← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 95

Sashe 53

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka Sadiya tace, har ana tunanin tare kuke sai daga baya su Yahya suka ce itama taje nemanki ne a lokacin."
"Wallahi tun bayan tafiyata ban taba ganinta ba sai a ranar da Aunty Sadiyan ta ganni itama."
"Kar ki damu Bintu, zancen Mairo mai sauk'i ne, naki daya had'a da hukuma shine a gabanmu yanzu, amma na san Adam zai yi duk kokarinsa don ganin munyi nasara akansu."
Jimlar sunan Adam ta dawo da wani tunani akanta, tunanin wannan Id card d'in dake cikin purse a kuma k'arkashin kayanta, amma sai tayi saurin ture shi, hakan ba abu ne mai muhimmanci yanzu ba.

"Bintu mutanen da suka rik'e ki masu karamci ne, munyi magana dashi Alhajin kafin yayi tafiyar data kama shi, Allah ya kaiki cikin kyakykawan hannu ki gode masa."
Bakinta yayi nauyi da jin hakan, don ta rasa ta ina ma zata fara gaya masa irin tarin alkhairi da kuma karamcin su Mami.

"Na gansu har su hudu sunzo, kuma sun tabbatar min maigidan ma zai taho da zarar ya dawo."
Sai ta kasa daurewa kawai, bakinta ya shiga furta masa duk wani tarin alkhairin su Mami a gare ta, tun daga ranar da suka kad'eta a mota, har zuwa sanda suke shirin bikin aurenta da jininsu.

Hakan ya d'auke su kusan awa d'aya tana zayyane masa duk wani abu daya faru da ita bayan barinta daga cikinsu har zuwa dawowarta yanzu.

Sai bayan daya tafi, mai tsaron nan ya sake rakata cikin cell dinta sannan komai ya dawo mata sabo, duniyar tayi duhu sannan ta had'u ta dunk'ule a cikin idonta, sai kawai ta koma can k'arshen cell d'in ta dukunkune jikinta waje d'aya.

Komai zai kare a d'an kankanin lokaci, komai zai wuce kamar ba'ayi ba, idan nayi bacci a yanzu zan farka inga an kammala komai, kamar yadda duk wani abu daya faru bayan barina daga Babban gida ya shud'e.

Da wannan k'aryar ta lallab'i kanta ta bari magungunan baccin da Mami ta bata kafin a shigo da ita ciki, suka sami damarsu akanta.
_____
WASHEGARI.
08:30AM.

Bayan rabuwarsa da gidan Kawu Ibrahim a lokacin, Adam ya shiga tunanin irin tambayoyin da zai yiwa yarinyar da aka shaida masa sunanta Bintu.

Ya riga ya gama tara tulin bayanai akanta daga wajen Sa'id da kuma Kawu Ibrahim d'in daya had'u dashi a yanzu.

Zai iya cewa ya san duk wani bayani game da ita na abinda ya shafi rayuwarta a IKARA, ya san asalinta tun daga tushensa har zuwa kan sanda ta gudu bayan zargin da ake mata, abinda ya rage kawai, shine yaji komai daga bakinta ya kuma san wani abu game da rayuwar da tayi bayan barinta Ikara daga marik'anta wanda Kawu Ibrahim d'in ya tabbatar masa da zai had'u dasu a kotun bayan ya gana da ita.

Ya juyo ya kalli Sa'id dake tuk'a motar da suke ciki, ya fahimci shi gabad'aya al'amarin nan ma baya kansa, harkokinsa kawai yake yi kamar baya cikin dangin da ake wannan rikicin, amma shi bai san me yasa ba, tun daga ranar da Kawu Ibrahim ya kira shi cewar ya koma lauya mai kare yarinyar nan ya kasa samun nutsuwa a zuciyarsa, kullum tunaninsa yana kan shari'ar ne da kuma son ganin an fara ta...

Amma shi Sa'id d'in daya san komai ma kuma akayi a gabansa bai damu haka ba.

