← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 95

Sashe 49

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dole ne muyi tunani akan lamarin nan Salame, wallahi jiya ko runtsawa banyi ba saboda tsananin mamaki, ace wai har ni zan yiwa Malam magana yasa k'afa ya tsallake ni ba tare da amsa ba, gashi labari ya baza koina cewar kotu za'a shiga.

Ni na rasa wane irin k'ulafuci ne da duk wad'annan shekarun bai ci ace sun hak'ura da mutuwar wannan tsinanniyar tsohuwar ba, Shu'aibu jiya har wani d'aga jijiyar wuya yake a tsakar gidan Asibi wai a daman ba tsayawa akayi da nemanta ba, kuma su Kawu D'anjuma basu janye shari'ar ba don haka dole ne aje kotun."
Salame ta tab'e bakinta.

"Wallahi har da ke kanki kika jawo wannan matsalar Habi, a daren da akayi abun wane irin baki ne ban baki ba kan muje a kashe yarinyar itama, amma kika tsaya cewar
da matsala za'a iya ganinmu, sai gashi ita ba wanda ya ganta ta samu hanya ta salallab'e ta gudu.

Sai a yanzu da kike tunanin zaki fara cin duniyarki da tsinke an gano ta komai ya dawo sabo."
"Ajiye batun cin duniya da tsinken nan Salame, kina gani Malam tun yanzu ya fara canja min fuska, tuntubarsa na fara yi kan maganar janye shari'ar nan amma wallahi 'ta tafasa, sauke' bai ce dani ba, kuma ke kin san uwar wahalar da muka sha zuwanmu Niger kafin a iya sake d'aure tunanin sa da na su Kawu D'anjuman amma ace shekaru basu rufa ba lamari ya fara rawa? yanzu ko yaya aka samu matsala a wannan gab'ar yaya kike gani?

Kin san dai bani da damar komawa Niger a wannan rikicin."
"Babu ma zancen komawa, don na gaya miki da idona naga aikin da Jaribi yayi kuma har gobe yana ci, don haka kautar da batun Malam a gefe, ina ga kai tsaye wajen Kawu D'anjuman zaki je mu san yadda akayi yasa baki don a janye shari'ar."
Habiba ta shiga kad'a kafafuwanta da d'aya ke kan d'aya sannan ta girgiza kanta, idonta na kallon jikin had'add'en labulen falon nata tace.

"Kayya Salame, wannan ba mafita bace don a tunani na fa har an basu rana, yaushe zai saurare ni."
"An saka rana?

Bayan yanzu haka ma ance ita yarinyar tana asibiti?"
"Eh, tana asibiti, haka su Yahyan suka ce da suka yo waya, tana can tare da wannan banbad'addiyar 'yaruwar tata da kuma mutanen da suka rik'e ta."
"Yo wai daman tare suke a can da Mairon?"
"Haka dai Sadiya da ta dawo take fad'i, amma su su Yahyan da suka je sunce tace wai itama a ranar da Sadiyan ta ganta itama taje nemanta, amma Kawu D'anjuma ma yace kar su bi ta kanta, don har yanzu ba gida ta dawo ba."
Salame ta girgiza kanta.

"Al'amarin ne a cakud'e wallahi, don kin san abinda yafi d'aukar hankalin mutane a zancen ma da akace wai har an fara yinin bikinta a can Habujan."
"Yo yarinyar da akace har k'asar waje ta taka tare da marik'an nata me yafi wannan mamaki?

Sannan wanda zata aura d'in ma sunce Balarabe ne daga dangin marik'an nata."
"Wannan ba mamaki yaga yaluwa mai irin nasu yalolon gashin ne, amma su dai masu rik'e tan ne suka yi kokari, ka tsinci d'a a titi ka jashi jikinka haka?"
Ganin hirar tasu na shirin karkata kan wani abun da ba shine a gabanta yasa Habiba ta gyara muryarta tace.

