Sashe 47
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin kuma ta fara jin kanta na sarawa da wani irin ciwo mai rad'adi sannan ta kula an soka allurar k'arin jini cikin hannunta na hagu wanda yayi mata nauyi sosai.
Da dukkan karfinta ta janyo kanta ta juya shi d'aya b'arin, anan ne idanunta suka ci karo da d'aya daga cikin tambayoyin dake shirin d'arsuwa ranta a lokacin.
Mami Safiyya.
Tana zaune kan wata kujera mai zaman jinya, fuskarta nad'e take cikin katon mayafi, sannan da littafin addu'o'i a hannunta tana karantawa, nad'in kanta iri d'aya ne sak! da wanda take yi sanda suna can k'asar America, hakan yasa kwakwalwarta tayi tunanin ko tunaninta baya ya koma da ita zuwa wani lokaci can da aka kwantar da ita a asibiti a washington, amma kiran sallar la'asar da aka fara a lokacin sai ya k'aryata zarginta, America babu masallaci cikin asibiti da zaka ji kiran Sallah haka.
Hakan kuma yasa a hankali kwakwalwarta ta tuna mata da duk abinda ya faru kagin sumanta, abinda ya faru ranar kamun bikinta daki-daki har zuwa k'arshe.
Amma in haka ne ina Mairon da ta gani a wancan lokacin?
Ina Aunty Sadiyar?
Ina sauran 'yanuwan Mami suke zaune su kad'ai a wajen nan?
Sai ta bud'e bakinta da kyar ta kira sunanta.
Da sauri kuwa Mamin ta d'ago da kanta, ganin idanunta a bud'e yasa ba shiri ta rufe littafin addu'arta ta taso, ta kamo hannunta d'aya da bashi da allurar ta rik'e cikin nata sannan tayi mata murmushi, wani murmushi da Fadeelah ta lura mai cike da taraddadi ne.
"Deelah kin farka? sannu kinji, yaya kike jin jikin naki?"
Kanta ciwo yake yi cikin azabar da take jin kamar zai dagargaje, amma maimmakon ta amsa sai tace.
"Da gaske ne naga su Mairo Mami?
Da gaske ne abinda ya faru ba mafarki nayi ba?" Muryarta da kyar take fita sanda ta tambaya.
Mamin ta d'anyi shiru kamar baza ta amsa ba kafin tace.
"Su kika gani deelah ba mafarki kika yi ba, bari a kira likita ya duba ki, tun jiya ake zaton farkawarki dama."
Jiya?
Fadeelah tayi tambayar cikin kanta.
Tun yaushe take kwance kenan?
Sai kuma ta tuna da d'aurin aurenta wanda a washegarin kamun ya kamata ya kasance, me ake ciki yanzu?
An d'aura d'in?
Ina Al'ameen d'in?
Ina su Daddy da duk sauran suke?
Ina su Mairo ma?
In da gaske ne sunzo ina suka tafi kuma?
Me yasa daga ita sai Mami?
Sai dai a lokacin da take wa kanta wad'annan tambayoyin, Mami ta riga ta saki hannunta ta nufi wajen wannan k'ofar data gani a rufe.
Kuma maimakon ta bud'e ta ta fita, sai taga ta kwankwasa kawai kamar mai jiran a bud'e su ta waje, bud'ewar kuwa akayi don taga sanda handle d'in ya motsa sannan k'ofar ta bud'e.
Wanda ya lek'o daga waje, ganinsa ne ya tattaro dukkan wani sauran azabar ciwo na duniya da baya faruwa a cikin kanta ya d'ora mata shi.
Wani murtuk'ek'en k'aton d'an sanda ne sanye cikin kakinsa da kuma bak'in gilashi, kalar fatarsa kad'ai ta kusa kamo ta kalar kayan jikinsa, duk da tsawon Mami amma sai ta zama kamar wata bebin roba a gabansa.
"Yallab'ai ta farka, ko zaku iya kira mana likita?"
Bakin Fadeelah ya bud'e a lokaci d'aya, gadinsu ake yi?
Shi yasa bata ga kowa ba sai Mami kad'ai?
To me yasa za'ayi gadinsu?