Idonsa ya koma kan titin sanda suka k'araso bakin gate d'in shiga kotun, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya gayawa kansa cewa 'An fara.'
Sa'id yayi parking a layi na k'arshe daga cikin jerin gwanon motocin dake harabar wajen sannan suka fito bakid'ayansu suka shiga wajen, wani mai tsaro ne ya kaisu har ofishin wanda ya kamata su gani.

Adam ya mik'a masa Id card d'insa sannan yace.

"Barka da aiki yallab'ai, suna na Adam Ahmad, nine lauyan da zai kare wadda ake zargi a shari'ar da za'ayi ranar goma sha biyar ga wata, nazo in gan..."
"Kar ka damu na fahimta, dama tun safe take jiranka."
Mutumin ya fad'a sannan ya mayar masa da Id card d'insa.

Adam ya d'an tsaya da mamaki yana kallonsa, Tana jiransa?

Waya gaya mata ta jira shi?

"Habu, jeka ka kaisu inda zasu zauna."
Mutumin ya fad'a yana kallon mai tsaron daya rako su.

Muryar mai tsaron nan na jiya ce ta yakice Fadeelah daga nauyayyan baccin da take yi, don har aka kwana aka tashi k'arfin magungunan nan da aka bata basu sake ta ba, ta fahimci dama amfaninsu kenan da aka bata daga asibitin, don ta samu isashshen hutu da nutsuwa akanta wanda zai sauk'ak'a ciwonta.

"Kina da Bak'o." Muryarsa ta fad'a sanda yake k'ok'arin bud'e cell din.

Sai ta d'ago da fuskarta daga dandaryar simintin da take kwance sannan ta murza idanunta don son wartsakewa.

Kwakwalwarta ta fahimci bak'o yace, don haka a take ta gane basu Mami bane da take jiran zuwansu, lauyan da Kawu Ibrahim yace mata zai zo ne.

Yaya ma sunansa?

Adam ko?

Ta mik'e a hankali jikinta ba kwari sannan tabi bayan mai tsaron zuwa magamar bak'i.
_____
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
"Inaga bari inje daga waje in jira ka a can."
Sa'id ya fad'a sanda suka fito daga ofishin mutumin nan, Adam ya juyo ya kalle shi.

"Saboda me?

Baka son ganinta ne?"
Ya d'aga kafad'unsa kad'an.

"Yaya tunda ta dawo ai zan ganta, akwai wayar da zanyi ne shi yasa."
Sai ya gyad'a masa kai kawai sannan ya bishi da kallo bayan yayi gaba, ko dai Sa'id ma baya goyon bayan shari'ar nan daya karb'a ne?

Ba abin mamaki bane hakan tunda mahaifinsa ma yana goyon bayan su Kawu Da'anjuma ne basu ba, ya rasa wace irin k'iyayya ce suke wa yarinyar nan haka.

"Ranka ya dad'e nan zaka shiga, yanzu za'a taho da ita."
Mai tsaron nan da yayi can gaba ya fad'a yana nuna masa wata k'ofa, sai ya maida Id card d'insa dake hannu cikin wallet sannan ya nufi wajen k'ofar, yaji shiga ya samu kujera ya zauna, duk wata kafa ta jikinsa ta shiga aiki a don bai taba jin son haduwa da client d'insa ba a tsawon shekarunsa na aiki kamar yanzu.

Daga d'aya b'angaren d'akin wata k'ofa ta bud'e, wani mai tsaron ya shigo sannan biye dashi ita.

Fadeelah ta kalli koina a d'akin bata ga kowa ba, tayi tunani zata zo ta sami mai neman nata zaune yana jira kamar yadda taga Kawu Ibrahim jiya.

"Yallab'ai gata nan."
Muryar mai tsaron ta musanta tunaninta, sai a sannan idonta ya kai gefe inda wanda aka kira 'yallab'ai' din ke zaune.

