Sashe 19
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya d'auki ragowar lemonsa dake gefe yana d'iga saboda rab'ar sanyi ya k'arasa shanye shi sannan ya zare bak'in gilashin dake fuskarsa, kwayar idonsa mai kyau ta haska a cikin d'an karamin mudubin dake gaban motar, gashin kansa a kwance yake cikin style mai kyau yana kyalli sannan yana da saje amma ba mai yawa ba, mai laushi wanda yabi ya kwanta kan fatarsa mai kama da launin chocolate mai haske.
Ba wai fuskar tasa yake kallo ba, a'a tunani ne fal a cikin kansa wanda zuciyarsa ke d'ebewa da tarawa a hankali.
A jiya ya gama case d'in da yake aiki akai kuma yayi nasara, yana fatan hakan ya bashi ikon samun hutun watanni ukun da yake nema wanda zai saita rayuwarsa dasu, ya san abu ne mai wuya a yanzu da ba lokacin leave d'insa ba ya samu hakan shi yasa ya dage iya k'okarinsa ba dare ba rana ya had'a evidence d'in da suka bashi damar cinye shari'ar da fatan a dubi nasararsa a bashi wannan damar.
Ya jawo 'yar k'aramar briefcase d'insa dake kan kujerar mai zaman banza sannan ya fita daga motar, ta tsakanin d'inbin motocin dake tsaye a wajen yayi ta kurd'awa har zuwa cikin tamfatsesiyar kotun.
"D'an k'araminsu babbansu kenan!"
Muryar wani abokin aikinsa ta fad'a sanda ya nufi hanyar elevator d'in da zai kaishi ofishinsa.
"Ka san jiya ban zauna ba, ashe an gama case d'in nan kuma kayi nasara, gaskiya Man na taya ka murna kayi k'ok'ari sosai, weldone Steve!
"
Ya kirashi da surname d'in da suke kiransa a kotun.
"Thank you Ryan, Nagode sosai."
Ya amsa da muryarsa mai zurfi sanda ya bud'e elavator suka shiga bakid'aya, sai dai kafin k'ofar ta kai ga rufewa wani lawyer mai suna John ya shigo rik'e da files d'insa, bai ko
kalle su ba ya nemi waje ya tsaya, lift d'in ya shiga d'agawa.
"Ka san me, zan zo in karb'i clues a wajenka, don ina assisting wani case lowcoast court shigen naka, wa ya sani mu ma muyi nasara in mun bi irin hanyoyin da kayi amfani dasu saboda..."
Ryan ya cigaba da magana lokacin da gravity na lift d'in ke d'aga su sama, sai da hankalin Adam kwata-kwata baya kansa, yana ga mutumin nan dake gabansa hannayensa rik'e da files, haka kurum jikinsa ya bashi wani abu, don mutumin yana d'aya daga cikin 'yan team d'in da suke adawa dashi tun farkon fara aikinsa a wajen wanda yanzu shekara guda kenan.
Zarginsa ya k'ara tabbatuwa lokacin da John d'in ya tsaya a hawan da office d'in shugabansu yake, saboda haka ya sawa zuciyarsa ta yarda cewa dole akwai wani abu da aka shirya masa yau wanda ke shirin faruwa, don ya fahimci cewa an daidaici lokacin zuwansa ne ma aka saka John yazo rik'e da wad'annan files d'in don a nuna masa daga ina koma meye ake shirin k'ulla masan ya fito.
Da kyar ya samu ya tserewa surutun Ryan ya k'arasa cikin office d'in nasa.
Kasancewar jiya ya gama case d'insa sai ya zama ba abinda zaiyi yau illa rubuta wasu dokoki da zai turawa wani d'an kasuwa kan sha'anin da ya shafi kasuwanci.
Wajen k'arfe goma ya jawo wayarsa ya danna kiran da kusan kullum yake saman call log na wayarsa, kiran kuma da ya san ba zai tab'a amfanarsa da komai ba.
