← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 95

Sashe 75

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da take a rayuwarta bata tab'a ganin naci irin na matar ba, ko kad'an rashin kulatan da take yi baya damunta, haka za tayi ta binta kullum da labarai marasa kan gado wanda ita bata fahimtarsu, a yau har sawa tayi aka canja mata aiki daga b'angaren surfen da aka kaita zuwa kicin, babban aikin da ta lura kowa ke rububinsa a kurkukun, don aikinsa a sauk'ake yake an riga anyi komai kan ya k'araso kicin d'in kuma abinci sai dai mutum ya ture shi.

Don haka sauk'in aikin da ta samu a yau yasa kantar hannun nata ta d'add'ago har da sab'a.

Ta d'ago da fuskarta ta kalli Matron d'in dake tsaye akansu, akwai banbanci mai yawa tsakanin Fadeelan da ta shigo cikin kurkukun 'yan kwanakin baya kad'an da kuma yadda take a yanzu, ta rame, tayi duhu, lallausar sumar kanta ta dunk'unk'une saboda rashin gyara, leb'b'enta duk yayi sab'a saboda bushewa sannan ga wani k'aton tabo a saman girarta na ciwon da taji da k'arfen gado.

Zuciyarta ta maimata abinda Mstron d'in ta fad'a sannan tasa jan fenti ta soke shi, tayi zaton ta sallami Kutama da kalmomin da ba lallai ya sake waiwayarta ba, me kuma ya sake dawo ya gaya mata?

K'ara tallata mata muhimmanci shaidun wajensa zaiyi ko kuwa gaya mata za
i yi ya saukar da farashinsu?

Wai lauyanta...

Lauyanta, ta sake maimata kalmar a zuciyarta, haka ya kira kansa ma a wancan zuwan nasa na farko, ya yaudari hukumar kurkukun suka shigo dashi wajenta ya kuma yaudare ta, ta kai kanta gabansa...

Amma ba'a cizon mumini a rami d'aya, ba dai k'afarta ta sake takawa taje wajensa ba, don bata fatan ko a kotun idonta ya sub'uce ya sake kallonsa.

"Bana buk'atar ganinsa Matron Salame, ace masa kawai ya tafi."
"Saboda me?

Kina sane kuwa cewa jibi za'a sake zaman shari'arki?

Ko wajen nan ya fara yi miki dad'in zama ne?"
Wata doka ce a kurkukun cewa ba'a k'in amsa maganar Matron, don hakan kad'ai zai iya jawo maka yini guda a d'akin duhu, d'akin da zaka ji kamar an maida kai cikin mahaifiyarka ne saboda duhu da kuma rashin iskarsa, ba don haka ba da Fadeelah tayi shiru kawai, don sabon abinda ya shiga cikin jerin abubuwan data tsana shine 'Rashin son magana'.

Ta girgiza kanta.

"Bana buk'atar ganinsa ne kawai."
Sak!

Wad'annan kalaman su Matron Salame ta koma ta maimaitawa Adam.

Shima ya maimaita su a zuciyarsa ya kuma maimaita su a fili.

Fadeelah bata buk'atar ganinsa... bata buk'atar ganinsa?

"A ina take yanzu?"
Kai tsaye ya tambayi Matron d'in wadda bata kawo komai ba ta amsa.

"Suna Harabar masallaci."
Ai tana rufe baki, bai jira komai ba ya shiga tsallake tarin fararen kujerun dake wajen ya nufi k'ofar zata kaishi cikin kurkukun, k'ofar da zata kaishi wajenta!

Matron salame na k'okarin dakatar dashi amma bai ko saurareta ba, ganin da gaske yake shiga zaiyi yasa tayi gaba da sauri, amma cikin rashin sa'a sai tayi tuntub'e da wata kujera ta fad'i har k'asa, k'ashin k'afarta ya gurd'e nan take!
****
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Basu barshi ya ganta ba.

Bai samu ya k'arasa inda zai ganta ba don kamar yadda ya kwana da sani ne, kowacce kurkuku a cike take da masu tsaro kota'ina da mutum bai isa ya k'arasa ciki ba, musamman wajen kwanan d'aurarrun, kuma a lokaci irin na dare.