Me suka yi...?
Ko kuma ita me tayi?
Kawu Yahya ya gyara zamansa kan kujerar da yake kai sannan ya kalli Daddy yace.
"Alhaji Ahmad, ina ga tun jiya muka gama yi maka bayanin cewa lauya zaka samo ka gaya masa duk wad'annan bayanan naka don mu duka nan manyanmu ne suka aiko mu bamu da iko akan lamarin nan, kuma, da zarar ta farka zamu tafi da ita, kuma ba jin akwai abinda zai dakatar da case d'inta shiga kotu, don haka nake ganin neman lauya shi ya kama ka a yanzu in har kuna son kare ta ne.
Daddy yayi ajiyar zuciya, sannan ya kalli inda suke zaune, cikin wani hotel da suka kama tun zuwansu garin Abuja kwanaki biyu da suka wuce, a safiyar da iyalinsa suka wayi gari a asibiti cikin tashin hankalin abinda ya faru gurin bikin Fadeelah, basu k'ara ganin matar data tada ballin a lokacin ba amma sunyi Imanin cewa ita ta kira wad'annan 'yanuwan nata da suka bada duk wata shaidar cewa Fadeelah 'yaruwarsu ce kuma suka kafa suka tsare cewar da zarar ta farka zasu wuce da ita ne can garinsu inda aka dad'e da mik'a case d'inta kotu cewar ta kashe mahaifiyarsu, wadda take kaka a gurinta.
Wai kisa!
Ta yaya Fadeelah zata iya kisa a rayuwarta?
Ita d'in da ba cikakkiyar lafiya ne da ita ba?
Yayi musu bayani da dukkan iyawarsa akanta amma babu alamun ma suna saurarensa balle su fahimci abinda yake son nusar dasu.
Babban abinda ke bashi mamaki shine ya yarda cewa 'yanuwanta ne, 'yanuwan mahaifinta ma a tak'aice amma ta yaya zasu iya rufe idonsu su dinga fad'ar wadannan abubuwan akan 'yar d'anuwansu?
Gashi sun k'i yarda su gaya masa komai akanta balle ma ya sami wani abin.
"Haka ne, Na fahimta kuma Nagode."
Ya yanke shawarar barinsu kawai don babu amfanin zaman, amma sai d'ayan daya fahimci sunansa Sulaiman ya tsaida shi.
"Idan zan baka shawara ka d'auka Alhaji Ahmad, ka rabu da case d'in yarinyar nan kawai, don kamar yadda ka fad'a ka tsince ta ne da girmanta da kuma wayonta, kuma d'an mutum a yanzu ko kai ka raine shi baka shaidarsa.
Mu san Bintu tun tana tsumman goyo don haka mun fika sanin abinda zata aikata da wanda baza tayi ba."
Idan har ya d'auki wannan shawarar suka rabu da al'amarin Fadeelah, to a baiyane yake cewa rayuwar gidansa baza ta tab'a dawowa daidai ba, don ya tabbata bashi kad'ai ba, har Mami da take Uwa banbancin da take ganin Fadeelah da Zahra na haihuwa ne kawai amma sun riga sun karb'eta cikinsu, don wasiyyar mahaifiyarsa ta k'arshe a duniya zancenta ne, ta yaya kuwa zai dauki wannan shawarar su hakura da ita suna ji suna gani?
Tunda Daddy yake a rayuwarsa bai tab'a alfaharin rashin samun 'yanuwa ba sai a lokacin da Kawu Ibrahim ke wannan zancen, don ji idan har d'anuwa zai rufe idonsa ya dinga irin wannan abin akan d'iyar d'anuwansa da baya duniya a lokacin, to meye amfanin 'yanuwantakar?
Gaskiya ne da ake cewa DANGI suna suka tara!
Lokacin da ya koma cikin asibitin da a yanzu ya zama matattarar iyalinsa, ya tarar Hadiza, yayar matarsa tazo tare da su Zahra da a yanzu suke wajenta, a hannunsu kulolin abinci ne kala-kala amma 'yansandan nan uku da aka sa gadi sun hana su k'arasawa ma d'akin da Fadeelan take balle su sa ran basu.
