Sashe 77
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu 'yan kad'an ne kawai da suka yiwa lamarin wata fahimta suke tunanin akasin hakan, amma ba wani abu ne babba ba, tunda an bamu damar magana yanzu zamu fahimtar dasu gaskiyar komai, zamu gyara musu tunaninsu su san cewa baki da laifi kuma ba zaki iya aikata irin wannan lafin ba..."
Ya d'anyi shiru yana kallonta, yana kallon yadda maganganunsa suke aiki a fuskarta kafin yace.
"Ina so ki kwantar da hankalinki ki bawa kotu amsar komai dalla-dalla kuma kamar yadda kika sani, ki sani cewa duk abinda kika canja komai k'ank'antarsa kotu zata iya ganewa kuma zai iya zame mana k'alubale wajen ganar da mutanen nan gaskiyar labarinki."
Ya rufe bakinsa da 'yan sakanni kafin muryarta ta fito, kuma a cikin amon muryar daga Adam har Alk'ali suka tsinto nasarar amfanin da maganganunsa suka yi.
"Zan fad'i komai kamar yadda yake kuma na sanshi, ban taba gayawa kowa k'arya akan shari'ar nan ba kuma insha Allah ba zan fara yanzu ba."
Adam ya d'an juya ya kalli yanayin fuskar Alk'alin sannan ya cigaba.
"Zaki iya fara gayawa kotu me ye alak'ar ki da marigayiya Hajiya Balaraba?"
Fadeelah ta gyad'a kai har yanzu idanunta na kallon yatsunta tace.
"Ni 'yar d'anta na hud'u ce, ma'ana ni jikarta ce."
"A wajenta kike zaune?
Ko kuwa sai bayan wani lokaci kika koma?"
"Sai bayan rasuwar mahaifina da aka raba gado sannan na koma wajenta."
Muryarta har yanzu a tsaye take sai dai da alamun sassauci.
Daga cikin 'yan kallo, Mairo ta d'auke kwalla da hannun hijabinta, k'ok'ari take sosai kar kukan daya taru a fal a k'irjinta ya fito fili.
"A lokacin kina da shekaru nawa?"
"Na shiga shekara ta goma sha hud'u."
"Yaya alak'arku da ita take bayan kin koma wajenta?"
"Tun kafin in koma wajenta, Hajiya bata k'aunata a dalilin rashin sonta da mahaifiyata tun farko, don haka bayan na koma wajenta hakan bai canja ba."
"Bai canja ba ta yaya?"
"Ta yarda har ta yanke karatuna da shekara biyu ina zaune a gida ba abinda nake sai hidimarta da ta duk wanda ya rab'e ta."
Adam ya had'iye wani guntun yawu kafin yace.
"Me ya faru ranar da Hajiya ta rasu?"
Tiryan-tiryan Fadeelah ta shiga zaiyano duk wani abu da kwakwalwarta zata iya tunawa daya faru a wannan ranar da ta zama sanadin tarwatsa rayuwarta.
Shirun kotun ya amsa da yadda kowa yayi tsit! yana sauraronta.
Adam ya gyad'a kansa bayan ta kai k'arshe, idonsa na kallon dogwayen gashin idonta yace.
"A rayuwar zamanki ta gidan, na tabbata zaki san gabad'aya mutanen cikin Babban gida da kuma iya wad'anda Hajiya tafi mu'amala dasu.
Haka ne?"
Fadeelah ta gyad'a kanta.
"Bayan Aunty Sadiya da take 'yarta, Hajiya tafi shiri da jikokinta akan matan gidan."
"Zaki iya lissafo sunayen wasu daga cikinsu."
Ta sake gyad'a kai.
"Akwai su yaya Fatima, Hadiza, Jamila, Abu, Nafisa da duk sauran irin sa'anninsu da suka yi aure.
A maza kuma akwai Salisu, Auwal, Sa'id, Yakubu, Amadu da kuma yaya Sule wanda kullum yana tare da ita."
An zo gab'ar, an zo inda komai zai kwance...
"Kika ce Sule shine wanda kullum yake tare da ita."
Fadeelah ta sake gyad'a kai.
"Eh suna shiri sosai da Hajiyar kuma ya dad'e bashi da aiki, don haka kullum yana wajenta."