Ya rufe idonsa ruf!

Gashin sama ya hard'e da na k'asa, lalube kawai yake a cikin kansa tun bayan dawowarsu gida, yana neman wannan dauriyar da yayi amfani da ita a baya, dauriyar da yayi shekara guda cif yana yawo da taswirar idanunta a cikin tunaninsa, don ya yarda wannan dauriyar ita kad'ai ce zata iya kwantar da hankalinsa a yanzu.

Kwana guda ba komai bane akan shekara guda.

Ya ayyana hakan sannan ya bud'e idanunsa a hankali daidai sanda iskar daminar dake shirin shigowa ta kad'a a harabar wajen, k'arfe d'aya ne na dare a lokacin, don haka garin na Zariya yayi bak'i da kuma shiru, Musamman a irin wajensu da babu mutane sosai, ya tabbata su Sa'id ma sunyi nisa cikin bacci don tun bayan da suka yi jam'in sallolin dake kansu, ya lalubi hanyar d'aki ya shige, amma shi har yanzu ko gezau idonsa bai yi ba.

Ya riga ya saba, duk sanda yaci karo da case mai sarkakiya, tarin tunanin cikin kansa baya tab'a barinsa ya runtsa, balle kuma irin wannan case d'in daya shafi wani sabon b'ari na rayuwarsa (Dangi) da kuma yarinyar da a yanzu yake jin zai iya komai don kare ta.

Ya mik'a hannunsa na hagu ya tsiyaya cikon kofi na k'arshe daga k'aton kwalin lemon dake gabansa.

Jibi ne.

Jibi ne ranar daya maka ta k'arshe a wannan shari'ar, kuma baya fatan daga jibin nan daga 'yan kallo har Alkalin wani ya k'ara takawa cikin kotun nan da sunan shari'ar Babban gida, ya riga ya tsara cewa daga gobe zai tattara komai ya kuma rufe komai d'in, sannan ya yarda har cikin zuciyarsa Allah zai taimake shi akan hakan.

Ya kai kofin bakinsa, ya kurb'i lemon, sanyin ya ratsa cikin k'irjinsa, sannan ya maida idanunsa ya sake rufe su, d'aya bayan d'aya jan hasken dake cikin idanun ya shiga haska masa abinda zai faru a gobe, jigo a ciki sune...

Ikara, Kawu Ibrahim, Sule..

Anna!

Iya wad'annan sunayen kad'ai yake hangowa.

Bai san cewa har da nasa sunan a cikin wad'anda k'addara ta tanadar ba!
****
WASHEGARI, 9:00 AM, IKARA.

"Babu inda zaki."
Kawu D'anjuma ya maimaita hakan karo na uku tun bayan shigowar Sadiya wadda ke magiya akan ya barta ta koma Abuja gidan aikinta.

"In kinga kin bar garin nan, to tabbas an gama shari'ar nan ne kuma komai ya lafa."
Sadiya ta muskuta ta sake muskutawa, ba fa zai yiwu ba, ta ayyana a ranta.

Yau kwanan maganin da ta karbo a wajen boka shida kenan kuma ya riga ya shaida mata in har ya kai wani satin ba zaiyi aiki ba sai dai ta dawo ta sake karb'ar wani.

Yo ina kuma taga wani kud'in bayan kusan duka abinda ta samu ta nad'o a gidan Hajiyar ta kai masa da alk'awarin in har ta samu ta ajiye k'ullin maganin da ya bata a makwancin Alhajin Hajiyar, to shikenan ba zai k'ara mararin wata mace a duniya ba sai ita, kuma ko bai saki Hajiyar ba, to tabbas ne ita sai ya aure ta.

Ta yaya kuwa zata zauna akan wata dokar Kawu D'anjuma tayi wasa da damarta, in har yana tunanin yadda ya tsaida abubuwa da yawa a gidan da wannan zancen nasa na sai 'bayan an gama shari'a, haka itama zai tsaida tata rayuwar to kuwa bai isa ba, yayanta ne shi amma a yanzu da take gab'ar cimma k'udirinta, bata tunanin ko ubanta ne ya fito daga kabarinsa ya hane ta zata saurare shi.

