← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya sani taji mutuwar Hajiyar har cikin k'ok'on ranta a lokacin, amma haka ta daure ta zauna tare da 'yanuwanta akayi ta karb'ar gaisuwa har ta kan taya bada hakuri ma ga wasu masu kukan, sannan ta k'arar da dukkan kud'in hannunta wajen siyan abin sadaka tana sawa a rabawa yara da cewa su yiwa Hajiyarta addu'a, ai kuwa haka a kullum kofar gidan nan ke rud'ewa da muryoyin yara suna.

"Allah ya jik'an Hajiya."
A wajensu wasa suka maida abin, suna yi kamar wak'a don a basu abin sadakar, amma ita da kowanne muryar yaro tana yarda cewa addu'ar na tafiya har al'arshin ubangiji, don ance addu'ar yaro ba juyayyiya bace wurin ubangiji, don shi mai wankakkiyar zuciya ne da bashi da koda d'igo na zunubi.

Bayan an share makoki ne kuma komai ya canja, aka barta gidan daga ita sai lami don iyalan Daddyn ma a lokacin sai suka tattara suka tafi can Abuja wajen danginsu.

Bayan Daddy, ita da Ladi sunfi kowa sabawa da Hajiyar a lokacin, saboda haka sai kewa da alhinin rashin suka yi sallama wa rayuwarsu, gidan yayi musu fadi haka ma komai na rayuwar, sai dai har gwara ladin don ita sai ta shafe yini
guda a d'aki tana kukan da bata yi tare da mutane ba, wani lokacin ma har sallah ta wuce ta.

Gani take kamar itama k'arshen tata rayuwar ne ke gangarowa tunda babu sauran mai taimakonta, k'ark'arin zamansu a gidan ba zai wuce na wata guda ba, don Ladi har ta fara shirin komawa garinsu kuma babu alamun a dangin hajiyar wani na da niyyar rik'eta, tunda ita d'in ai ba hakkinsu bace.

Wannan yawan tunani da damuwar su suka haddasa mata wani sabon ciwon, kwakwalwarta kuma ta
kasa karb'ar shi ta d'ora akan na da, saboda haka sai komai ya sake shafe tunaninta a karo na biyu, ta manta komai ta manta kowa... ba hajiyar ba, ba 'yanuwanta ba, ba Ladin da kullum suke tare ba balle kuma d'an Hajiyar Daddy.

Saboda haka sanda Daddyn ya tashi komawa tare da ita bisa umarnin mahaifinsa, da kyar ta yarda ta bishi can Abuja inda akayi fafutukar sama mata visa sannan suka d'unguma har da matarsa wadda ta karb'eta hannun biyu da kuma 'ya'yansu.

Shekara guda a bak'uwar duniya tare kuma da bak'in mutane kafin ta iya sakin jikinta ta karb'i rayuwar da k'addara ta bata, sai dai har a lokacin bata iya tuna Hajiyar Daddy sosai balle kuma rayuwarta ta baya, ta maida hankalinta kawai ga rayuwa cikin su Mami ta kuma saba dasu, a haka har Daddy ya samo mata malamin lesson a gida, bayan watanni shida tayi jarabawar makarantarsu Faruq kuma ta shiga, makarantar da ta hadu da k'awayenta biyu da kuma Adam, mutum guda d'aya daya kasa barin zuciyarta tsawon wannan lokacin.

Daga nan kuma wata k'addarar ta kawo Al'ameen cikin gwagwarmayar rayuwa da kuma ciwonta, zuciyarta ta bashi dama har suka yi sabon da ko a rayuwarta ta baya bata yi da wani namiji ba.

K'addara ta raba su kuma wata k'addarar ta dawo dashi har a yanzu da aure ke shirin shiga tsakaninsu!

Ta tuna komai kuma ta tuna kowa, yanzu abinda ya rage shine ta tashi ta fuskanci k'addarar da ta gujewa tun a farkon lokaci, k'addarar data haddasa faruwar d'inbin abubuwa a rayuwarta, don a yanzu ta banbanta da wannan 'yar k'aramar yarinyar data baro Babban gida cike da tsoron mutanen cikinsa, Tayi wayo kuma duniya ta koya mata cewar rauni baya cikin hanyar nasara.

