← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 95

Sashe 69

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bintuuu Abubakar...!"
Sai da ta tabbatar babu wadda ke shirin mik'ewa a cikin tarin matan wajen sannan ta mik'e a hankali ta nufi can gaban.

"Kece Bintu Abubakar?"
Matron d'in ta tambaya kamar gatse.

"Eh."
"Lauyanki ne yazo ganinki."
Zuciyar Fadeelah tayi fiffike ta tashi sama, ta zagaya kaftanin wajen.

Adam ya dawo, Ita dama ta san ba abunda zai same shi, ba zaiyi nisan da zai barta cikin wahala ba..

Wani abu ne kawai ya rik'e shi amma ya gama ya dawo, zai sa a maida ita can wannan k'azamin cell d'in da a yanzu take masa kallon Rahma.

Ta kasa saita bakinta wajen kokarin yin murmushi sanda aka saka wata Matron d'in ta jata hanyar d'akin ganawa da bak'i na kurkukun.

Kamar lokacin karatunsu ne a cikin library, kamar kuma lokacin da take ganinsa a cikin kotu, _Isolated places.._ wajajen da babu mutane ya zame musu wajen had'uwa a kodayaushe.

Suka isa k'ofar ginin wajen, Matron d'in ta bud'e suka shiga...

K'aton waje ne mai d'auke tarin kujeru fal, kuma farare kamar tattabaru, amma bata damu da k'arewa wajen kallo ba, in har ta gama tattaunawa da Adam, nazarin wajen zai biyo baya.

"Gashi can yana jiranki..."
Fadeelah ta juya ta kalli inda Matron d'in take nunawa, a lokacin taji kamar wani yasa kwari da baka ya harbo wannan zuciyar tata da tayi tsuntsuwa ta tashi sama, zuciyar ta juya ta kuma juyawa sannan ta fad'o k'asa wanwar!

Kutama yayi murmushi daga inda yake zaune yana kallonta.
****
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Ya sake sakin wani guntun murmushin yana k'are mata kallo.

"K'araso ki zauna mana." Fadeelah taji amon muryarsa ya amsa a wajen kamar yadda ta saba jinsa a kotu.

"Me ya kawo ka wajena?"
Tata muryar ta fito a karye, karyewar ganinsa a maimakon wanda zuciyarta ke nema.

"Alheri 'yanmata, Alheri irin wanda kike nema."
Kanta ya d'aure, wane alheri ne zai had'a ta dashi?

Me zai kawo shi wajenta?

"Nayi zaton babu Alheri tsakanina da kai."
"Shi yasa nace ki karaso ki zauna don in cire miki zaton."
Ta girgiza kai, ta yaya zata saurari mutumin dake kokarin hallaka ta?

Wata irin shaida ce bai bayar ba don shar'iah ta d'aure ta?

"Babu abinda zan tattauna da kai, Nagode."
Ta juya ta nufi k'ofa.

"Shikenan in baki damu da jin me ya kawo ni ba na san zaki so sanin inda Lauyanki yake."
Cak!

K'afafunta suka tsaya jin hakan, lauyanta!

Adam yake nufi.

Ta juyo da sauri ta kalle shi.

"Kamar yaya?

Ina yake?

Wani abu ya faru dashi ne?"
Bai ce komai ba kawai ya nuna mata kujerar gabansa, ta kalli kujerar, ta hango amsoshin tambayoyin da tayi masa sannan tayi ajiyar zuciya ta k'arasa ta zauna.

"Hajiya Bintu, zan fara da gaya miki dalilin zuwa na tukunna kafin muje ga abinda kike son ji...

Ina tunanin kin san cewa ni ba lauyan gwamnati bane ko?"
Ba tace komai ba ya cigaba, yatsunsa hard'e kan teburin dake gabansu.

"Ni lauyan kasuwa ne, 'yanuwanki sun d'auko ni ne sun biya ni na shiga shari'ar har na tara isassun shaidun da suka kawo ki har cikin kurkukun nan."
Yayi tunanin jin muryarta a yanzu, amma bata sake cewa komai ba, tayi shiru kawai tana cigaba da kallonsa.