"Hello, barkan ka dai, kana magana _ne da gidan kula da tsofaffi da masu rauni na garin Leicester a k'asar England."
Ya lumshe idonsa kad'an jin wata sabuwar murya ba ta matar daya saba ji in ya kira ba.
A hankali ya amsa.
"Barkanki da aiki, ina neman wata mata ne mai suna Magareth, ance min tana tare daku."
"Haka ne kwarai Magareth tana tare damu, waye kai a wajenta? d'anuwa ne?"
"A'a..." ya amsa abinda yake fad'a kullum, sannan ya cigaba da k'arashen.
"Ina son inyi mata wasu tambayoyi ne game da IYAYENA!"
"Na fahimta amma sai dai kayi hakuri, magareth ta tsufa da yawa kuma tana da lalurar kunne bata iya amfani da yawa, sai da kazo da kanka in har kana son amsar tambayoyinka, zata ji dad'in zuwanka!"
D'ib! ya kashe wayarsa sannan ya koma da baya ya kwanta a jikin kujerar, a kowacce safiya dake fitowa magareth k'ara tsufa take, don haka dole ne yayi k'ok'arin samun lokacin da zai isa gareta kafin ta mutu, damar da yake da ita guda d'aya ta tankwab'e.
Da kyar ya samu ya saita tunaninsa, sannan ya koma kan aikinsa ya cigaba.
Da misalin k'arfe sha biyu na wannan ranar kuma ya samu kiran da ya sawa zuciyarsa tsammaninsa, ya samu kiran da ya canja akalar rayuwarsa kamar yadda igiyar ruwa ke tambali da k'aramin jirgi a tsakiyar teku.
"Na taya ka murnar samun nasara akan case d'inka."
Muryar shugaban nasu ta ambata lokacin da yake zaune a kujerar tsallaken teburin bayan ya amsa kiransa.
"Nagode sir." Adam ya fad'a a hankali kamar koyaushe.
"... sannan naga proposal d'inka cewa ka nemi hutu na wata uku ko?"
"Haka ne sir, ina da wani abu mai muhimmanci ne da nake son yi a yanzu."
Sai ya tab'e bakinsa kad'an.
"Amma ka san baka dad'e da karb'ar hutu ba ko?"
"Na sani, shi yasa na nemi hakan a matsayin alfarma."
Shiru ya biyo baya kafin ya sake magana.
"Mu ajiye zancen hutunka a gefe Steve, akwai aikin da shigo yanzu kuma ba wanda ya dace dashi sai kai... saboda haka wannan ba case ne da zaka yi din ra'ayinka ba, case ne da ya zama umarni bama daga ni ba, daga can shugabanmu gabad'aya kuma babu wanda ya isa ya canja shi."
Adam bai ko yi motsi ba balle yayi magana har zuwa lokacin da hannun shugaban ya d'auko wannan file d'in daya gani d'azu a hannun John, a sannan ne yaji zuciyarsa tayi wani irin motsin da shi kad'ai ya san ma'anarsa.
"Case ne akan wani mutumi da ake zargi da kisan kai daga can garin Alaska, an neme shi an rasa sai a yanzu ake tunanin ya gudo daga garin yazo nan ya bud'e sabuwar rayuwa a matsayin malamin makaranta, saboda haka babu hanyar da za'a tabbatar da hakan sai ta 'Private investigation'.
Saboda haka zaka b'ad da kamannika sannan kaje makarantar da yake a matsayin d'alibi, kabi dukkan wasu hanyoyin da zai amince da kai a harkokinsa yadda zaka sami enough evidence d'in da zamu iya tunkararsa, daga nan sai ka dawo kotu ayi handling case d'in."
Saurararsa kawai yake yi amma kwakwalwarsa ta gagara saita maganganun akan layi d'aya, yaje wata makaranta a matsayin d'alibi? ta yaya hakan zai yiwu? ta yaya zai rage shekarunsa? me yasa ma sai shi d'in?