"Idan kika ce shiri wane iri kenan?"
Ta mutstsika yatsun hannunta sannan ta amsa.
"Shiri sosai yadda baya iya tsallake duk wani umarninta."
"Ke kad'ai kika san da hakan ko akwai wad'ansu?"
Ta sake girgiza kanta.
"Ba ni kad'ai bace, ko bak'o yazo Babban gida zai gane hakan, don Hajiya ko aike bata yi sai in yana kusa."
Adam ya gyad'a kansa, ya cije lebbensa kad'an sannan ya fad'i tambayar da zata kaishi ga manufarsa.
"Tambaya ta k'arshe, idan akace miki Sule zai iya cutar da Hajiya zaki yarda?"
K'arashen zancen nasa ya had'o tare da d'agowar idanunta, ta sauke su kuwa a cikin nasa da kallon da yaji kamar k'afafunsa sun k'ara nauyi, sai dai Kutama ya katse maganar dake shirin fitowa daga bakinta.
"K'orafi ya mai shari'a, Lauyan mai karewa na k'okarin shigo da sabon abu cikin shar'iar da ta riga tayi nisa."
Alkali ya girgiza kansa.
"K'orafi bai karb'u ba, lauyan na da ikon yin binciken da zai iya bi ta kan kowa."
Kutama ya koma ya zauna.
Adam ya gyara tsayuwarsa sannan ya maimaitawa Fadeelah tambayarsa, sai ta sauke idanun nata k'asa.
"Babu wanda ya san zuciyar d'an Adam sai Allah, don haka zuciya sab'anin hankali ce zata iya yin abinda baka zato.
Misali, a baya in da wani zai ce min 'yan uwan mahaifina zasu d'ora min wannan zargin har a kawo ni gaban hukuma ba zan tab'a yarda ba."
"Kenan zaki iya yarda in akace miki Sule ya cutar da Hajiya?"
Sai ta gyad'a kanta a hankali.
"Eh zan yarda."
Ya sake gyad'a kansa kad'an.
"Nagode."
Da haka ya juya zuwa teburin zaman lauyoyi, ya kalli Kutama cikin ido yace.
"Your witness..."
Kutama ya mike, da wani faffad'an murmushi a fuskarsa ya taho wajen akwatin tsayuwar masu shaidar, gaban Fadeelah.
"Hajiya Bintu, muna yi miki barka da zuwa wannan kotun daga b'angarenmu."
Sautin muryarsa yasa Fadeelah had'iye wani k'aton abu cikin k'irjinta jin yadda muryarsa ta fito babu ko tsoron Allah kamar wannan ne ganin da yayi mata na farko.
Bata ko kalle shi ba, kuma bata ce komai ba ya cigaba.
"Mun ji dukkan labarin da kika bayar kuma kinyi kokari da baki canja komai ba kamar yadda muke dashi a rubuce, sai dai kuma kin yanke wani waje a labarin baki k'arasa ba, don a yadda muka sami rahoto ance daga wannan ranar rasuwar kika gudu daga Babban gida...
Haka ne?"
Ta mutsikka yatsun hannunta cikin dauriyar kar ta fad'a masa maganganun da basu dace ba a gaban kotu kafin ta d'aga kai.
"Haka ne, daga wannan ranar na bar Babban gida bisa k'arancin shekaruna da suka sa naga hakan ne kawai hanyar da zan tsira, tunda zargin kowa yana kaina ni kad'ai."
"K'arancin shekaru?
Kenan dukkan tsawon shekarun da aka d'auka har zuwa sanda aka gano ki, baki yi hankalin komawa gida ba?"
Ta girgiza kanta.
"Idan har kana da rahoton komai zaka ga cewa a wannan ranar dana bar gida na gamu da hatsarin mota wanda ya haddasa min ciwon kwakwalwa, na manta komai da kowa da na sani, saboda haka wad'annan shekarun nayi su ne cikin ciwo ba wai zaman dadi ba."
Kutama ya gyad'a kansa.
"Ko zaki iya gayawa kotu waye Sule a wurinki?"
Ta gyara tsayuwarta.