"Bayan wad'ancan shaidun kuma da na bayar a kotu, a yanzu haka ina da kwararan shaidu guda biyu
da a gaba zan gabatar, kuma ina tabbatar miki cewa in har na fito dasu babu abinda zai hana a zartar miki da hukunci na k'arshe akansu.

Sai dai kuma zuciyata na gaya min cewa bai kamata a bar yarinya irinki ta k'are rayuwarta a kurkuku irin wannan ba saboda na san ba lallai a yanke miki hukuncin kisa ba, kotu zata yi miki rangwame a barki a nan wajen har iya rayuwarki.

Don haka ne kwanakin baya na yanke shawara, na sadaukar da nasarar da zan iya samu a shari'ar nan, naje na sami lauyanki kafin tafiyarsa na gaya masa cewa zan iya siyar muku da wad'annan shaidun biyun da nake dasu a yanzu, in kuma baku lagon sauran abubuwan da 'yanuwanki suka bani, amma fur!

Yak'i saurarata a lokacin.

Game da duk bayanan dana tara, na yarda baki da laifi a cikin wannan al'amarin Bintu, duk da cewa ban san waye ainihin mai laifin ba amma tausayin irin rayuwar da shari'ar nan zata kaiki yasa nazo wajenki, abinda nayi da kuma wanda nake yi yanzu kuskure ne ko a cikin aikinmu, amma na ture komai saboda kawai in taimake ki.

A yanzu kin kwana biyu a cikin kurkukun nan Bintu, kinga irin rayuwar da ake kwad'antawa, kuma na san baza ki so ki dauwama a cikinta ba, baza ki..."
"Me kake so?"
Muryarta ta katse shi a tsaye babu wani gargada.

Ya d'an tsaida idonsa a kanta, maganar da tayi a kusa dashi ya tabbatar masa cewa bai tab'a jin muryarta ba, amma sai ya ture hakan ta hanyar kaurara muryarsa sannan ya fad'i abinda ya dad'e yana shirya masa.

"Ki sa 'yanuwanki su sayi shaidun wajena, ni kuma nayi miki alkawari zanyi sanyi a b'angarena yadda zaku iya yin nasara."
Ya k'ara da cewa.

"Ba lallai sai lauyanki ya sani ba tunda tun farko yak'i amincewa, in har kun siya shaidun zamu yi komai ne a rufe."
"Wad'anne irin shaidu ne?"
Sai yayi guntun murmushi jin hak'ansa ya fara cimma ruwa.

"Idan muka yi ciniki zaki gansu, kuma ina mai tabbatar miki ba za kuyi dana sanin karb'e su daga hannuna ba."
Fadeelah ta cije k'arshen lebb'enta tana kallonsa, tunani take a cikin kanta ina ma tana da recorder ta nad'i maganganunsa tun daga farko! _ya riga ya san baki da ita ai._ Zuciyarta ta rad'a mata.

"Wannan damarki ce Bintu, damar da idan ta kub'uce zaki zo kina dana sanin ta tsawon rayuwarki."
Muryarsa ta sake fitowa cikin sigar hila, sai tayi wani guntun murmushi wanda ya fito a bushe kan lebb'enta, ta sunkuyar da kai ta kalli yatsunta sannan ta d'ago ta kalli idanunsa dake nuna jiranye.

"Kana tunanin kai kake da k'addarar rayuwata a hannunka?"
Lauya ne shi, mai kama da dillali, wanda ya san ma'anar duk wani motsi da futucin kostomansa, don haka a take ya gane ina maganarta ta dosa.

Ya saki nasa murmushin shima mai fad'i da zurfi.

"Kin b'arar da damar kenan?"
Fadeelah tace.

"Na cillar da ita, b'ari wani lokacin a rashin sani ake yinsa, amma jifa babu wanda zaiyi bai kudirta hakan ba."
Ya tab'e baki kad'an, da dai murmushin sannan yace.

"Sai ince miki barka da shigowa sabuwar rayuwa, Binbi!"
Sunan ya dake ta, kamar dukan gudama a tsakiyar kai amma bata nuna ba, balle ta nuna mamakin yadda akayi ya sani don ko Matron d'in data rako ta zata iya fad'a masa.

