa fad'i hakan..." Wani Ibrahim d'an bayan layin ya sako baki.
"Sanda ya dage yana karatunsa, ba daku ake kafa hirar wai shi ya nacewa boko zai je ya dawo ya same ku ba, daya gama ya fara zama a shagon babansa wace irin dariya ce ba'ayi daku anan ba, yanzu ai gashi nan tana kai masa."
"Ni yazu duk ba wannan ba..." Cewar Aminu yana gyara zamansa.
"...
Rayuwata ce ta shiga kwale-kwale zuwan mutumin nan wallahi, don tunda yazo Asma'u ta fara canja min fuska, itama ta shiga layin haukan dake tashi a cikin gidan wallahi."
"Haukan me?" Buhari ya tambaya yana gaftarar raken hannunsa.
"Au wai kai baka san me akeyi ba?
Lallai an barka a tasha wallahi." Cewar Saminu.
"Dan Allah me yake faruwa?" Ya tambaya da zumud'i.
"Tsaya in fara tambayarka a hankalinka kwana biyun nan baka ga yadda ake bawa Kawu Ibrahim wani girma bane?"
"Eh na lura kuwa don d'azu ma ina ji Ramatu tana cewa 'yarta ko za'a kai masa me?"
"Toh yanzu duk Babban gida, ba zan d'ebe maka kowa ba sai masu yara k'anana, fata suke Kawu Ibrahim ya had'a ya'yansu aure da wannan baturen hatta su 'yanmatan kuwa, duk hankalinsu ya koma kansa don sunga yadda yake jin maganarsa."
"In dai Kawu ne kuwa zasu yi su gama ne, don in baiyi niyyar abu ba, babu mai saka shi."
Kafin d'aya daga cikinsu ya sake cewa wani abun, suka hangi tahowar wata mulmulalliyar mota da tayo full light jan layin kuma daidai saitin Babban gida inda suke zaune.
"Toh 'yan gida sai su shirya ga wani baturen nan."
"Kai haba?" Cewar Isa yana d'ago da kansa.
"Duba da kyau ka gani, duk layin nan ka san ba mai wannan motar kuma ku kad'ai ne ke da 'yanuwa masu irin wannan k'ashin arzik'in."
"To kuma an ta zuwa kenan?" Cewar Saminu yana kallon motar da babu tantama saitinsu ta take tahowa.
"Kut!" Cewar Buhari.
"Allah yasa da gaske kuwa wani baturen ne yanzu in samu wajen zuwa wallahi."
Ya fad'i hakan ne daidai sanda motar ta tsaya gaba kad'an dasu, kuma ba da wani b'ata lokaci ba k'ofar gaba ta mai zaman banza ta bud'e, sannan wata mace ta fito daga ciki.
Hasken kwan lantarki, hasken farin wata da kuma hasken fitilar motar dake gefe ya shaida musu siffar wata kyakkyawar matashiyar mace sanye da dogon hijabi, basu take kallo ba k'ofar Babban gidan dake gefensu nan ta kafe idanunta ba ko k'itawa tana kallo, duk cikinsu ba wanda ya gane ta saboda haka suka sake bin mutumin daya gito daga mazaunin direba da kallo shima.
Sai dai me?
Saminu na d'ora idanunsa akan mutumin daya zagayo inda macen ke tsaye wani tunani ya d'arsu, da sauri ya sake maida idonsa kan macen, ai kuwa bai san sanda ya saki raken hannunsa ba sannan bakinsa ya lailayo wani irin zagi.
"Ashe Sadiya da gaske take kenan?
Jama'a baku gane ta bane?
Mairo ce fa."
"Wace Mairon?
Da yawansu suka hada baki wajen tambaya.
"Mairo dai ta gidan man, k'anwata!"
Gabanta fad'uwa yake yi a lokacin da dukkan wata ma'anar tsoro ta duniya, likacin da tayi ar ba da tsirawa barandar k'ofar gidansu kuma mahaifarta, barandar kofar gidan waje ne da Babanta yake zama tare da abokansa kullum bayan sallar magriba, wani lokacin har ta fito musu da abincin dare suci anan sannan suyi isha kafin ya shigo gida.
Sai ta motsa kafafunta ta nufi ciki, ba abinda take fahimta na gefenta har ta shiga cikin zaure na farko wanda banda shafen farar k'asa, bai canja ba ko kad'an daga yadda yake, zaure na biyu ma yana nan d'auke da d'akuna guda uku na yayyenta maza a wancan lokacin. ('Yayan Gwaggo lami.)