"Sule d'a ne a wajen k'anin mahaifina, mahaifinsa ya rasu tun kafin rasuwar nawa mahaifin, don haka a tsari na 'yanuwantaka kamar wa yake a wajena."
"Kenan shima yana d'aya daga cikin jikokin Babban gida?"
"Haka ne."
"Ko zaki iya gaya mana adadin jikokin da suke cikin gidan?"
"Ba zan iya ba, don a wancan lokacin ma na san an doshi mutum saba'in."
"Kuma duk a cikin wannan taron kice Sule kad'ai Hajiya ta tsamo tafi k'auna a cikinsu?"
"Bance shi Hajiya tafi k'auna ba, nace tafi shiri dashi ne saboda kullum yana d'akinta saboda bashi da aikin yi kuma bai damu da fita kamar sauran maza ba."
Kutama ya sake gyad'a kansa.
"Ba kya ganin za'a iya danganta karin maganar 'idan jifa ya wuce kanka, ya fad'a kan uban kowa' game da yarda da kika yi cewa Sule zai iya cutar da Hajiya?"
Tun da Kutama ya fara tambayoyinsa har zuwa k'arshe, Adam bai katse shi ba ko sau d'aya, yayi shiru kawai yana sauraran komai, kuma cikin sa'a Fadeelah bata bashi wata k'ofa da zai d'ago wani abu ba har ya gaji ya zauna.
Shaida ta biyu da Adam ya kira Kawu Bashir ne wanda yazo ya fad'i nasa b'angaren game da rayuwar Fadeelah a Babban gida da kuma rasuwar Hajiyar, sai dai duk ba wannan ne mai amfani ba, Adam yayi masa wad'annan tambayoyin ne don a hankali su k'araso ga tambayar da tafi kowacce muhimmanci.
"Zaka iya yiwa Kotu bayanin waye Sule?"
Kawu Bashir ya gyara tsayuwarsa.
"Sule d'an wajen K'ani na ne da muka had'a uba d'aya, yana zaune ne a b'angaren mahaifinsa daya rasu tare da babarsa da k'annensa mata hud'u kafin ayi wa guda d'aya aure."
"Bayan shirin da kowa ya sani tsakaninsa da Hajiya, akwai wani abu da ka sani ya tab'a shiga tsakaninsu?"
Ya d'anyi shiru kafin ya amsa.
"Eh toh, gaskiya babu wanda ya tab'a jin kansu, don ko bayan rasuwar mahaifinsa ma da ta hana a raba musu gado shi Sulen baice komai ba, yana yi mata biyayya sosai shi yasa ma tafi yarda dashi fiye da kowa."
Sanda Kawu Bashir yake wannan bayanin, idanun Adam na kan Alk'alin nan yana son ya tsinto abinda yake fata a fuskarsa.
Bayan Kawu Bashir, Habiba ce tazo a shaidar Adam na gaba, 'yan k'alilan d'in shaidun daya tsara zai rufe shari'ar nan dasu. ta tsaya da kyar cikin akwatin, saboda ciwon k'afarta da a yanzu ya tsananta.
Kamar yadda ya fara da lallashin Fadeelah a d'azu, haka ma ya yiwa Habiba, ya k'are da cewa.
"...ki kwantar da hankalinki sosai, ki bawa kotu amsar da kika sani dalla-dalla, ba ke kika kashe Hajiya ba na sani...
Don haka ina so ki bani dama mu baiyanawa kotu hakan."
Wad'annan kalaman su suka d'an kwantar da hankalin Habiba daga k'ink'inar da ta fara a farko amma duk da haka bata saki jiki sosai ba, don ta san abinda ya fad'a karya ne, ita ta kashe Hajiya ba wani ba.
Bayan wasu 'yan tambayoyi da mafi yawanci gaskiya ta fad'a, Adam ya tafi ga tambayar da zata amfane shi.
"Ina so ki tabbatarwa da kotu cewa kamar yadda kowa ya sani tun daga farko akwai rashin jituwa tsakaninki da Hajiya mai rasuwa."
Idanunta a zare kuma sun zurma ta kalle shi kafin ta juya gefe kuma ta kalli Alk'alin sannan ta dawo da idonta kansa.
"Eh, eh haka ne yallabai."
Bai tsaya ba ya cigaba kai tsaye.