Sashe 89
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lokacin da aka kaini kurkuku, Kutama yaje ya same ni a can."
Ba shiri ya juyo ya kalleta da tsantsar mamaki, Kutama?
Me yaje yi wajenta?
Me yayi mata?
"Na san komai ya wuce amma a wajenka irin wannan shari'ar kana yinta ne kullum, shi yasa nake so na fad'a maka koda wata shari'ar zata sake had'a ka dashi."
So yake ta tsallake duk wannan bayanin na gabatarwa ta fad'a masa abinda ya faru kai tsaye kawai, amma saboda tsabar abinda ya fara ji a zuciyarsa game da sunan Kutaman data ambata sai ya kasa tsinto muryarsa.
"Yaje ne da zancen cewa mu sayi wasu shaidu a wajensa in har ina son in samu 'yancina, don wai da wad'annan shaidun biyu kad'ai kotu zata iya yanke min hukuncin kisa ko na d'aurin rai da rai a kurkukun, amma in har muka siya, to zai tattaro komai ya bamu shi kuma ya fasa gabatar dasu a kotun yadda zamu yi nasara, yace min kaima ya same ka da zancen amma baka yarda ba, sai dai na san ba haka bane shi yasa na fad'a maka."
Sanda ta fad'i hakan, Fadeelah taji kwalla na neman cika mata idanu kamar yadda yake faruwa duk ranar da ta tuna rayuwar cikin kurkukun nan da hargitsin cikinta, wutar Nepa ta d'auke a daidai wannan lokacin, watakila kuma a sannan ma maigadi ya zab'i lokacin wajen yin zagaye a unguwa don ba'a kunnan metre solar a take ba kamar yadda ya saba.
Saboda haka duhu ya mamaye koina, kuma manya- manyan labulayen falon suka taimaka wajen hana hasken farin wata shigowa, d'akin yayi dind'im bata iya ganin komai kuma bata iya ganinsa, amma tana iya shak'ar wannan k'amshin da ta dad'e da yiwa tambari da NASA.
"Bayan haka me ya faru?"
"Ban yi niyyar saurarensa ba da farko, amma ya tsayar dani cewar ya san inda ka tafi a lokacin."
"Ya fad'a miki kuma?"
"A'a, yayi amfani da wannan damar ne kawai don in saurare shi."
"Kuma kin yarda dashi a lokacin?"
Muryoyinsu a hankali suke fita suna kanannad'ewa da junansu ta cikin duhun d'akin, kuma tasirin duhun yasa Fadeelah taji kwallar idonta na k'aruwa, saboda haka muryarta na rawa tace.
"Ba zan tab'a yarda da mutum irinsa ba a rayuwata."
Ta yaya kuwa zata yarda dashi?
Bayan tana ganin yadda yake dagewa a kotu wajen ganin an hukunta ta saboda wasu 'kud'ad'e kawai da duk yawansu ba zai shafe dogon lokaci yana ganinsu ba, zuciyarta ta matse da tunanin mutane nawa Kutama yasa aka kashe a baya ko kuma aka datsewa rayuwar 'yanci akan gaskiyarsu, wanda itama ba don taimakon Allah ba da tuni ta shiga jerin lissafinsu.
Muryarta ta shaida masa cewa kuka ne ke shirin kwac
e mata kuma ya san tunanin halin data shiga a baya ne yasa hakan.
Bayan gama shari'ar nan, yasa an tsoratar da kutama tsawon sati biyu da wata takadar bogi ta cewa za'a kore shi daga aiki, don ya riga rantse cewar sai nasa idanun suma sun shiga irin firgici da tashin hakalin da yasa idanun Fadeelah a baya, sai dai da ace bayan ya san wannan
maganar ne, da sai yabi duk hanyar da zai iya a maida takardar nan ta gaske yadda zai shima shafe rabin rayuwarsa yana jin zafin hakan.
Duk da duhun d'akin, yana iya ganin yadda take kai hannunta tana goge hawaye a fuskarta, sannan yana iya jin sautin ajiyar zuciyar da take yi ma, zuciyarsa ta had'e waje d'aya, yana son ya rarrasheta amma kuma yana tsoron kar hakan yaja shi ga yin wani abun daban.
Sai dai bayan wani lokaci ya kasa daurewa zuciyar tasa, kuma bai san sanda ya kai hannu ya kamo nata cikin nasa ba, yaji sanda hannun nata yayi rawa kad'an amma kuma daga nan bai k'ara jin komai ba don taushinsa kamar na wani sabon pillow ne mai laushin gaske.
"Nasha wuya sosai a wajen nan..." Bai zata ba amma muryarta ta sake fitowa cikin kuka, a shirye don fitar da d'acin dake damunta.
"...
'yan kwanaki ne kad'an amma naji kamar an canja ni zuwa wata duniyar ne, duk irin wahalar dana sha a babban gida ba d'aya bace da wannan wajen, shi yasa ya nemi ya tsorata ni da hakan don in yarda dashi, ban san kuma yaya zanyi ba da ace..."
D'aya hannunsa ya samo kuncinta a lokacin, ya shiga share hawayenta da babban yatsansa yayin da sassanyan k'amshinta mai dad'i ke juya masa kwakwalwa, sannan a hankali ya sunkuya daidai kunnenta ya rad'a mata,
"Komai ya wuce lealah, insha Allah daga yanzu ba abinda zai k'ara shigowa rayuwarki sai alkhairi..!"
A wannan lokacin Fadeelah bata san ko kuka take yi ko kuma k'ok'arin nemo hanyar da iska zata shiga kirjinta ba.