Ta sake cije lebb'enta kad'an sannan ta tambayi abinda yasa tun farko ta saurare shi.

"Ina lauyana ya tafi?"
Sautin dariyarsa ne ya fito kafin amsarsa, dariyar data tsinto ciwon tayinsa da ta tankwab'e a ciki.

"Hajiya Bintu kin tab'a ganin inda mai siye ya kushe kayan mai siyarwa sannan ya nemi da yayi masa kwatancen wajen wani mai siyarwar?"
Ta tamke k'asan lebb'enta data cije kamar zata datsa wajen, ya kamata tun farko ta hango wannan amsar, Babu ta yadda za'ayi Kutama ya san inda Adam yake alhalin ko Kawu Ibrahim bai sani ba.

Sai ta mik'e tsaye kawai ba tare da ta ko kalle shi ba, ta ture kujerar data zauna sannan ta juya tabi ta cikin sauran fararen kujerun ta nufi hanyar fita daga wajen.

Kutama ya bita da kallo, ji yake kamar hayakin tiriri ne ke fita daga kunnensa saboda haushin yadda ya fito da zalamarsa gaban yarinya k'arama irinta ita kuma ta watsa masa k'asar kunya a ido.

Ya gyad'a kai a hankali sannan ya rantse a cikin ransa sai ya toshe duk wata k'ofa da zata iya sawa suyi nasara, yadda zata shafe tsawon rayuwarta tana takaicin abinda tayi masa.

Matron d'in dake tsaye a bakin wajen tabi Fadeelah da kallo sanda ta fito tazo ta wuce ta, mamakin halayyarta ya sake kamata, tun sanda aka kawo su ta lura yanayinta daban ne dana masu laifi da yawa da ake kawowa, bata nuna tsoro game da abubuwa da yawa na wajen, zuciyarta a dake take kamar a baya ta fuskanci wani abu da yafi k'arfin zaman kurkukun nan.

Da k'arfi ta tsaida ita ganin tana neman yin nisa.

"Ke tsaya nan in maida ke!"
Fadeelah ta ji ta amma bata tsaya d'in ba, da kowanne taku k'irga kwanakin da suka rage a sake zaman shari'arta take yi, ta san ko'ina Adam yaje kuma komai rintsi zai dawo a sannan!

A cikin garin Ikara, cikin Babban gida, b'angaren Kawu Ibrahim, Daddy ya kalli Kawu Ibrahim yace.

"Wad'annan 'yanuwan mahaifiyata ne na can Kano, suma sun san Fadeelah lokacin da ta zauna tare da mahaifiyar tawa kafin rasuwarta, shi yasa suka zo don suyi muku jaje."
"Allah sarki, sannunku, sannunku...

Sannu da zuwa, Mun gode wallahi."
Kawu Ibrahim ya fad'a yana sake mik'a musu hannu suka gaisa a karo na biyu, Kawu Bashir da Kawu Nura ma dake gefensa suma suka k'ara mik'a musu hannu suka gaisa.

Daddy ya sake gyaran murya yace.

"Daga can Kurkukun muke yanzu mun samu damar ganin _Warden_...

Ina nufi shi shugaban prison d'in, yayi mana bayanin cewa su yanzu basu da ikon sakinta, daga can Kotun da aka kawo ta ne zasu iya yin magana sannan a iya maida ita can amma yace su babu abinda zasu iya yi."
"Kamar dai yadda wancan mutumin ya fad'a mana tun da fari." Cewar Kawu Ibrahim.

"Karka damu Alhaji, komai mai wucewa ne insha Allahu yarinyar nan zata fito komai ya zama tarihi." Cewar d'aya daga cikin bak'in Kanon nan.

"In Allah." Kawu Bashir ya amsa.

Kawu Ibrahim ya sake cewa.

"Bana cire rai daga hakan insha Allah, tunda na san koi'na shi lauyan nata ya tafi zai dawo kafin a sake wani zaman, kuma saukinta ma yana tare suke da d'an gidan Nura..." Ya nuna Kawu Nura dake gefensa.

"...
Chapter 69 · 0% Book details