← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 95

Sashe 76

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawu Yahya ya bita da kallo sannan ya tab'e baki ya juya.

Yafi kowa jiran ranar da zata koma aikatau d'inta, don tun farko yana d'aya daga cikin wad'anda suka sa baki Kawu Danjuman ya barta ta tafi, ba don komai ba sai irin uwar masifar dake tsakaninta da matarsa, kullum babu ranar da zata zo ta fad'i ba'aji kansu ba, sau da yawa ma har da dambe. amma kuma duk da haka shiri suke sosai da Babbar 'yarsa, don a lokacin da yarinyar ke tashi, matar tasa ta yar da ita saboda kunyar 'yar fari, ita Sadiyan ce ta d'auketa ta kula da ita har ta girma, don ko aure tayi da ita take tafiya.

Yanzu kuma dawowarta ance masa ta koyo wasu k'arin d'abi'un na wulakanci, don ance tunda tazo ko ruwan gidan bata sha sai na roba, kud'i ne tazo dasu mak'il a cikin jakarta wanda yake da tabbacin sato su tayi don ba'a biyan 'yan aiki irin haka.

Fatansa d'aya ace yanzu Kawu D'anjuman ya bata izinin tafiya ne tun kafin taja ra'ayin 'yarsa tace itama zata bi ta.

Kamar zai shiga ciki kuma sai ya fasa, zuciyarsa ta bashi shawarar yabi bayanta yaji abinda ya faru, don haka ya maida takalmansa ya juya.
****
10:00 AM, IKARA.

K'arfe goma daidai Sa'id ya faka motar daya tuko daga cikin garin Zariya jikin katangar Babban gida.

Babu bata lokaci Adam ya bud'e murfin k'ofarta ya fito.

Ya kalli k'ofar shiga Babban gidan wadda ke wangale kar mai yi musu maraba, idonsa kuma ya kai kan samarin dake zaune a baranda wad'anda suka taso ganin tsayawarsu, sannan ya juya ya kalli k'atuwar motar 'yansandan da suka taho da ita, wadda ke k"ok'arin tsayawa a bayansu.

A yau komai zai k'are.

Ya ayyana hakan a zuciyarsa.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Babbar kotun dake cikin jihar Zariya ta zauna akan shari'ar da Iyalan Malam Idris Musa suka shigar game da k'arar 'yar d'anuwansu Bintu Abubakar Idris bisa zarginta da kashe mahaifiyarsu Hajiya Balaraba.

Bayan duk wasu bayanai na gabatarwa, Alk'ali ya d'ago ya kalli Adam yayi magana cikin harshen turanci.

"The defense may begin to present its case."
Tafintan dake gefe yana fassara dukkan magana daga turanci zuwa Hausa, Hausa zuwa turanci ya fassara hakan kamar yadda ya saba.

"Lauyan mai karewa zai iya fara gabatar da hujjoji da kuma shaidunsa."
Adam ya mik'e a hankali daga mazauninsa ya taho gaban Alk'alin, takunsa cikin nutsuwa yake sannan babu abinda mai kallo zai iya tsintowa a yanayinsa, ya tsaya a daidai saitin gaban alk'alin sanda gefen idonsa ya hango Fadeelah wadda ke zaune daga can k'arshe a teburin magatakarda, kanta a sunkuye yake tana kallon yatsunta, don haka bai hango idanunta ba, wad'annan idanun da suka yi barazanar karya zuciyarsa a d'azu daya fara ganinta...

Yana tsaye daga saman benen koton a lokacin bayan ya gujewa masu neman rahoton dake ta bibiyarsa tun daga wajensu Kawu Ibrahim, shi da Jabir ne, (mataimakin aikinsa) wanda ke nuna musa sakamakon bincikar lafiyar kwakwalwar Anna da yasa ayi a wani asibitin kud'i.

Dama tun dawowarsa Jabir ya shaida masa cewa yanzu case d'in Fadeelah yayi girman da har ya isa kunnen Media kuma an samu k'arin wasu gidajen rediyo da suka nuna ra'ayinsu akan shari'ar har ma sun samu sunyi magana da Kutama, saura shi suke nema ido rufe a yanzu.