"Salame yanzu duk ba wannan ba, kin san Allah jikina yana bani wannan yaron d'an gidan Ahmadun nan da yazo zasu ce ya karb'ar musu shari'ar tunda shima lauyan ne, kuma daga ganin k'irarsa wannan ba mutunci zaiyi ba ya rayu cikin turawa, tsorona Allah-tsorona Annabi Salame d'an nan zai iya gano abinda muka shirya."
"Habi ko shi maye ne bana jin zai iya gano komai a lamarin nan, tunda ko a wancan lokacin kowa ya yarda babu hannunki a ciki, sannan ba mahalukin daya ganta sanda ta shiga b'angarenki karb'ar kokon, k'arewa ma tsohon da ya samo mana gubar ya bar garin nan, watakila ma ya mutu can inda ya tafi.

To saboda Allah gaya min me wani zai iya ganowa anan?"
"Rigakafi yafi magani dai, Ni yanzu kiran dana yi miki k'auyen Kaduna zaki raka ni gobe, can wajen bokan daya fara yi min aiki akan Malam (mijinta) mu samu ko yaya ne a hallaka yarinyar nan tun yanzu a can asibitin da take ba tare da wani zargi ya d'arsu akanmu ba."
"Kin yarda da aikinsa ne?

Naga ko shekara ba'a rufa ba wancan karon Malam ya daina baki kudin ribar gonarsa."
"Salame harkar nan fa sa'a ce kawai, naga gashi yanzu ina gaya miki aikin na Niger d'in ma ya fara rawa, da mun take ta kawai shikenan!"
Da wannan zancen washegari Habiba da Salame suka buga sammako kan hanyar Kaduna ba tare da wani mahaluki ya san da fitarsu ba.

A B U J A.

A hankali duhun dake cikin idonta ya yaye, haske tar!

Ya maye gurbinsa tare kuma da shigowar muryoyi, sai tayi saurin maida idon nata ta runtse sakamakon shigowar hasken da sara har cikin kanta, bayan wani lokaci kad'an ta sake bud'e su.

Wata iska mai sanyi ta zarce har cikin k'irjinta, hakan ya harba wani tsini mai zafi kirjin nata, ta kasa banbance zafin rashin jin iska na tsawon lokaci ne ko kuma zafin ciwon da take ciki ne.

Hoton d'akin mai rawa ya shaidawa kwakwalwarta cewa a asibiti take, asibitin dai da ta farkavwancan karon ta ganta a cikinsa, sai dai wancan d'akin da kuma wannan da banbanci, tun yaushe aka kawota nan kenan?

Tsawon wane lokaci aka d'suka daga waccan farkawar tata zuwa wannan?

Ba zata iya tuna sanda ta bar haiyacinta ba, abu na k'arshe da zata iya tunawa shine Mami ta fad'a mata 'yanuwata suka kawo 'yan sandan da ta gani suna gadinsu wancan karon, daga nan tunaninta ya hargitse, abubuwa game da rayuwarta ta baya suka shi dawowa cikin kanta, kwakwalwarta na dawo mata da su daki-daki cikin kanta tare da wani irin matsanancin ciwo dake shaida kwancewar duk wani k'ulli na mantuwa cikin kanta.

Tun a baya, likitanta ta America, Dr.

Florence ta riga ta shaida mata cewa kwakwalwarta ta fara taka matakin warkewa wato 'Retrival stage' matakin dake nufin duk sanda taci karo da wani abu daya danganci rayuwarta ta baya, kwakwalwarta zata yi reacting akansa ta hanyar jin ciwo ko kuma ta saka ma ta fita daga haiyacinta.

