← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 95

Sashe 40

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sau d'aya ya taba zuwa wajen,
amma tsayin shekarun basu sa idanunsa sun kasa gane kabarin da yake nema ba, cikin mintuna 'yan kad'an kuwa ya hak'e gefensa ya ciro layar mutum-mutumin daya tab'a binnewa da hannunsa a wani dare!

A dai larabar kuma, wata mata daga cikin k'awayen Aunty Hadiza yayar Mami Safiyya, tayi wata sabuwar 'yar aiki fil! daga garin IKARA.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
I K A R A
"Wai da gaske ne Sadiya aikatau ta tafi?"
Ladi, k'awa ga Zainab matar Rabi'u d'aya daga cikin 'ya'yan BABBAN GIDA ta tambaya lokacin da ta shigo sashen Zainab d'in a ranar juma'a.

Zainab ta tab'e baki tana yanka albasa kan kwad'on zogalen bishiyar tsakar sashenta data dafa tace.

"Haka dai ake cewa, amma waya sani ko dadironta ta tafi, tunda ansha zaman gida shekara da shekaru ba bazawari."
"Ke Zainab mutuniyar taki kike wa wannan zaton?"
"Wace mutuniyar tawa?

Ai shi yasa nace miki kin dad'e baki shigo gidan nan ba, tun yaushe na fita harkar wannan munafukar, ke ni gidan nan ma yanzu in gaya miki in kika d'auke manya irinsu Kawu Danjuma, to ko shi Rabi'u da nake zamansa ba wanda zan d'ebe ince miki baya ji da nasa munafuncinsa, kallon kowa nake yi kawai."
Ladi ta jinjina kanta.

"To Allah ya kyauta!

Ni a tunanina duk wannan baya rasa nasaba da yadda Habiba ta kankane kusan komai na gidan nan."
"Ke raba kanki, ai yanzu ba cikin gidan nan kad'ai ba har a waje kusan kowa da Hajiya yake kiranta, makkarta biyu fa."
Wannan karon Ladi ce ta tab'e nata bakin.

"Wato kema ba kya ganin laifinta kenan, shikenan ta had'e ku gabad'aya gidanta shanye, ai ni
tunda na shigo gidan nan bayan watanni biyu kawai da rasuwar Hajiya Balaraba na san abinda Habiba ke fata ya faru,
ta samu damar watayawa ta juya kowa yadda take so kamar yadda ta maida mijinta,
shi yasa dama basa tab'a shiri da ha..."
"A'a Ladi tsaya!

Ya naji kina neman karkace hanya ne ki danganta rasuwar Hajiya kuma da Habiba, meye had'in anan?

Abu da ya riga ya shud'e kowa kuma ya san wannan tsinanniyar yarinyar ce ta kasheta ta gudu."
"Kinga nifa ba wani abu nace ba,
nufina tunda babu Hajiya a yanzu,
habiba ta samu damarta ne
kawai ba wani zance ba."
Zainab ta juya ta cigaba da yanka koren tattasai kan had'in zogalen sannan tace.

"A'a to, ai gwara inji ne da kyau don kin san fa har yanzu zancen na gaban hukuma, su Kawu d'anjuma sun sha alwashin sai dai in ba'a ga Bintu a duniyar ba,
amma babu abinda zai hana su mik'ata gaban hukuma a rataye ta itama."
"Ina zancen da ake cewa ta MUTU?"
"Babu inganci a cikinsa gaskiya,
tunda Rabi'u yace min a motar da akace ta hau anyi hatsarin, mutum d'aya ne kawai ya mutu shima wani tsoho, amma ita ance bata ma ji rauni ba kawai dai an samu akasi an sallameta ne kafin daga nan gida a isa can kanon."
"To Allah ya kyauta, amma ni wallahi 'yar tausayi take bani,
ba uwa ba uba sannan ga wannan bak'in fenti haka?"
Zainab ta shiga yanka wani k'aton tumatir jawur dashi sannan tace.