Ba sauraran Jabir yake sosai a lokacin ba, rabin hankalinsa na kan gate d'in shigowa kotun da yake iya hangowa daga inda suke tsaye, saboda kamar kowa a wajen shima jiran k'arasowar Fadeelah yake yi.

"A k'arshe dai babu wani ciwo da result d'in yake nunawa, don haka su sun fi danganta matsalarta da rashin kulawa kawai, amma ni a nawa hangen ina ganin kamar har da matsalar aljanu ( spritual problem) da kuma rashin samun fahimtar hakan daga 'yanuwanta balle har a bata agaji."
Jabir ya k'arashe zancensa daidai sanda motar dake d'auke da tambarin kurkukun mata ta karyo kwana cikin wajen, ba shiri ya sakarwa Jabir takardun hannunsa yace masa ya jirashi sannan ya juya yayi hanyar sauka k'asa.

Yallab'ai me zaka iya cewa game da yadda wannan shari'ar ke tafiya?
...kana ganin zaka yi nasara bayan duk shaidun da aka gabatar?..
...me zaka iya cewa akan yau da zaka karb'i shari'ar?

Yallab'ai da gaske ne akwai wata alak'a tsakaninka da wadda ake zargi da laifin?
....zaka iya gaya mana meye ainihin dalilinka na karb'ar wannan shari'ar?..

Masu neman rahoton suka yanyame shi daga k'afar benen daya sauko, bai ko saurare su ba ya ratsa ta cikin su ya nufi inda motar kurkukun ke kokarin parking, sai a sannan suma suka kula da hakan saboda haka suka rufa masa baya da sauri amma cikin sa'a sai masu tsaron da suka fito daga cikin motar suka tsaida su da tunanin Fadeelan zasu je yiwa magana.

Amma shi ya samu wuce su har zuwa gabanta, a lokacin ta fito daga motar kanta a sunkuye tana k'okarin cire takalmin k'afarta daya hard'e cikin riga, don haka mai tsaron dake rik'e da ita ce ta fara yi masa magana.

"Yallab'ai ba'a a bamu damar kowa yayi mata magana ba don haka ciki kawai zamu shiga da ita."
Ta fad'i haka ne bayan karanta Id-card d'in dake sak'ale a wuyansa wanda ya nuna mata shi lauya ne, sai dai shi idonsa na kan Fadeelan don haka yaga sanda ta lura da tsaiwarsa a gabanta da kuma sanda ta d'ago gabad'aya ta kalle shi.

Abinda yake hasashe ne ya tabbata a lokacin...

Idanunta sunyi fari kuma sun d'ashe d'as!

Babu abinda ya iya gani a cikinsu sai tashin hankali, rud'ani da kuma firgici, sannan a lokacin tana kallonsa da dukkan wani mamaki na duniya, don haka in ma tayi murnar ganinsa wad'annan abubuwan sun danne hakan.

Ya had'iye yawu cikin mak'ogwaronsa sanda ya lura duk wani mahaluki dake cikin kotun ya d'ora hankalinsa a kansa, tun daga d'azun bai sake ganinta ba kuma basu yi wata maganar kirki ba saboda hayaniyar mutane da kuma shirye-shiryen zaman kotun, amma tun daga d'azun bai san sau nawa zuciyarsa ta rantse sai ya d'auki fansa akan Kutama ba, sai ya kuntata masa kamar yadda ya yiwa idanun da ya shiga kowanne k'alubale na rayuwarsa ya fito tare dasu.

Ya gyara tsaiwarsa daidai saitin alk'alin, sannan ya d'anyi gyaran murya kad'an ya fara magana.

"Ya mai girma mai shari'ah, daga lokacin da aka shigar da k'arar nan zuwa yanzu, mun saurari hujjoji daga b'angaren masu shigar da k'ara da kuma bayanai daga b'angaren shaidun da aka gabatar, wanda dukkaninsu suna tafiya ne kan irin tunanin abokin aikina, saboda haka duk wasu maganganu dashi ko shaidunsa suka tsaya anan suka fad'a, sunyi su ne bisa rashin sanin gaskiyar lamarin nan da kuma ainihin wanda ke bayan laifin.

