← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma babu kyankyami balle tunanin wani abu haka Adam yasa hannu ya d'andana abincin mafi yawan kwanukan nan ba tare da ya san sunan yadda aka sarrafa ko abu guda da yake ci ba.

B'angaren Kawu Ibrahim aka shirya masa d'aki guda na musamman ya kwana anan, rana ta farko a rayuwarsa Adam ya kwana cikin rufin wani irin gini da bai taba gani ba,
rana ta farko daya kwana a d'akin da babu kyale-kyale irin wanda ya saba sannan rana ta farko daya shigo cikin kabilarsa da bai tab'a gani ba.

Sai dai tunda babu sauro kuma akwai fankar dake juyawa da wutar lantarki, sai yayi wani irin bacci da rabon da yayi shi tun zamanin da bai san wanene shi ba, yayi bacci da zuciyarsa sakayau babu wannan nauyin daya saba ji a kodayaushe.

Kamar kullum yau ma babu fashi, abu na k'arshe da ya gifta cikin idanunsa shine nata idon, sai ya lumshe nasa cikin nata a hankali kamar mai son yin magana da ita.

Washegari, da tarbar cima ta musamman ya bud'e ido, kayayyaki ne barkatai na duk kayan da suka san zai iya cinsu, saboda haka sai da ya cika cikinsa taf sannan ya shirya ya fita cikin jagorancin Sa'id, da ya zama tafintansa tun jiya.

A falon Kawu Danjuma ya zauna,
inda manyan mutane da dama suka yi ta zuwa ana gaya masa cewa suma 'yanuwa da abokan arziki ne na dangin mahaifin nasa, hatta matan cikin Babban gida daga tsofaffinsu har kanana sai da suka zo ganinsa.

Anan ya fahimci cewa asalin 'ya'yan Babban gida wato sauran 'yanuwan mahaifinsa su ashirin da biyu ne,
kuma hud'u ne kawai a ciki suka rasu,
banda mahaifinsa sauran goma sha bakwai d'in duk suna cikin Babban gida da 'ya'yayensu da kuma tarin jikoki dake tasowa gasu nan birjik!

"A cikin masu rasuwar mata uku ne, kuma suma wasu daga cikin 'ya'yansu suna nan tare damu, wasu sunyi aure,
wasu kuma suna can wajen dangin iyayensu maza."
Kawu Ibrahim ya fad'a masa bayan zuwan mutanen ya lafa a ranar, Sa'id na daga gefe yana fassara masa.

"Amma d'aya daga cikinsu ita bata yi aure ba ta rasu,
wadda itace k'anwarmu jummai da muke uwa daya uba daya da ita nida mahaifinka, d'ayan kuma magidanci ne k'anninsu Kawu Jamilu d'an gidan Hajiya balaraba dana shaida maka itace ta k'arshe mai rasuwa a cikin matan gidan.

Yana da ma mata uku da 'ya'ya takwas shima, shida duk maza ne babarsu d'aya kuma yanzu haka suna zaune a can gidan nasa,
sai kuma mata biyu da suma babarsu d'aya, d'aya matar ita bata haihu dashi ba har ya rasu."
Haka kurum sai Adam ya samu kansa da tambayar ina mata ta biyun da kuma 'ya'yan nata.

"Ita ta rasu tun kafin rasuwarsa 'ya'yan kuma basa nan yanzu haka."
Da wannan Kawu Ibrahim bai k'ara komai akai ba, don tunaninsa bai bashi cewar daga shigowarsa cikinsu ya dace ya fara sanin wasu munanan abubuwan ba.

Sai yamma lis! sannan Adam ya samu keb'ewa da Sa'id wanda ya fara sabawa dashi a lokacin,
babu wata kwana-kwana ya shaida masa cewa yana son ya musulunta ne... yana son komawa addininsu da kuma na mahaifinsa.

Maganar ta daki Sa'id ya tsaya kawai yana kallonshi, yanzu dama shi ba musulmi bane kenan?

Ta yaya to sunansa ya zama Adam?