"Meye abin tausayi anan Ladi, bak'in halin uwa ne fa ta d'auko, ko kin manta yarta Mairo ma guduwa tayi da saurayi tun iyayen na da rai, ai ni wallahi a zaman yarinyar gidan nan har bana son a aiko ta sashena, kinga wannan d'an banzan farin nata da yalolon gashin nan, mayya sak! nake kallonta."
Ladi ta kyalkyale da dariya harda buga cinya sannan tace.

"Allah ya shiryeki Zainab, maita ai ba'a fari take ba."
"Ke dai bar mutum kawai, ai shi yasa a ranar da Hajiya ta mutun nan, na zage iya k'arfina nima na shiga aka jibgeta don wallahi bana d'auke kokonton yawan laulayin yusufa (d'anta na biyu) daga ita ne,
don ina dab da haihuwarsa ta dawo gidan nan."
Ta fad'a daidai sanda ta gama yankan tumatirin, sannan ta saka k'aton cokali ta juya shi tsaf komai ya had'e, ta janyo wani k'aramin filas dake gefen tabarmar da suke kai ta d'ebi na maigidanta da yaran da suka tafi makarantar allo sannan ta juyo musu da ragowar suka shiga ci.

Sai dai basu kai ga saka loma ta biyu a bakinsu ba, Salihu babban d'anta ya rugo cikin tsakar gidan sakale da allonsa a hammata.

"Kai don ub*nka haka ake shigowa gidan mutane ba sallama kamar wani kafiri?"
Ta daka masa tsawa lokacin da yaja birki a gaban tabarmarsu.

"Ina sauran suke?" Ta katse rawar zancen da bakinsa ke yi.

"Suna can gindin motar suna kallo."
"Motar wa kuma?"
"Mama, Mama wani balarabe ne yazo daga Makka a cikin wata had'addiyar mota, tun muna addu'ar tashi muka ganshi ya wuto mu, yanzu haka dukka su Kawu sun cika wajen Kawu d'anjuma jingim!"
Ita da Ladi kallonsa kawai suke da mamakin yadda ya rikice haka.

"Wajen Kawu Danjuman yazo?"
"Eh mana, kuma naji su yaya Sule suna fad'in wai d'anuwanmu ne!"
"Sule me ya faru ne haka?" Me akeyi?"
Kawu Ibrahim ya tambaya sanda ya shigo gidan shida babban d'ansa Harisu da la'asar lis!

Daga zagayen gonakinsa da suka dawo.

Banda tarin yara birjik da suka wuce a k'ofar gida sun yanyame wata mota,
yanzu kuma ya shigo gidan yaga kusan duk samarin da ba'a fiye samunsu a wannan lokacin ba suna tsaitsaiye kan hanyar shiga sashen Kawun.

Sule ya d'an sunkuyar da kansa ya gaishe shi sannan yace.

"Kawu bak'o akayi ne daga wata k'asar ina jin, kuma naji su Kawu Sulaiman suna cewa wai d'an gidan Baba Ahmadu ne."
Cak!

Bugun zuciyarsa ya tsaya na wasu 'yan dak'k'ai, ya kalle shi sosai sannan ya tambaya.

"Wane Baba Ahmadun?"
"Wanda dai ake bada labarin cewa ya b'ata shekarun baya da ak..."
Ai bai ko tsaya saurarar k'arashen ba ya wuce su duk ya durfafi hanyar sashen Kawu Danjuma.

Tun daga adadin takalman dake cire a waje zuciyarsa ta tabbatar masa cewa zancen Sule gaskiya ne, don yaushe rabon da a hudu duk a irin wannan lokacin?

Sai ya cire nasa daga gefe shima sannan yasa kai cikin d'akin.

Zai iya cewa kowa na nan, yayyensa dama k'annensa da suka manyanta, irinsa masu uzirin nesa kad'an ne basa nan sannan ga Kawu d'anjuma zaune a tsakiyar shimfidarsa, sai dai duk lura da wannan yazo ne bayan siffar Ahmadu k'aninsa daya hanga zaune a gefen Kawu d'anjuma,
Ahmadunsa sak!

Kaninsa da duk fad'in babban gida daga shi sai k'anwarsu jummai ne suke uwa d'aya uba d'aya.

Amma wannan da yake gani Fari ne ba bak'i ba, sannan in ka d'ebe lallausar sumar kansa, to ba abinda zai banbanta shi da wancan Ahmadun daya bar gida a irin wannan shekarun.