A yau zan fito da komai kuma zan baiyanawa kotu yadda rasuwar marigayiya ta kasance da kuma wanda ke da alhakin wannan kisan.

Ba kamar yadda kotu ta d'auka bane tun farkon shari'ar nan, babu laifin Bintu wadda Lauyan masu shigar da k'ara ke zargi ko kuma wadda ake zargi daga baya wato Habiba."
Ba 'yan kallo ba hatta sauran lauyoyin dake zaune sai da suka k'ara tsaida idonsu akansa jin ysla ambaci cewa babu laifin Habiba.

Adam ya d'an murza yatsunsa na dama sannan ya fad'i abinda ya kwana ya tashi dashi a ransa.

"Ina neman Kotu ta bani damar gabatar da shaiduna."
Alk'ali ya gyad'a kansa.

"Kotu ta baka dama."
"Zanso in kira Bintu Abubakar a matsayin shaidata ta farko."
Sunan ya fito kai tsaye kuma ya daki tunanin kowa a wajen, hakan ya sanya tashin 'yan maganganu daga wajen 'yan kallo, hatta Alk'alin saida ya gyara zaman gilashinsa ya k'ara kallonsa.

"Tana cikin jerin sunayen shaidun da ka bayar?"
"Sunanta yana ciki ya mai girma mai shari'ah."
Alk'ali ya gyad'a kansa.

"Kotu ta baka dama."
Sai kawai ya juya ya kalli inda Fadeelan ke zaune, idanun da yake jin ciwonsu na tsaye suna kallonsa amma wannan karon fayau suke, babu mamaki ko rud'ani irin na sauran mutanen dake bayanta, bata san zai kirata ba amma bata tsorata ba, ya lura ta dad'e da cire kalmar tsoro daga zuciyarta tun daga lokacin da ta karb'i shari'ar nan..._ranar da ya fara ganinta, sanda ta ture mamakin ganinsa tayi masa bayanin komai dalla-dalla, da kuma ranar da za'a fara zaman kotun, sanda yaje lallashinta a matsayin wadda zata fara shiga kotu da zargin kisa, amma bud'ar bakinta tambayarsa kawai tayi 'Habiba tazo?'
Fadeelah ta mik'e daga inda take zaune, zuciyarta a dake ta nufi wajen tsayuwar masu shaida.

Magatakarda yace.

"Ki fad'i sunanki kuma ki fad'i kowacce kalma dalla-dalla don za'a rubuta."
Idanunta na sunkuye amma muryarta a tsaye kyam! tace.

"Bintu Abubakar, _B-i-n-t-u A-b-u-b-a-k-a-r_
Kotun ta d'auki shiru a lokacin da ake rantsar da ita, mafi yawan mutane daga cikin 'yan kallo hannayensu motsi suke na k'aguwa a fara shari'ar.

Daga teburin zaman lauyoyi kuwa Kutama ya kalli mataimakinsa suka yi murmushi a tare.

Adam ya matsa jikin akwatin da take tsaye bayan gama rantsuwar, amon muryarsa a tausashe fiye da k'aidar yadda yake ya fara magana.

"Na san zuciyarki tana cikin wani irin hali yanzu Bintu, rayuwarki ta hargitse kuma an k'untata miki ta hanyoyi da dama akan laifin da baki aikata ba, na san cewa kin shiga wata mummunar rayuwar da baki tab'a sani ba akan zargi kawai, an saka ki..."
"K'orafi ya mai shari'a!" Muryar Kutama ta karad'e wajen, idanun kowa ya juya kansa amma banda na Adam da Fadeelah.

"Lauyan mai karewa yana b'atawa kotu lokaci da kalaman da basu da amfani."
Alk'ali ya girgiza kansa.

"K'orafi bai karb'u ba."
Adam bai jira zaunawar Kutama ba ya cigaba.

"Kar ki damu kanki, wannan shar'iar gabad'aya an fara ta ne don a wanke ki daga zargin nan, sannan mafi yawan mutanen da kike gani anan..."
Yatsansa d'aya ya nuna sama sannan yayi alamun zagaye, ma'ana gabad'aya kotun.

"..sunzo ne don ganin kin fita daga wannan halin kin samun 'yancinki na rayuwa tamakar a baya.
Chapter 76 · 0% Book details