Fassarar tunaninta d'aya ce da karin maganar...

Tayi nisa bata jin kira.

Ta sake gyara zama.

"Kawu gaskiya wannan ba hukunci bane, Hajiya fa ta rasu tsawon shekaru kenan ba wai zaman makokin ake yanzu ba, don haka bai kamata kawai don ana shari'ar bincike ace za'a tsaida abubuwa ba ciki kuma har da aikina, mutanen nan ma ai sun min mutunci, yau watana d'aya da d'oriya fa kenan a gida, inda wasu ne da tuni sun nemi wata sun rabu dani.

Ya kamata a duba gaskiya."
"To su nemi wata mana, ai ba su kad'ai ne gida a habujar ba, duk sanda kika koma ba zaki rasa wani wajen ba.

Karki manta cewa tun da fari fa ni ba son wannan aikin naki nake ba."
Yana rufe baki kuwa karaf ta amsa.

"Kawu zancen son aiki yanzu bai taso ba, an riga an rufe maganar nan tun farkon tafiyata, jikina zan bautar ba na wani ba don haka ba ruwanku."
Kawu D'anjuman ya d'anyi jim!

Ganin yadda ta amsa masa maganar gatse-gatse ba kamar yadda ta saba a baya ba.

Sai ya gyad'a kansa kawai sannan ya k'ara jaddada maganarsa.

"Babu inda zaki sai an gama shari'ar nan Sadiya, inda ke wata mai hankalin ce ba sai an gaya miki ba, kishin mahaifiyar ki kad'ai ya isa yasa ki gane hakan, amma na fahimci tun bayan aurenki na biyu kwakwalwarki ta toshe, in banda duniya babu komai yanzu a gabanki."
Maganar tayi mata zafi duk kuwa da ta san hakan ne, amma sai ta kawar ta hanyar yin wani guntun murmushi kafin ta bashi amsar da ta shayar dashi mamaki.

"Ai kuwa k'arya ne ace bana kishin Hajiya wallahi, naga waye ma ya farfad'o da shari'ar in bani ba, ina ce ai daga Bintun har 'yaruwar tata ni na gano su a can Abujan, don haka kuwa in ba'a yabawa aikina ba ai ba'a zageshi ba.

Sannan duk toshewar kwakwalwata Kawu ai ba ni na kai shari'ar nan kotu ba, bani nayi abin kunyar kai 'yar d'anuwana kotu ba, iyakata shaida.

Sannan kuma na tabbata babu sunana a wad'anda za'a nunawa Alhaji (Tana nufin mahaifinsu) a matsayin masu tada husuma bayan ransa.

Tana fad'in haka ta mik'e, tayi hanyar fita, bata ko kalli fuskarsa ba dake cike da mamakin nuna masa ainihin halinta da tayi, dama biyayyar da take masa a da fiye da rabi saboda abin hannunsa ne ba wai matsayinsa na yayanta ba, a yadda take hango kanta a yanzu kuwa ita mai arzikin kanta ce.

To meye ma?

Ai manta wannan 'yar maganar zaiyi da zarar ta kawo Alhajinta a matsayin manemin aurenta.

A k'ofar d'akin taci karo da Yahya, sarai ta san zancen shari'a yazo yiwa Kawu D'anjuman don haka bata ko kalle shi ba ta zura wani kwancen takalmi mai tsini da Hajiyarta ta bata sannan ta nufi hanyar barin sashen, daga Bintu har Hajiyar da aka kashe yanzu basa gabanta...

Wanda yake da rai ko kuma abin mora ai shi duniya ke yayi ta ayyana hakan a ranta tana tafe tana gurd'ewa saboda yadda tsinin takalmin ke shigewa cikin k'asa, lissafawa kawai take da taje d'aki zata buga wayar Hajiyar ta shaida mata gobe zata taho, zuwan da daga shi kuma sai dai ta dawo Ikara a d'aura mata aure ta koma a matsayin matar gida!
Chapter 75 · 0% Book details