Ganin 'yaruwarta Mairo da tayi da kuma Sadiya a baya, shi ya hargitsa kwakwalwarta da ciwon daya haddasa sumanta a wancan lokacin, amma a yanzu da Mami ta shaida mata abinda ya zamto sanadiyyar faruwar abubuwa da yawa na rabin rayuwarta sai komai ya sake hargitse mata da wani irin ciwo da kuma rud'ad'i, ciwo irin wanda ke shaida cewa alamu ne na warkewar duk wani sauran duhu dake cikin kwakwalwar tata, don ji take kamar dukkan azabar duniya aka tattaro aka saka cikin kanta.

Komai na rayuwarta ta baya ya dawo tar cikin idanunta, tun daga yarintar ta da zata iya tunawa har zuwa kan duk wani hargitsi daya faru akanta, tana iya tuna komai kamar a sannan suke faruwa, komai ya had'a tun daga farko har k'arshe, lokacin da tayi wata tafiya mai nisa a cikin duhun titunan dake bayanta, jikinta na rawa ta cikin cukurkudadden hijabinta.

Da sanda gari ya waye ta isa tasha ta hau motar Kano, da sanda motar ta gama cika suka fita daga tashar suka hau kan titi, da sanda bayan tafiya mai nisa motar tasu ta tarwatse a tsakiyar titi... k'arshen rayuwarta ta farko kenan!

BAYAN TA MUTU kuma, sai ta tsinci kanta a asibiti inda bayan Nurses d'in da suka zo kansu ita da sauran mutanen motar dake kwance cikin jini, ita aka sallame ba tare da wani dubawa ba sai don ganin ko kwarzane babu a jikinta.

A sannan ne kuma ta fahimci cewa ba ita ce ta mutu a wancan lokacin ba, kwakwalwarta ce!

Kwakwalwarta ta mutu don ta fita daga asibitin nan ne babu ilimin sanin wacece ita kanta balle koda mutum d'aya a duniya, sai sanin yanayin mu'amala na rayuwar al'umma kawai!

Abinda ya rik'e ta tsawon kwanaki tana walagigi a cikin garin Kano kenan ba tare da ta san inda ta nufa ba.

Ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba, ruwan sama yasha yi mata d'anbanzan duka tsakar dare saboda rashin ko da wajen fakewa ne ma balle makwanci, hakanan ba sau d'aya ba sau biyu ba tasha yini ta kuma kwana da yunwa sakamakon rashin sanin hanyar da zata nemi abinci.

A yadda idanunta ke nuna mata watakila tayi kusan wata guda a hakan don tana iya tuna lokuta da yawa da take cikin mawuyacin hali kafin wata k'addarar tazo ta gifta.

Daddy ya kad'eta a mota lokacin da ya d'auko hajiyarsa zai kaita asibiti check-up na ciwon zuciyarta, daga nan suka d'auketa zuwa asibitin da suka nufa, inda anan ne bayan d'inmbin gwaje-gwaje da tambayoyi aka tabbatar musu cewa kwakwalwarta ta bugu da wani abu ne kuma ta manta dukkan rayuwarta ta baya, abinda ya sanya tausayinta a zuciyar hajiyar Daddy kenan ta yanke shawarar d'aukarta ta rik'e ta a wajenta, wanda ba'a yi hakan ba sai da yardar hukuma da kuma cike-cike wajen 'yan sanda sannan ta koma wajenta da zama.

A cikin shekara guda, tayi rayuwa da Hajiyar Daddy cikin dad'i da aminci, duk da cewa rabin lokacin ta shafe shi ne a asibiti da taimakon wata ma'aikaciyar hajiyan mai suna Ladi, inda suka yi ta zaryar ciwonta da yake yawan tashi a sannan, amma a d'an lokacin nan ta kyautata zamanta da hajiyar iya iyawarta ta yadda lokacin da ciwon zuciyarta ya tashi har ta kai an kira Daddy dake can America, wasiyyar da ta fito ta k'arshe daga bakinta shine ta dank'a amanar cigaban kulawarta a hannun Daddyn.
Chapter 49 · 0% Book details