← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan Allah ku taso mu tafi ko zamu samu mu dawo da wuri, wallahi azumin yau da d'an wuya."
Bayan sun gama siyayyar a cikin wani katafaren shago da Abdul da Faruq suka kaisu, suka iso wajen biyan kud'i inda daga bayan cashier akan rataye 'yan alawowi da kuma magazines ko 'yan riguna don k'arin talla, anan idanun Fadeelah suka hango mata wata magazine guda d'aya ta fashion daga gefe ajiye cikin wani rack, hoton wani kyakkyawan saurayi ne a ciki mai kama da tsantsar jinsin shuwa ko fulani, amma ba wai kammaninsa ne suka d'auki hankalinta ba, A'ah gashinsa, style d'in gashinsa yadda ya kwanto gaban goshinsa a barbaje... sak! irin yadda Adam ke yiwa gashinsa ne.

Adam.

Wani halitta guda d'aya da har yau zuciyarta ta kasa manta shi balle alkhairinsa, tayi kokarin shafe duk wani abu na rayuwar washington dan ta bud'e sabon shafi na rayuwar da take ganin itace tata, ciki kuwa harda k'awayenta su Melissa da bata biye hirarsu a social media, sai dai lokaci zuwa lokaci su gaisa kawai, balle kuma 'yan uwan Daddy na can da dama ba wani sabawa dasu tayi ba.

Sai dai mutum guda biyu ne kawai manne cikin tunaninta, Al'ameen da duk sanda taga su Rahma tare da samarinsu musamman in suna waya sai ta tuna shi a wannan kwanakin da suka shafe tare kullum mak'ale a waya cikin wata guda d'ayan nan tal!, ko kuma duk sanda wani abu ya bata dariya sai zuciyarta ta hasko mata hotonsa, don shine mutum na farko daya fara koya mata wata hanyar nishad'in ta daban a sabuwar rayuwarta.

Amma Adam zata iya cewa kusan kullum yana mak'ale ne cikin ranta, Allah ya sani a cikin shekara guda data rabu dashi ba zata ce ga wata rana data zo har ta fad'i bata ga wani abun daya tuna mata dashi ba, kai wani lokacin hatta ta cikin reflection d'in cokali kawai sa ta hango fuskarsa a ciki, tun abin na damunta har dai tazo ta yarda cewa, kirkin da yayi mata ne kawai ya manne tunaninsa a cikin ranta.

Sau da yawa sai tayi tunanin cewa zai iya nemanta a wancan layin da a yanzu ba zaiyi amfani a k'asar nan ba, amma kuma sai taga me zai nemeta yace? abinda ya had'a dasu ya riga yazo k'arshe kuma for crying out loud har yanzu shi ba musulmi bane, ina wannan ragowar tsanar da bata gama fita daga ranta ba?

"Muje Deelah.."
Rahma ta katse tunaninta sanda ta mik'o mata wasu daga cikin ledojin da aka d'ura kayansu.

Ta karb'a sanda idonta ya sake kallon magazine d'in, fuskar Adam ta haska a maimakon ta kai, da wannan lumsassun idanun nasa yana kallonta.

"Kun san Allah, wata shekarar sai dai ku nemi mai kawo ku siyayya, don ba zai yiwu kuzo ku shanya mu a mota wajen awa guda a banza ba."
Abdul mai bin Rahma ya fad'a sanda suka koma wajen motar.

"Toh uban 'yan mita, shi Faruq dake tuk'in ma baiyi magana ba sai kai." Cewar Fatima, Rahama tace.

"Rabu dashi wata shekarar ma ina zai ganmu, sai dai ya kai 'yan matansa, yayi jiran banzan nan gaske."
"Ai gwara wannan, dama ni na matsu a senda ku wallahi, in banda aike ba abinda kuka sani, ku dai kawai azo ayi muku."
Sun gama saka kayan a booth suna shirin shiga motar amma zuciyar Fadeelah ta kasa nutsuwa, hango magazine d'in nan kawai take yi tana ganin kamar Adam ne zata tafi ta barshi a baya.

Suka shiga motar, farouq ya tayar, yaja suka bar harabar parking lot d'in,
zuciyarta ta tsinke, idonta ya hango mata ranar da suka yi sallama da Adam, sai ta kasa daurewa.

"Faruq dan Allah ku tsaya, nayi mantuwa ban siyo wani abin ba."
"Me kika manta?" Rahma ta tambaya.

"Wannan mayafin da Asiya tace a d'auko mata? mun siyo ai."
"A'ah, wata magazine ce naga wani abu da zan duba a ciki, bari inyi sauri."
Bata ko bari Faruq ya juya ba, ta fita daga motar, ta shiga ratsawa ta tsakanin motocin dake jere a wajen har hanyar data sada ta da k'ofar shagon ta baya, ta dinga wuce mutane akan benen daya kaita hawa na uku, ta k'arasa wajen inda ake biyan kud'in nan...

Sai dai me?

Wajen da magazine d'in take fanko, babu ita ba alamarta sai sauran gasu nan rututu!

"Dan Allah wata magazine da na gani yanzu a wajen nan nake nema."
Mutumin ya kalli wajen data nuna sannan yace.

"Yanzun nan aka siye ta wallahi, ina tunanin ma kin had'u da matar da ta siya a hanya."
"Ya salam!

Babu wata kuma?"
"Babu irinta gaskiya, amma ga wasu na fashion d'in nan..."
"A ina kake ganin zan sami irinta?" Ta katse shi da sauri.