***
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
Komai yana tafiya ne daidai a cikin wannan satin, a yanzu shi da ita sun sami fahimtar juna sosai, don a cikin 'yan kwanaki kawai Adam yayi nasarar zabge fiye da kashi saba'in na waccan rayuwar da suka fara a cikin sati biyu.
Yana mutukar k'okarin ganin cewa yayi duk abinda zai ja hankalinta don ta fahimce shi duk sanda ya tashi sanar da ita cewa wancan alkawarin da yayi mata ba mai faruwa bane, ba don komai sai don su raya fatan su Kawu Ibrahim akansu kuma watakila don a yanzu ya fahimci cewa yana son matarsa kuma baya son rabuwa da ita.
He just kept falling for her, one of the few things he think gravity can't explain.
Fadeelah ta zama duniyarsa a yanzu, ya gane cewa zuciyarsa ta karb'eta tun daga ranar daya fara tozali da idanunta, abinda ya hana shi gane hakan tun a baya shine, saboda abubuwa sun danne zuciyarsa bai maida hankalinsa kanta sosai ba, amma a yanzu da komai ya lafa ya zama daga ita sai shi...
Ya fahimci ya dad'e da k'aunarta, don abinda yake ji game da ita yana tasowa ne tun daga k'asan zuciyarsa, musamman in ta kalle shi da wad'annan idanun nata dake karya duk wani kuzarinsa.
Tana k'ara shiga cikin zuciyarsa a duk sanda yake tare da ita, tana k'ara burge shi da calm personality d'inta wanda ke mannewa a zuciya da ruhin duk wanda ke tare da ita, bata da magana can sosai, amma duk sanda take magana muryar nan tata na fita a hankali, mantawa yake da komai na duniyar nan sai ita kawai, ita dashi da kuma gidansu.
Tsawon rayuwarsa a baya, bai tab'a saka aure cikin lissafinsa ba balle har ya dinga hango kansa a ciki, amma a yanzu da k'addara ta kawo shi cikinsa kuma ya saba da matar tasa, baya jin zai iya wata rayuwa mai kyau a gaba in har ba tare da ita ba, shi yasa ba abinda zuciyarsa ke fata irin ya k'are rayuwarsa da ita har ma su had'a zuri'a...
Zauciyarsa ta matse da tunanin halittar da zata zama combination dinsa shi da ita, watakila ko mace ce ko namiji, babyn zai iya d'auko siffar wad'annan idanun nata...
Ya kan tsayar da kansa duk sanda tunaninsa ya fara zurfi haka, don ya san hakan ba abu ne mai faruwa ba sai in har ya gaya mata manufar wancan alk'awarin da yayi mata kafin ta shigo gidansa kuma ta yarda dashi, amma har yanzu ya gaza samun damar hakan, saboda a kullum ya koma gida ya tarar da ita cikin simple kwalliyarta mai kyau tana jiransa, sai gwiwarsa ta durk'ushe, ya rasa kwarin da zai
iya gaya mata cewa shi da ita yanzu abu d'aya ne, ba zasu tab'a iya rabuwa ba ko da kuwa duniyar kaf zata kama da wuta!
A b'angaren Fadeelah, babban abinda bata gane ba har yanzu shine meye manufar da Adam zai kyautata zamansu in har bashi da buk'atar cigaba da zama da ita?
Me yasa zai haifar da hira da shak'uwa tsakaninsu bayan ya san zai kasance a rayuwarta ne na d'an lokaci kawai?
Me yasa zai ginata don ya ruguza ta?
Yana kallonta ne a kullum kamar ita kad'aice abu mafi muhimmanci da ta rage a duniya, yana bata wata tsananin kulawar dake sawa ta manta duk hargitsin rayuwarta ba baya, sannan yana yi mata kirkin daya narkar da duk matakan da ta d'auka akansa da kuma kad'aicin da take ciki a kwanaki.
Bata san ya akayi ba ko me ya faru ba amma tun daga waccan ranar daya rike ta, shashasahar zuciyarta ta ture komai ta karbi abinda lokaci ya bata, don in ma wasa yake da hankalinta to yayi nasara, a yanzu ba abinda zuciyarta tafi sak'awa sai tunanin yaya zata ji duk sanda ya sake rik'eta... ta riga ta manta da wannan alkawarin da yayi mata a baya, ta fad'a cikin yanayin da take gujewa tun farko, don a yanzu ko barinta kawai akayi da yadda ta saba da hirarsa, ta san dole ne zuciyarta ta rugurguje a duk ranar daya tashi sallamarta.
A ranar laraba da Adam ya koma gida, Fadeelah na tsaye a cikin falon rik'e da kaskon turaren wuta ta juya tana kokarin zuba turaren, bata san ya shigo ba don da k'arar muryar Tv bata ji motsin bud'ewar kofarsa ba kuma baiyi sallama ba... baiyi sallamar bane don bakinsa ya k'ulle da ganin shigarta.
Shigarta ta wata atamfa nai haske da aka watsa mata adon orange flowers, sannan tayi d'auri tun daga goshinta ya kuma d'age daga baya hakan yasa gashinta ya fito waje, gashinta mai laushi yana d'aure bak'i k'irin dashi cikin katon bun.
She just look like the rest of his life!
Sai ya rufe idonsa a hankali sannan ya bud'e don ranar shine ganinsa na farko da sumar kanta... wallahi tayi kyau, tayi masifar yi masa kyau!
A lokacin ita kuma ta lura da tsaiwarsa a bakin k'ofar, ta juyo da fuskarta daidai sanda da hayakin turaren wutar ya bad'e fuskarta, amma duk da haka yana iya hango murmushin da take masa, murmushin dake ruguza dukkan wani abu a zuciyarsa in ba tunaninta ba.