Tabbas ya san a labarinsa ya fad'a musu cewa turawa ne suka raine shi, amma ba shi kad'ai ba ya san har ga Allah duk cikinsu babu wanda ya kawo wannan tunanin akansa.

To ta yaya ma zasu yi bayan wannan kamilalliyar siffar tasa na nunawa wasu cewa shi balarabe ne ma.

Babu wani b'ata lokaci ya shaidawa su Kawu Ibrahim, kuma anan cikin falon Kawu D'anjuma aka MUSULUNTAR da Adam, ya koma Adam na gaske don ya zab'i sunansa akan canjin wani tunda ko a musuluncin sunan mai ma'ana ne, daga nan Kawu Ibrahim ya d'ora Sa'id kan alhakin koya masa abubuwan da suka shafi tsarki na musulunci da kuma karatukan daya kamata ya sani a yanzu tunda shima Sa'id da d'an iliminsa.

Cikin kwanaki biyar a garin Ikara, Adam ya sake sosai cikin 'yanuwansa kuma ya san abubuwa da yawa na al'adar bahaushe tsantsa!

Watakila rashin sabon wani abu kan takura shi a wasu lokutan, misali ruwan wanka,
na sha da kuma harkar d'aukewar wutar lantarki, amma daidai da rana d'aya bai bari hakan ya hauro kan fuskarsa ba, har mamaki Sa'id yake na yadda yake sakewa yaci abincinsu,
gashi kuma a cikin kwanaki biyar d'in kawai ya fara iya rik'e wasu kalmomi na hausa.

A sannan ne kuma ya shirya tafiya don bayan zuwansa Nigeria a ranar ya hawo wani jirgin zuwa Kaduna,
inda ya kwana d'aya anan washegari kuma ya sayi mota sannan bisa jagorancin wad'ansu, ya d'auko direban tasha ya kawo shi har cikin Ikara.

Saboda haka yanzu zai koma can ABUJA ne inda d'aya daga cikin manyan ma'aikatar da yake aiki dasu a America yayi recommending d'insa zuwa wata k'ungiya irin tasu ta lauyoyi mai zaman kanta anan Abujan.

Kawu d'anjuma ne ya bada shawarar cewa sai dai ya tafi tare da Sa'id don ya dinga k'ara wayar dashi akan abubuwan Nigeria da kuma harkar karatun addininsa ma.

Ai kuwa babu wani kokonto Sa'id ya had'a kayansa ya bishi tunda dama ya gama karatunsa anan ABU ta zariya kuma yanzu ba abinda yake sai taya mahaifinsa aiki a shagon awonsa.

Ya tafi ya barsu da d'imbin alkhairi na kud'i yadda hatta k'ananun yara a babban gida sun shaida da zuwan BATURE ADAM!

A B U J A
"Kin Amince?" Al'ameen ya tambaya a hankali cikin wayar.

"Me Maminka tace?" Muryar Fadeelah ta biyo bayan wani lokaci.

Yawu ya zarce cikin makogwaronsa, a hankali ya tattara saura ya had'iye sannan ya amsa.

"Da da yanzu ba d'aya bane Fadeelah,
idan Mami bata so ki a da ba, yanzu komai ya canja ai,
saboda haka karki damu yadda mahaifina ya bada goyon bayansa haka itama bata ce komai ba."
Maganar da nauyi, kuma yarda da ita da wuya, amma zai mata k'arya ne?

Zai fadi abinda ba haka ba alhali duk daren dad'ewa dai zata je ta fuskanci Aunty Miryaman?

"Kinyi shiru Fadeelah, ko sai zuciyata ta k'arasa fitowa ne waje gabad'ayanta?"
"To me kake son ince Al'ameen?"
Ya lumshe idanunsa kadan jin yadda ambaton sunansa da muryarta ya ratsa ko'ina a jikinsa.

"Cewa zaki yi na amince da kai Al'ameen kuma ina sonka da dukkan ruhina."
Murmushi ya sub'uce mata, tana murza yatsunta cikin junansu tace.