Dole ne ta tashi don ta fuskanci wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya, idan har sun rufe idonsu daga kawaicin DANGANTAKAR dake tsakaninsu, to itama zata yakice cewa sune wannan DANGIN da tsawon shekaru take masifar son tuna su da komawa cikinsu, ta jawo sanin cewa sune dangin da suka yi sanadiyyar hargitsewar rayuwarta, sune sanadin ciwon data sha wahalarsa kuma sune wad'anda har Innarta ta koma ga ubangiji da bak'in cikinsu a ranta!

Daga yanzu ta tashi daga wannan Fadeelan mai sauk'in kai da rauni, ta koma Bintun ta ta asali, mai dakakkiyar zuciyar da har ta iya barin gida a k'ananun shekaru.

Habiba!

Ina Habiba take ne?

"Ina ga kamar ta farka, idanunta na shirin bud'ewa."
Muryar wani akanta data tabbatar likita ne ya fad'a.

Sai tayi murmushi kad'an sannan ta bud'e idanun nata bakid'aya.

Ba zata k'ara asarar lokaci ba wajen komawa IKARA!

Adam ya bud'e k'ofar office d'insa a hankali sannan ya zare muk'ullin ya shiga ciki.

A kwanaki biyu kawai da bai zo aiki ba har kan table d'inshi yayi kura don bai bada spare key wanda za'a dinga shiga ana gyara masa ba, ya yarda cewa office musamman nasa, waje ne dake buk'atar sirri.

Ya ajiye jakar daya shigo da ita sannan yayi amfanin da wayar cikin office din ya kira can reception kan a turo masa mai shara.

Ya matsa ya karkad'e wata kujera dake can jikin k'aton windon office d'in sannan ya zuge labulen jikinsa haske ya shigo ciki, akwai d'an k'aramin tebur na d'ora k'afa a wajen saboda haka ya d'ora labtop d'insa akai sannan ya zauna, ya shiga bin duk bayanan da ya rubuta game da abinda su Kawu yahya suka gaya masa kwanaki biyu da suka wuce.

Ya fahimci komai kuma ya gano hanyar da zai bi komai, zaiyi amfani ne da mutane kawai har ya kai ga
evidence d'in da zasu fito da komai d'in, don bayan wad'annan shekarun baya jin kai tsaye zai samu ko tsinke ne da ya danganci lamarin.

Sai dai abu d'aya da bai fahimta ba shine a yadda yaga tsari da kuma had'in kai na Babban gida me yasa zasu kasa yafewa 'yar d'anuwansu wannan laifin?

Shi lauya ne ya san muhimmanci da kuma ciwon laifin kisa musamman ace na mahaifiyarsu, ya san kuma ko da d'anuwan nasu ne zasu iya k'in yafe masa suce sai an hukunta shi, amma yarinya k'arama irin haka?

Shekaru ashirin da biyu?

Me zai sa suk'i yafe mata?

Sun kuwa san cewa kashe ta za'ayi in har komai ya tabbata?

Dole ne ma ya sake tuntunb'ar Sa'id, ya fahimci akwai wani abu dashi da Kawu Ibrahim basu gama baiyana masa ba game da Babban gida.

K'ofar Office d'in ta bud'e, wani abokin aikinsa ne ya shigo maimakon mai sharar da yake jira.

"So yau kaga damar shigowa kenan?"
Nasir ya fad'a da murmushi sanda ya k'araso ciki, shima murmushin yayi masa sannan cikin tattausar muryarsa yace.

"Wallahi Nasir, hayaniyar case d'in can ya wahalar dani, shi yasa na nemi hutun kwana biyu wanda da kyar ma aka bani."
Nasir ya nemi waje ya zauna.

"Ai dole ne a baka da kyar, mutane irinku hutunsu kad'an ne Adam, ko jiya na shiga office d'in Haro naga an kawo wani case suna requesting d'inka."
Ya girgiza kansa a hankali.