"Kai, kusan ta wata shida baya ce fa, ta dad'e ne anan ba'a siya bane da sai ince ki duba k'asa ko wasu shagunan, amma yanzu da wuya gaskiya ki same ta wannan watan, sai dai kamfanin amma..."
Bata tsaya jin k'arshen zancen ba, ta bazama k'asa hawa na biyu, ta tambayi cashier d'in nan shima yace mata Babu, haka tayi ta bi waje-waje cikin shagon nan amma babu alamun magazine d'in nan mai irin gashin Adam.

Daga k'arshe ta koma wajen cashier ta tambaye shi yanayin matar data siya, ya zaiyana mata cike da mamakin me zata yi da magazine d'in haka.

Sai da ta tambaya sannan itama taga shirmenta, matar fa ta riga ta gama siyan kayanta ta tafi, a ina zata ganta?

Haka ta koma wajen su Rahma da suka fara mamakin dad'ewarta da nauyin zuciya.

Sanda tazo kwanciya a wannan daren data k'ara hasko hoton magazine d'in a idonta, da sanda ta juya baya ta tafi ta barta, da sanda ta juya bayan sunyi sallama da Adam ta tafi ta barshi tsaye a jikin motarsa, sai taji wani abu mai kama da kwalla ta cika idanunta!

BAYAN SATI DAYA.

A lokacin an shigar tsakiyar azumin Ramadan Daddy ya dawo, wata ranar Lahadi ce da daddare bayan ansha ruwa Faruq da Abdul da yanzu suka zama direbobin k'arfi da yaji suka je suka d'auko shi, su a can airpot d'in ma suka sha ruwa saboda sai da suka jira saukar jirgin tukunna.

Gidan ya rud'e da murna sanda ya shigo su faruq suka biyo bayansa da kaya.

Iman ta d'ane shi tana ta ihu yayin da bakin Mami ya kasa rufuwa, shima murna yake sosai don hatta Zahra sai da ya d'aga ta har sama, a cikin sati uku kawai sunyi kewarsa kamar shekara uku.

"Naga wannan abin a hanya na siyo miki."
Muryar Faruq ta fad'a daga gefen Fadeelah sanda ya shigo janye da wani akwati da bana Daddy bane.

"Wanne?"
"Kadaya yake ko me?"
Ta zare idonta da sauri, ta gane kad'anya yake nufi, wani abu da take mutuk'ar so tun daga ranar data fara shansa a wajen Hajiya Amarya.

"Da gaske kake Faruq?"
"Allah kuwa, yana mota bari in ajiye wannan in d'auko miki."
Ai tana jin yace mota tabi ta bayansa da sauri ta fita daga falon, yadda suka yi parking motar a harabar gidan tana fuskantar ta ne, don haka taga booth daga baya a d'age amma bata damu da tunanin me yasa ba'a rufe shiba, ganin ma sauran kofofin motar duk a bud'e suke.

Ta san Abdul ne yayi driving don haka ta gefen kujerar mai zaman banza ta zagaya ta bud'a, ilai kuwa, sai ga kad'anya fal a ciki wata yellow leda, ranta yayi fari k'al a take, sai dai kuma a taken farin cikin nata ya rugurguje har garinsa, tsantsar mamaki ya maye gurbinsa!

Taji sanda aka sauke booth d'in motar, sai dai kafin ta iya juyawa wannan muryar ta shiga cikin kowacce jijiya dake amfani da harkar sauti a jikinta.

"Hello, memory loss girl!"
Wannan husky muryar ce mai cike da tarin kwarjini.

A hankali ta juya gefe, cikin kallo d'aya idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala fiye da wanda ta sani a baya!

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... ta biya hakan ta kuma tuno da tsohuwar haddar da ta yiwa kammanin Al'ameen!

Waye ya hango k'addarar data fara a shafin nan?

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
"Jiya Daddy yake gaya min naji haushin maganar sosai Miryam, ace muna zaune a gari amma har Al'ameen zai zo ya bi wasu abokanan aikinsa su sauka a hotel? ko bamu da guri ne ai sai haka."
Mami ta fad'a a safiyar washegarin da Al'ameen ya kwana a gidan, suna cikin kitchen ita da Fadeelah a lokacin suna had'a abincin karin safe, yayin da sauran 'yan gidan ke can kowa na fafutukar shiryawarsa.

Ta cikin wayar muryar Aunty Miryama tace.

"Ai ba wani abu bane Saffiya da baku d'orawa kanku d'awainiya ba wallahi, watak'ila shi sai yafi sakewa ma acan."
Daga yanayin fuskar Mami bata ji dad'in maganar ba, amma sai ta daure tayi murmushi kad'an kafin tace.

"Da nan d'in da can duk d'aya ne ai babu takura Miryaam, shima kuma na san zai so..."
Fadeela ta d'auke hankalinta daga kan saurarenta ta juya wainar kwai ta k'arshe da take soyawa sannan ta kwashe ta a cikin plate.

Daga daren jiya zuwa yau bata san me take ji a ranta ba, watakila abu biyun da suka damu zuciyarta ne suka had'u suka zuk'e duk wani emotion d'in da take dashi, kuma ta karb'i hakan hannu biyu don ita kanta a yanzu bata da tabbacin abinda take ji.

Har yanzu akwai wani nauyi a gefen zuciyarta tun daga ranar data rasa wannan magazine d'in mai irin gashin Adam, nauyin daya zama kamar wani abu daya k'ara ingiza tunaninsa a ranta, har ya kai ta binciko takardun lesson d'insu don kawai kullum ta kalli rubutunsa, wannan tsantsareren rubutun da kamar buga shi akayi tsabar tsaruwarsa daki-daki, ta dad'e da fahimtar cewa komai nasa a tsare yake cikin nutsuwa, kamar wannan muryar tasa da in yana magana dole ne ko waye ma ya saurare shi.
Chapter 26 · 0% Book details