"Ko ban fad'a ba, hakan ba zai canja komai ba,
karka manta fa Daddy har Kano yaje sunyi maganar da 'yanuwan hajiyarsa."
"Wallahi zai canja Fadeelah,
zai canja abubuwa da yawa fiye da zatonki,
so dan Allah ki fad'a min, ko kin manta irin rabuwar da muka yi ta k'arshe ne kafin barinki America?"
Wallahi bana sonka Al'ameen, kuma bana tunanin zan tab'a sonka!

Maganar baya ta haska tar cikin kanta, lallai d'an adam ba'a bakin komai yake ba kuma baki shi ke yanka wuya, da ace a lokacin da take fadin hakan za'a nuno mata sanda take kokarin yin abubuwan da zata burge shi da kuma yanzu da aka saka ranar aurensu, watakila zata hak'a k'asa ne ta shige don kunya.

Shi yasa a kullum yanke hukunci cikin fushi baya tab'a zama alkhairi don ko ka yanke din, a haka hukuncin ubangiji zai zo danne naka, kak'i tsira da komai sai tarin kunya da kuma dana sani!

"Ki fad'a min." Taji muryasa tayi k'asa sosai kamar har sai da numfashinsa ma ya busa akan fatar kunnenta.

"Ina sonka Al'ameen, ina sonka saboda na yarda da kai kuma kaima ka yarda dani a lokacin da ko ni ban yarda da kaina ba, ka bani farin cikin da wani bai tab'a bani irinsa ba,
saboda haka duk abinda zance ko na fad'a a baya, k'aryar zuciyata ce wannan."
A hankali Al'ameen ya lumshe idanunsa sannan babu gargada ya fadi kalaman dake azabtar da zuciyarsa a kullum.

"Ban san lokacin da na fara sonki ba Fadeela,
watakila babu farko kuma babu k'arshe, kin riga kin zama wani b'agare na jikina kuma ina sonki ba tare da tsoron komai ba ko son samun wani abun, sai don kema ki soni
kuma ki bani damar da zamu k'are rayuwarmu tare har abada."
Ta koma da baya ta jingina da allon gadon da take zaune sannan murmushi ya sake subucewa a kumatunta.

"Na baka wannan damar Al'ameen,
ka riga ka sameta sai dai fatan Allah ya sada mu da alkhairin dake cikinta."
Bata ko jira ya amsa 'Amin' din ba ta katse kiran da sauri sannan ta janyo filon gefenta, ta rungume shi sannan ta cusa kanta cikinsa dad'i na nukurkusar zuciyarta!

Al'ameen ya sauke wayar daga kunnensa a hankali, tunani biyu na ratsa shi,
Farko dad'in kasancewar ya shawo kan Fadeela a yanzu kuma komai zai tafi tsakaninsu.

Na biyu ruftawar da zuciyarsa tayi ta bar wani tangamemen rami game da k'aryar da yayi mata, k'aryar da ya san duk daren dad'ewa zata zo ta fahimta,
watakila ma ba sai an kai ga daren dad'ewar ba gaskiya zata baiyana kanta.

Amma ya zaiyi ne in ba haka ba?

Bari zaiyi komai ya sake cakud'e masa irin farko?

Damarsa ta biyu da ya samu ya kankaro da kyar ta sake subuce masa?

Ya mik'e daga zaunen da yake kan kujerar karatu ta cikin d'akinsa ya fad'a toilet.

Tun bayan dawowarsa daga Nigeria,
har yanzu ba'a d'ora shi kan wani sabon case ba saboda haka yake hutunsa yadda yaga dama, baya ma shiga ma'aikatar tasu da wuri.

Bayan ya fito ne ya shirya cikin wata riga mai dogon hannu kalar ruwan toka da wando bak'i, ya dora wata katuwar jacket akai kalar maroon saboda sanyi da ake surawa cikin garin a lokacin sannan ya sunke kafafunsa cikin safa mai kauri itama.

Al'ameen mai kyau ne,
Fadeelah tasha fada...

Irin samarin nan ne da ko daga nesa ka hango su cikin tarin mutane zaka ji zuciyarka ta tsaya akansu su kad'ai!

Ita kanta mahaifiyarsa babban alfaharinta game dashi na kyawunsa ne.
Chapter 41 · 0% Book details