"Da kamar wuya in karb'a, don ina da wani case din yanzu."
"Anan ne?" Nasir ya tambaya.

Ya sake girgiza kansa.

"Na waje ne, ko kuma ince na gida ne...

Daga Family na ne."
"Allah ya taimaka, thou na san ma zaka yi nailing d'insa."
Kafin ya amsa, had'addiyar wayarsa daya nemo a daren jiya ta shiga vibrating a gefen labtop d'insa.

Kawu Ibrahim ne saboda haka ya gyara zamansa kad'an sannan ya amsa.

"Kunyi magana dasu Yahyan?"
Kawu Ibrahim d'in ya tambaya bayan 'yar gajeriyar gaisuwar daya bada dama suka yi.

"Eh, Baba sunyi min bayanin komai, munje asibitin ma har sau biyu amma bamu ga yarinyar ba, ance ta shiga cikin d'an k'aramin coma ne, sai dai su marik'an nata muka gani."
"Yawwa, tunda ka fahimci komai yanzu so nake in tambaye ka zaka iya yi min wata alfarma?"
Bai san kalmar alfarmar ba, amma fahimci ma'anarta, ya fahimci yana rok'onsa yayi masa wani abu ne don haka kai tsaye yace.

"Insha Allah Baba, ka fad'i ko meye."
Baya fatan Allah ya kawo ranar da zaiyi koda musu dashi ne kan wani abun balle kuma bijirewa.

"Adamu so nake yi ka juya akan case d'in yarinyar nan, maimakon lauyan masu shigar da k'ara, so nake ka koma lauyan da zai kare ta!"
Adam ya had'iye wani abu da bai san menene ba cikin mak'ogwaronsa, a yanzu ya k'ara tabbatarwa kansa akwai wani abu game da rayuwar yarinyar nan!

Al'ameen ya shak'i iska a hankali lokacin da yake kallon waje ta tagar motar da Kamaal ke tuk'awa, zuciyarsa tarawa take da kuma d'ebewa, ya san baiyi amfani da tunaninsa ba ko kad'an wajen tursasa mahaifinsa su b'oyewa wa Maminsa zancen aurensa da Fadeelah.

Gashi a yanzu komai ya cakud'e lokaci na shirin k'ure masa, don ranar da Mami ta sanya na aurensa da Hamida a can na k'ara gabatowa alhali bai cimma komai anan ba.

Shi yasa ya kasa d'aukan wayar da tayi ta masa jiya, me zai ce mata?

Zaman makokin ne ba'a gama ba alhali mahaifinsa ya koma tuntuni?

Allah kad'ai ya san damuwar da take ciki yanzu na rashin ji daga gareshi, ya maida kansa ya jingina a saman kujerar yana kallon saman motar.

"Wai me kake tunani ne?"
Kamaal ya tambaye shi cikin harshen turanci.

"Abubuwa da yawa." Ya amsa a tak'aice.

"Yau zamu karb'i license d'in nan, sannan na gaya maka shari'ar nan mai sauk'i ce, zamu samu duk evidence d'inmu tunda yarinyar ta aikata ne kafin ta kai shekaru...?"
"Bata aikata ba Kamaal, ni na san Fadeelah bata yi kisan nan ba."
"Sorry, ina nufin suna zarginta da kisan ne a lokacin da shekarunta basu kai sha takwas ba, to komai zai zo mana da sauk'i.

Meye sauran damuwarka?"
"Mami." Ya furta sunan tare da furzar da iska daga bakinsa.

"Ban tab'a mata k'arya ba sai yanzu, gani nake ban kyauta ba, na zalunceta, na zalunci duk k'ok'arinta akaina Kamaal."
Kamaal baice komai ba yayi shiru kawai ya cigaba da tuk'insa, don ya san baza'a rufa awa d'aya ba zai zo kuma yana gaya masa cewa zai iya bijirewa kowa akan Fadeelah.

Zuwa can wayar Kamaal d'in tayi k'ara
akan dashboard, ya mik'a hannu ya d'auka sannan ya kara ta a kunne sa.
Chapter 50 · 0% Book details