Wani irin tsoro ne da fargaba suka haska cikin idanunta lokacin da kwakwalwarta ta shaida mata abinda ta gani...

Wane irin magungunan bacci ne haka da baza su sake ta ba har yanzu?

Sai ta juya baya da sauri ta murza duka idanunta biyun da duka ragowar k'arfinta, saboda babu ta yadda za'ayi ta yarda da abinda take gani.

Sai dai me?

Da ta sake juyowa ba abinda ya canja, idanunta dai wani mutum mai siffar Adam d'in data sani a can America take gani, wannan karon shima ya mik'e tsaye sannan wad'annan lumsassun idanun nasa na nuna mamaki makamancin nata.

Ta girgiza kanta da sauri, wannan mafarki ne ba zai yiwu ba, ta sake juyawa baya ta mutstsika idanunta sannan ta k'ara juyowa...

Ya salam!

Tayi zaton kwakwalwarta ta warke daga dukkan wani ciwo, in ba haka ba me yasa take nuna mata kammanin Adam har yanzu?

Sai ta tsaya kawai ta k
asa gaba ta kasa baya, ta kuma kasa daina kallonsa, kwakwalwarta na bata shawarar cewa ta koma ta k'arasa ragowar baccin dake kanta zata ga komai ya dawo daidai, zata dawo ta tarar da wani mutum a matsayin lauyan nata na gaske.

Abu na farko da Adam ya fara lura shine idanunta, ya tsaida ganinsa akansu cike da tsantsar mamaki, wad'annan idanun da kullum ke manne cikin nasa, idanun daya shiga duk wata gwagwarmayar rayuwarsa kuma ya fito tare dasu, idanun da a lokuta da yawa suka zama abinda ke bashi kwarin gwiwa da juriya, Sannan idanun da bayan shekaru kusan biyu ya cire rai da sake ganinsu...

Idanun Fadeelan Washington!

Abinda ya fara fahimta kenan kafin kuma wani mamakin ya dake shi a tsakiyar kansa...

Don babu wata kwana-kwana kwakwalwarsa ta saita masa cewa Fadeelan daya sani a America ita ce dai Bintun da yazo gani.

"..a cikin watan nan zamu koma k'asarmu, don haka jarabawar da muke ta wannan tanadin don ita ba zan sami damar yi ba."
Maganar ta a ranar da zasu rabu na karshe suka haska cikin kansa, sannan ta Kawu Ibrahim a d'azu.
...

Bayan barinta daga wajen mu, ance tayi kusan shekara biyu a k'asar America tare da marik'an nata kafin su dawo...

Hakan kad'ai ya isa ya fahimtar dashi duk wata amsa da yake nema, amma da mamaki, da mamaki ace duk duniya k'addara Fadeelah kawai ta zabo ta d'ora a wannan muhallin, ya had'iye yawu a mak'ogwaronsa kad'an sannan ya karb'i shawarar da zuciyarsa ta bashi a lokaci guda.

"Ki k'arasa ki zauna." Mai tsaron nan ya fad'a daga gefe ganin bata da niyyar k'arasawa, a nasa tunanin rashin gaskiyarta ne ya sa mata shakka.

Bai daina kallonta kamar yadda itama take kallonsa har sanda ya nuna mata kujerar gabansa alamun ta zauna, sai komai ya canja a idanun Fadeelah, d'akin ya juye mata zuwa library d'in makarantarsu na can washington, taga kamar a lokacin da suke lesson dinsu na Maths ne, banbancin kawai, wancan Adam d'in sanye yake da kaya irin na matasan can da kuma gashinsa a barbarje, wannan kuma farar longsleeve ta k'asan suit ce a jikinsa, gashinsa a kwance kuma a tsare sannan alamu na girma da class sunfi fitowa a wannan na tsayen.

Sai ta rufe idonta sannan ta sake bud'ewa, ya Allah!

In har shine da gaske ta yaya yazo nan?

Waye ya kawo shi?

Sannan me yake yi anan d'in?
Chapter 53 · 0% Book details