Tun daga ranar Kamun nan taron bikin ya tashi gabad'aya, mutanen da suka zo washegari d'aurin aure haka akayi ta binsu da hak'urin cewa ga abinda ya faru an fasa sai komai ya lafa tukunna, don Al'ameen ya tubure cewa bai yarda a d'aura auren da Fadeelah a cikin wannan halin ba.
"Barka da zuwa Daddy."
Muryar Al'ameen d'in dake sanye cikin wata doguwar jacket ta fad'a daga gefe.
Ga duk ya sanshi kallo d'aya zaiyi masa ya lura cewa ya canja, idanunsa sun zurma kamar zasu koma raminsu saboda tashin hankalin da ya ke ciki kala-kala, bayan wannan al'amarin na Fadeelah daya faru, a can America ya san mahaifiyarsa na dab da tsine masa albarka ta kuma yakice shi daga inuwar 'ya'yanta in har ta san ba ta'aziyya suka zo yi Nigeria ba, watakila harda wannan dalilin ne ya bashi k'arfin gwiwar cewa a dakatar da d'aura auren sai taji sauki tukunna.
Sauk'in da a yanzu bayan ya fahimci komai yake hango wahalarsa, don tun sanda ya fara sanin Fadeelah, ya santa da son warkewa daga ciwonta har ta tuna rayuwarta ta baya wadda ta had'a da 'yanuwanta.
Ashe reshe ne zai zo ya juye da mujiya, maimakon 'yanuwan nata su karb'eta a yanzu da komai ya baiyana, sai suke kokarin cutar da ita da kansu.
"Barka dai Al'ameen, ka dawo?"
Daddyn ya tambayeshi don sunyi waya a d'azu yace dashi zaije raka mahaifinsa da sauran 'yanuwansa da suka zo d'aurin aure airpot zasu koma, don yau kwanansu biyu kenan a garin, yanzu daga shi sai abokinsa Kamal ne kawai suka rage.
"Eh na dawo Daddy, ka same su d'in?"
Kafin ya bashi amsa, su Aunty hadizan suka k'araso inda suke tsaye, bayan 'yar gajeriyar gaisuwa, Aunty Hadiza tace.
"Wata Nurse ta shaida mana cewa Fadeelan ta farka har likita ya shiga wajenta."
Hakan labari ne mai dad'i, amma ga Daddy bai masa dad'i ba, don daga yadda ya lura da mutanen nan, ya san da zarar Fadeelah taji sauk'i baza su b'ata wani lokaci ba zasu tafi da ita.
Bayan su Aunty Hadiza sun koma sun zauna ne ya kalli Al'ameen yace.
"Basu saurare ni ba kamar jiya Al'ameen, sunce an riga an shigar da zancen kotu da dad'ewa don haka sai dai mu d'auki lauya kawai."
Ga mamakinsa sai kawai yaga Al'ameen ya gyad'a kansa yace.
"Kar ka damu Daddy, na san hakan zasu ce dama, muna ta fafutukar licence din Nigeria ni da Kamaal, sannan za'a turo min da takarduna nan da kwana biyu insha Allah komai zai daidaita."
Da mamaki Daddy yace.
"Al'ameen kai fa lauyan kamfani ne kawai, ta yaya zaka d'auki shari'ar kisa?"
"Kowanne lauya ya iya komai Daddy, zab'ar b'angaren aiki ra'ayi ne kawai, kuma na tabbata case d'in nan ba zaiyi wuya sosai ba zamu tsayawa Fadeelah ni da Kamal insha Allah."
A lokacin da yake fad'in hakan ne gefen idonsa ya hango masa wannan matar mai kama da Fadeelah sak! da aka ce dashi yayarta ce, tana zaune a can kujerar data zama makwancinta tun kwanaki biyun da aka kawo Fadeelah asibitin, ya lura bata taka k'afarta waje ko sau d'aya ba, anan take kwana take tashi tare da d'anta, sai dai mijinta yazo da d'aya 'yar ta su ya kawo mata abinci, da daddare kuma su koma, a yanzun ma yana zaune a gefenta rik'e da d'an nasu yayin da ita kuma take cusa abincin da ya zuba mata a bakinta.