"Saboda kaine mai k'ananan shekaru duk cikin ma'aikatar nan kuma kai ne kad'ai baka tab'a magana da media ba ba ka fara aiki bada dad'ewa ba, babu wanda ya sanka sosai, sannan akwai wanda zai kula da harkar kammaninka a gefe guda, shi zai saita ka akan duk abinda zaka bi ka koma irin yanayin d'aliban makarantar."
Bai yarda da zancen ko kad'an ba, don
ya riga ya san su waye suka yi masa cunen wannan aikin, amma kamar yadda shugaban ya fad'a ne a farko ba yadda ya iya dole ne ya amsa, saboda haka ya gyad'a kansa sannan yace.'
"Na fahimta kuma zanyi dukkan k'ok'arina ranka ya dad'e babu matsala, a bani files d'in da kuma sauran abubuwan da zan buk'ata."
Watak'ila ya fahimci cewa dauriya kawai yayi ya fad'i hakan, don maimakon ya amsa sai ya kira sunansa da wani irin amo
mai jan hankali.
"Yes sir."
Ya amsa shima cikin malalaciyar muryarsa.
"Idan har kayi nasara a wannan case d'in, na tabbatar maka ni da hannuna zan yi signing cewa a baka leave na shekara guda."
Sai ya d'ago da fuskarsa sosai ya kalle shi, da gaske yake zai nema masa hutu har na tsawon shekara guda? a hankali yaji wani abu kamar sabon k'arfi da kuma son case d'in ya gifta a zuciyarsa, yaji cewa dama zai iya gama aikin a cikin 'yan kwanaki kawai!
"Amma akwai wani hanzari ba gudu ba Steve, mutum da zaka yi binciken akansa, yana da tsananin k'in wannan addinin na musulunci, saboda haka abinda zaka fara yi shine had'a k'ungiyar da zata dinga sukar wannan addinin, ta nan zai fara lura da kai bayan ka shiga k'ungiyarsa ta kwallon k'afa sannan..."
Adam bai san zancen da ya cigaba da yi bayan ya fad'i cewa sai ya zama mai sukar musulunci ba, ubangiji ya sani shi BA MUSULMI bane amma musulunci bai tab'a damunsa ba don ya san abubuwa da yawa game dashi, kuma yana ji a jikinsa cewa ba zai so ya zama mai takurawa mabiyansa ba.
Sai dai mafitar da yake nemarwa kansa tafi k'arfin wannan a lokacin, saboda haka daga wannan lokacin yabi umarninsu ya aske gemu da sajensa, ya barbaza gashinsa da kullum yake a kwance sannan ya shiga bin duk wata hanya da mutumin da aka d'auko ke nuna masa yadda zai koma yaro matashi mai irin shekarun samarin makarantar.
Daga wannan lokacin kuma, k'addarar rayuwarsa ta had'u ta kanannad'e data Fadeelah!
"Deelah, saura wad'annan plates d'in na can sama."
Mami ta fad'a lokacin da Fadeelah ta taka can saman kata tana mik'o mata kayayyakin da suka dad'e basu yi amfani dasu ba, kayayyakin data rasa meye amfanin d'ebo sun da ake yi.
Suna kitchen ne gabad'ayansu a ranar Asabar, ita tana d'ebo kayayyakin, Mami kuma tana ware wad'ansu sannan ta mik'awa Zahra dake bakin sink ta shiga wankewa.
Beeem!
Wayarta dake ajiye daga gefen k'afarta akan durowar data taka tayi k'ara alamun shigowar message, ta sunkuyo da kanta daga tsayen sanda k'arfin ganin gilashin idonta ya nuna mata d'an k'aramin hoton fuskar Al'ameen da kuma sak'onsa a gefe.
Dan Allah ki gaya min baki yi fushi ba, I'm so sorry sai yanzu naga message d'inki wallahi.