Daga nan sai k'ofar da zata kai ka cikin gidan, tun kafin ta shiga, kwakwalwarta ta tuno mata da yadda cikin gidan yake, k'aton tsakar gida mai d'auke da bishiyar darbejiya wadda take kamar ruhin gidan don kusan komai a k'ark'ashinta ake yi, sai
daga gefen dama kuma d'akin iyayensu jere cikin layi kowanne ciki da rumfa, dakin Baba da wani store da yake ajiye amfanin gonarsa sune a farko kafin a kai ga nasu inartata, sai daga d'aya bangaren mai kallowa kuma d'akuna biyu ne kowanne falle d'aya, na farko na saukar baki ne sai kuma nata da Baba ya ware mata tun daga sanda ta shiga boarding.
Kicin da makewayi suna daga b'arin hagu na k'aton tsakar gidan sannan kuma garkensu in an zagaya baya.
Sai dai me, tana karya kafarta cikin tsakar gidan, wata irin hayaniya ta daki kunnuwanta, hayaniyar da har ta k'are rayuwar gidan kaf bata taba sanin makamanciyarta ba.
"Na rantse da mahallicina sai dai ayi uw*ar da za'ayi yau a cikin gidan nan amma sai na kwaci hakkina, bashi har wata nawa."
"To ba sai ki kwata ba mu gani, in kin isa ke 'yar halak ce Safiya ki shiga d" akina ki yashe shi tsaf shine zan yadda kin damu da bashinki."
Idanun Mairo suka gane mata mata fal an taru a k'asan wannan darbejiyar sai rik'e mutum biyu akeyi wanda da alama sune masu fadan, bata yi ko sallama ba amma da idon wata daga cikinsu ya hangota sai tace.
"Wa'alaikum salamu shigo."
Jin hakayasa kusan duk suka maida hankalinsu kan k'ofar kafin wata ta sassauta murya tace.
"Larai, kinga dai ga bakuwanan, kiyi wa girman Allah ki hak'ura kar..."
Kalmar Bakuwa ta daki Mairo a tsakar kai, itace bak'uwa?
Itace yau ta zama bak'uwa a gidan ubanta?
"Sannu da zuwa Hajiya, Gwaggon kike nema?"
Wata Dattijuwar mace ta fada tana kokarin durkusawa Mairo, sai tayi saurin fakatar da ita ta hanyar cewa.
"Inna Amina nake nema?"
"To fa?
Kuma a gidan nan aka kwatanta miki ita?" Cewar wata data k'araso.
Muryarta na shirin rawa tace.
"A gidan nan take, matar gidan ce."
"Ai Amina a gidan nan d'aya ce, kuma watan daya mutu ma suka tashi, tunda taje gida wankan haihuwa bata dawo ba."
"Ita wadda nake nema babba ce."
"To Hajiya anya kuwa nan ne?"
"Sai dai ko a tambayo Gwaggon." Cewar wata matashiya goye da d'a."
"To Inna Saratu fa?"
Matashiyar tayi dariya tace.
"Hajiya ni kad'ai ce Saratu a gidan nan amma ni ba Inna bace."
"Kinga bari dai a kaita wajen Gwaggon, shigo muje Hajiya."
Sai ta taka ta bita ba musu, sauran matan na tsaye sai kallonta suke yi kamar sun ga wani abin mamakin, amma ita ba tasu take yi ba, idonta na kan ginin d'akunan gidan, komai yana nan yadda yake sai k'ara tsufa da yayi, ga tarkace nan a jibge koina, mamaki ya kamata, ta tuno sanda koina yake fes!
Sanda zata d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan nan duk girmansa.
Kafin ta waiga ta hango k'ofar d'akinta suka sha kwanar da zata kaisu garke.
Sai dai a yanzu ba garken ne a wajen ba, gini ne a tsaye kyam na bulo har da fentinsa kalar ruwan madara.
"Salamu Alaikum, Gwaggo bak'uwa kika yi."
Kubra ta fad'a sanda ta tsaya a k'ofar d'akin.
Numfashin Mairo yayi kokarin zarcewa sanda muryar Gwaggo Lami ta kwararo daga cikin d'akin, gwaggo lami dai data sani Uwargidan mahaifinta.
"Bana son rainin hankali Kubra, wace bak'uwa zanyi a daren nan?