Kwanan nan zan hutar da kai yaya, kwanan nan zaka manta da wahalar noman nan, sai dai kana zaune ka saka ayi maka, kwanan nan yaya!

Maganar wancan Ahmadun ta dawo cikin kansa tar!

Maganar da ita ta zama magana ta k'arshe da ta shiga tsakaninsa da d'anuwansa, don daga wannan ranar Ahmadun yayi b'atan damo daga cikin rayuwarsu gabad'aya, aka neme shi aka rasa.

"Karaso mana Ibrahim, taho kaga ashe bamu sani ba Ahmadu ya mutu ya bar jininsa a duniya."
A hankali Kawu Ibrahim ya k'arasa ya zauna a gefen d'an baturen Ahmadun da yake gani.

"Wannan yayan mahaifinka ne da suke uwa d'aya uba d'aya."
Kawu d'anjuma ya fad'a sanda ya juya yana kallonsa, sai dai yana rufe baki Sa'idu ya d'auka, ya fad'i abinda kawun ya fad'a sak amma da turanci.

"Baya jin hausa Ibrahim sai turanci, yace daga America yazo."
Kawu d'anjuma ya tari mamakin daya nuna akan fuskarsa.

"America kuma Kawu?

Shi Ahmadun can yaje ya haife shi?"
"I, nima abinda nace kenan, da mamaki da d'aure kai amma gashi yazo da shaidun da suka nuna shi d'an nasa ne."
"Ko ba shaida Kawu na yarda wannan d'an Ahmadu ne, zan iya tsayawa gaban ko waye kuwa in tabbatar da hakan."
Adam bai san me yace ba, amma sai ya zab'i daidai wannan lokacin ya matso gabansa sannan ya rik'o hannayensa, iya hasashensa ya yarda cewa duk cikin mutanen nan wannan shine madadin mahaifinsa, uwa d'aya uba d'aya yafi k'arfin komai.

Kwalla mai d'umi ta gangaro kan kumatun Kawu Ibrahim, don gani yayi sak!

Kamar k'anin nasa ne ya dawo gabansa yake neman gafararsa, sai shima ya damk'e nasa lallausan hannayen da suka shaida cewa ko daga ina yake, bai tashi cikin wahala kamar Ahmadunsa ba.

Tiryan-tiryan, Adam ya zauna ya shaida musu tarihinsa da kuma na iyayensa da yaji daga Magareth, shakka babu sun tausayawa irin rayuwar da d'anuwansu ya tsinci kansa, sannan kuma Adam yasha godiya da jinjina kan kokarin da yayi har ya nemo su bai kyamaci cewa su dangin nasa basu zo a irin wajen daya taso ba.

Kawu Ibrahim shi ya shaida masa sai bayan shekaru biyu da b'acewar Ahmad ne suka sami labari cewa wani aboki ya had'u dashi daya kwad'aita masa sana'ar shigar da kwayoyi k'asashen k'etare da cewar kud'i ake samu masu yawa, kuma daga nan basu k'ara jin labarinsa ba.

Da wannan Adam ya had'a ya fitar da cewar an kama mahaifinsa ne a kokarinsa na shigar da kwayoyin k'asar America kuma aka mik'a shi kurkuku daga nan, tunda kuma k'asa ce da bashi da kowa haka ya zauna har zuwa lokacin da aka zo aka d'ebe su zuwa filin yak'i inda anan ya hadu da mahaifiyarsa.

A wannan ranar Adam yaga k'auna kala-kala ba daga iya mutanen babban gida ba harda sauran gidajen da duk su Kawu suka san akwai wad'anda suka san Ahmadu cewa ga d'ansa ya dawo suzo su ganshi.

Ba kowa ke iya magana dashi ba saboda haka har yara haka yayi ta binsu da gaisuwar hannu ba tare da ya damu da banbancin tsaftar jikinsu da nasa ba, Abinci kuwa har daga can bakin layi haka akayi ta aikowa daga gidaje-gidaje cewa na saukar d'an bature ne...

Al'ada dai irin ta mutanen da wayewar zamani bata ratsa su sosai ba.
Chapter 40 · 0% Book details